2025-06-01@16:38:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3638
«tekun Indiya»:
Haka kuma an yi zaratan ‘‘yan kwallo irin su Johan Cruyff da Eusébio da Gerd Müller mahaifin Muller na yanzu da Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil da sauransu amma tabbas ba a samu zazzafar muhawara ba saboda bbau kafafen sadarwa na zamani wadanda yanzu kusan su ne suka hura wutar zazzafar muhawarar a sassa daban-daban na duniya da ake Kallon kwallon kafa. A yanzu dai Messi ne ya fi lashe Ballon d’Or, inda yake da guda takwas: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021 da 2023, sai Cristiano Ronaldo mai guda biyar: 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017. Sannan Messi ya zo na biyu sau biyar, shi kuma Cristiano Ronaldo ya zo na biyu sau shida, sannan dukkansu sun...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Darakta-Janar Na Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho. A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan sabon ci gaban da aka samu a shawarwarin nukiliyar da kuma dage takunkumin. Sun kuma tattauna rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan Iran. Haka nan kuma yayin da yake ishara da yadda Iran ke ci gaba da ba da hadin kai ga hukumar ta IAEA, da aiwatar da...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gargadi Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Da Wasu Kasashe
Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka yi a baya, yana mai jaddada cewa Iran za ta dauki natakin da ya dace daidai ayyukan da sauran bangarori suka dauka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a na kasa da kasa ya mayar da martani a jiya Lahadi kan rahoton babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi kan wasu batutuwan kariya da suka shafi Jamhuriyar...
Yanzu haka, akalla ana iya karbar sama da Naira miliyan 100 daga wannan PAYE a kowane wata. Wasu hanyoyin samun kudaden shiga, sun hada da haya na kasa (ground rent), harajin haya (tenement rate), da harajin wuraren kasuwanci. Har ma da noma, ana sa wa haraji a Suleja, duk da cewa; gwamnan jihar manomi ne. Ya dace gwamnati ta tabbatar da cewa; ana samar da kayayyakin more rayuwa masu inganci a Suleja, ko da don a samu karin haraji ne. Idan har gwamnatin tarayya ba ta yaba da sadaukarwar da Suleja ta yi ba, to akalla Gwamnatin Jihar Neja; ya kamata ta fi mayar da hankali wajen samar da ci gaba a Suleja, domin karrama gudunmawar da garin ke bayarwa...
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake yi kutse cikin garin Al-Qunaitra na kasar Siriya tare da kafa wurin bincike lamarin da ya fusata al’ummar yankin Sojojin mamayar Isra’ila da suka sake yin Kutse cikin yankunan kasar Siriya sun gudanar da sintiri a yankunan tare da kafa shingen binciken ababan hawa tsakanin Khan Arnabeh da kauyen Jaba da ke lardin Quneitra. Sintirin ya kunshi yahudawan sahayoniyya goma masu magana da harshen Larabci na ka’ida kuma suna sintirin ne a motoci kirar Hummer. A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya, sojojin mamayar Isra’ila biyu kuma sun kutsa kai a tsakanin garuruwan Jaba da Khan Arnabeh, kusa da tsohon wurin binciken ababan hawa na Al-Saqri. Sun samu rakiyar motocin sojoji dauke masu rakiya...
Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin. Sannan ma’aikatar lafiya ta Sudan da kungiyoyi da dama suna ci gaba da kokarin shawo kan cutar don kada ta zama annoba wadda za ta yadu zuwa jihohi da dama. Wakilin gidan...
A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya. Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu. Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Sam-sam hakan ba shi da wani alfanu domin yana kawo matsaloli da dama wanda babu lokacin lissafosu. Kalubalen da ka iya afkuwa kuwa shi ne; wadansu ‘yan matan ba sa tan-tance wadanda za su sa da wadanda ba za su saka ba, har da masu saka ‘yan’uwan miji, kawaye da ‘yan’uwa na cikin dangi duk a bi a cakuda su guri guda, kuma ba sa yin komai a lissafance ba sa tunanin a cikin yawan al’umman da ke ciki har da shaidani ciki ba, dan akwai wacce abu ya faru da ita daga bude group na biki (sabe the date) abu ya dawo babbar rigima har ta kai ga ‘police station’ kuma ba komai ya kawo hakan ba sai rarrabuwar...
Iran ta tabbatar da cewa ta samu shawarar da Amurka ta gabatar mata daga hannun kasar Oman game da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya da ake tattaunawa a kai. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ta samu wani bangare na shawarwarin daga Amurka daga Oman mai shiga tsakani kan batun a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X. Ya karbi sakon ne daga hannun takwaransa na Oman Badr Albusaidi, wanda ya gudanar da wata gajeriyar ziyara a Tehran. Saidai ministan harkokin wajen Iran din bai bayyana abinda shawarwarin ke kunshe da ba, amma ya jaddada cewa za a duba su a kuma mayar da amsa wacce ta yi daidai da muradin...
Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah. Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa. Wani jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta CNN a ranar Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ba za ta hada kai da hukumar Falasdinu ta PA ba da ke neman karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya. Jami’in ya bayyana ziyarar a matsayin tsokana, yana mai...
Wani rahoto da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya nuna cewa Gaza na fuskantar bala’i mafi muni tun soma yaki a Zirin a watan Oktoban 2023. Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya zargi gwamnatin Isra’ila da yin amfani da batun agajin jin kai da gangan domin ci gaba da aiwatar da munanan laifukan da take aikatawa a Gaza. Francesca Albanese a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: “Dukkan wadannan matakan an boye su ne a karkashin sunan agaji don karkatar da hankulan kasashen duniya.” A wani labarin kuma Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya shaida wa manema labarai a...
Iran ta soki sabon rahoton da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya fitar, tana mai cewa rahoto ne dake kunshe da tuhume-tuhume mara tushe kan shirin nukiliyar kasar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Tehran za ta mayar da martani ga duk wani matakin da bai dace ba daga kasashen Turai da Amurka. Faransa, Jamus da kuma Ingila, tare da goyon bayan Washington, suna son yin amfani da wannan rahoto don aiwatar da wani tsari da zai ba da damar maido da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran. A cikin rahoton nasa, Rafael Grossi ya bayyana...
