2025-06-06@05:29:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5387
«a iskar gas»:
Kafafen watsa labarun kasar ta Zambia da kuma jam’iyyarsa ta “PFT” sun sanar da cewa; Tsohon shugaban kasar ya fadi ne a lokacin da yake motsa jiki a gidansa dake birnin Lusaka. Bayan da aka kai shi asibitin soja na “Maina Soko” likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu. Gwamnatin kasar ta Zambia ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar, tare kuma da shelanta ranakun alhini na kasa. Shi dai Lunga ya jagorancin kasar ta Zambia ne daga 2015 zuwa 2021 da ake yabonsa da gina muhimman cibiyoyi a kasar, sai dai kuma hakan ya bar kasar da dimbin bashi. Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da lokacin da za a yi jana’izar tsohon shugaban kasar ba.
Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano ta ce ta gurfanar da mutum 29 da ta kama bisa zarginsu da hannu a kashe DPO na garin Rano da ke jihar, CSP Baba Ali da sauran laifuffuka. Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, inda ya ce an gurfanar da su ne a gaban kotun majistare mai lamba 20 da ke Nomansland a Kano. Gurfanarwar dai ta biyo bayan kammala bincike kan kisan wanda ya ja hankalin mutane a ciki da wajen jihar. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah Sojoji sun dakile hare-haren ‘Yan Boko Haram biyu a Borno Kiyawa ya ce 14 daga cikin mutanen,...
Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata kasar Amurka ta daidaita matsayinta kan batun Taiwan da idon basira, kada masu neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin su tura Amurka da Sin cikin rikici. A nasa bangare, shugaba Trump na Amurka ya ce, yana matukar girmama shugaba Xi Jinping, kuma huldar dake tsakanin Amurka da Sin tana da muhimmanci. Ya ce kasar Amurka ta yi farin cikin ganin karuwar tattalin arzikin kasar Sin. Kana, hadin gwiwar dake tsakanin Amurka da Sin za ta ba da gudummawa ga kasa da kasa. Ya ce a nan gaba kuma, kasarsa za ta ci gaba da bin manufar kasar Sin kasa daya tak a duniya. Bugu da kari, ya ce kasashen...
A yau Alhamis, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tattauna da shugaban Amurka Donald Trump bisa bukatar hakan da Trump ya gabatar. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Alhamis, ma’aikatar ciniki ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci kasar Amurka da ta yi watsi da amfani da batun tsaron kasa barkatai wadda ta mayar da shi mai gamewa gaba daya da kuma wuce gona da iri, kana ta hada kai da dukkan bangarori wajen kiyaye tsarin cinikayya tsakanin sassa daban-daban. A wani taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar, He Yongqian, ta bayyana hakan a lokacin da aka bukaci ta tofa albarkacin bakinta game da matakin da Amurka ta dauka na kara haraji kan karafa da holoko da kayayyakin da ake sarrafawa da su wadanda ake kaiwa kasar, daga kashi 25 zuwa 50 cikin dari. Ya ce...
Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna tace shirin Bus Rapid Transit BRT da ake shirin kaddamarwa zai taimaka matuka wajen rage kudaden sufuri ga mazauna jihar, da zarar an fara aiwatar da shi. Daraktan Hukumar, Injiniya Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kada Hive da ke Kaduna. An shirya taron ne domin wayar da kan jama’a game da shirin BRT, sannan matakan da aka dauka ya zuwa yanzu. Taron an gudanar da shi ne domin sauraron ra’ayoyin al’umma kan yadda za a aiwatar da shi cikin nasara. Injiniya Inuwa ya bayyana cewa tsarin BRT zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa...
A yayin da al’ummomi a fadin Najeriya ke shirin Sallar Idi, daya daga cikin manya-manyan bukukuwan Musulunci, Kano, cibiyar al’adun arewacin Najeriya, na shirin gudanar da wani biki Mai kayatarwa wanda Malta Guinness, ɗaya daga cikin samfuran kayan sha Mai dandanon Dadi da yayi fice a ƙasar nan, zai ƙaddamar da wannan biki na kwanaki uku da nufin zurfafa ruhin al’umma ta hanyar raba alheri da kyaututtuka ga masu rabo. An tsara shirin ba a matsayin nunin tallace-tallace ba amma a matsayin taron nunin al’adu da ke tattaro irin kade-kade, da wasan kwaikwayo na gargajiya don nishadantarwa. Za’ayi wannan ruguntsumi ne, a Dakin taro na Ado Bayero Hall, dake Kano, daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Yuni, 2025. A...

Ma’aikatar Harkokin Waje: Kasar Sin Ta Kasance Gwarzuwa Wajen Samar Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
Yau ce ranar muhalli ta duniya. An yi sharhi a baya cewa, a cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta jagoranci ayyukan samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a duniya, da samun gagaruman nasarori a fannin raya makamashin da ake sabuntawa da sauran fannoni, da taimaka wa sauran kasashe masu tasowa wajen aiwatar da ayyukan sauyin makamashi. Yayin da yake amsa tambayoyi a wurin taron manema labaru da ya gudana a yau, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance mai fafutukar neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a ko da yaushe, kana mai taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi ta wannan fuskar...
A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025. Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro, tare da haɗin guiwar sauran jami’an tsaro inda suka nufi wurin da nufin daƙile fashin. Da isarsu wurin, suka fara musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu wanda hakan ya janyo da dama daga cikin ‘yan fashin suka gamu da raunuka na harbin bindiga sannan an harbe daya ya mutu nan take. LEADERSHIP ta rawaito cewa, an miƙa gawar Shagari ga...
“Al’ummar kasa da kasa da yawa sun sauya ra’ayinsu mai kyau game da Amurka zuwa mummunan ra’ayi, yayin da yawan masu nuna kauna ga kasar Sin ya karu.” Wani bincike da kamfanin bincike na Morning Consult na Amurka ya fitar kwanan nan ya nuna cewa, har zuwa karshen watan Mayu, yawan al’ummar duniya dake nuna kauna ga Amurka ya ragu zuwa -1.5, yayin da adadin ya karu zuwa 8.8 ga kasar Sin. Ko da yake sakamakon ya fito ne daga hukumar bincike guda daya kawai, amma yana da ma’ana sosai wajen yin kashedi, idan aka yi la’akari da cewa binciken ya shafi kasashe da yankuna fiye da arba’in, inda akasarinsu su ne muhimman abokan huldar Amurka a fannin tattalin arziki...

