2025-05-28@19:04:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5074
«samar da mai»:
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta ce kamfanoni mallakin gwamnatin kasar, sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata cikin watanni hudu na farkon shekarar nan ta 2025, inda jimillar kudaden shigarsu ta ci gaba da karuwa bisa daidaito a shekara guda. Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, sun nuna tsakanin watan Janairu zuwa Afirilu, jimillar kudaden gudanarwa na wadannan kamfanoni ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 26.276, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.65, adadin da ya nuna daidaito matuka idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2024. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya fara wata ziyarar aiki a kasar Oman mai manufar karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu aminnan juna. Shugaba Pezeshkian ya yaba da rawar da Oman ta taka a tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka, kuma tana fatan za a cimma sakamako mai kyau. Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ya yi da Sultan Haitham bin Tariq na Oman a birnin Muscat a yammacin yau Talata. Da yake jaddada matsayin kasar Oman a cikin manufofin ketare na Iran, Pezeshkian ya ce Tehran na da cikakkiyar amincewa ga Oman, kuma wannan amana na karfafa alaka tsakanin kasashen biyu. Shugaban ya ce Iran a shirye ta ke ta inganta hadin gwiwa da Oman a dukkan fannoni,...
Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza. Babbar jami’ar diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta bayyana cewa Tarayyar Turai ba ta goyon bayan sabon tsarin raba agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke kokarin aiwatarwa wanda ke kaucewa hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji. Kallas, ta kuma bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza sun wuce abun da suke bukata wajen yakar Hamas, a yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ke ci gaba da karuwa. Tun bayan da Isra’ila ta dawo da yaki a watan Maris bayan ruguza yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma...
Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba. Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba. Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani. Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka. Ministan ya...
A nasu jawabin, kwamishinonin kudi da kasafin kudi Misis Augustina Wandamiya da Mista Emanuel Pridimso sun bayyana cewa, an yi bitar kasafin ne da nufin gano wuraren da aka samu rarar kudi da kuma tabbatar da cewa, an kashe kudin kasafin shekarar 2024 a inda ya dace. Sun kara da cewa, jihar ta kula da tsari wajen aiwatar da kasafin kudi, tare da tabbatar da gaskiya, wanda hakan, ya taimaka wajen samar da kyakkyawan aiki a ayyukan raya jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...

Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya
Wasu masu binciken fasaha na kasar Sin, sun cimma sabon sakamako a fannin saurin sadarwa tsakanin tauraron dan adam da doron duniya, inda suka karya matsayin saurin da ake da shi a baya, ta amfani da salon X-band mai tasha guda. Rahotanni na cewa masu binciken, daga cibiyar binciken harkokin sadarwar samaniya ko AIR, karkashin hukumar lura da binciken kimiyya ta kasar Sin, sun cimma nasarar gudanar da sadarwa da saurin da ya kai megabit 2,100 duk dakika, adadin da ya haura wanda ake iya samu ta fasahar “microwave”, da karin kaso 75 bisa dari na saurin sadarwar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
A jiya Talata ne aka fitar da sanarwar hadin gwiwa ta taron kolin ASEAN-Sin-GCC karo na farko a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia. Sanarwar ta ce bangarorin uku sun amince hulda, da mu’amalar al’adu, da kuma hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da Sin, da kuma kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC na da dogon tarihi, don aka ana fatan kara inganta dangantakar sassan uku karkashin jagorancin ka’idoji, da ra’ayoyi, da manufofi, da alkawuran da aka cimma matsaya daya kan su, ciki har da tsarin dokokin MDD. A cikin sanarwar, an kuma yabawa kasar Sin, bisa muhimmiyar gudummawa da take bayarwa wajen inganta zaman lafiya,...
Ra’ayoyi daga sassan kasa da kasa sun karkata ga muhimmancin taron kolin ASEAN-Sin-GCC karo na farko da ya gudana a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia a jiya Talata 27 ga watan nan. Daga mahanga ta shiyya, taron bangarorin uku ya mayar da hankali ga manyan sassa uku, wadanda suka hada da gabashin Asiya, da kudu maso gabashin Asiya da yankin Middle East, tare da cewa ba kasafai ake samun irin wannan hadin gwiwar shiyyoyi a yankin Asiya ba. A gabar da ake fuskantar tarin kalubale a matakin kasa da kasa masu matukar sarkakiya, da raunin bunkasar tattalin arzikin duniya, Sin da ASEAN da GCC na aiki tare domin gina da’irar tattalin arziki ta bai daya da ci gaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce jami’an FEMD, FRSC da ‘yansanda sun gaggauta zuwa wurin domin gudanar da aikin ceto. Mohammed ya ja kunnen direbobi da su tabbatar motocinsu na cikin ƙoshin lafiya kafin su hau hanya. Ya kuma shawarci jama’a da su rika kiran lambar gaggawa 112 idan wani lamari ya faru. Wannan hatsari ya ƙara tayar da hankali kan lafiyar hanyoyi, inda hukumomi ke kira da a dunga bin dokokin kula da lafiyar motoci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Uba Sani ya amsa da cewa gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan 100 cikin watanni shida don magance matsalar ƙarancin ruwa a faɗin jihar, tare da alƙawarin cewa za a maye gurbin dukkan kayan aikin da suka lalace. Ya ƙara da cewa an riga an kashe sama da Naira miliyan 400 wajen gyara da maye gurbin bututun ruwa da aka lalata, kuma kafin ƙarshen shekara Kaduna za ta fara samun ruwa ba tare da katsewa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyoyin labarai a kasar Yemen sun bayyana cewa HKI ta kai hare-hare a kan tashar Jiragen sama a birnin San’aa inda a wannan karon suka lalata hanyar tashin jiragen sama a tashar. Tashar talabijan ta Al-manar ta kasar Lebanon ta kanalto majiyar HKI tana tabbatar da wannan labarin. Tashar radio ta HKI ta nakalto ministan yakin HKI Yasra’il Katz yana tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hare-haren ta sama sun wargaza wani bangare na tashar jiragen sama na birnin, sannan ya lalata jirgin sama tilo wanda ya rage a tasahr jiragen. Hakama tasha ta 12 ta HKI ta nakalto Katz yana cewa jiragen yaki fiye da 10 ne suka yi aikin hare-hare a kan tashar jirage na...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump a tattaunawa ta wayar tarho da firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bukace shi ya daina shiha a cikin tattaunawar da Amurka take da JMI. Kafin haka dai firai ministan ya sha barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran a dai-dai lokacinda ake tattaunawar. Wanda kuma yake tasiri a cikin abubuwan da ake tattaunawa tsakanin kasashen biyu. Sishshigin da HKI suna zama manya-manyan labarai a kafafen yada labarai na duniya, wanda kuma yakan sa JMI ta maida martani. Don haka kutsawar da HKI take yi yana rikita tattaunawar, wasu suna fadar cewa HKI ce take fadar abinda wakilin Amurka zai fada a tattaunawar. Ya zuwa yanzu dai Washington da Tel Aviv suna da sabanin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington, Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba barin Iran ta tashe makamashin Uranium a cikin kasar. Ministan ya kara da cewa Mandelson yana son ya karkatar da tattaunawan da Iran take da Amurka. Ya kuma kara da cewa Iran ce take sanar da kasashen turai yadda tattaunawa tsakanin Amurka da ita ke tafiya, tun Amurka ta waresu daga tattaunawar. Yace, idan har haka ne tunanin kasar Burtaniya wacce take cikin kasashen da suka sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu, yana ganin mai yuwa Iran ta dakatar da sanar da su abubuwan da ke tafiya a tattaunawar. Ya zuwa zagaye har 5 wadanda Amurka da...