Ta hanyar da za ki gano kuwa ita ce, ki kai mata ziyara ta wuni daya kuma idan kin je ki kula da yaya yanayin huldodinta da kuma gyaran jikinta suke a cikin gidanta, ta nan ne za ki fahimci matsalar rashin jituwarta da mijin na ta. Domin ita matsalar rashin kulawa da gyaran jiki wani namiji ba zai iya bude baki ya fada ba. Koda ita matar ma ba zai iya fada mata ba sai dai kurum ka ga ana rigima ita tana ta ganin yana yi mata wulakanci shi kuma ga abin da yake gani daban, don haka yana da matukar muhimmancin ga ma’aurata da su himmantu wajen gyara jiki ba su kadai ba, har da wanda ba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwaman ya umarci mai rikon mukamin Shugaban ma’aikata, Hukumar bada tallafin karatu ta Jihar, ma’aikatar ilimi,da kuma kungiyar APWEN reshen Maiduguri cewar wadanda suka cika sharuddan da ake bukata ya dace a basu tallafin na karatu. Lokacin taron ya taya Shugabnnin kungiyar amsu barin gado da kuma wadanda za su gaje su kan jajircewar da suka nuna wajen daukakalamarin da ya shafi kwararru ta bangaren Injiniya. Da take gabatar da kasida mai taken, “Muhimmancin daukar nauyin da jawo hankalin’ ya’ya mata su yi karatun Injiniya da daukar abin a matsayin aiki a Nijeriya, ”Uwargidan gwamnan Borno,Dakta Habiba Babagana Zulum, ta lura da cewar daukar nauti wani lamari ne na yadda ake bunkasa ci gaban kwararru,inda ta yi nunu da cewa...
Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup ta bana da ta kunshi kasashen Ghana, Trinidad And Tobago, Jamaica da Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Abin da ake cewa Layya shi ne duk wata halastacciyar dabba da aka yanka domin neman kusanci ga Allah. Layya tana da asali a cikin Kur’ani da Hadisin Annabi (SAW). A cikin Kur’ani Allah (TWT) Yana cewa: “Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka.” (Kausar: 2). A Hadisi kuwa Anas bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi layya da raguna biyu bakake, masu kahonni. Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefen wuyansu” (Muslim ya ruwaito). Za a yi Huɗubar Ranar Arfa a harsunan Najeriya 3 Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno Akwai Hadisai masu yawa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah Al-khomaini (q) wanda ya kafa JMI. Ministan da sauran manya-manyan ma’aikata a ma’aikatar harkokin wajen kasar sun je hubbaren Imam ne don jadda bai’a ko alkawali da shi kan tafiya a kan tafarkin da ya barsu a kai. A cikin wani wuri a Jawabinsa Ministan ya kara da cewa a cikin kundin tsarin mulkin JMI ya zo kan cewa Iran ba zata danne wata kasa...
“Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da suka kamata tun lokacin da aka kaddamar da dokar ta bacin.An horar da Malaman makarantun gwamnati,ana kuma ci gaba dayin hakan. “Saurin biyan kudaden bashi da Hukumomin WAEC da NECO ya kawo kwanciyar hankali ga daliban da suka kammala makaranta da rubiuta jarabawa, sai dai basu samu ci gaba da karatu ba saboda Hukumomin jarabawar sun rike masu sakamakon jarabawar da suka yi. Daga...
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana alhininta bisa rasuwar wasu ‘yan wasa daga jihar Kano a wani hadarin mota. A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar, ya ce hadarin ya faru ne yayin da tawagar jihar ke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala a jihar Ogun. Kungiyar ta NGF ta mika ta’aziyyar ta ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano,da ma kasa baki daya. Kungiyar ta roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ji kan ‘yan wasan, Ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi. Ali Muhammad Rabi’u
A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan. Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da...
Masu zanga zanga kimani makunni uku da suka gabata a kasar Libya sun bukaci firai ministan kasar Abdulhamid Dubba ya sauka saboda shi ne ya haddasa rikicin da ya faru a cikin yan makonnin da suka gabata a kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa masu zanga zanga kimani 200 sun taro a tsakiyar birnin Tripoli sun rera takin Dole Dubah ya sauka, wanda kuma suna rera wasu taken. Tun shekara ta 2011 ne a lokacinda kungiyar tsaro ta nato ta goyi bayan yantawaye suka kashe shugaba Kaddafi ne kasar Libya ta rabu gida biyu, bangaren da MDD ta amince da ita a birnin Tripoli da kuma wacce Khalifa Haftar yake jagoranta daga gabacin kasar.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Naija na tarayyar Najeriya NSEMA ya basa sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ranar Alhamis data gabata a karamar hukumar Mokwa ya kai 151 bayan an sake gano karin gawakin mutane 36. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Abdullahi Arah yana cewa banda wadanda suka rasa rayukansu mutane 11 ne suka ji rauni. Sannan mutane 3018 suka kauracewa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa bayan ruwan sama na sa’oii masu yawa. Arah yace gidaje 503 ne suka rushe a jihar sannan wasu 265 suka lalace. Banda haka akwai gadoji biyu da hanyoyi biyu wadanda ruwan ya sharesu.
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, da yin “amfani da talauci a matsayin makami” domin juya ’yan Najeriya. Da yake jawabi a Abuja ranar Asabar a wajen lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, mai taken “Amfani da Talauci a Najeriya,” Atiku ya yi zargin cewa gwamnati tana amfani da matsalar tattalin arziki don sarrafa ’yan kasa. Ya ce, “Abin da muke fuskanta a halin yanzu a Najeriya shi ne gwamnati tana amfani da talauci a matsayin makami.” Atiku ya yi nuni da bambancin yanayin rayuwa a yanzu da lokacin ƙuruciyarsa, inda ya ce a lokacin Kano...
A ganin kasar Sin, kafuwar hukumar za ta ba da damar kara shigar da kasashe masu tasowa cikin aikin kula da al’amuran duniya, da tabbatar da daidaita rikici ta wata hanya mai adalci, da bai wa kasashe masu tasowa karin ikon fadin albarkacin bakinsu. A shekarun baya, kasar Sin ta taimaka wajen tabbatar da samun sulhu tsakanin kasar Saudiyya da ta Iran, da ganin yadda bangarorin siyasa daban daban na Falasdinawa suka kulla yarjejeniyar sulhu a birnin Beijing na Sin. Kana a wannan karo, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kokarin kulla yarjejeniyar kafa hukumar shiga tsakani. Duk wadannan abubuwa sun nuna yadda Sinawa suke darajanta sulhu da zaman lumana a duniya. (Bello Wang) Daga kanmu,...
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin ciki da alhini kan mummunan haɗarin mota da ya yi ajalin wasu ‘yan wasa daga jihar Kano, yayin da suke dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a jihar Ogun. Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fitar da wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a yau Asabar, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Kano. Mutane 21 Sun Mutu A Tawagar Ƴan Wasannin Kano A Hatsarin Mota Ahmed Musa Ya Angwance Da Matarsa Ta 4 A Kano “Muna miƙa ta’aziyyar ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano da kuma ɗaukacin ma’abota wasanni a faɗin kasar nan,” in ji sanarwar. Gwamna AbdulRazaq ya...