Sabbin Matakan Amurka Game Da Masu Shiga Kasar Sun Ci Karo Da Ikirarinta Na Mutunta Hakkokin Bil Adama
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gidauniyar ta kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammed Aliyu Shaaba, inda wakilan fadar suka yi maraba da tawagar wakilan gidauniyar tare da jinjina taimako da goyon bayan da aka nuna musu a wannan hali da suke ciki na ibtila’i. Kamar yadda Babban daraktan yankin, Musa Aliyu ya bayyana, gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki ta kai taimakon kuɗi domin tallafawa waɗanda suka tsira da masu taimaka musu. Sannan ya yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da ɗaiɗaikun mutane da su taimakawa al’ummar garin Mokwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sabon injin jirage masu saukar Ungulu kirar kasar Sin samfuin AES100, ya samu shaidar amincewar inganci da damar sayar da shi a kasuwanni, matakin da ya kafa harsashin bunkasa samar da kayayyakin bukata a fannin kirar ababen hawa masu tashi kurkusa da kasa. Kungiyar makera injuna ta kasar Sin ce ta sanar da wannan ci gaba a yau Alhamis, inda ta ce sabon samfurin injin shi ne irinsa na farko da aka kera a Sin bisa fasahohin kasar na kashin kai, wanda ke da fasahar karfin “kilowatt 1,000”, ya kuma yi nasarar cika darajar karko ta kasa da kasa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
A wani hari ta kasa da na sama, rundunar sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wasu manyan hare-haren ta’addanci guda biyu a ranar Alhamis a Jihar Borno. Dakarun sun kashe da dama daga cikin maharan tare da kwato tarin makamai da alburusai. Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano Mahajjata kusan miliyan biyu na hawan Arfa a Saudiyya Rahoton da hukumar tsaron sojan Najeriya suka fitar na nuna cewar, dakarun sojan rundunar ta OPHK an kaddamar da hare-haren ne a wasu wurare daban-daban na sojoji a Buratai da ke karamar hukumar Biu da kuma Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam. An bayyana cikakkun bayanan hare-haren a cikin wata sanarwa da Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na...
Hakika abin da suke yi shi ne kokarin cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta sanya, na taimakon yankunan karkara na kasashen Afirka wajen samun hakikanin ci gaba, inda za a kyautata muhallin rayuwar mutane, da fitar da su daga kangin talauci, maimakon samar da karuwar adadin tattalin arziki kawai. Kana a bayan manufar ta kasar Sin akwai wani tunani mai muhimmanci da kasar ta rike, wato na “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. A ganin kasar Sin, dukkan al’ummun kasashe daban daban suna zama a duniya daya, don haka suna da makomar bai daya. Saboda haka ya kamata a lura da bukatun sauran kasashe, da tabbatar da ci gaban mabambantan kasashe na bai daya, yayin da...
Wani matashi dan shekara 33 mai suna Muhammad Sagir ya rasa ransa bayan ya fada rijiya a unguwar Kawon Alhaji Sani da ke karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano. A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, mataimakin jami’in kashe gobara (ACFO) Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:42 na rana a ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025. Tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Jibril Aminu, ya rasu Ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga wani mai suna Sabi’u Muhammed, inda ya sanar da su lamarin. “Nan da nan aka tattara tawagar ceto daga hedkwatar hukumar zuwa wurin.” “Da isowar jami’an, ma’aikatan sun gano wani mutum guda...
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiyan ya zanta ta wayar tarko tare da shugaban kasar Masar abdulfatta Assisi, inda suka taya juna murnar tahowar sallar Babba. Shugaban ya bayyana cewa kasar Iran tana da tsari ta makobta farko, don haka ne take, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma musamman kasar ta Masar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wata wayar tarho ta daban shugaban ya zanta da Yarima mai jiran gadon sarautan saudiya kuma Firay ministan kasar Muhammad bin Salman inda ya taya shi murnar zagayowar ranar Sallah babba sannan suka yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu. Duk tare da bambancin ra’ayin da kasashen biyu suke da shi dangane da yadda za’a warware...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai bawa jagoran Juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya sake tabbatar da cewa kasar Iran ba zata dakatar da aikin tace makamacin Uranium kamar yadda gwamnatin Amurka take so ba. Sannan ya kara da cewa kasar tana kokarin sake gabatar da wata shawara daban ga kasar Amurka. Ali shamkhani ya fadawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon a wata hira da ta hadasu a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu suna rubutun wata shawagara ga gwamnatin Amurka dangane da hakan. Shamkhani ya kara da cewa wasikar da Amurka aikawa Tehran bata ambaci batun daukewa kasar takunkuman tattalin arziki ko kadan ba. Ya kuma soki kasar ta Amurka a wasikar da...
Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran. Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango. Kazem Jalali ya bayyana a yau Alhamis kan cewa kasar Rashe ce kasa tilo wacce ta zuwa jarin dalar Amurka biliyon $8 a bangaren gas da man fetur. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe dala $ 5bl daga cikinsu. Banda haka zata kashe kudade don kammala layin dogo wacce ake kira hanyar Arewa zuwa Kudu. Banda haka Rasha zata fara tura danyen man fetur daga Rasha zuwa Iran don...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qolibof ya bayyana cewa kungiyar BRICS wata dama ce ta kaucewa danniya da babakeren da Amurka take kudaden sauran kasashen duniya. Qolibof yana bayyana haka ne a lokacin ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar Brazil Dowi Alku-Lomubre a gefen taron shuwagabannin majalisun dokokin kungiyar BRICS wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Brazia na kasar Brazil. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin Iran yana fadar cewa kasashen Iran da Brazil suna da fahinta iri guda dangane da yenci da kuma zama yentacciyar kasa. Don haka tare da wannan ana iya gina dangantaka ta bunkasar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu tare da wannan fahintar. Qolibof ya kara...
Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya Laraba yana dan shekara 85 a duniya. Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an yi masa sallar Jana’iza a babban masallacin kasa a Abuja a yau Alhamis. Sannan za’a maida shi garinsa Song na jihar Adamawa inda za’a rufe shi. A rayuwarsa dai Farfesa AAmin likitan zuciya ne, sannan malami da shugaba Jami’ar Maiduri na Jahar bornin a wani lokaci, ya kuma karantar. Har’ila yau Farfesa Amin ya rike kujerar Ministan ilmi da manfetur, sannan jakadan Najeriya A Amurka...
Daraktan hukumar kashe gobara a jihar, Alhaji Sani Anas ya bukaci jama’a da su sanya ido sosai, musamman ganin yadda bukukuwan Sallar layya ke gabatowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan ya bayyana gabatarwar da C-WINS ta yi a matsayin mai motsa zuciya kuma mai cike da ƙarin haske. Ya ce: “A yau na koyi abubuwa da dama. Yawancin ’yan Nijeriya, kamar ni kai na, sun san cutar masassarar cizon sauro amma ba su san da ƙyandar jamus da mummunan tasirin ta ba. “Gaskiya batun cewa za a iya haihuwar yara makafi, kurame ko kuma masu nakasar zuciya sakamakon kamuwa da ƙyanda daga uwa a lokacin ɗaukar ciki babbar masifa ce da ya kamata mu haɗa kai mu daƙile ta.” Ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta haɗa hannu da sauran hukumomin da suka dace wajen tsara saƙonnin faɗakarwa da shirye-shiryen ilimantar da al’umma. Ya kuma shawarci tawagar da su...