Majiyar kungiyoyin bada taimakon gaggawa a Gaza sun bayyana cewa ya zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Laraba, sojojin yahudawan Sahyoniyya sun kashe akalla mutane 16. Shafin labarai na Arab News ta kasar Saudia ya nakalto Mahmud Bassal kakakin wata kungiyar bada agaji na Gaza yana cewa da misalign karfe biyun dare jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan gidan Osama Al-arbeed dan jarida mai daukar hotuna a gidansa da ke arewacin Gaza, inda harin ya raunata Osman Arbeed sannan ya kashe wasu daga cikin yan gidansa. Har’ila yau wasu mutane 6 sun kai ga shahada a yayinda wasu 15 suka ji rauni daga ciki har da yara kanana, a garin Khan Yunus a safiyar yau Laraba. A lokacin...
A wani wasa da masana ke ganin zai matuƙar ƙayatarwa a gasar kofin Unity, yau Laraba za a buga wasa tsakanin manyan ƙasashen Afrika biyu Nijeriya da Ghana, ba kawai wasan ƙwallon ƙafa bane yau, kare mutunci, da ɗaukaka martabar ƙasa da kuma ramuwar gayya duk suka haɗe a wasan da za a buga a filin wasa na Gtech dake birnin Landan. Babu kanwar lasa a cikin ƙasashen biyu in dai batu ake na taka leda a nahiyar Afrika duba da cewa dukkansu sun lashe manyan kofuna na cikin gida kuma sun nuna abinda zasu iya a fagen ƙwallon ƙafa a Duniya, Ghana ta lashe gasar AFCON ta ƙasashen Afrika sau huɗu a tarihi yayin da Nijeriya ta lashe sau...
Kungiyar kare hakkin bil’aama ta “Amnesty International” ta bayyana cewa; mai yiyuwa ne kungiyar ‘yan tawaye ta m23 da kuma sojojin gwamnatin DRC sun aikata laifukan yaki. A wani rahoto da aka buga a jiya Talata, kungiyar kare hakkin bil’adam ta ce; Kungiyar M23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta kashe mutane da dama, da kuma azabtar da su bayan da ta tsare su. Kungiyar ta M23 ta kwace iko da yankin gabashin kasar mai cike da albarkatun karkashin kasa da su ka hada Bukavu da Goma. Tare da cewa an kulla yarjejeniya a tsakanin M23 da gwamnatin DRC sai dai kuma har yanzu suna ci gaba da fada.
Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa; Gwamnati ta amince da a ci gaba da yin wasu dokokin da hana mu’amalar kasuwanci da matsugunan ‘yan share wuri zauna da ba su bisa doka, domin an yi su ne akan kasar Falasdinawa.” Daga cikin kayayyakin da Majalisar dokokin ta Ireland ta haramta, da akwai ‘ya’yan marmari da itatuwa. Ministan harkokin wajen Ireland Simon Harris ya fada wa ‘yan jarida cewa, yana fatan ganin...
Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na yankin zirin Gaza da su ka hada da sansanonin ‘yan hijira da kuma rusa gidajen da su ka saura a tsaye. Tashar talabijin din ‘almayadin” ta bayyana cewa; An sami shahidai 7 da safiyar yau Laraba, bayan harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai akan wani gida da yake a Deir-Balah,dake tsakiyar zirin Gaza. A can sansanin ‘yan hijira dake kusa da filin wasa na ‘al-Anan’ kuwa mutane 4 ne su ka jikkata. A yankin Safdawi dake cikin birnin Gaza, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan wani gida wanda ya haddasa gobara, da kuma shahadar mutane 8. A unguwar “Shuja’iyya” sojojin na mamaya sun rushe gidaje da...

Arakci: Idan Birtaniya Ta Ci Gaba Da Batun Dakatar Da Tace Uranium A Iran, Za A Dakatar Da Tattaunawa Da Ita
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Akaci ya bayyana cewa; Idan har kasar Birtaniya tana ci gaba a kiran Iran ta dakatar da tace sanadarin uranium a cikin kasarta, to kuwa Iran din za ta yanke tattaunawar da take yi da ita. Ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya rubuta a shaifnsa na hanyar sadarwa ta jama’a cewa: Iran ta tuntubi Birtaniya ne da kyakkyawar manufa,haka nan sauran kasashen turai da aka yi yarjejeniyar Nukiliya da su, duk da cewa, Amurka ba ta son su shiga cikin tattaunawar.” Arakci ya kuma ce; Idan har matsayar Birtaniya shi ne ta ga an daina tace sanadarin uranium baki daya a cikin Iran, wanda hakan keta yarjejeniyar da ita kanta tana...
Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42. Mahukunta a yankin sun sanar da cewa; an gano gawawwakin mutane 32 da aka kashe sanadiyyar harin da aka kai kauyukan Ahume da Aodona, yayin da aka gano wasu gawawwakin mutane 10 a kauyukan Tyolaha, Tse-Ubiam, kamar yadda shugaban karamar hukuma Gwer ta yamma Victor Omnin ya bayyana. Shugaban karamar hukumar ya bayyana wa ‘yan jarida abinda ya faru da cewa; na takaici ne, domin a wannan lokacin da muke Magana ana ci gaba da gano gawawwaki.” Jahar Benue tana tsakiyar kasar Nigeria ne a yankin da ake kira : Middle-Belt”. An kuma dauki shekaru masu...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Kabo a jihar Kano, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo. Wannan cibiyar ilimi, wacce aka kafa a shekarar 2022, yanzu ta zama jami’a ta uku ta gwamnatin tarayya a jihar, bayan Jami’ar Bayero Kano da kuma Jami’ar Ilimi ta Tarayya da aka assasa a kwanan nan, wacce aka sanya wa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule. Matashi ya shiga hannun ’yan sanda kan kisan matar aure a Kano Tinubu zai ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje Kano na kuma da jami’o’o’i biyu mallakin gwamnatin jiha. Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da damuwa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli. A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace ‘yan mata goma a ƙasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa makaranta lokacin da take jinin al’ada, saboda rashin kayan tsafta, ruwa da kuma tsaftatattun ban daki. Irin wannan matsala na addaban mata marasa galihu da wadanda ke zama a karkara. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA...