Karatu, rubutu,da kuma dabarun lissafi wasu dabaru ne da ake samu ta hanyar iulimi. Wadannan dabarun suna bada dama ta dogaro da kai da kuma samarwa kai aiki. Karatu yana bude hanyar sanin ilimi da labarin duniya. Saboda mutane suna fara kasuwanci ne idan har za su iya kasafi,da kuma gane abubuwan da aka kashe a kalla. Ilimin iya karatu da rubutu,da kuma iya samar da hanayar da za aji ra’ayoyi,hakan na kara iya dogaro da kai da kuma samun a rika jin babu wata kasala ko faduwar gaba. Ilimi yana taimakawa mutane wajen yadda wasu daga zama Sanuwar ware. Yin makaranta yana koyawa mutane duk wani matakin da za su dauka ya kasance mai ma’ana, wannan kuwa yana sa...
Aƙalla mutum 20 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da tawagar Jihar Kano da ke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa (NSF) da aka kammala a Jihar Ogun. Lamarin na ban tausayi ya faru ne a ranar Asabar a garin Dakatsalle, kimanin kilomita 50 daga Kano, yayin da tawagar ke gab da isa gida. Rahotannin farko daga masu bada agajin gaggawa da shaidun gani da ido sun nuna cewa waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun haɗa da ’yan wasa da ɗan jarida, ma’aikatan lafiya da jami’an gudanar da harkokin wasanni. Shugaban ƙungiyar marubutan wasanni ta Najeriya (SWAN) reshen Kano, Zahraddeen Saleh, ya tabbatar da wannan mummunan lamari. Ya kuma ƙara...
Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata, sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa motar da ke ɗauke da ‘yan wasan, wadda ke ɗauke da mutane 30, ta faɗa gadar ta Dakatsalle da ke jihar ta Kano. “Yayin da nake magana da ku yanzu, mun kirga gawarwaki 19,” ya fada cikin tashin hankali. Ado Salisu, tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida da ke kula da lamuran Wasanni ta Najeriya (SWAN), ya ce an kai...
Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ahmed Musa, ya auri matarsa ta 4, Asmau Moriki, a wani biki na sirri da aka gudanar a jihar Kano, Musa da amaryarshi Asmau sun zama mata da miji watanni kadan bayan haduwarsu, Musa ya bar sansanin tawagar Super Eagles dake birnin Landan domin ya halarci bikin wanda aka gudanar a birnin Kano. Dan wasan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya shiga wasan da Nijeriya ta doke Ghana da ci 2-1 a minti 60 na wasan, Musa na daya daga cikin yan wasan da sukafi taka leda a tarihin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya inda kuma ya zamo wanda yafi jefawa Nijeriya kwallaye a gasar kofin Duniya a...
A kwanan baya, tsohuwar firaministar kasar New Zealand, Madam Jennifer Shipley, ta yi hira da wakilin CMG, inda ta ce, ya dace a koyi ingantattun dabarun kasar Sin a fannin raya kasa. Ta ce yadda kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya, da bai wa sauran kasashe dabaru da fasahohin da ta samu na da ma’ana matuka. Saboda kasar tana kan gaba a duniya, a fannin raya al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. A cewar Madam Shipley, ya kamata a dora muhimmanci kan basirar kasar Sin, saboda an samu isassun shaidun dake nuna cewa, idan an yi amfani da dabarun Sin yadda ya kamata, to, za a samu nasarar raya aikin ilimi, da samar...
A wancan lokacin, sojojin Nijeriya sun musanta batun Shehun Borno, amma wasu na ganin cewa akwai kashan gaskiya dangane da wannan al’amari, sakamakon irin yadda ‘yan ta’addan ke cin karensu babu babbaka a wadannan yankuna. Shi ma a nasa bangaren, mai sharhi kan kungiyoyin ta’addanci a Cibiyar Tony Blair, Barista Bulama Bukarti, ya ce, “A binciken da muke da shi, mun gano yadda Boko Haram suke amfani da jirage marasa matuka wajen kai wasu hare-hare a sansanonin sojojin Nijeriya.” Idan an yi la’akari da wadannan bayanan sun nuna cewa kungiyar Boko Haram tana ci gaba da fadada ayyukanta a fannoni daban-daban ba tare da an taka mata birki ba. Bisa ga wannan ne, Sanata Mohammad Ali Ndume, mai wakiltar kudancin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan shi ne babban abin alfahari da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ke jagoranta. A yayin tattaunawar manyan jami’an biyu a Berlin tare da ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul, Tuggar ya nuna bajinta. “Ba manufar Nijeriya bace ta fitar da mutane zuwa wasu kasashen waje ba, sai don nuna gwanayenta,” in ji shi, tare da sake sanya haske a manufinta. A cikin shekarun baya-bayan nan, yawan al’ummar Nijeriya sun kasance ana sanya su a matsayin wadanda ke cikin rikici, miliyoyin matasa marasa aikin yi, masu karatun digiri, da kwararru an nuna musu halin ko-in-kula. Amma Tuggar, gogaggen jami’in diflomasiyya kuma mai tunani na Afirka, yana ganin abin da mutane da yawa ke watsi da shi dama ce....
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya soki tsarin shugabanci na Najeriya na yanzu, inda ya bayyana cewa ‘’yan bindigar birni’ sun karɓe ragamar mulkin ƙasar. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a Abuja, yayin taron lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, mai taken ‘Amfani da Talauci a Matsayin Makami a Najeriya.’ El-Rufai ya bayyana cewa a yanzu ne Najeriya take fuskantar matsalolinta mafiya muni tun bayan samar da ita da matsayin ƙasa ɗaya a shekarar 1914. “Shi ya sa muke tare muna aiki tare da shirya wani haɗin gwiwa don dawo da Najeriya kan turbar da ta dace saboda ta riga ta kauce hanya,” in ji shi. Mutanen da...
Wadanda ake zaton mawallafin wasikar sun yi jayayya cewa ya kamata a janye tuhumar da ake yi wa Giwa saboda “adalci, daidaito, da aiki mai kyau.” Giwa, tare da mai kula da kadarorin Cecil Osakwe da sauran su, za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda tara da suka hada da fitar da mutane ba bisa ka’ida ba, cin zarafi, barazana ga rayuwa, da barnar dukiya da suka kai Naira miliyan 300. Laifukan da ake tuhumar Giwa da Bukola sun hada da hada baki wajen aikata jabun takardu da aikata laifuka (wanda za a hukunta shi a karkashin sashe na 97 na dokar Penal Code Act, 2004), da rashin gaskiya da aiwatar da takardar damfara (Sashe na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503. Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a...
Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503. Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa. A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada cewa al’ummar ƙasar nan suna tare da su a wannan lokaci na jimami, kuma ba za a yi ƙasa a gwiwa wajen tallafa masu ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Limamin Sallar Juma’ar Tehran Ya Jaddada Cewa: Babu Wanda Zai Dakatar Da Iran Tace Sinadarin Uranium
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Iran ba ta neman mallakar makamin nukiliya, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana ba. Ya kara da cewa: Iran tana inganta sinadarin Uranium kuma za ta ci gaba da yin hakan domin bunkasa harkokin ci gaban kasarta musamman harkar lafiya, wutan lantarki, likitanci, noma da sauransu. Limamin Juma’ar Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Hakika dogaro da...
Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa a yayin bikin nasarar da aka yi na aikin tiyatar dashen na’urar magance matsalar Rashin ji da rauninsa sau 1,500 a lardin Khuzestan dake kudu maso yammacin ƙasar. Wadannan tiyata sun bayyana kwarewar aikin likita da basirar likitoci a lardin, wajen maido da ji da magana ga wadanda suka rasa jin tun da fari. Bikin dai ya samu halartar likitoci da ma’aikatan jinya da yara...
Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen. Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa. Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga...
Haka zalika, ya kara da cewa; gwamnatinsa ta bayar da kimanin Naira biliyan biyu, domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani mai amfani da hasken rana a garin Baga. Gwamna Zulum ya ci gaba da cewa, kwanan nan ya tura wata tawagar bincike, don yin bincike tare da gano gaskiya zuwa Gamborun Ngala, sannan kuma tawagar ta tabbatar mana da samun albarkatun ruwan karkashin kasa, wadanda za mu iya amfani da su wajen noman rani ta hanyar ban-ruwa. Kazalika, ya sanar da cewa, an kuma kebe karin wasu Naira biliyan 1.5, domin gudanar da irin wadannan ayyuka a garuruwan Gamborun Ngala da Marte, wadanda a halin yanzu an kusa kammala su baki-daya. Bugu da...
Maƙabartar Kuka Bulukiya maƙabarta ce mai daɗaɗɗen tarihi a cikin ƙwaryar birnin Kano, wadda bayanai suka nuna an shafe sama da shekara 500 ana binne mamata a cikinta. Wannan daɗaɗɗiyar maƙabarta tana da matuƙar muhimmanci musamman la’akari da yawan unguwannin da suka kewaye ta da yawan mutanen da aka binne a cikinta da kuma fitattun mutanen da suke kwance a cikinta. Maƙabartar Kuka Bulkiya ta yi iyaka da unguwannin Dala da Madabo da Yalwa da Kwanar Taya da kuma Gwammaja, sa’annan akan kawo gawarwaki hatta daga unguwanni irin su Gwauron Dutse da Ƙulƙul da Dogon Nama da Madigawa da Sanka da Makafin Dala da dai sauran su. Asali dai an sanya mata sunan Bulukiya ne saboda wata bishiyar kuka mai...
A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar. Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin. A cewarsa, za su tabbatar da aiki da ka’idojin duniya wajen tsafta, yanka da kuma sarrafa nama. Jami’in ya kuma yaba wa gwamnan na Jihar Gombe, Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa na kokarin kyautata samar da kayan more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Shi kuwa a nasa jawabin, shugaban gudanarwa na kamfanin Arch. Yunusa Yakubu, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci, sannan...
Sojoji sun yi nasarar cafke wani mutum da ake zargi dan ta’adda ne tare da gano ma’adanar makamai a yayin wani samame da suka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato. Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama ɗin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da alhakin kisan wani makiyayi da satar shanu 1,250 a ƙauyen Tomborong, Ƙaramar Hukumar Riyom, a ranar 27 ga watan nan na Mayu. A safiyar ranar Juma’a, sojoji suka kama wanda ake zargin, bayan samun rahoto game da inda ake zargin ɗan bangar yake ɓoye a ƙauyen Hura. Yayin wani bincike da aka yi a maboyar wanda ake zargin, jami’an tsaro sun gano bindigar AK-47 guda daya, tare...
Akasari kafin a girbe ta, tana kaiwa kwanaki 60 zuwa 100 bayan an shuka ta. Kazalika, cikin sauki ake mallakar gonar da ake shuka Masara a Nijeriya, ana kuma shuka Irinta sannan a sayar da ita ga makwabta. Dankali: Dankali na dauke da sinadarin ‘calories’ dan kadan, sannan mutane da dama na kasar nan na sarrafa shi a matayin abinci tare da yin amfani da shi. Yana daukar watanni biyu zuwa uku bayan an shuka shi. Bugu da kari, ana iya shuka shi a kowacce irin kasar noma. Tumatir: Ana matukar amfani da tumatir a Nijeriya, ko danyensa ko kuma busasshe. Yana dauke da sanadarin ‘bitamin C’, yana kuma taimakawa wajen rage kamuwa da cututtuka kamar wadanda ke yi wa...

Macron : Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba
Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba, inda kuma ya bukaci kasashen duniya da kada su jajirce wajen tunkarar matsalar karancin abinci a Gaza. A wani taron manema labarai a Singapore a ranar Juma’a, Macron ya ce dole ne Turawa su “tsaurara matsayinsu na hadin gwiwa” kan Isra’ila, “idan babu wani mataki da ya dace da yanayin jin kai, a cikin sa’o’i da kwanaki masu zuwa” a zirin Gaza. Macron ya ce, “Katange ayyukan jin kai yana haifar da yanayi mara kyau,” yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Firaministan Singapore Lawrence Wong. Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da gwamnatin...

Nukiliya : Iran ta kirayi mai kula da harkokin Ostiriya da ke birnin Tehran kan wasu kalamai na tsokana
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi babbar mai kula da harkokin kasar Ostiriya da ke birnin Tehran domin nuna rashin amincewa da zarge-zargen data danganta da na ‘’tsokana” da hukumar leken asirin cikin gidan kasar ta Turai ta yi dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Shugaban ofishin sashen yammacin Turai na ma’aikatar harkokin wajen Iran Alireza Molaqadimi ya gayyaci Michaela Pacher a ranar Juma’a, inda ya nuna bacin ran kasar iran game da zarge-zargen. A cikin rahotonta na shekara-shekara kan barazanar da duniya ke fuskanta, hukumar leken asiri ta kasar Ostiriya (DSN) ta yi ikirari a ranar Litinin cewa Iran na ci gaba da aiwatar da shirin kera makaman nukiliya tare da fadada karfinta na makamai masu...
Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na farko a kan tsoffin kawayenta tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce ta sanya “bama-bamai” kan motar dakarun da HTC ke jagoranta a lardin Suwayda da ke kudancin kasar. Wannan dai shi ne harin farko da Daesh ta yi ikirarin doka kan sabuwar gwamnatin ta Siriya. Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) ta bayar da rahoton cewa, a yayin harin, wasu mambobi uku na runduna ta 70 na rundunar HTC sun jikkata, a yayin da suke sintiri yayin...
Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki. “Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin shigar da shi ba a lokacin da jama’a a gefen iyakar ke fama da yunwa, a yayin da muke jin ministocin Isra’ila suna cewa sun ayin hakan ne don matsa lamba kan al’ummar Gaza,” in ji Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher a wata hira a ranar Jumma’a. Irin wannan na a matsayin laifin yaki ne,” in ji shi. Baya ga hakan...
Burkina faso ta musanta labaren da ake yayatawa na aikata kisan kiyashi a arewacin kasar. Ministan Tsaron kasra na mayar da martani ne ga labarin da aka buga a wannan Alhamis, na RFI, na kisan kiyashi da kungiyar sa kai ta kasar (VDP) ta yi a kauyukan Dori da Gorgadji. Ministan Tsaron Burkina Faso ya ce “mummunan zarge-zarge ne kawai ake wa kasar da nufin “dagula zaman lafiyar kasar” da kuma “bata sunan” sojojin da VDP. Ya ci gaba da yin kira ga al’ummar Burkina Faso da su yi taka-tsan-tsan game da bayanan “farfaganda” da ke da nufin haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummomin kasar. A cikin sanarwar da ya fitar, Céletin Simporé, ya sake nanata kudurin gwamnati na...
Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani kwamandan ’yan ta’adda, Amir Abu Fatima da aka sanya ladar Naira miliyan 100 ga duk wanda ya kama shi ko ya tona asirin inda yake, aka kama shi. Sojoji sun halaka Abu Fatima ne a wani samame na musamman da suka kai a yankin Arewacin Jihar Borno. Majiyar leken asiri ta sanar da Zagazola Makama cewa an kai harin ne da sanyin safiyar Juma’a, a yankin Kukawa da ke yankin Tafkin Chadi. Majiyoyin soji sun tabbatarwa da Zagazola Makama cewa, wannan aikin wani shiri ne da aka tsara a tsanake na halaka ‘yan ta’adda da nufin kashe Abu Fatima, wani babban jigo na ‘yan tada kayar baya. Dakaru na musamman sun kutsa cikin...
Alkaluma daga hukumar lura da kudin musaya ta kasar Sin, sun nuna yadda kasar ta samu karuwar darajar cinikayyar waje ta fuskar hajoji da hidimomi, wadda a watan Afirilun da ya gabata ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 4.37, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 606.8, karuwar da ta kai ta kaso 6 bisa dari a shekara. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan, sun nuna karuwar darajar hajoji da hidimomi da Sin ta fitar ketare zuwa dala biliyan 326.5, yayin da darajar wadanda ta shigo da su ta kai dala biliyan 280.3, inda aka samu rarar dalar Amurka biliyan 46.2. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...

Adadin Zirga-Zirgar Fasinjoji Ta Jiragen Kasa A Sin Na Iya Kaiwa Sama Da Miliyan 80 Yayin Hutun Bikin Duanwu
Hukumar lura da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin, ta yi hasashen samun adadin zirga-zirgar fasinjoji ta jiragen kasa sama miliyan 80.5, yayin kwanaki biyar na hutun bikin Duanwu ko bikin tseren kwale kwale na bana. An fara samun dandazon matafiya ta jiragen kasa a kasar Sin tun daga yau Juma’a, kwana guda gabanin kwanakin hutun uku, yayin da ake sa ran kaiwa kololuwar yawan matafiyan a gobe Asabar, inda ake hasashen adadin zirga-zirgar zai kai kusan miliyan 18.3. Alkaluma daga kamfanin 12306, mai samar da hidimar yankar tikitin jiragen kasa na kasar Sin, sun nuna wuraren da matafiya suka fi yankar tikitin zuwa, wadanda suka hada da biranen Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Chengdu, da Hangzhou. Sauran su...
Wani mutum mai suna Adamu Muhammed Tenimu ya suma bayan da samu labarin cewa matarsa ta haifi jarirai ’yan uku a asibitin koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lokoja babban birnin Jihar Kogi ranar Juma’a. Shaidu sun ce, mutumin da ya ji cewa matarsa ta haifi ‘ya’ya mata uku, sai ya faɗi ya suma a harabar asibitin nan take. Zazzaɓin Lassa da sanƙarau ya kashe mutum 366 a jihohi 24 – NCDC Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni Jami’an asibitin da masu jajantawa sun yi wa mutumin agaji inda cikin gaggawa aka samu ya farfaɗo. Jim kaɗan da farfaɗowarsa, Muhammed, wanda aka ce ya kasance mai neman aikin yi na tsawon shekaru, ya ce...
Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk jarirai 1000, yayin da na yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu zuwa yara 5.6 cikin duk yara 1,000, adadin da ya yi kasa sosai cikin jerin kasashen duniya, dake rukunin masu al’ummun dake sama-sama a matsakaicin samun kudin shiga. Shen Haiping ta kara da cewa, idan aka nazarci wadannan alkaluma, za a ga cewa cikin sama da shekaru goma da suka gabata,...
Rahotanni daga kasar ta DRC sun ambaci cewa an ga tsohon shugaban kasar Joseph Kabila a jiya Alhamis a garin Goma wanda yake a karkashin ikon ‘yan tawayen kungiyar M23. Majiyar malaman addinin kirista a yankin ce ta sanar da cewa, ta gayyace shi ne domin ya shiga Tsakani a kawo karshen yakin da ake yi a yankin. Bishop Joel Amurani ne ya sanar da cewa, su ne su ka gayyaci tsohon shugaban kasar wanda ya kasance akan karagar Mulki daga 2001 zuwa 2019. A yayin ziyarar tashi a garin na Goma, Kabila ya gana da bangarori mabanbanta da su ka hada da malaman addinin yankin. A can birnin Kinshasha, gwamnatin Felix Tshisekedi tana zargin Kabila da cewa yana goyon...
Mamakon ruwan sama da ya sauka a jihar Rivers ta Najeriya ya yi gyara, tare da daukar rayukan mutane 25,kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasar ta sanar. Ruwan da ya sauka a garin Okrika ya haddasa zaizayar kasa,wacce ta binne gidaje da dama, da kuma yin awon gaba da mutane. Masu ayyukan ceto sun ce har yanzu ana ci gaba da gano gawawwakin mutane a karkashin baraguzai. Haka nan kuma mutane da dama sun rasa matsugunansu. Duk da cewa ana ci gaba da ayyukan ceto said ai har yanzu da akwai yankuna da ba za a iya shiga cikinsu ba saboda sun yi lungu.
MDD ta yi gargadi akan yunuwar da mutanen Gaza suke fama da ita, sannan ta kara da cewa: Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji, kuma rabin cibiyoyin kiwon lafiya na yankin sun daina aiki saboda rashin isar da kayan agaji daga waje.” Ofishin MDD wanda yake kula da ayyukan agaji ne ya yi wannan gargadin, sannan ya kara da cewa: Yankin Gaza shi ne wurin da aka fi fama da yunwa a duniya baki daya.” Mai Magana da yawun ofishin na MDD ya ce: da akwai manyan motoci 600 da suke dauke da kayan agaji da su ka isa kan iyakar Gaza, amma asalinsu 900 ne da bisa wasu dalilai an hana su isa bakin iyaka.” Haka nan kuma...