A wani cigaba makamancin haka, dakarun Mallam Fatori suma sun daƙile wani yunƙurin hari daga ‘yan ta’adda da suka zo ta wurare daban-daban. Ya ce bayan sa’o’i na musayar wuta, dakarun sun bi ‘yan ta’addan da suka tsere, inda suka hallaka da dama, wasu kuma suka gudu da raunukan harbin bindiga. An kuma kwato muggan makamai da dama kamar bindigogi AK-47, da bindigar kakkaɓo jirgi (RPG), da sauran kayayyakin yaƙi. Yanzu haka Sojojin na ci gaba da sintiri a yankin, tare da goyon bayan jiragen sama da na leƙen asiri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Ƴansanda sun kara da cewa za a ci gaba da sanar da jama’a yayin da bincike ke ci gaba da tafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon malamin makaranta, dan siyasa kuma ambasada, Farfesa Jibril Aminu ya rasu yana da shekara 85. Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar, kuma Kwamishinan Gidaje da Raya Birane na jihar Adamawa, Hon Abdullahi Prambe ma ya tabbatar da haka. Ya ce, “Ba za a taba mantawa da gudunmawar shi ba musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma shugabanci.” Wata majiya da ke da kusanci da mamacin ta ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a Masallacin Kasa da ke Abuja. Sai dai kawo yanzu, iyalai da ’yan uwan mamaci bas u fid da cikakken bayani kan yadda za a yi jana’izar mamacin ba ko kuma musabbabin rasuwarsa. An haifi Farfesa Jibril...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Babu makawa Amurka abokiyar laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa ne a Gaza A safiyar yau Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da kira ga mahajjatan dakin Allah. Yana mai jaddada cewa; Aikin Hajji ba kamar sauran tafiye-tafiye ne da ake nufi kasuwanci, yawon bude ido, ko wasu abubuwa daban-daban ba, wadanda wani lokaci sukan hada da ibada ko ayyukan alheri. Motsa jiki ne na ƙaura daga rayuwar da ta saba zuwa rayuwar da ake so. Rayuwar da ake so ita ce rayuwar tauhidi, wacce ta kunshi muhimman abubuwa masu muhimmanci na dindindin kamar: dawafi akai-akai a kusa da kusurwoyin gaskiya, da jajircewa a tsakanin...
Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun da wuri, musamman ganin yadda aka ce ta bazu zuwa ƙasusuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mahajjata aikin hajjin bana suna ci gaba da tururuwa zuwa tsayiwar Arafat a yau Alhamis Mahajjata na ci gaba da tururuwa zuwa Arafat domin gudanar da muhimmin rukunnan aikin Hajji. Mahajjata suna gudanar da ranarsu tun daga ketowar alfijir har zuwa bayan sallar isha’i a filin Arafat, bayan sun gudanar da ibadar ranar Tarwiyah, wadda mahajjaci ya yi a Mina, yana taqaita salloli ba tare da hada su ba. A safiyar rana ta goma, mahajjata za su sake komawa Mina don jifan Jamarat al-Aqaba, kafin su yi aski ko saisaye, su yanka dabbar layya, Sannan su nufi dakin Ka’aba domin yin Tawafin Hajji.
Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filin jirgin saman Lod da ke Jaffa da aka mamaya da jiragen sama biyu marasa matuka ciki Sojojin Yemen sun sanar da kai wani farmakin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma nuna tsananin Rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a zirin Gaza. Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, inda ta ce farmakin da rundunar sojin saman Yemen ta kai da jiragen saman yaki marasa matuka ciki kirar Yaffa guda biyu, ya samu nasarar cimma burin da ake bukata. Rundunar...
Al’ummar Musulmin yankin Kudancin Kaduna, sun shirya taron addu’a na musamman a sakatariyar karamar hukumar Sanga da ke Gwantu, Jihar Kaduna, kan neman zaman lafiya. A yayin taron dai Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya na dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin kasar tare da yin kira ga ’yan kasa da su mara wa kokarin hadin kai da ci gaban kasa baya. Janar Musa wanda Rear Admiral Ibrahim Aliyu Shettima ya wakilta, ya ce zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaba da bunkasar kasa. Ya bukaci ’yan Najeriya baki daya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, da su bayar da gudummawarsu wajen gina kasa. Barazanar Yajin Aiki:...
Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata. A makon da ya gabata, rundunar ta kashe aƙalla ‘yan ta’adda 20 a wani samame da aka kai Garin Mani, da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara. Wannan farmaki ya biyo bayan luguden wuta da aka riƙa yi wa ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka. Shugaban sojin ya ce motsa jiki abu ne da ya zama dole ga dukkanin ma’aikata, kuma babu wanda zai samu ƙarin girma ba tare da...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya. Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027. Barazanar Yajin Aiki: Abuja da wasu jihohi 3 za su faɗa cikin duhu A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Saraki, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu na PDP, ya faɗi haka ne a wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Ilorin. Ya amince cewa wasu sun bar jam’iyyar, amma mutane da dama suna ci gaba da shigowa jam’iyyar. “PDP ce kawai jam’iyyar adawa ta haƙiƙa,” in ji shi. “Eh, muna fuskantar ƙalubale, amma muna...
Sannan Annabi (SAW) ya ce “Babu wata rana mafificiya a wajen Allah kamar Ranar Arfa”, haka nan kuma ragowar kwanakin da ke cikin 10 na farkon watan nan, Ranar Arfa ta ninninka su falala. Don a wannan ranar ce Annabi (SAW) ya ce Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya (Kamar yadda ya dace da Shi (SWT). Ire-iren waɗannan Hadisan ne ake ce musu “Mutashabihai”. Ana kawo bayanansu ne ta yadda za a yi mana kwatance amma ba kamar yadda ma’anar lamarin yake a hulɗar da ke tsakaninmu ba. Wajibi ne yin imani da Hadisan don rashin yin imani da su ridda ne, amma ba kuma a riƙa fassarawa da yadda ƙananan ƙwaƙwalenmu ke ɗaukawa ba. Duk wanda ya ce zai...
Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata. Sun kuma ce an ƙi biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka wajen samar da kuɗin...
Mazauna unguwar da asibitin kula da ido ta kasa yake wato Mahuta da ke jihar Kaduna sun amince da Gwamna Uba Sani ya zarce karo na biyu, biyo bayan warware takaddamar filaye da aka dade ana yi wanda ya yi sanadiyar rushe gidaje da dama a gwamnatin da ta gabata. Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta hannun hukumar kula da bayanan kasa ta jihar Kaduna (KADGIS) ta bayar da shedar mallakar filayen sama da 300 ga al’ummar da rusau da aka yi a zamanin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya shafa. Da yake jawabi a madadin mazauna yankin, Kanar Haruna Idris Zaria mai ritaya, ya yabawa Gwamna Sani bisa abin da ya bayyana a matsayin tsarin sa...