Sun kara da cewa, kasashen Afirka za su kafe kai da fata wajen mutunta ka’idar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ta yi na kare ikon ’yancinta da cimma burin sake hadewar kasar, da yin adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana suka ce, kasashen Afirka za su kiyaye manufofi da ka’idojin yarjejeniyar kafa MDD, tare da kare muradu na bai daya na kasashe masu tasowa da kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...

Sin Za Ta Kara Zurfafa Dunkule Rawar Yankunan Raya Tattalin Arziki Da Fasahohi A Fannin Janyo Jarin Waje
Mataimakin ministan ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Ling Ji, ya ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa dunkule rawar da yankunan raya tattalin arziki da fasahohi mallakin gwamnati ke takawa, a fannin janyo jarin waje, a gabar da kasar ke kara fadada matakanta na bude kofa ga kasashen waje. Ling Ji, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin wani taron manema labarai da ya gudana, ya ce a halin yanzu yanayin hada-hadar tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa na cikin wani halin ha’ula’i, kuma sakamakon haka, matsayar yankunan raya tattalin arziki da fasahohi na muhimmin jigon daidaita hada-hadar cinikayyar waje, da zuba jari na kara bayyana a fili. Ya zuwa shekarar 2024, adadin irin wadannan...
Da yake magana da tashar talabijin ta ON Sports, Salah ya ce “Zan daina wasa ne kawai idan na fara jin gajiya a jikina”, “Idan ka tambaye ni ra’ayi na, ina tsammanin zan iya taka leda har zuwa shekaru 39 zuwa 40 amma idan na ji ina so in daina, zan daina, na samu abubuwa da yawa a harkar kwallon kafa”, inji Salah wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Firimiya Lig ta bana. Salah ya ci wa Liverpool da Chelsea kwallaye 186 a gasar firimiya kuma ya na matsayi na biyar a jerin wadanda suka fi kowa zura kwallo a raga inda kwallo daya kacal ta rage ya cimma tsohon dan wasan Newcastle da Manchester United Andrew Cole,...
Ya ce, mahajjaciyar ta kamu da rashin lafiya ne jim kadan bayan kammala Tawafi – zagaye dakin Ka’aba, inda daga nan aka kai ta asibiti a ranar Lahadi, a ranar Litinin kuma Allah ya yi mata cikawa. “Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, an yi jana’izar ta a Makkah a wannan rana, kuma an sanar da danginta a Jattu Uzairue a hukumance,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Nuna Misali Na Bude Kofa Da Raya Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da ASEAN Da GCC
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga aiwatar da matakai da za su zamo misali na bude kofa, da raya hadin gwiwa, da dunkule mabanbantan wayewar kai tsakanin Sin da ASEAN da GCC. Li Qiang, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, cikin jawabinsa ga bikin kaddamar da dandalin Sin da ASEAN da GCC, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia. Li, ya kuma yi kira ga sassan uku da su samar da wani salo na yin komai a bude tsakanin shiyyoyi, duba da cewa adadin al’ummunsu, da darajar tattalin arzikin da suke da shi ya kai rubu’in na duniya baki daya. Don haka dinkewar kasuwannin sassan 3, zai samar da babban fage na...
An bukaci Maniyyatan Jihar Jigawa su yi addu’o’i ga jihar da kasa Najeriya domin samun zaman lafiya a yayin zaman su a kasa Mai tsarki. Amirul Hajj na Jihar, Mai Martaba Sarkin Kazaure Dr Najib Hussaini Adamu yayi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga Maniyyatan Jihar a Kasar Saudi Arabia. Amirul hajjin ya hori Maniyyatan da suyi addu’a tare da karkatar da zukatansu ga dabi’u nagari, inda ya bayyana cewar canza dabi’u tare da komawa ga Allah ne kadai hanyar da za’a bi don magance matsalolin da suka addabi kasa Najeriya. Dr Najib Hussaini Adamu, yace Allah ya albarkaci Jihar Jigawa da ni’imomi da dama, a don haka ya bukace su da su kara karfafa...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Dole Ne A Dauki Kwararan Matakan Don Dakatar Da Laifukan Gaza
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a dauki kwararan matakai don dakatar da laifukan da ake yi a Gaza A yayin ganawarsa da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif da tawagarsa a yammacin yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin gudanar da ayyukan hadin gwiwa da inganci tsakanin kasashen Iran da Pakistan domin dakile laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza. A farkon taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana matsayin Pakistan na musamman a duniyar Musulunci, inda ya bayyana jin dadinsa da kawo karshen yakin da ake yi tsakanin Pakistan da Indiya, tare da bayyana fatansa na warware sabanin da ke tsakanin kasashen biyu ta hanyar lumana. Haka...
Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar alaka da kasashe makwabta, kuma alaka tsakaninsu tana bunkasa kowace rana. Shugaba Pezeshkian da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Mehrabad ya bayyana cewa: A halin yanzu yawan ciniki tsakanin Iran da Oman ya kai dalar Amurka biliyan 2.3, yana mai jaddada bukatar ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Shugaba Pezeshkian ya ce: Zai gudanar...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Batun Dakatar Da Sarrafa Uranium Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta daina sarrafa sinadarin Uranium a kowane hali ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar a wata hira da tashar CNN ta Amurka cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da hakkinta na tace sinadarin Uranium a kowane hali ba. A yayin da yake mayar da martani game da kyakkyawan fata na shugaban Amurka Donald Trump game da shawarwarin nukiliyar da aka yi tsakanin gwamnatinsa da Iran da kuma yadda yake kallon ci gaban da aka cimma, Baqa’i ya ce: Idan manufar Amurka ita ce tabbatar da cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ba zata yi amfani da shi wajen karfin soji ba, to yana ganin...
Mijinta mai suna Ibrahim Mohammed ne ya gano ta, inda aka garzaya da ita asibiti, daga bisani aka tabbatar da mutuwarta. “Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda ya amince da haurawa cikin gidan matar, inda ya shake ta, sannan ya daba mata wuka a wuya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarta. Sanarwar ta kara da cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gujewar da Trump ta yi daga yakin Yemen ya harzuka mahukuntan gwamnatin Isra’ila da kasashen Larabawa da suka dogara da shi Shafin Jaridar Hill ta Amurka ta buga wani sabon labarin da ke bayyana irin kayen da Amurka ta sha a Yemen da kuma irin dimbin hasarar da Amurkan ta yi domin kare yahudawan sahayoniyya kafin ficewa daga kangin matakin martanin kasar Yemen. Labarin da Imran Khaled ya rubuta mai taken “(Al’ummar Yemen) sun yi tsayin daka da kuma ja da baya da Trump ya yi… Shin Amurka za ta fice daga Yemen?”, yarjejeniyar “dakatar da kai hare-haren wuce gona da irin Amurka kan Yemen” ta bayyana yadda Amurka ta yin watsi da kawayenta cikin sauki, wanda ke nufin gwamnatin...
Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakan ‘yan tawayen kasar na kungiyar Rapid Support Force daga sansanoninsu da ke kudancin Omdurman Hukumomin sojin Sudan a birnin Omdurman na jihar Khartoum, sun sanar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun tsare sun bar makamai da alburusai da dama da suka hada da haramtattun makamai da aka hana amfani da su a dokokin kasa da kasa, bayan da suka sha kashi a yankin Al-Saliha da ke kudancin birnin. Majiyoyin sun kuma tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawan suka kwace gidajen zaman jama’a da karfi da yaji domin amfani da su a matsayin ma’ajiyar makamai. Yakin baya- bayan nan da sojojin Sudan suka yi da dakarun kai daukin gaggawa...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron kasa karo na tara na kungiyar yara jagorori na kasar Sin (CYP), wanda aka bude a yau Talata a birnin Beijing. Xi ya jaddada muhimmancin ganin kungiyar ta bi sawun jam’iyyr kwaminis ta kasar Sin a da kuma yaye hazikai masu gina kasa da za su raya hanyar gurguzu mai sigogin kasar Sin. A game da bikin ranar yara ta duniya da za a yi a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, ya taya musu shiryawa murna a madadin kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ya mika sakon gaisuwa ga dimbin yara jagororin, da masu dora su a kan hanya, da bangarensu na...
An kammala gasar fada tsakanin mutum-mutumin inji cikin jerin gasannin mutum-mutumin inji ta kasa da kasa a ran 25 ga watan nan da muke ciki a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. Gasar ta fada tsakanin mutum-mutumin inji da aka yi a wannan karo, ita ce irinta ta farko a duniya, inda kuma ta zama wani dandali dake yi wa masu kallo a daukacin duniya karin haske game da kimiya da fasaha a wannan bangare. An watsa gasar ga masu kallo na cikin gidan kasar Sin da ketare kai tsaye, matakin da ya ba su damar sanin gajiyar da ake ci daga kimiya da fasaha. CMG ta gabatarwa al’ummun duniya wata dama mai kyau ta fahimtar kimiyyar mutum-mutumin inji...
A cewar Mukaddashin Daraktan, ‘yan ta’addar sun yi yunkurin kutsawa inda sojojin suke, amma suka gamu da karfin soji. Ya kara da cewa, Rundunar Sojan Sama ta bayar da bayanan sirri tare da karfafawa sojin kasa, wanda ya kai ga halaka sauran ‘yan ta’addan da suka tsere. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya zama wajibi duk wata kasa dake son samun ci gaba mai dorewa, ta rike asalinta, ta kare al’adunta, ta zabar wa kanta hanya mafi dacewa da ita kamar yadda kasar Sin ta yi, domin har kullum, Sin za ta ci gaba da zama abin koyi ga sauran sassan duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumomin Kasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Zulhajji a ranar Talata, wanda ke nuna cewa ranar Laraba 28 ga Mayu, 2025, ita ce 1 ga watan Zulhajji, 1446 Bayan Hijira. Hakan yana nufin Alhzai za su yi Tsayuwar Arfa ranar Alhamis, a yi Babbar Sallah ranar Juma’a na mako mai zuwaa yi
’Yan sanda sun kama babban wanda ake zargi da kisan wata matar aure masi shekaru 22 a gidanta da ke unguwar Tsamiyar Duhuwa da ke yankin Farawa a Jihar Kano. A ranar 6 ga watan Afrilu ne aka tsinci gawar matar mai suna Rumaisa Haruna, ne a gidanta bayan an yi mata kisan gilla. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar kama wanda ake zargin mai shekaru 35 mazaunin unguwar Madatai ne a ranar 23 ga watan Mayu ta hanyar binciken sirri. Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a hannun ’yan sanda, inda ya bayyana cewa ya shiga gidan wadda aka kashe ne ya shake ta, sa’annan ya soka mata wuka a wuya, lamarin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa, a watan Mayun bara. Aikin sabunta masallacin ya kunshi gina makarantar Islamiyya tare da ofis da bandaki da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da tankin ruwa na sama. Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sanar amincewar sake gina masallacin ya biyo bayan alkawarin da Gwamna Abba Kabir ya yi a lokacin da ya...
Kan batun gyaran gidajen yari kuwa, ministan ya nuna damuwa kan halin da gidan gyaran hali ke ciki, inda ya bayyana cewa fiye da fursunoni 4,000 na tsare ne saboda gazawarsu na biyan tara kamar Naira 50,000. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An samu Shafi’u da laifuka hudu, ciki har da kisan kai da kuma barna ta hanyar gobara. Baya ga hukuncin kisa, alkali ya ba da umarnin a yi masa bulala 150, tare da biya tarar N1,500, sannan kuma a kwace babur dinsa mai kafa uku, inda za a sayar, a yi amfani da kudin da aka samu wajen gyaran masallacin da ya lalace. Yayin shari’ar, masu...
Gwamnatin Jihar Kano ta cika alƙawarin da ta ɗauka ga al’ummar ƙauyen Gadan, ƙaramar hukumar Gezawa, inda aka kona masallata a lokacin Sallar Asuba. Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Litinin, yana mai cewa gwamnati ta amince da kashe Naira miliyan 151,863,895.97 domin gudanar da muhimman ayyukan ci gaba a garin. Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kona Masallata A Kano Yadda Rikici Ya Yi Sanadin Kashe DPO A Kano Ayyukan sun haɗa da gyara da faɗaɗan masallacin da aka ƙona masallatan a ciki, da ginin sabuwar makarantar Islamiyya da ofishin malamai, da gyaran banɗakuna guda shida, da kuma aikin famfon tuka-tuka mai amfani da...
Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Francesca Albanese tana fadar haka a shafinta na X a jiya Litinin. Ta kuma kara da cewa an kashe mutane da yawa, kuma an kashe yara da yawa. An kona su da ransu, a cikin makarantar inda suke mafaka a ciki. Albanese ta hada da hotunan bidio wanda suke nuna irin yadda wuta take kona Falasdinawa a cikin makarantar, ta turasu a shafin nata....
Majalisar dokokin kasar Iran ta sake zaben Mohammad Baqir Qalibof a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar na wata shekara a zaben da aka gudanar a cikin majalisar a jiya Litinin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa ya sami kuriu 219 daga cikin Jimillan kuri’u 272, wanda ya bashi babban rnjaye a kan sauran wadanda suke takara da shi. Wannan kuma ya nuna cewa shugaban majalisar ya na da karbuwa a cikinta. Kuma yana da tasiri a cikin al-amuran gwamnati musamman a lokacinda kasar take fama da barazana a ciki da wajen kasar, musamman dangane da tattaunawa kan shirin makamashin Nukliyar kasar, wanda ake tattaunawa a kansa da Amurka. An gudanar da wasu zabubbuka a cikin majalisar...
Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin. Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun falasdinawa a yakin shekara 1967 tsakanin yahudawan da kuma larabawa. Birnin Qudus ta gabas dai nan ne masallacin Al-aksa yake, kuma nan ne Falasdinawa suke da dama. Yahudawan dai su na ganin dukkan birnin Qudus wanda ya hada har da inda masallacin Al-aksa yake mallakinsu ne kuma su na da shirin rusa masallacin don gina wurin bautansu a inda masallacin yake.