Da yake jawabi ga ɗimbin mutanen da suka halarci wannan tattaki, Gwamna Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kawar da duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar, tare da mai da hankali sosai kan ‘yan bindiga. Ya ce, “A yau mun fito dubunnan mu domin mu yi tattakin samun zaman lafiya, domin mu sanar da duniya cewa Zamfara ta samu ci gaba sosai ta fuskar tsaro. “Gwamnatina ta ba da himma da kayan aiki masu yawa don ƙarfafa sojoji, tattara bayanan sirri, da haɗa kai don dawo da zaman lafiya a jihar. “Mun sami gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga, yawancin wuraren da ake fama da rikici a baya, a halin yanzu sun kasance cikin kwanciyar...
Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutane 366 a sakamakon zazzaɓin Lassa da cutar sanƙarau a ƙasar, lamarin da aka bayyana da ƙalubalen kiwon lafiyar ga al’umma sanadin waɗannan cututtuka. Daga ranar 1 ga Janairu zuwa 18 ga Mayu, 2025, NCDC ta tabbatar da ɓullar cutar zazzaɓin Lassa guda 733 daga mutane 5,118 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗin jihohi 18 da ƙananan hukumomi 95. Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa A cikin wannan lokacin, ƙasar ta sami rahoton mutuwar mutane 141 masu nasaba da zazzaɓin Lassa, wanda ke nuna adadin waɗanda suka mutu ya...
Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar, sun nuna daga watan Janairu zuwa watan Afirilun bana, masana’antun samar da manhajoji da ayyukan ba da hidimomin fasahohin sadarwa na Sin sun bunkasa lami lafiya. Alkaluman sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Afrilun bana, jimillar kudin shiga da masana’antar ta samu, ta haura yuan tiriliyan 4.25, adadin da ya karu da kaso 10.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara. Kazalika, jimillar ribar masana’antar manhajojin ta kai yuan biliyan 507.5, yayin da saurin karuwar jimillar ribar masana’antun ta yawaita zuwa kashi 14.2 bisa dari. Har ila yau, jimillar kudin shigar masana’antun fitar da kayayyakin manhajojin ta kai dalar Amurka biliyan 17.26, adadin...
Kwararran likita tiyata, Farfesa Sani Ali Aji ya bayyana cewa kwarrun likitocin tiyata guda 6 ne kacal suka rage a Jihar Kano, wanda ake has ashen tana da al’umma fiye da miliyan 20. Farfesa Sani ya kara da cewa wannan karanci na likitoci ya faru ne sakamakon karancin albashi, karanci kayan aiki na zamani da sauransu, wanda hakan ya sa kwararrun likitoci suka koma kasashen Turai da na Larabawa domin samun alfashi mai tsoka. ‘Yansanda Sun Kama Mutane 41 Da Ake Zargi Da Kisan DPO A Kano Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kano Ya bayyana cewa maganin wadannan matsaloli shi ne, samar da kayan aiki wadatace da albashi ga ma’aikata mai tsoka da sauransu. Farfesa Sani...
A bikin cikarsa shekaru 6 cur yana mulkin Jihar Yobe, Gwamnan jihar Mai Mala Buni da aka gudanar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu akan harkokin ilimi da noma, inda ya ce akasarin waɗanda suka amfana a waɗannan fannoni guda biyu matasa ne. Da yake jawabi a yayin wannan taro na bikin cikarsa shekaru 6 akan mulki da aka gudanar a babban ɗakin taro na Banquet da ke gidan gwamnatin Jihar a garin Damaturu tare da ma su ruwa da tsaki na Jihar. An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMA Gwamnan ya bayyana ƙudirinsa na ci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A bikin cikarsa shekaru 6 cur yana mulkin Jihar Yobe, Gwamnan jihar Mai Mala Buni da aka gudanar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu akan harkokin ilimi da noma, inda ya ce akasarin waɗanda suka amfana a waɗannan fannoni guda biyu matasa ne. Da yake jawabi a yayin wannan taro na bikin cikarsa shekaru 6 akan mulki da aka gudanar a babban ɗakin taro na Banquet da ke gidan gwamnatin Jihar a garin Damaturu tare da ma su ruwa da tsaki na Jihar. An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMA Gwamnan ya bayyana ƙudirinsa na ci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sako daga Bilal Salisu Gabasawa: Ina so a mikan sakon gaiswa ta zuwa ga masoyiya Habiba, abar kaunata in sha Allah har karshen rayuwa, da fatan ta yi juma’a lafiya. Sako daga Suwaiba Lawan Jihar Kano: Ina so a gaishe mun da mahaifana da kuma.mijina uban ‘ya’yana daya tamkar ya dubu rabin raina Nasir Muhd, Allah ya sa sakon ya isa gare shi, ina yi muku fatan alkhairi. Sako daga Abba Ahmad Kaduna: Ina gaishe da mahaifina da kuma mahaifiya ta, ina gaishe da kannena; Momi, ikram, sadiya, hafsa, sadik, sannan ina gaishe da duk kanin al’ummar musulmi bakidaya, Allah ya sa mu yi juma’a lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da haƙƙin da doka ta tanada ba ta fannin inganta sinadarin uranium, domin inganta harkar kiwon lafiya, aikin gona da masana’antu, yana mai jaddada cewa: makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin koyarwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ziyarar da ya kai masarautar Oman, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a wata hira da gidan talabijin na kasar, ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da kuma muradun yankin da na kasa da kasa na Iran da Oman, da kuma muhimman batutuwan...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Hanyar Warware Takaddamar Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan hasashe game da kusancin cimma yarjejeniyar nukiliyar da ke gudanarwa tsakanin Amurka da Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hanyar diflomasiyya tana bukatar a dage dukkan takunkumai da aka kakabawa Iran da kuma mutunta hakkin mallakar makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: Hanyar cimma yarjejeniya ta ta’allaka ne ta kan teburin tattaunawa, ba ta hanyar kafafen yada labarai ba. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya fada a jiya Alhamis cewa: Kafafen yada labarai na yada jita-jita game da yarjejeniyar da ake shirin kullawa tsakanin Iran da Amurka. Araqchi ya ci gaba da yin tsokaci a shafinsa na Twitter a dandalin Twitter, inda ya ce: “Muna shakkar...