Amurka ta sake hana kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kiran tsagaita bude wuta da kuma kai agajin jin kai a Gaza. Wannan hawa kujerar na-ki shi ne irinsa na farko na sabuwar gwamnatin Trump kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan ci gaba da yakin da takeyi a gaza dama hana shigar da kayan agaji. Daftarin kudurin da aka gabatar wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba ya bukaci “a gaggauta tsagaita wuta na dindindin” da kuma sakin wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba. Kudirin da kasashe 10 wadanda ba mambobin kwamitin na dindindin ba suka gabatar, ya samu sahalewa...
Yau Alhamis 9 ga watan Zul Hijja, ita ce ranar da miliyoyin Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudiyya ke hawan Arfa, wato daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji. Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya kunshi dawafi da zaman Mina da tsayuwar ta Arfa da kuma jifar shaidan. A washegarin ranar ne kuma sauran Musulmai a duk fadin duniya su ke shagulgulan Sallar layya. Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramtawa kasashen duniya 12 shiga Amurka a wani mataki da ya ce na kare kasar ne daga “yan ta’adda na kasashen waje. Wata takarda da fadar White House ta fitar a ranar Laraba ta ce haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yuni, ya shafi kasashen Afghanistan, Burma, Chadi, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, da kuma Yemen. Baya ga hakan akwai wasu kasashe bakwai su ma da aka gindawa wasu sharudda da suka hada da Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da kuma Venezuela. A cewar Amurka matakin bai shafi mutanen da balaguron su zuwa kasar ke da amfani ga muradun kasar ba.” Haka ma...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah. A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa Sai dai masana sun ce wannan abu na iya haifar da matsaloli ga lafiya da kuma gurɓata muhalli. Wannan shi ne abin da shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kai, yayin da ake Bikin Ranar Muhalli ta Duniya kwana ɗaya kafin Babbar Sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
Kasar Sin ta ci gaba da yin tsayin daka kan matsayinta na guje wa yin katsalandan musamman a Afirka. Ba kamar kasashen yammacin duniya da suka tsunduma cikin harkokin soji da makamai ba, kasar ta mai da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki, kamar zuba jari mai yawa a kasashen Afirka da dama ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba. Wannan tsarin ya taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a yankin. Kazalika, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sulhunta rikici a yankin Asiya, inda ta samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici da juna maimakon samar da mafita ta hanyar karfin soja. Sulhunta tsakanin Saudiya da Iran a shekarar 2023, tare da daidaita harkokin diflomasiyya...
Da safiyar yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Belarus Aleksandr Lukashenko a nan birnin Beijing. Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya sake taya takwaran nasa na Belarus Aleksandr Lukashenko murnar nasarar yin tazarce. Xi ya ce, Sin na daukar huldar sassan biyu da muhimmanci, kuma tana raya ta bisa hangen nesa kan manyan tsare-tsare, tare da fatan kara hadin gwiwa da Belarus, don gaggauta bunkasa huldarsu, da ma cimma moriya tare cikin hadin gwiwa. Ya kara da cewa, dole ne kasashen biyu su kara hadin kai, da marawa juna baya karkashin kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da MDD da SCO da sauransu, don taka rawarsu tare wajen dakile babakere, da kiyaye...
Wasu direbobin manyan motoci sun rufe hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta da ke Jihar Kogi domin nuna fushinsu bayan jami’an tsaro sun harbi ɗaya daga cikinsu da kuma mataimakinsa. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da jami’an tsaro suka harbi mutanen biyu saboda sun ƙi tsayawa a wajen binciken da aka tsayar da su. Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agaji Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano Sai dai, babu wanda ya mutu sakamakon harbin. An garzaya da su asibiti domin ba su kulawar gaggawa. Hakan ne, ya sa sauran direbobin suka fusata, suka toshe bakin gadar Ganaja da ke babbar hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta. Sun ƙi...
Har ila yau, ya bayyana cewa, bangaren tekun kudancin kasar Sin gaba daya yana cikin kwanciyar hankali kuma babu wata matsala game da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da na sama da dukkan kasashe ke morewa bisa doka. Ya ce, a ko da yaushe, kasar Sin na dagewa kan amfani da tattaunawa da tuntubar juna wajen warware sabani da magance abubuwan da aka sha bamban a kai game da teku yadda ya kamata a tsakanin kasashen da abin ya shafa kai-tsaye, bisa mutunta hakikanin tarihi na gaskiya. Haka nan, ya kamata kasashen da ba na yankin ba su mutunta kokarin da kasashen yankin suke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, maimakon haddasa fitina...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta shirya tsare-tsaren tsaro domin ganin an yi Sallar Idi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa za a tura ’yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa filayen Idi, Masallatai, da wuraren taro domin kula da tsaro da zirga-zirgar jama’a. Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agaji Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano Za a sanya ido sosai a manyan hanyoyi musamman waɗanda ke kai wa zuwa wuraren sallah, domin rage cunkoso da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a. An ware ƙofofin shiga da fita a filayen Sallah domin a riƙa duba mutane da kayan da suke ɗauke da...

Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An gano gawar yara bakwai a yankin Mokwa, da ke Jihar Neja, bayan ambaliyar ruwa da ta afka wa garin mako guda da ya wuce. Yawan adadin waɗanda suka rasu kawo yanzu ya kai mutum 160, amma wasu jami’ai sun ce za a iya gano gawar sama da mutum 200. Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan Sanda Ambaliyar ta kuma tafi da motar haya mai kujeru 18 ɗauke da fasinjoji. Kawo yanzu, bayan kwana shida da faruwar ambaliyar, ba a ga motar ko wani daga cikin fasinjojin ba. Wani mazaunin garin, Baba Abu, ya ce: “Direban bai nemi ƙetare ruwan ba. Ya...

Babban Sauyi Da Ba a Taba Ganin Irinsa Ba a Karni Guda: Alkiblar Da Sin Take Bi Wajen Samun Bunkasuwa
Yanzu haka an shiga shekaru 10 na zagaye na 2 na karni na 21, kuma duniya na fuskantar kwaskwarima, da sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a tarihi, wanda ya zarce tunanin da ake yi. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana kwaskwarimar da ake fuskanta a matsayin “Babban sauyi da ba a taba ganin irinsa ba cikin karni daya”, wanda ya hada da kyautatuwar karfi tsakanin mabambantan kasashe da ya zarce zaton da aka yi a baya, matakin ya tabbatar da alkiblar da Sin za ta bi, har ma ya kunshi sauye-sauyen al’adu da wayewar kan Bil Adama. Yau za mu ganin ma’anar maganar Xi Jinping kan wannan batu dake jawo hankalinmu. Daga kanmu, magana ta...