Ga shi abin ci ya yi tsadar da samun a ci sau uku yana da wajala, balle kuma a nemi mai gina jiki. Kwananan masu sayar da ƙwai suka koka saboda rashin ciki, masu kifi dai haka abin yake balle kuma masu nama. Duk da hakan bai hana yara murmushi ba wataƙila saboda ba su da masaniyar irin wahalar da iyayensu ke sha wajen ganin sun samar musu da rayuwa mai inganci. Lallai ya kamata ƴan majalisa su matsala ƙaimi a samar da wani yanayi ga yara musamman wajen kare su daga faɗawa ƙangin talla ko bautar aikatau ko kuma zama ƴan jagorar masu bara, hakan kuwa zai faruwa ne idan aka aiwatar da dokar kare ƴancin yara. Daga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina. Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance har ya kai ga kisa. Amaryar, mai shekara 23 a duniya, ta yi wa uwargida wannan aika-aika ne ranar Lahadi a unguwar Sabon Gari, daura da Makaranta Firamare ta Daɗi. DSP Abubakar Aliyu, ya ce a ranar ce bayan mijinsu ya dawo daga kasuwa ya kai ƙara Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Daura cewa ya iske uwar gidansa kwance a cikin jini. An yanke...
Kotu ta yanke wa wani magidanci mai shekara 56 hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan laifin yin fyaɗe ga agolarsa ’yar shekara 14. Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa mutumin hukuncin ne byan an gurfanar da shi kan zargin aikata laifin a watan Oktoban shekarar 2024, watanni bakwai da suka gabata. A yayin zaman kotun da ke zamanta a garin Ado-Ekiti, mai gabatar da ƙara, Julius Ajibare ya gabatar da shaidu shida da ke tabbatar da laifin da ake tuhumar mijin mahaifiyar yarinyar da yi mata fyaɗe. Kazalika ya gabatar da wasu hujjoji da kuma sakamakon gwajin asibiti da suka tabbatar da laifin da ake zargin magidancin da aikatawa. Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano ...
Mutanen garin Rano ake Jihar Kano sun kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta Fitattun jama’ar gari sun kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Rabin hari ne a sakamakon mutuwar matashin a hannun ’yan sandan. Wasu sanarwar da kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, S.P. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga mutuwar wani wanda ake zargi da aka tsare. Ya bayyana cewa an kama matashin ne bisa laifin tuka babur ba cikin danganci kuma zargin yana yin haka ne bayan shaye-shayen ƙwayoyi. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su Wani abu ya fashe...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su. Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun dade suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a kwarya. NAJERIYA A YAU: Tasirin Dangantakar Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan Talaka DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu” Yayin da ake bikin Ranar Yara, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan halin da ya...
Sojojin kasar Yemen sun sake kai wani hari da makali mai linzami da safiyar yau Talata wanda ya sa jiniyar gargadi ta kada a cikin yankuna da dama na HKI. Wannan dai shi ne karo na 3 a cikin sa’o’i 24 da kungiyar Ansarullah ta Yemen ya harba wa HKI makamai masu linzami. Sojojin HKI sun bayyana cewa, makamin da aka harbo daga Yemen ya sa jiniyar gargadi ta kada a cikin yankuna masu yawa a Falasdinu dake karkashin mamaya. Yemen dai tana kai wa HKI hare-hare ne saboda taimaka Falasdinawa dake yi wa kisan kiyashi fiye da shekara daya da rabi,wanda kuma har yanzu bai tsaya ba. Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Husi ce; matukar ba a kawo karshen...
Shugaban kasar Iran wanda ya karbi bakuncin Fira ministan Pakistan da marecen jiya Litinin, ya bayyana cewa; Kasar Pakistan, makwabciyar jamhuriyar musulunci da muhimmanci, ta dubban shekaru. Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake Magana a lokacin taron manena labaru na hadin gwiwa da Fira ministan na Pakistan, ya kuma ce; Da akwai haduwar mahanga a tsakanin kasashen biyu akan batutuwa masu yawa da su ka shafi wannan yankin da kuma duniyar musulunci da kuma a fagen siyasar kasa da kasa.” Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce: “A yayin ganawar da mu ka yi da dan’uwana Fira minisan Pakistan da tawagar da taek tre da shi, mun jaddada yadda za a bunkasa alaka ta siyasa, tattalin arziki da al’adu.”...
Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wa gabashin zirin Gaza da kuma Khan-Yunus hare-hare, bayan sa’oi daga kisan kiyashin da su ka yi wanda ya ci rayukan mutane 80. Saandiyyar sabon harin na safiyar yau, wani karamin yaro ya yi shahada, a yankin al-karama dake Arewacin Gaza. A daren jiya ma dai sojojin na HKI sun kai wasu hare-haren a unguwar ” Zaytun” dake gabashin Gaza. Tashar talbijin din ‘al-Aqsa” ta bayar da labarin dake cewa; Unguwar Shuja’iyya’ da wasu unguwannin a gabashin birnin Gaza sun fsukanci hare-haren ‘yan sahayoniya daga manyan bindigogi. Wasu hare-haren na ‘yan sahayoniya sun shafi Arewacin zirin Gaza da su ka yi sanadin rushewar gidaje, haka nan kuma asibitocin da...
Kasar Najeriya ta sanar da Shirin fara aiki a wasu sabbin masana’antu domin sarrafa sanadarin Lithium Ministan ma’adanai na kasar ta Najeriya Daili Alaki ne ya sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a wannan shekarar da ake ciki ta 2025, da hakan zai samar da gagarumin sauyi a fagen kayan da kasar za ta rika fitarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin “Reuters” ya ambato ministan ma’adanai na kasar yana ci gaba da cewa; ‘yan kasar China ne za su zuba hannun jari mafi grima a cikin wannan Shirin da hakan zai samar da ayyukan yi a cikin kasar da kuma bunkasar harkokin kere-kere. Haka nan kuma Alaki ya yi ishara da cewa; Msana’antar sarrafa Lithium din da za...

Ma’aikatar Kudi Ta Sin Ta Yi Tsokaci Game Da Matsayar Kamfanin Moody’s Bisa Kiyaye Mizanin Matsayin Kasar
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, tun daga rubu’i na hudu na shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da matakai a jere na kula da harkokin tattalin arziki, da kyautata yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma hasashen kwarin gwiwa da ake yi kan kasuwanni cikin kwanciyar hankali. Matakin da kamfanin nazari na Moody’s ya dauka na tabbatar da daidaiton mizanin matsayin kasar Sin, wani lamari ne mai kyau, na kyakkyawan fatan bunkasar tattalin arzikin kasar. Ma’aikatar kudin ta kasar Sin ta bayyana cewa, a mataki na gaba, wasu tsare-tsare za su gudana tare, kuma za su ci gaba da yin tasiri, da samar da cikakken goyon baya ga bunkasar tattalin arziki...