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami lamarin da ya tarwatsa cinkoson jama’a a filin jirgin Sojojin Yemen sun sanar da kai farmakin soji kan filin tashi da saukan jiragen saman Ben Gurion tare da yin barazanar ci gaba da toshe hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa na haramtacciyar kasar Isra’ila muddin bata kawo karshen killace Zirin Gaza da ta yi ba. Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: Wannan farmakin ya samu nasarar cimma burin da aka sanya a gaba, wanda ya tilastawa miliyoyin ‘yan sahayoniyya ‘yan mamaya tserewa zuwa maboyar karkashin rami tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin. Sari’e...
A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan ya biyo bayan sauya ra’ayi da Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bisa la’akari da goyon bayan siyasa da na soji da Amurka ke ba shi, a cikin shiru da kasashen duniya suka yi da kuma gazawar da ba a taba gani ba daga kungiyoyin kasa da kasa. Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa: Sojojin...
PUNCH Metro ta tuna cewa a kwanakin baya jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a cikin hadaka a Kananan Hukumomin Ilorin da Ifelodun na jihar. Oyewale ya ce an tare wadanda ake zargin ne a madatsar ruwa ta Asa da yankin Jami’ar Al-Hikmah da yankin Gaa-Odota da ke Ilorin da kuma yankin Ganmo da Amoyo na jihar. “Kamen da aka yi a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya alakanta wadanda ake zargin da ayyukan damfara ta Intanet a jihar. Sanarwar ta kara da cewa, “Kayan da aka kwato daga hannunsu da aka kama sun hada da manyan motocin alfarma...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin tsaro na cikin matsalolin da suke ci gaba da ci wa ’yan Najeriya da dama tuwo a kwarya, har a wannan lokaci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yake cika shekara biyu a kan mulki. Wasu rahotanni da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar dai sun koka da yadda suke ganin matsalar ta kara kamari a wadannan shekarun. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan matsala ta rashin tsaro. Domin sauke shirin, latsa...
Wani masanin tattalin arziki, Ademola Adigun, ya ce, duk da janye tallafin mai, sashin mai a Nijeriya ba ya tafiya kan ka’ida. Ya yi bayanin cewa kawai an rage biyan tallafin ne amma ba wai an daina biya gaba daya ba, kuma babu gasa tsakanin ‘yan kasuwa wanda shi ma na haifar da nakasu. Adigun ya soki tsarin sayar da danyen mai a kan kudin naira domin zabar da masu saye, ta yadda za a samar da lamari kamar na ‘ya’yan mowa da bora, da ke iya korar ‘yan kasuwa masu zaman kansu, lamarin da ya tilasta wa kusan gidajen mai 5,000 rufewa. Adigun, duk da ya nuna farin ciki kan yadda masu zuba hannun jari suke nuna sha’awar zuba...
A wannan zango na shekaru biyun Tinubu, ma’aikatar yada labarai ta kasa; ita ce ginshikin aiwatar da wadannan dabaru da tsare-tsare, musamman ta fuskar sake fasalin hukumomi, aikewa da sakwannin jan kunne da ladabtarwa da kuma jin ra’ayoyin daidaikun mutane, wanda hakan ya bai wa gwamnatin damar sanin matsalolin ‘yan kasa da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance su. Tunda farko, ma’aikatar karkashin jagorancin ministanta, Alhaji Mohammed Idris, ta yi kokarin aiwatar da aikin da ta sanya gaba; ta hanyar nuna babu sani babu sabo ga ma’aikatun gwamnatin da suka keta doka da oda baki-daya, domin kuwa haka ma’aikatar ta kasa zaune, ta kasa tsaye wajen bibiyar ‘yan Nijeriya a wureran ayyuka da sauran wuraren zamansu, don jin...
Sulhu da ‘Yan Bindiga Ya Fi Zubar Da Jinin Ɗan Adam A Kaduna – Uba Sani Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa Kazalika, wasu kwararrun, sun ayyna larurar, a matsayin cieon da ke yiawa mutane, kisan mummuke, musamman duba da cewa, bata nuna wasu alamu, idan an kamu da ita, sai dai kawai, ta ci gaba da zama barzana ga lafiyar ‘yan Adam, kamar kamuwa da masu larorin da suka hada da; mutuwar barin Jiki, lalata Koda da kuma rashin iya gani. An kiyasta cewa, a daukacin fadin duniya, sama da mutane, biliyan 1.3 ke fama da ciwon, wanda kuma rabin adadin wannan alkaluman ne kacal, aka yi masu gwaji aka...
Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ta afka wa yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a ranar Laraba. Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na Laraba, ta kuma lalata dukiyoyi da dama, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu mutanen da suka bace. Garin Mokwa dai ya shahara da zama wani zango na direbobin manyan motoci, wanda hakan ya sa garin ya zama daya daga cikin mafiya hada-hadar mutane a jihar ta Neja. NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ambaliyar ruwa ta kashe sama da...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci, wadanda suka hada da kafa sabuwar cibiyar karatu ta gaba da sakandare, da kuma yana gyara dokar kotunan gargajiya na jihar. Dokar farko ta tanadi kafa Kwalejin Fasahar Noma, da ke Samaru Kataf, bisa dokar kafa Kwalejin Fasahar Noma ta shekarar 2024. Yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin, Barrista Mahmoud Lawal Isma’ila, dan majalisa mai wakiltar Birnin Zariya kuma Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisa, ya bayyana cewa wannan doka tana da nufin bunkasa koyarwa da bada horo, tare da gudanar da bincike a fannin fasahar noma. A cewar Barrista Isma’ila, wannan kwaleji za ta kasance cibiyar kwarewa ta musamman a fannin ilimin noma, inda za a...
“Ina isar da wannan sakon ba wai a matsayina na tsohon shugaban kasa ba, har ma a matsayina na dan jihar Ogun cike da alfahari, na kasance tare da ku a lokacin bikin bude gasar, na kalli wasannin a cikin dakina, kuma hakika wasannin sun nuna cewa ba wai kawai wasanni ba ne, alama ce ta hadin kai, baje kolin hazaka, da kuma kishin kasa. “Daga karshe Obasanjo ya jinjinawa jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya, da kuma kananan kungiyoyin da aka gayyata bisa jajircewarsu, inda ya kara da cewa, kwamitocin da suka shirya gasar, abokan hadin gwiwa, da masu aikin sa kai na hukumar wasanni ta kasa sun cancanci a yaba musu saboda mayar da wannan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce, ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan DPO ɗin Rano, CSP Baba Ali. Rundunar ta bayyana lamarin, wanda ya janyo kace-nace, a matsayin harin kai tsaye kan sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi, waɗanda suke sadaukar rayuwarsu domin kare al’umma. NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 NDLEA ta kama maniyyata aikin hajji ɗauke da hodar iblis A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce rundunar ’yan sanda na aiki tuƙuru domin ganin an gurfanar da duk waɗanda ke da hannu wajen kisan, da kuma masu alaƙa da ƙone-ƙone. Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rundunar ta...
