2025-06-06@08:31:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1091
«a tallafawa»:
Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar. An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa akan hanyoyin magance cutuka mabanbanta da su ka hada da riga-kafi. Wadanda su ka halarci tattaunawar ta bidiyo sun hada shugabannin kasashen Angola, Namibia, Malawi da kuma DRC. Shugaban kasar Zambia Hakayinde Hichilema ya bayyana cewa; Da akwai bukatar nahiyar Afirka ta fara samar da magunguna cikin gaggawa tare da dogaro da nahiyar wajen samar da kudaden da ake bukata domin yin hakan, saboda kaucewa dogaro da waje.” Haka nan kuma shugaban kasar ta Zambia ya ce: Saboda kwalara idan ta barke ba ta san iyakar kasashe ba, ya kamata...
“Al’ummar kasa da kasa da yawa sun sauya ra’ayinsu mai kyau game da Amurka zuwa mummunan ra’ayi, yayin da yawan masu nuna kauna ga kasar Sin ya karu.” Wani bincike da kamfanin bincike na Morning Consult na Amurka ya fitar kwanan nan ya nuna cewa, har zuwa karshen watan Mayu, yawan al’ummar duniya dake nuna kauna ga Amurka ya ragu zuwa -1.5, yayin da adadin ya karu zuwa 8.8 ga kasar Sin. Ko da yake sakamakon ya fito ne daga hukumar bincike guda daya kawai, amma yana da ma’ana sosai wajen yin kashedi, idan aka yi la’akari da cewa binciken ya shafi kasashe da yankuna fiye da arba’in, inda akasarinsu su ne muhimman abokan huldar Amurka a fannin tattalin arziki...
Gidauniyar ta kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammed Aliyu Shaaba, inda wakilan fadar suka yi maraba da tawagar wakilan gidauniyar tare da jinjina taimako da goyon bayan da aka nuna musu a wannan hali da suke ciki na ibtila’i. Kamar yadda Babban daraktan yankin, Musa Aliyu ya bayyana, gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki ta kai taimakon kuɗi domin tallafawa waɗanda suka tsira da masu taimaka musu. Sannan ya yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da ɗaiɗaikun mutane da su taimakawa al’ummar garin Mokwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon malamin makaranta, dan siyasa kuma ambasada, Farfesa Jibril Aminu ya rasu yana da shekara 85. Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar, kuma Kwamishinan Gidaje da Raya Birane na jihar Adamawa, Hon Abdullahi Prambe ma ya tabbatar da haka. Ya ce, “Ba za a taba mantawa da gudunmawar shi ba musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma shugabanci.” Wata majiya da ke da kusanci da mamacin ta ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a Masallacin Kasa da ke Abuja. Sai dai kawo yanzu, iyalai da ’yan uwan mamaci bas u fid da cikakken bayani kan yadda za a yi jana’izar mamacin ba ko kuma musabbabin rasuwarsa. An haifi Farfesa Jibril...
Miliyoyin alhazai ciki har da ’yan Najeriya ne suka taru a Dutsen Arfa domin tsayuwa a yayin Aikin Hajjin bana duk da tsananin zafin ranar da ake fama da shi a kasar Saudiyya. Ministan Aikin Hajji na kasar dai ya shawarci mahajjatan da su kasance a cikin tantinansu tun daga tsakain karfe 10 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma, saboda tsananin zafin rana. Ko a ranar Lahadi sai da Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasar (NCM) ta yi gargadin cewa zafin zai iya kai wa ma’auni 47, inda ta shawarce su da su dauki matakan kariya. Musulman Kudancin Kaduna sun yi taron addu’ar zaman lafiya Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano To...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya. Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027. Barazanar Yajin Aiki: Abuja da wasu jihohi 3 za su faɗa cikin duhu A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Saraki, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu na PDP, ya faɗi haka ne a wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Ilorin. Ya amince cewa wasu sun bar jam’iyyar, amma mutane da dama suna ci gaba da shigowa jam’iyyar. “PDP ce kawai jam’iyyar adawa ta haƙiƙa,” in ji shi. “Eh, muna fuskantar ƙalubale, amma muna...
Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake tabbatar da cewa Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba kan ‘yancinta na tace Uranium, yana mai cewa ci gaban da kasar ta samu a fannin makamashin nukiliya ya samo asali ne sakamakon sadaukarwa da kuma saka hannun jari na kasa. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya ce, ba batun inganta makamashin Uranium a duk wata yarjejeniyar nukiliya da za a yi nan gaba. “Iran ta saka kudi da yawa domin kai wag a wannan mataki, sannan kuma ba zai sa mu yi watsi da sadaukarwar da ‘yan kishin kasa sukayi don tabbatar da burinmu. Araghchi ya bayyana tace...