Wata kotu da ke unguwar Noman’s Land a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare fitaccen ɗan TikTok, Abubakar Kilina, a gidan gyaran hali har zuwa ranar 17 ga Yuni, 2025. Wannan hukunci ya biyo bayan tuhumar da Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta shigar da ke zargin sa da aikata halaye da suka saɓa wa tarbiyya da al’adu Hausawa. Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan Sanda Ba zan yi musayar yawu da yara ba — Martanin Amaechi ga Wike Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na yunƙurin hukumar na daƙile yaɗuwar rashin ɗa’a a kafafen sada zumunta, musamman TikTok. “Mun ƙudiri aniyar daƙile duk wani abin...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran siyasa da yankin kudancin Asiya tare da kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto aragchi yana cewa dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hizbullah dangane ce wacce ta shafi yankin kudancin Asiya gaba daya. A nashi bangaren shugaban kungiyar Hizbullah sheikh Naem Kassem ya godewa JMI ta irin tallafin da take bayarwa ga kungiyoyi da kasashen kawancen masu gwagwarmaya a yankin wadanda suka hada da Falasdinawa da Lebanon da sauransu. Aragchi ya kara da cewa Iran a shirye take ta taimakawa kasar Lebanon a...
Jami’an Yansanda masu kula da ayyukan ta’addanci da kuma hana aukuwarsu a nan Iran sun sami nasarar kama wasu yan kungiyar ISIS 13 a duk fadin kasar daga ciki har da shugabansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Saeed Montazer al-Mahdi kakakin rundunar FARAJA mai kula da fada da yan ta’adda yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa yan ta’addan su 13 daga cikin har da shugabansu, sun kuduri anniyar kai hare-hare a cikin Jama’a su kuma kashe mutane a wasu tarurrukan da aka gudanar a kasar nan. Labarin ya kara da cewa an kama yan ta’addan na ISIS a biranen Tehran, Qum, Esfahan da kuma Albus. Kuma an kama tare da su kayakin...
A jiya Talata ce babban zaureb MDD wanda yake da mambobi 188 a majalisar a jiya Talata sun zabi kasashen Bahrain, Colombia, Democradiyar Congo, Latvia,da Liberia don aiki a kwamin tsaro na Majalisar har zuwa shekara 2027. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afroca News” yace ana gudanar da zaben ne a cikin zagaye guda kacal na zabe. Labarin ya kara da cewa kasashen zasu fara aiki a bangarin majalisar wanda yake da alhakin tabbatar da sulhu da zaman lafiya a duniya ne daga cikin watan Jenerun shekara ta 2026. Har zuwa karshen watan Dcemba na shekara ta 2027. Wato shekaru biyu cur. Labarin ya kara da cewa a yankin Asiya dai an zabi Bahrain da kuri’u 186, sai kuma kasashen...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan Sallah da ke tafe. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, wanda mataimakinsa DCP Saleh Sama’ila ya wakilta, ya bayyana haka ga manema labarai bayan zaman kwamitin tsaron jihar da aka gudanar a Damaturu. Ba zan yi musayar yawu da yara ba — Martanin Amaechi ga Wike Tinubu ya gana da Fubara a Legas Taron ya samu jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Baba Malam Wali, a madadin Gwamna Mai Mala Buni. A cewar CP Emmanuel, rundunar ‘yan sandan tare da sauran hukumomin tsaro sun ɗauki matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sai dai fatan su shi ne Allah Ya...
An kama su da manyan makamai ciki har da bindiga ƙirar GPMG, bindigu ƙirar AK-47 da sauransu. Mutanen sun amsa laifin da ake zargin su, inda suka ce an biyasu Naira 500,000 domin su kai makaman daga Jihar Binuwsi zuwa Kwara. Rundunar ‘yansandan ta ce da ba a kama su ba, makaman na iya shiga hannun ‘yan ta’adda. Ana ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a wannan harkar safarar makamai. Kwamishinan ‘yansandan, ya ce Nasarawa ba mafaka ba ce ga masu laifi, kuma za su ci gaba da yaƙi da masu safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba. Ya kuma roƙi jama’a da su riƙa sanar da duk wani abin da suka gani mai kama...
A nasa bangare kuma, David Perdue ya ce, shugaba Donald Trump yana matukar girmama shugaba Xi Jinping, kuma yana da muhimmanci a ci gaba da karfafa mu’amala dake tsakanin shugabannin biyu. A matsayin jakadan kasar Amurka a kasar Sin, yana fatan yin mu’amala da bangaren Sin yadda ya kamata, bisa ka’idar girmama juna, da sauraron ra’ayoyin juna. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin da ya sa ya naɗa Nyesom Wike a matsayin Shugaban Ma’aikata a lokacin da yake Gwamnan Jihar Ribas, maimakon Kwamishinan Kuɗi. Amaechi, ya ce ya zaɓi Wike ne a matsayin Shugaban Ma’aikata domin ya samu damar sanya ido a kansa. Tinubu ya gana da Fubara a Legas Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja “Na so ya zama shugaban ma’aikata ne saboda na riƙa sanha ido a kansa. “Ban ba shi kujerar kwamishinan kuɗi ba,” in ji Amaechi a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise da yammacin ranar Talata. Wannan martanin ya biyo bayan kalaman Wike ne, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin...
A watan Oktoban 2024, wani jirgin ruwa ya kife da kusan mutum 300 a Mokwa, na Jihar Neja. Haka kuma, a watan Satumban 2023, mutum 24 sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a Jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah. Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu na shirin amfani da hawan Durbar domin tayar da hankali da barazana ga tsaro da doka a jihar. Rundunar ta taba sanya irin wannan haramci a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama da suka gabata, kuma an yanke shawarar ci gaba da dokar har zuwa Sallah Babba. Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ɗauki...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki. Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar. A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya. Ya naɗa...
Jami’an hukumar tsaro ta DSS da na rundunar sojojin Najeriya sun ce sun hallaka ’yan bindiga akalla 45 a kusa da garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja. An dai sami nasarar ce sakamakon wani harin da dakarun suka kai cikin sirri a ci gaba da yakin da suke yi da ’yan bindiga a yankin. Majiyoyi daga cikin jami’an tsaro sun bayyana cewa jami’an DSS sun bi sahun wasu ’yan bindiga ne inda suka dakile yunkurinsu na kai munanan hare-hare, wanda kasurgumin dan bindigar nan, Dogo Gide da yaransa suka shirya kai wa. Kasa ta danne almajirai 11 sun mutu a Kaduna Uba ya harbe ɗansa har lahira saboda zaton biri ne Majiyar ta ce bayanan sirrin...