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, bayan ya ziyarci wurin da kuma kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Rano, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dr. Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19), ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya don gano musabbabin faruwar lamarin da gaggawa da kuma gurfanar da wadanda suka aikata duk wani laifi a gaban kotu. Rundunar, ta jajantawa iyalan marigayin DPO da ya rasu yayin aiki, ta kuma yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa daukar doka a hannunsu. Sannan, su kuma bar binciken ya ci gaba da tafiya ba tare da katsewa ba. Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa al’umma aniyarta na ci gaba da wanzar...
Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta buƙaci al’ummar da ke kewayen hanyar Mararaba zuwa Nyanya su kwantar da hankalinsu bayan jin ƙarar wani abu da ya fashe a yammacin ranar Litinin. Lamarin ya faru ne a wata tashar bas da ke kusa da barikin sojoji na Mogadishu a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya. A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Josephine Adeh, ta ce tuni ta tura jami’anta wajen domin bincike da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin. Kwastam ta kama Tiramol ta N150m, ta miƙa wa NAFDAC a Kano FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji “A ranar 26 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 2:15 na rana aka yi...
Rundunar ‘yansanda ta fara gudanar da bincike kan fashewar wani abu a mashigar babban birnin tarayya Abuja a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya a ranar Litinin. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu rahoton kiran gaggawa a ranar 26 ga watan Mayun 2025 da misalin karfe 2:50 na rana, dangane da fashewar wani abu a kan hanyar. Sin Za Ta Harba Na’urar Binciken Samaniya Ta Tianwen-2 FCTA Ta Rufe Hedikwatar PDP Ta Ƙasa Saboda Ƙin Biyan Harajin Ƙasa “Bayan samun rahoton, nan take aka tura jami’an sashin warware bama-bamai (EOD) inda lamarin ya afku, cikin gaggawa aka killace yankin da lamarin ya shafa domin tantancewa...
Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da shirye-shirye, domin harba na’urar binciken samaniya ta kasar Sin mai lakabin Tianwen-2, a ranar Alhamis 29 ga watan nan, na’urar da ake fatan za ta samar da bayanai game da sirrin dake tattare da tauraron dake kusa da sararin samaniyar bil adama, da karamin tauraron dake kewaya da’irar dake shiyyar, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta sanar a Litinin din nan. Ana sa ran na’urar Tianwen-2, za ta tattaro samfura daga tauraro mai lamba 2016HO3, aikin da zai zamo irinsa na farko a fannin, kana zai kewaya karamin tauraron “comet 311P”. Yanzu haka dai ana ci gaba da shirye-shirye domin tabbatar da nasarar...
Iran ta yi kira da a karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka bisa tsarin yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar A yayin bikin karo na 62 na kafuwar kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a birnin Tehran, ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar Iran na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka, musamman ta hanyar yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA). A cikin jawabin da ya yi ga jakadun kasashen Afirka a Iran, Araghchi ya yaba da dabi’u da tarihin gwagwarmayar al’ummar Afirka, yana mai cewa Afirka, mai al’umma biliyan 1.4, na zaman kawa a huldar tattalin arziki ga Iran. Ya kara da cewa: “Iran da kasashen Afirka za...
Firaministan Pakistan Muhammad Shehbaz Sharif ya na ziyara a birnin Tehran domin inda yake ganawa da manyan jami’an kasar kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu, shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya. A yau litinin ne Sharif ya jagoranci tawaga a Tehran bisa gayyatar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi masa. Da yake magana a wata hira da IRNA gabanin ziyarar tasa, Sharif ya yaba da diflomasiyyar zaman lafiya ta Iran a matsayin abin a yaba, yana mai jaddada goyon bayan al’ummarsa ga Jamhuriyar Musulunci. Ya ce babban makasudin ziyarar tasa a Tehran ita ce nuna godiya ga Iran bisa goyon bayan da ta bayar, musamman yadda ta amince da diflomasiyyar Iran a yankin, a lokacin da...
Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya a ƙarƙashin jam’iyyar Labour a Zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ba dole ba ne sai ya zama shugaban ƙasar nan ba. Sai dai Peter Obi ya ce yana so ya ga ƙasar tana aiki yadda ya kamata a ƙarƙashin jagoranci nagari. Rikici ya barke a taron Atiku da kungiyoyin Arewa Kwastam ta kama Tiramol ta N150m, ta miƙa wa NAFDAC a Kano Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Obi yana bayyana haka ne lokacin bikin murnar cika shekara biyu kan mulki na Gwamnan Abia, Alex Otti. Ya ce ya kamata a samu shugabanni waɗanda mutane za su yi alfahari da su. Ya ƙara da cewa haƙƙin shugaba ne ya kare muradun waɗanda yake mulka....
Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai hari a makarantar Fahmi al-Jarjawi da ke yankin Daraj na zirin Gaza, inda daruruwan iyalai da suka rasa matsugunansu daga garin Beit Lahia da ke arewacin kasar da Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai suka samu mafaka. Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwakinmutum 20 daga makarantar, ciki har da yara da dama. A...
A cewar jami’ai, za’a tsara yadda tsarin fitar da barasar zai kasance ta hanyar tabbatar da cewar an ba da horo ga masu sayar da ita da kuma basu takardar lasisin sayar da barasar. Hakazalika, za a tsaurara ka’idoji akan sayar da barasa a kasar, gwamnati ta jaddada cewa ana gabatar da sauye-sauyen ne cikin taka-tsantsan tare da kula da al’adun al’ummar kasar. “Manufar ita ce, maraba da duniya ba tare da rasa asalin al’adu ba, sanya Saudiyya a matsayin mai ci gaba, duk da haka mai mutunta taswirar yawon shakatawa na duniya,” in ji hukumomin Saudiyya a cikin wata sanarwa. Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Saudiyya ke neman yin gogayya da kasashe makwabta kamar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An fi sanin tsarin kusurwa uku a matsayin tsari mafi ba da fa’idar halitta, kuma tsarin dunkulewar aikin ba da ilmi da kimiyya da kwararru na Sin ya yi kama da tsarin kusurwa uku, hakan ya sa yake da ingantaccen karfin zamanintar da al’ummar Sinawa a sabon zamani. Wannan mataki ne da gwamnatin Sin ke dauka dake hada tarihi da kirkire-kirkire tare don raya kasar. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Matakin na FCTA ya kara jaddada daukar tsauraran matakai kan wadanda suka saba ka’idojin amfani da filaye a babban birnin kasar. Jami’an sun ce, rufewar za ta ci gaba da aiki har sai an warware basussukan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Kasar Kenya: FOCAC Ya Samar Da Damammaki Ga Sin Da Afirka Wajen Inganta Hadin Kansu Da Samun Moriya Tare
Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a sabon zamani. William Samoei Ruto ya shedawa manema labaran CMG cewa, dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka na FOCAC ba samar da wani dandalin mu’ammalar ra’ayoyi kadai ya yi ba, ya kuma shimfida sharadi mai kyau ga bangarorin biyu wajen fidda sabbin damammakin hadin gwiwa da samun moriya tare. Ruto ya ce, FOCAC ya samar da wani ingantaccen dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Kwastam reshen Kano da Jigawa, ta kama nau’in ƙwayar Tiramol katan 491,000, tare da miƙa su ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC). An ƙiyasta kuɗin magungunan da aka kama sama da Naira miliyan 150, kuma an gano su a cikin wata mota ƙirar Lexus SUV, a hanyar Gumel zuwa Maigatari da ke Jihar Jigawa. FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato Kwanturolan hukumar a yankin, Dalhatu Abubakar, ya ce an yi wannan nasara ne bisa sahihan bayanan sirri, kuma yana daga cikin ƙoƙarin da suke yi tun bayan shigarsa ofis a watan Fabrairun 2025. Abubakar, ya ce an shigo da ƙwayoyin ne...
Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA), ta rufe hedikwatar jam’iyyar PDP da ke unguwar Wuse a Abuja. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:05 na ranar Litinin. Wike ya rufe ofishin FIRS da Bankin Access kan rashin biyan haraji Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato Jami’an FCTA sun isa ginin tare da jami’an tsaro, inda suka rufe ofishin. Wasu ma’aikata sun nuna rashin jin daɗinsu, bayan tafka sa-in-sa na tsawo mintuna 15, jami’an FCTA sun bar ma’aikata su fitar da motoci da kayayyakinsu kafin kulle ginin. A makon da ya gabata, FCTA ta sanar da cewa za ta ƙwace sama da kadarori 4,700 a Abuja saboda rashin biyan haraji na tsawon shekaru 10 zuwa 43....
Wani haɗarin mota da ya faru a yau Lahadi a hanyar Lokoja-Obajana ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, yayin da wasu 8 suka jikkata. Sakataren FRSC na jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da cewa haɗarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce ƙima. Mota bas da wata babbar mota sun yi karo da juna a Gada biyu, inda yara 5 suka ƙone har lahira. Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC Kashi 25 Kawai Na Motocin Da Ke Nijeriya Suke Da Inshora – FRSC “Mutane 27 ne haɗarin haɗarin ya rutsa da su, 8 kacal suka tsira,” in ji Tsukwam. An kai wadanda suka tsira asibitin Fisayo a Obajana don samun kulawa. FRSC ta yi...
Hukumar Kula da Babban Birnin (FCTA) Tarayya ta rufe ofishin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kuma ginin Bankin Access kan rashin biyan haraji na sama da shekaru 25. Daraktan Kula da Filaye na Hukumar FCTA, Chijioke Nwankwoeze, ya bayyana cewa hukumar bin ginin da bankin Access yake bashin harajin shekara 35, ofishin FIRS da ke unguwar Wuse Zone 5 kuma bashin harajin shekara 25. Babban Ofishin na FIRS na daga cikin fitattun gine-gine da Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji na Babban Birnin ta rufe a safiyar Litinin, kan zargin rashin biyan haraji. Sauran sun shafa da ginin Bankin Access da da ofishin kamfanin mai Total Energy da fitaccen otel din Ibro Hotel a unguwar Wuse, da sauran wurare 4,700...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana. Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara suna gudu a cikin wuta suna kokaron kubutar da kansu. Labarin ya kara da cewa makarantar tana unguwar Daraj na birnin Gaza, mai suna Fahmi al-Jarjawi. Majiyar kungiyar kula da fararen hula a gazar ta bayyana cewa yahudawan kai hare haren a safiyar yau litinin a lokacinda suke barci. Labarin ya kara da cewa a cikin wadanda yahudawan suka kashe a Gaza, akwai Mohammad Al-kasih...
Shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar Burtaniya ya bayyana cewa HKI tana yakar Falasdinawa a Gaza ne a madadin gwamnatin kasar tunda har yanzun gwamnatin kasar Burtaniya tana ganin gwamnatin HKI tana kare kanta daga mayakan Hamas, kuma bata daukar abinda HKI take yi a Gaza, kissan kiyashi ne. Badenoch shugaban jam’iyyar ‘ Conservative’ ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Sky News dake birnin London a jiya Lahadi. A lokacinda aka tambaye shi idan ya yarda da maganar Banyamin natanyaho kan cewa hamas yan ta’adda ce, kuma yana kokarin kwace gaza da shafi yan ta’adda ne, sai shugaban Conservative ya ce banzo nan don binciken kalmomin Natanyahu ba. Abinda nake son bada sanarwansa shi...
Kasar Uganda ta dakatar da aikin hadin giuwa na soje dake tsakanin kasashen biyu, saboda sukan da jakadan kasar Jamus yayiwa dan shugaban kasar yake kuma goyon bayan wata jam’iyyar adawar kasar. Shafin yanar gizo na labarai Afirka News ya nakalto jami’iyyar shugaban kasar Uganda People’s Defence Forces (UPDF) tana bada rahoton cewa Jakada Schauer na kasar Jamus a Kamfani ya halarci wata taro tare da wata jam’iyyar adawa inda yake sukar dan shugaba Uwere Musevene jan yadda jam’iyyarsu take gudanar da harkokin shugabancin kasar. Kasashen Uganda da Jamus sun dade basu sami irin wannan rashin jituwa ba. Kuma harkokon kasuwanci tsakanin kasashen biyu yakai dalar Amurka miliyon $335 a shekara 2023 kadai. Sai dai muna iya cewa wannan ba...

Ministan Harkokin Wajen Iran Yace Faransa Bata Da Yencin ZarginWata Kasa Dange Da Kare Hakkin Bil’adama
Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Bayan matsayinta a kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan yana maida martani ne ga tokwaransa na kasar Faransa Jean-Noel Barrot ya fada bayan da wani ba’irane ya sami lambar yabo mafi girma a gasar fina-fina mafi girma a duniya da ake kira ‘ Cannes Film Festival’ . Jafar Panohi dan kasar Iran ya lashe kyauta mafi girma a gasar ne saboda wani film da ya yi, wanda ya bashi makin samun wannan kyautar. Aragchi ya bayyana cewa, Faransa...
05-Majiyar Sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar a safiyar yau ma sun cilla makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) na HKI. Inda faduwar makaman ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama a tashar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Yahyah Sari yana fadar haka a yau, ya kuma tabbatar da cewa, makamin samfurin Bilistic ya sami bararsa kamar yadda aka tsara. Ya ce faduwar makamin ya dakatar da dukkan ayyukan sauka da tashin jiragen sama a wannan tashar banda haka cilla makamai ya sa miliyoyin yahudawa rugawa zuwa wararen buya. Tun watan maris da ya gabata ne sojojin yahudawan sahyoniyya suka sake farfado da yaki...
Daliget sun tayar da jijiyoyin a wurin taron haɗakar siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi domin fafatawa da shuagaban kasa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. Ana tsaka da taron Kungiyar Tuntubar Siyasa ta Kasa Reshen Arewa a Abuja ne hayaniya ta kaure bayan tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya sanar da wanda suna daliget da zai wakilci Jihar Jigawa. Rashin gamsuwar sauran daliget din jihar dadi ba suka tayar da jijiyoyin wuya, inda suka hau kan mumbari suka dauke wanada aka ayyanan suka hana shi magana da yawunsu. Daba bisani an yi nasarar shawo kan rikicin, inda aka zabi dan...
Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da furucin ministan harkokin wajen kasarsa da ya shafi batunci ga Iran. Muhammad Tanhaye wanda shi ne mai kula da bangaren kasashen turai a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, ya bukaci Karin bayani a hukumance dangane da abinda ministan harkokin wajen Faransa Jean Nuel Barrot ya fada akan Iran a yayin bikin ” Cannes” na fina-finai a da wani daga cikin fina-finan Iran ya sami kyauta. Har ila yau, Tanhaye ya yi suka akan yadda gwamnatin ta Faransa ta yi amfani da bikin fina-finan domin yada manufofinta na siyasa. Haka nan kuma ya ce; Faransa wacce kasa ce...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya danage da zagayowar cikar shekaru 25 daga korar ‘yan sahayoniya daga kasar Lebanon da gwgawarmaya ta yi, ya jaddada cewa; “Gwagwarmaya ba za ta yi shiru ba, ba kuma za ta mika wuya ba, tana yin hakuri ne saboda ta bayar da Karin lokacin,don haka ya zama wajibi a yunkura.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Gwamnati ce mai hakkin ganin an...
Hare-haren sojojin HKI a yankin Gaza sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 57 Majiyar Asibiti a yankin na Gaza,ta sanar da cewa sojojin mamayar sun kai hari ne akan makarantar ” Fahmi al-jarjawi” wacce take a yankin al-Darj’ a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 25.” Harin ya yi sanadiyyar konewar gawawwakin shahidan da kuma tashin gagarumar gobara a makarantar da ‘yan hijira Falasdinawa suke ciki. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa ya haura dubu 53 da 939. Haka nan ma’aikatar ta ce; Wadanda su ka jikkata kuwa a wannan tsakanin sun kai dubu 122 da 797. Sojojin HKI sun shelanta yaki ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma. A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci-gaban kasa. Sai dai a Najeriya, a wasu lokutan akan zargi ’yan majalisa da zama ’yan-amshin-Shata. Ko me ya sa haka? Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya? NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Baki a Nijeriya da abokansu Sinawa sun nishadantu yayin da suka halarci taron gabatar da fasahar hada shayi ta 2025 da al’adun Yaji, wanda aka yi jiya Asabar a Abuja babban birnin kasar. An gudanar da taron ne a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin da hadin gwiwar cibiyar raya al’adu ta lardin Zhejiang, wadda ta samu wakilcin masana hada shayi da ‘yan wasan kwaikwayo na Yue Opera da masu wasan kayan Pipa. Taron ya samu halartar mutane daga dukkan bangarorin rayuwa da suka hada da jami’an diplomasiyya da na gwamnati da malamai da daliban sakandare da ‘yan wasa da manema labarai da masoya al’adun shayi ta kasar Sin. An kuma gabatar da fasahar rubutun gargajiya ta Sin da...
Adadin “nau’i uku na manyan kamfanoni 500” da suka halarci bikin baje kolin a bana ya kai 114, wanda ya kai kashi 55.6 bisa dari. Daga cikin su, akwai kamfanoni 61 dake cikin manyan kamfanoni 500 na duniya, adadin da ya karu da kashi 74.3 bisa dari kan na baje kolin da ya gabata. (Bello Wang, Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An shiga ruɗani a unguwar CBN Quarters da ke cikin birnin Sakkwato, inda wani ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu mai suna Ayman Abubakar, ya ɓace, amma daga bisani aka gano gawarsa a cikin ramin sokawe. Ana zargin wani maƙwabcin iyayen yaron da wata mata da aikata wannan ɗanyen aiki. An kashe matashi yayin rikici a ƙauyukan Kano Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole Ƙngiyoyi da ke fafutukar kare haƙƙin yara da martabar bil adama sun bayyana wannan kisa a matsayin babban cin zarafi. A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, shugaban NACTAL na ƙasa Abdulganiyu Abubakar, Usman Ahmad daga ƙungiyar kare haƙƙin yara, da Rabi’u Bello Gandi shugaban hukumar kare...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya bayyana cewa: Suna yin aiki ne bisa maslahar kasa, kuma ba su yarda da karbar umarni daga waje ba Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, ya ce Iran tana dogara ne kan manufofinta na kasa da kuma manufofinta na koli, kuma ba zata yarda wasu kasashen waje su tsara mata ko bata umurnin abin da zata yi ba. Kalaman na Islami sun zo ne a lokacin da yake halartar wani taron juyayin tunawa da shahadar marigayi tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian a jiya Asabar, wanda ya samu halartar manyan jami’an siyasa da na diflomasiyya. A cikin jawabin nasa, Islami ya jaddada cewa asalin kasa da dabi’unta sune abubuwan...
Mene ne dalilin da ya sa Amurka da Isra’ila suke barazanar jefa bama-baman nukiliya a Gaza? Masanin siyasa kuma mai sharhi Abdel Bari Atwan ya rubuta labarin game da barazanar da Amurka ta yi na kai wa Gaza hari da makamin nukiliya, yana mai cewa; “Domin dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican Randy Fein ya yi kira da a kai hari kan Zirin Gaza da bama-baman nukiliya, kwatankwacin abin da kasarsa ta yi a Hiroshima da Nagasaki na Japan, a karshen yakin duniya na biyu, da kuma samun wanda ya yaba masa a gwamnatin Shugaba Donald Trump, wannan shi ne kololuwar ta’addanci, rashin mutuntaka, da kishir ruwan zubar da jini a duniya daga jagororin da ke da’awar kare hakkin bil’adama...

Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Birnin Tul-Karam Na Falasdinu
Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tulkaram da sansanoninsa da ke gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tulkaram da sansanoninsa a rana ta 119 a jere, da kuma sansanin Nour Shams a rana ta 106, a daidai lokacin da sojojin suke ci gaba da tsananta kai hare-hare kan yankuna Falasdinawa da kuma kma su tare da yinawungaba da su zuwa wuraren da baa san ko’ina ba ne. Da sanyin safiyar Lahadi ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki gidan Essam Odeh, sakataren kungiyar hadin kan iyalan shahidai da ke yankin kudancin Falasdinu, inda suka kama shi da diyarsa Sarah mai shekaru 20...

‘Yar Majalisar Dokokin Ireland Ta Yi Suka Kan Shugabannin Turai Tare Da Neman Afuwa Daga Falasdinawa
‘Yar majalisar dokokin Ireland ta yi kakkausar suka kan shugabannin Turai tare da neman afuwa daga Falasdinawa Tana jaddada cewa: Muggan makaman gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da lakume rayukan fararen hula a zirin Gaza. Sannan a wani sabon kisan kiyashi, an kashe Falasdinawa 7 a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza. A wani kisan kiyashi kuma jami’an tsaron farar hula a Gaza sun sanar da mutuwar yara tara da suka kone kurmus a wani harin da sojoji mamayar Isra’ila suka kai kan Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza da aka killace. An kuma kashe wani Bafalasdine tare da raunata wasu a wani harin da...