Yau Alhamis 9 ga watan Zul Hijja, ita ce ranar da miliyoyin Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudiyya ke hawan Arfa, wato daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji. Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya kunshi dawafi da zaman Mina da tsayuwar ta Arfa da kuma jifar shaidan. A washegarin ranar ne kuma sauran Musulmai a duk fadin duniya su ke shagulgulan Sallar layya. Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramtawa kasashen duniya 12 shiga Amurka a wani mataki da ya ce na kare kasar ne daga “yan ta’adda na kasashen waje. Wata takarda da fadar White House ta fitar a ranar Laraba ta ce haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yuni, ya shafi kasashen Afghanistan, Burma, Chadi, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, da kuma Yemen. Baya ga hakan akwai wasu kasashe bakwai su ma da aka gindawa wasu sharudda da suka hada da Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da kuma Venezuela. A cewar Amurka matakin bai shafi mutanen da balaguron su zuwa kasar ke da amfani ga muradun kasar ba.” Haka ma...
Gwamnatin kasar Amurka wacce ta bude cibiyoyin rarraba kayakin Agaji a Gaza, ta ce zata rufe cibiyoyin zuwa ranar Alhamis mai zuwa don sake tsara ayyukan Rabomn. Majiyar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda sojojin yahudawan suna kashe falasdinawa wadanda suke fama da yunwa a lokacinda suka iso cibiyoyin raba abincin ko kuma suka hau kan hanyar zuwa karban abincin. Labarin ya kara da cewa a jiya Talata kadai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa mayunwata 27 a kokarinsu na karban abinci. Sannan a yau Laraba ya zuwa lokacin bada wannan labarin sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 32 a hare-haren da suka kai kan yankuna daban-daban a Gaza. Majiyar ta kara da cewa Palasdinawa 95 ne...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah. Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu na shirin amfani da hawan Durbar domin tayar da hankali da barazana ga tsaro da doka a jihar. Rundunar ta taba sanya irin wannan haramci a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama da suka gabata, kuma an yanke shawarar ci gaba da dokar har zuwa Sallah Babba. Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ɗauki...
Alhazan Jihar Jigawa sun fara ayyukan hajji cike da kwarin gwiwa yayin da aka kaisu Mina daga birnin Makkah, inda za su wuce zuwa Dutsen Arafat domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Aikin hajji na farawa ne daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Dhul Hajj a duk shekara, inda ake daukar alhazai zuwa sansanin Mina sannan su wuce zuwa Arafat, zuwa Muzdalifa, sannan Jamarat (Jamratul Akbah), kafin su dawo Makkah inda za su kammala da Dawafi. Yawancin Alhazan da suka zanta da Rediyon Najeriya sun bayyana cewa, duk da wahalhalun da ke tattare da aikin hajji, sun kuduri aniyar gudanar da hajjin lafiya kuma cikin nasara. Wasu daga cikin Alhazan daga kananan hukumomin Jahun da Kiyawa, Hajiya...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman. Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa. Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata. Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate,...
Rasha ta ce hare-haren Ukraine a kan yankunanta, musamman na baya-bayan nan zasu fuskanci martani mai zafi. Da yake sanar da hakan Mataimakin shugaban kwamitin sulhu na Tarayyar Rasha Dmitry Medvedev ya ce, sojojin kasar za su ci gaba da kai farmakin har sai an kawar da makiya gaba daya. Ya kuma kara da cewa babu makawa Rasha za ta mayar da martani kan ayyukan zagon kasa da sojojin Ukraine suka yi. A cewarsa, za a ci gaba da kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba, kuma wadanda ke da alhakin wadannan ayyuka. Hukumar tsaro ta Ukraine dai ta ce an kai wa wata gada mai muhimmanci hari da ta hada Rasha da yankin Crimea da bamabamai. Ta ce an...
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sake haramta duk wani nau’i na hawan Sallah a yayin bukukuwan Babbar Sallar da ke tafe. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Talata, ya ce har yanzu haramcin da rundunar ta fitar na nan daram kuma za su tabbatar da an yi aiki da shi a yayin bukukuwan Babbar Sallah ta 2025. Ya ce sun dauki matakin ne bayan wani zama da ilahirin shugabannin hukumomin tsaro a jihar suka yi, inda ya ce sun gano wani yunkuyi da aka yi wajen yin amfani da hawan wajen yi wa harkokin tsaron jihar zagon kasa, kamar yadda aka samu yayin Karamar Sallar da ta gabata....
Ya yaba musu cewa, sun yi kokari sosai wajen kashe wani babban kwamandan kungiyar ta’addanci ta ISWAP tare da wasu mutane biyu kwanaki kadan da suka gabata. LEADERSHIP ta tuna cewa, babban kwamandan ISWAP da aka kashe, Abu Fatima na cikin jerin sunayen ‘yan ta’addan da sojojin Nijeriya ke nema ruwa a jallo tare da saka ladar Naira miliyan 100 kan duk wanda ya kawo mata shi. An ce Abu Fatima shi ne ke da alhakin kai hare-hare a arewacin jihar Borno, musamman ma yankin Baga. An fara kama dan ta’addar na ISWAP a raye amma daga baya ya mutu sakamakon zubar da jini mai yawa bayan Harbin da aka yi masa. Daga kanmu, magana ta...