Alhazan Jihar Jigawa sun fara ayyukan hajji cike da kwarin gwiwa yayin da aka kaisu Mina daga birnin Makkah, inda za su wuce zuwa Dutsen Arafat domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Aikin hajji na farawa ne daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Dhul Hajj a duk shekara, inda ake daukar alhazai zuwa sansanin Mina sannan su wuce zuwa Arafat, zuwa Muzdalifa, sannan Jamarat (Jamratul Akbah), kafin su dawo Makkah inda za su kammala da Dawafi. Yawancin Alhazan da suka zanta da Rediyon Najeriya sun bayyana cewa, duk da wahalhalun da ke tattare da aikin hajji, sun kuduri aniyar gudanar da hajjin lafiya kuma cikin nasara. Wasu daga cikin Alhazan daga kananan hukumomin Jahun da Kiyawa, Hajiya...
Wasu almajirai su 11 sun rasa rayukansu bayan kasa ta danne su a kauyen ’Yardoka da ke karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna. Bayanai sun nuna almajiran sun rasu ne lokacin da suke tsaka da hakar kasa domin taya malaminsu buga bulon kasa da zai yi gini da shi. Lamarin ya faru ne wajen misalign karfe 1:45 na ranar Litinin. ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Ambaliyar Mokwa: Yawan mutanen da suka salwanta ya haura 700 Almajiran dai da aka bayyana rasuwar tasu sun hada da Muntari Abdulkadir da Aliyu Abba da Ali Umar da Mubarak Haruna da Usain Isa da Yusuf Shafiu da Mujitafa Jibril da Yusha’u Saidu da Aliyu Abdu da Hamisu Mohammed da kuma...
Kamar yadda majiyar ta bayyana, bayanan sirri da hukumar DSS ta samu sun nuna cewa, ‘yan ta’addan da suka fito daga dajin Bilbis da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da wasu sassan jihar Kaduna, Gide ne ya gayyace su da su kai farmaki a kauyukan Kuchi. Majiyar ta ci gaba da cewa, “da sanyin safiyar ranar Litinin, 2 ga watan Yuni 2025, ‘yan bindiga daga jihohin Kaduna da Zamfara, wadanda yawansu ya kai 100, dauke da muggan makamai, sun nufi garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya. “Amma jami’an tsaro, suka yi musu kwanton bauna a wani hari na bazata inda suka tarwatsa ‘yan ta’addan a wajen garin Kuchi, inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar,...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman. Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa. Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata. Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate,...
ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke Unguwar Mu’azu, inda manyan masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi, musamman shugabannin addini da na al’umma, suka halarta. Da yake jawabi a wajen taron, Ko’odinetan ROOSC a Jihar Kaduna, Mr. Ezra Angai, ya bayyana cewa wannan shiri hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da abokan ci gaba da kuma kungiyoyin aiwatar da shirin, domin inganta samun ilimi mai nagarta ga yaran da ba...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium shi ne mabuɗin batun nukiliya, don haka Iran ba zata taba yin watsi da shi ba A jawabin da ya gabatar a safiyar yau Laraba, a daidai lokacin da ake cika shekaru 36 da wafatin jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khumaini (Allah ya jikansa), Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a matsayin martani ga shawarar Amurka, ya jaddada cewa inganta sinadarin Uranium shi ne mabudin batun nukiliya, kuma ba za su taba yin watsi da shi ba. A wajen wannan juyayi, bayan karatun kur’ani mai tsarki da yabon Ahlul-baiti (a.s) jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa inda ya...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Zata mayar da martani mai gauni kan yadda ake siyasantar da batun nukiliya a cikin kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya jaddada cewa: Idan aka mayar da batun Iran na nukiliya siyasa a taron kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA, bai kamata daya bangaren ya sa ran Iran za ta ci gaba da yin aiki da cikakken kamun kai ba tare da mayar da martani ba. Maimakon haka, Iran za ta gudanar da mu’amalarta da siyasarta daidai da halayensu da manufofinsu. A cikin wata sanarwa da ya fitar ta gidan talabijin na Iran a yammacin jiya Talata, dangane...

Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Amurka Da Isra’ila Suna Da Mugun Nufi Kan Iran Da Kasashen Musulmi
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suna da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi. A yayin wani jawabi da ta gabatar a wajen juyayin tunawa da rasuwar Imam Khumaini {r.a}, Pezeshkian ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta iya aikata wani aiki hauka da wauta ba, idan kasashen musulmi suka hada kansu. Pezeshkian ya kara da cewa: Wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama suna kare “haramtacciyar kasar Isra’ila” mai laifi, kuma suna ci gaba da adawa da shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Ya ci gaba da cewa: “Babu mutum...
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurium a wani aiki na musamman na tallafawa al’ummar Gaza Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagaruminj hari kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2. Hari ya gudana daidai inda aka tsara shi, kuma ya haifar da firgici da ya kai ga miliyoyin yahudawan sahayoniyya gudu tare da shigewa maboyar karkashin kasa kamar burage. Har ila yau, harin ya dakatar da dukkan ayyukan filin jirgin, tare da hana wani jirgin dakon kaya na sojan Amurka sauka a filin jirgin sama na Ben Gurium a rana ta biyu a jere. A cikin wannan yanayi ne...
Sojojin mamayar Isra’ila sun sanar da kaddamar da farmaki kan yankin kudancin Siriya Sojojin mamayar Isra’ila sun sanar da cewa: Da sanyin safiyar yau Laraba, jiragen yakinsu suka kaddamar da farmaki kan wasu wuraren soji a kudancin Siriya, kuma sun dora alhakin halin da ake ciki a kan gwamnatin Ahmed al-Sharaa. Rundunar sojin mamayar Isra’ila a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: A wani lokaci kadan da ya gabata, bayan kai hare-hare kan yankunan haramtacciyar kasar Isra’ila, jiragen saman yakin na haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wuraren makaman gwamnatin Siriya a kudancin kasar ta Siriya. Ta kara da cewa: Halaltacciyar gwamnati ce ke da alhakin halin da ake ciki a kasar Siriya, kuma za ta...
Cibiyar mai suna ‘Continental Events and Sport Arena’ ta kunshi bangarori daban-daban da suka hada da manyan dakunan taro guda uku da bangarorin wasannin motsa jiki na gyms da na kwallon kwando na raga da dai sauransu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya sanar da cewa, nan da kwanaki masu zuwa Iran za ta mayar da amsa kan shawarar da Amurka ta gabatar kan shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya. A cewarsa, shawara da Amurka ta gabatar tana bukatar zurfafa bincike. M. Araghchi, ya bayyana hakan ne ziyarar da yake a birnin Beirut, na kasar Lebanon inda ya jaddada cewa, amsar da Iran za ta mayar zata kasance bisa tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da manufofinmu da kuma kare muradun al’ummar Iran. Ya nanata cewa inganta makamashin Uranium tamkar “jan layi” ne ga Iran, yana mai cewa Tehran ba ta bukatar neman izini daga kowa don ci gaba da ayyukanta da suka dace da shari’a kuma...