A yau Alhamis ne aka gudanar da dandalin “Kasa da kasa na tattaunawa tsakanin magadan biranen duniya na Shanghai, da dandalin kawancen birane na kasa da kasa na Shanghai na shekarar 2025.” Magadan birane da wakilai daga birane 26 dake cikin kawancen, daga sassan kasashen duniya 22, sun hallara a bakin kogin Huangpu, domin tattaunawa, da musaya game da yanayin makomar birane a nan gaba, da hadin gwiwa, inda suka mayar da hankali kan “Bunkasa birane masu korayen itatuwa, da karancin fitar da iskar carbon, da ci gaba da kirkire-kirkire”. Kazalika a yau din, birnin Shanghai ya sanya hannu kan takardun bunkasa kawance da musaya tare da Tbilisi na Georgia, da Vientiane na Laos da sauransu. A shekarun baya bayan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Da yake jawabi ga manema labarai a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja kafin jirgin maniyyatan ya tashi zuwa Saudiyya, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce aikin Hajjin bana ya samu nasarori da dama da suka nuna ci gaba da inganta aikin hajjin Nijeriya. NDLEA ta kama maniyyata aikin hajji ɗauke da hodar iblis ’Yan bindiga sun kashe makiyaya 2, sun sace shanu 320 a Kaduna Ya ce, an yi jigilar maniyyata 41,568 ta jiragen sama 105. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ya nuna matuƙar godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed...
Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin inganta sinadarin Uranium don bunkasa harkokin ilimi cikin gida ta hanyar fasahar makamashin nukiliya. A yayin ganawar tasu, Ali Akbar Ahmadian, sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, da mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil Celso Amorim, sun jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu masu cin gashin...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa: “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa: “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.
Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da yin kutse cikin Masallacin Al-Aqsa, yayin da kungiyar Hamas ta yi kira da a kalubalance su Daruruwan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a safiyar yau Alhamis suka kutsa cikin harabar Masallacin Al-Aqsa, karkashin kariyar da ‘yan sandan gwamnatin mamayar Isra’ila, yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen gudanar da taron gangami da kuma jaddada rashin amincewa da keta hurumin alkiblar musulmi na farko, kuma daya daga cikin Masallatai masu daraja na al’ummar musulmin duniya. Majiyoyin daga Qudus sun ba da rahoton cewa: Tsagerun yahudawan sahayoniyya mazauna matsugunai da dama sun gudanar da rangadi masu tayar da hankali a harabar Masallacin Al-Aqsa mai albarka, ciki har da gudanar da ibadar Talmud da raye-rayen neman tsokana.
Ambaliyar dai, ta afku ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama yana sauka a daren Laraba. Wani mazaunin garin, Mohammed Usman ya ce tuni aka fara tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwan, amma wasu da dama ba a iya ganin su ba musamman a wuraren da gidaje suka nutse. Daraktan yada labarai da ayyuka na musamman a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Dakta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shugaban Hukumar da ke yaƙi da shan miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA Janar Buba Marwa (mai ritaya), a ranar Laraba, ya bayyana kamen wasu mutum biyu da suka yi yunƙurin safarar hodar Iblis a lokacin da ake jigilar maniyyata aikin hajji a kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Saudiyya don gudanar da Hajjin bana. Da yake jawabi a wajen buɗe taron kwamitin kula da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Abuja, Marwa ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun haɗiyi miyagun ƙwayoyin ne, inda suka nuna cewa su Musulmi ne masu kishin addini da suke shirin gudanar da aikin hajji. ’Yan bindiga sun kashe makiyaya 2, sun sace shanu 320 a Kaduna Ɗalibai sun maƙale lokacin da gini ya rufta suna...
Wasu ’yan bindiga sun kashe wasu makiyaya biyu da suka haɗa da: Mudda Shannon da Suleiman Bello, yayin da suka raunata ɗaya a ƙauyen Kurmin Lemu da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna. Wani ɗan unguwar Kurim Lemu mai suna Shuaibu Ibrahim ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 12:07 na tsakar dare. Ɗalibai sun maƙale lokacin da gini ya rufta suna jarrabawa Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ya ce, ’yan bindigar da suka zo adadi mai yawa tare miyagun makamai sun mamaye sansanin makiyayan inda suka buɗe wuta, inda suka kashe biyu daga cikin makiyayan nan take. Ya ce, ɗaya daga cikin makiyayan...

Sin Da Kasashen Yankin Pasifik Sun Yi Nasarar Gudanar Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Karo Na Uku
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da shugaban kasar Kiribati, kuma ministan harkokin wajen kasar Taneti Maamau, sun jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashen yankin Pasifik karo na uku a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin. A yayin taron, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda shida kan kafa kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin Pasifik. Na farko shi ne dagewa kan mutunta juna. Ya ce kasar Sin tana goyon bayan kasashen yankin wajen kiyaye cikakken ’yancinsu, tsaro da muradunsu na ci gaban. Kuma Sin ta yi imanin cewa, kasashen yankin za su ci gaba da bin manufar kasancewar kasar...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmaci a makon da ya gabata, wanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamnatakewa tsaro da sauransu. Inda muka yi masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin. ///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da zaben majalisun dukoki na kasa da kuma larduna a kudancin kasar Lebanon inda kungiyar Hizbullah da kuma Amal ta mabiyan mazhabar iyalan gidan manzon All..suka fi rinjaye. Inda zamu ga yadda Hizbullah ta lashe dukkan bazabun da yakamata ta lashe haka ma...
Mutanen da ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba sun rasa rayukansu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja. Mazauna yankin sun kuma ce babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin Najeriya da ta bi ta yankin ita ma ambaliyar ta yanke ta. Kodayake dai har yanzu babu cikakkun bayanai a kan ambaliyar, amma mazauna yankin sun kiyasta cewa mutanen da suka rasa ransu za su kai 50. NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu? ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su Gidaje da sauran kadarori na miliyoyin nairori ne dai suka salwanta, yayin da wasu...
Shima a nasa jawabin Janar Martin Luther Agwai cewa ya yi, “Aikin wanzar da zaman lafiya na daya daga cikin muhimman aikin Majalisar Dinkin Duniya da ake iya gani, inda sama da sojoji 87,000 ke sanye da rigar wanzar da zaman lafiya da farar hula suka taka rawa a cikin wasu ayyuka 12, daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa Lebanon, daga Sudan zuwa Mali. Nijeriya kuma na wakiltar ayyuka guda 8.” Wadannan jajirtattun maza da mata suna taimakawa wajen daidaita yankuna, ba wa fararen hula kariya, tallafawa tsagaita wuta, da sake gina da amana inda ta lalace. Mahimmanci lamari shi ne, tun lokacin da aka kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta farko a shekara ta 1948,...