Rasha ta ce hare-haren Ukraine a kan yankunanta, musamman na baya-bayan nan zasu fuskanci martani mai zafi. Da yake sanar da hakan Mataimakin shugaban kwamitin sulhu na Tarayyar Rasha Dmitry Medvedev ya ce, sojojin kasar za su ci gaba da kai farmakin har sai an kawar da makiya gaba daya. Ya kuma kara da cewa babu makawa Rasha za ta mayar da martani kan ayyukan zagon kasa da sojojin Ukraine suka yi. A cewarsa, za a ci gaba da kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba, kuma wadanda ke da alhakin wadannan ayyuka. Hukumar tsaro ta Ukraine dai ta ce an kai wa wata gada mai muhimmanci hari da ta hada Rasha da yankin Crimea da bamabamai. Ta ce an...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bukaci hadin kan al’ummar kasar Lebanon wajen warware matsalolin kasar, yana mai kira da a yi shawarwarin kasa tsakanin dukkanin kungiyoyin siyasa domin cimma matsaya daya. Araghchi ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi a ranar Talata, da shugaban kasar Labanon, Joseph Aoun a birnin Beirut. Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada aniyar kasarsa na bunkasa alakarta da kasar Lebanon, bisa mutunta juna. Ya kuma sanar da cewa, kamfanonin Iran a shirye suke su marawa gwamnatin Lebanon baya a kokarinta na sake gina kasar. A nasa bangaren shugaba Aoun ya jaddada tsarin gwamnatinsa na bunkasa alaka da dukkan kasashen duniya tare da tabbatar da aniyar kasar Lebanon na...
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sake haramta duk wani nau’i na hawan Sallah a yayin bukukuwan Babbar Sallar da ke tafe. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Talata, ya ce har yanzu haramcin da rundunar ta fitar na nan daram kuma za su tabbatar da an yi aiki da shi a yayin bukukuwan Babbar Sallah ta 2025. Ya ce sun dauki matakin ne bayan wani zama da ilahirin shugabannin hukumomin tsaro a jihar suka yi, inda ya ce sun gano wani yunkuyi da aka yi wajen yin amfani da hawan wajen yi wa harkokin tsaron jihar zagon kasa, kamar yadda aka samu yayin Karamar Sallar da ta gabata....
Ya yaba musu cewa, sun yi kokari sosai wajen kashe wani babban kwamandan kungiyar ta’addanci ta ISWAP tare da wasu mutane biyu kwanaki kadan da suka gabata. LEADERSHIP ta tuna cewa, babban kwamandan ISWAP da aka kashe, Abu Fatima na cikin jerin sunayen ‘yan ta’addan da sojojin Nijeriya ke nema ruwa a jallo tare da saka ladar Naira miliyan 100 kan duk wanda ya kawo mata shi. An ce Abu Fatima shi ne ke da alhakin kai hare-hare a arewacin jihar Borno, musamman ma yankin Baga. An fara kama dan ta’addar na ISWAP a raye amma daga baya ya mutu sakamakon zubar da jini mai yawa bayan Harbin da aka yi masa. Daga kanmu, magana ta...
Wasu mutum bakwai sun rasa ransu sakamakon hatsarin kwale-kwale lokacin da suke tafiya daga kauyen Gidan Husaini zuwa Gwargawu na karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato ranar Litinin. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da mamatan ke tafiya a wani kogi, lamarin da ya jefa mutanen yankin cikin jimami da alhini. Ba a dai bayyana sunayen wadanda suka rasun ba, amma hukumomi a yankin sun tabbatar da cewa dukkan mamatan ’yan asalin kauyen na Gidan Husaini ne. Ambaliyar Mokwa: Yawan mutanen da suka salwanta ya haura 700 Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zabo Da ya jagoranci wata tawagar gwamnatin jihar domin yin ta’aziyyar mamatan, Kwamishinan Kudi na jihar, Muhammadu Jabbi Shagari, ya bayyana...
Irin manufar bude kofa da gyare-gyare ta kasar Sin duniya da jama’arta suka fi bukata, domin ita ce za ta bada damar samun dunkulewar duniya da ci gabanta kamar yadda ake fata, har ma da kai wa gina duniya mai kyakkyawar makoma ga dukkannin dan adam. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”. Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro,...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, a yau Talata ya yi watsi da ikirarin da Amurka ta yi na cewa kasar ta Sin na karya yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin kasashen biyu a tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci da aka yi a Geneva, inda ya bukaci Amurka da ta daina yada labarun kanzon kurege. A yayin taron manema labarai na yau da kullum, Lin ya bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakin da ya dace, tare da daukar yarjejeniyar da aka cimma a shawarwarin Geneva da muhimmanci, tare da aiwatarwa yadda ya kamata. Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya Sallah: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Naira Miliyan...

Karuwar Darajar Sana’ar Samar Da Kayan Laturoni Da Dangoginsu a Sin Cikin Watanni 4 Na Farkon Bana Ya Karu Da 11.3%
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar. “An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.” In ji Rundunar Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar. “An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.” In ji Rundunar Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

An Samu Karuwar Kaso 2.7 Na Yawan Tafiye-Tafiye Zuwa Ketare Yayin Hutun Bikin Dragon Boat Na Kasar Sin
Cikin kwanaki uku na hutun bikin Dragon Boat na kasar Sin, an samu karuwar tafiye-tafiye zuwa ketare da suka kusa miliyan 5.91. Masu tafiye-tafiye sun karu matuka tun daga Asabar har jiya Litinin, inda aka samu karuwar kaso 2.7 bisa dari kan adadin da aka samu a bara. Alkaluman da hukumar lura da shige da ficen al’umma ta kasar Sin ta fitar a Talatar nan, sun nuna karuwar baki masu shigowa kasar Sin daga ketare, musamman wadanda suka ci gajiyar manufar nan ta kawar da bukatar biza. Albarkacin wannan manufa, adadin baki daga ketare da suka shigo kasar Sin yayin ranaku uku na bikin ya kai 231,000, adadin da ya karu da kaso 59.4 bisa dari kan na shekarar bara....
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon a yau Talata a birnin Beirut babban birnin kasar. Aragchi ya ce kasar Iran tana goyon bayan kasar Lebanon ta hanyar kungiyar Hizbullah. Kuma tana goyon bayanta kan HKI wacce take mamaye da wasu yankuna a kasar. Muna goyon bayan gwamnati da mutane a duk wani kokarin da zasu yi na kwato yankunan kasar wadanda HKI take mamaye da su. Ministan kafin haka ya bayyana cewa JMI tana daga cikin kasashen da zasu...
“Bisa ga hakan ne, Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris ya bayar da wannan tallafin don gudanar da shagalin sallar cikin walwala da Jin dadi”. Shugaban ya gode wa Gwamnan jihar kan wannan kokarin da yayi na tunanin a zakulo mata uku a kowace rumfar zabe a duk mazabun kananan hukumomin 21 na jihar don basu tallafin N30,000 don gudanar da shagalin sallar Eid-kabir, “muna masa godiya a madadin matan da suka ci gajiyar tallafin”. Daga karshe, Zuru ya yi kira ga sauran shugabanni da su yi koyi da Gwamnatin jihar Kebbi kan tallafa wa al’umma a jihar musamman a irin wannan lokaci ga wannan lokaci da jama’a ke da bukatar yin layya. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Wata kotun kasar Mali ta kori karar da aka shigar a gabata, don neman soke matakin da majalisar soj0jin kasar ta dauka na rusa jam’iyyun siyasa gaba daya. A ranar 13 ga watan Mayu ne da ya gabata ne majalsiar koli ta sojojin kasar Mali ta fitar da dokar haramta dukkan jam’iyyun siyasa a kasar wadanda yawansu ya kai 300, tare da manusar sake fasalinsu. Wasu lauyoyi da kuma ‘yan siyasar kasar ne dai su ka shigar da karar a gaban kotu, daga cikinsu har da ‘Montagal Tal’ wanda ya kasance jagoran daya daga cikin jam’iyyun da aka majalisar sojojin ta soke. Masu shigar da karar, sun bayyana matakin da majalisar sojan kasar ta dauka da cewa keta hurumin ‘yancin...

Guardian: Isra’ila Tana Kai Wa Makarantun Dake Dauke Da ‘Yan Gudun Hijira a gaza Hari, Tana Sane Da Hakan
Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba. Jaridar ta kara da cewa: Isra’ila ta ayyana wasu Karin makarantu wadanda Falasdinawa suke samun mafaka a cikinsu domin kai musu hare-hare a nan gaba. A lokacinda HKI ta kasa ganin mayakan Hamas a fili sojojinta sun koma kan kissan Falasdinawa fararen hula, wadanda suke samun mafaka a makarantu. A cikin watanni da suka gabata sojojin mamayar sun kai hare-hare akan wasu gine-ginen 6 wadanda suka kasance makarantu ne, wadanda...
Daya daga cikin manyan-manyan jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa: “Babu tantama gwamnatin HK Isra’ila ta tafka laifukan yaki a kan Falasdinawa a zirin Gaza da ta killace. Matthew Miller wanda ya yi aiki a matsayin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun daga 2023 har zuwa karshen gwamnatin Joe Biden, ya fada wa tashar talabijin ta Sky News kan cewa; Isra’ilan ta tafka laifukan yaki. Da aka yi masa tambaya a kan yakin Gaza a fadar White House, Miller ya ce; An yi ta samun tsabani dangane da yakin, sabani manya-manya wani lokacin kuma kananan sabani, kan yadda za a kare dangantakar Amurka da HK Isra’ila duk tare da abinda take aikatawa.”. Amma Miller ya...
Ofishin shugaban kasar Turkiya, ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya a birnin Istanbul, za ta kai ga tsayar da tsagaita budewa juna wuta wanda kuma zai ga, kawo karshen yakin baki daya. Ofishin shugaban kasar Turkiya ya bayyana haka a yau Talata, ta kuma kara da cewa,; Tattaunawar da aka gudanar a jiya Litinin a tsakanin Rasha da Ukiraniya a kuma fadar shugaban kasar Turkiyya dake birnin Istanbul tana cike da fata na tsayar da yakin. Kamfanin dilalncin labarun “Sputnik” na kasar rasha ya ambato majiyar fadar shugaban kasar ta Turkiya tana cewa; Shakka babu duk wata tattaunawa da bangarori za su zauna akan teburi, tana tattare da kyakkyawan fata, a dalilin haka,...
A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN. Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan. Sanarwar ta jaddada cewa, da zarar an fitar da kudaden, dole ne a aiwatar da duk wasu bukatu da kungiyar ta JUSUN ta gabatar ba tare da bata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Yau Talata, kungiyar masu jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman watanni 4 na farko na bana, wadanda suka nuna cewa, a watan Afrilu, sha’anin jigilar kayayyaki ya bayyana inganci da boyayyen karfi, kuma duk da kalubaloli da matsin lamba daga ketare da aka fuskanta, ya tafi yadda ya kamata tare da samun bunkasuwa. Kana daga watan Janairu zuwa na Afrilu, darajar hajojin da aka yi jigilarsu a kasar ta kai dalar Amurka triliyan 16, wadda ta karu da kashi 5.6 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokaci a bara. Kazalika, yawan hajojin da aka yi jigila yana cikin wani yanayi mai dorewa, bisa la’akari da yadda jigilar kayayyaki ta amfani da layin dogo da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu kuma sun ce akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan da mahaifinsa, Oba Akinruntan. Bayan saukar Akinruntan, an zaɓi Ololade Gbegudu daga Okitipupa a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar. Gbegudu, mai shekara 42, ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin tsaro da ci gaban al’umma a majalisar kafin wannan sabon muƙamin. Oluwatoyin James daga Akoko ta Arewa Maso Gabas ne, ya ayyana sunansa, yayin da Chris Aiyebusiwa daga Okitipupa I ya mara masa baya. Haka kuma, tsohon jagoran majalisar, Ogunmolasuyi daga Owo I, ya sauya wajen aiki da Olatunji Oshati daga mazaɓar Ose, wanda yanzu shi ne sabon shugaban masu rinjaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, yace nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru biyu kadai shaida ce ta shugabanci mai hangen nesa da jaruntaka. Ya bayyana haka ne a yayin taron farko na National Dialogue on Citizen Engagement and National Security da aka gudanar a Abuja, mai taken “One Voice, One Vision: Uniting Perspectives for a Stronger Nigeria.” A cewar Ministan, wannan taro ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke kokari yi amfani da damamaki da ke gabanta. Ya jaddada cewa wannan dandali da Voice of Nigeria (VON) ta shirya ba kawai taron tattaunawa kan manufofi bane, sai dai wata kafa ce da aka tanada domin hada ra’ayoyi da...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Alakar Iran Da Lebanon Tarihi Ce Mai Tushe Da Ta Ginu Kan Mutunta Juna
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Dangantakar Iran da Lebanon tarihi ce, mai tushe, kuma ta ginu ne bisa mutunta juna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana alakar da ke tsakaninta da kasar Lebanon a matsayin mai tarihi, mai tushe, kuma ta ginu ce bisa mutunta juna. Ya ce: “Kasashen biyu sun kuduri aniyar bunkasa wannan alakar. A jawabin da ya yi a filin jirgin sama na birnin Beirut, inda wakilin kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon ya tarbe shi, Araqchi ya yi nuni da cewa ziyarar wani bangare ne na rangadin da yake yi a yankin bayan ziyarar da ya kai birnin Alkahira na Masar, kuma zai gana da jami’an kasar ta Lebanon. Ya kara da...