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar. “An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.” In ji Rundunar Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar. “An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.” In ji Rundunar Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon a yau Talata a birnin Beirut babban birnin kasar. Aragchi ya ce kasar Iran tana goyon bayan kasar Lebanon ta hanyar kungiyar Hizbullah. Kuma tana goyon bayanta kan HKI wacce take mamaye da wasu yankuna a kasar. Muna goyon bayan gwamnati da mutane a duk wani kokarin da zasu yi na kwato yankunan kasar wadanda HKI take mamaye da su. Ministan kafin haka ya bayyana cewa JMI tana daga cikin kasashen da zasu...

Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Na Da’awar Mallakar Wasu Yankunan Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin watsi da ikirarin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Fasha karo na...
Rikici tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar yana ci gaba da habaka a wurare da dama na kasar Kasar Sudan dai na fuskantar tabarbarewar harkokin tsaro cikin hanzari, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF), a cikin sarkakkiyar yanayin jin kai da na siyasa da kuma fadadan rikici a jihohi daban-daban. Fadace-fadace a Sudan suna ci gaba da karuwa, inda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan kungiyar Rapid Support Forces, inda sojojin saman Sudan suka zafafa kai hare-hare ta sama ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki, kuma suka yi luguden wuta kan wasu muhimman...
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince da biyan ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho da ke fadin jihar kyautar Sallah (Eid-el-Kabir) a matsayin alawus-alawus da ake yi a fadin jihar domin nuna tausayi da jajircewa wajen kyautata rayuwar ma’aikata. Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Gusau. A cewar sanarwar, matakin na Gwamnan na da nufin rage wa ‘yan kasa matsalar kudi a lokacin bukukuwan Sallah da kuma ba su damar gudanar da bukukuwan cikin farin ciki da mutuntawa. Gwamnan wanda a halin yanzu yake aikin hajji a birnin Makkah na kasar Saudiyya ya mika gaisuwar Sallah ga al’ummar Zamfara....
Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan ya jaddada goyon bayan da kasarsa take bai wa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya, ya kuma kara da cewa; Ana yin nazarin yadda za a gana, a kuma tattauna tsakanin shugabannin kasashen biyu.” Fidan ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa tattaunawar da aka bude a yau ta kai ga haifar da daa mai ido. Haka nan kuma ya ce, kasarsa za ta yi duk abinda za ta iya, domin ganin cewa kasashen biyu sun kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu. Kafar watsa labaru ta Axios; ta ambato majiyar Ukiraniya na cewa, Rasha ta gabatar da tsarin zaman lafiya wanda ya kunshi yadda za a kawo karshen yaki....
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da suka yi tawaga zuwa wajen raba kayan agajin jin kai a garin Rafah Rahotonni sun bayyana cewa: A rana ta biyu a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar zirin Gaza da ke fama da yunwa. Shafin yanar gizo na Falestine Today ya watsa rahoton cewa: A safiyar yau Litinin 2 ga watan Yunin shekara ta 2025, sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da wani sabon laifi ta hanyar kai hare-hare kan Falasdinawa a kusa da cibiyar bada agajin Amurka da ke birnin Rafah. Ya zuwa yanzu dai wannan aika-aika ya yi sanadin shahadan Falasdinawa 3 tare da raunata wasu 60, ba a ma...
Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa. Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti. Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani...
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa...
Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A bisa sanarwar da kasar Saudiyya ta yi na ganin watan zulhijja, a ranar 27 ga watan Mayu, za a yi hawan Arfa a ranar 5 ga watan na Mayu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Binciken CGTN Ya Nuna Kaso Kusan 90 Bisa Dari Na Masu Bayyana Ra’ayoyi Na Kokawa Da Makomar “Mafarkin Amurka”
Kafar CGTN ta kasar Sin ce ta wallafa binciken jin ra’ayin jama’ar kan dandalolin harsunan turancin Ingilishi, da Sifaniyanci, Faransanci, da Larabci, da harshen Rasha, inda masu bayyana ra’ayoyi 6,886 daga sassan kasashen ketare daban daban suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Haka kuma an yi zaratan ‘‘yan kwallo irin su Johan Cruyff da Eusébio da Gerd Müller mahaifin Muller na yanzu da Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil da sauransu amma tabbas ba a samu zazzafar muhawara ba saboda bbau kafafen sadarwa na zamani wadanda yanzu kusan su ne suka hura wutar zazzafar muhawarar a sassa daban-daban na duniya da ake Kallon kwallon kafa. A yanzu dai Messi ne ya fi lashe Ballon d’Or, inda yake da guda takwas: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021 da 2023, sai Cristiano Ronaldo mai guda biyar: 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017. Sannan Messi ya zo na biyu sau biyar, shi kuma Cristiano Ronaldo ya zo na biyu sau shida, sannan dukkansu sun...
Iran ta tabbatar da cewa ta samu shawarar da Amurka ta gabatar mata daga hannun kasar Oman game da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya da ake tattaunawa a kai. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ta samu wani bangare na shawarwarin daga Amurka daga Oman mai shiga tsakani kan batun a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X. Ya karbi sakon ne daga hannun takwaransa na Oman Badr Albusaidi, wanda ya gudanar da wata gajeriyar ziyara a Tehran. Saidai ministan harkokin wajen Iran din bai bayyana abinda shawarwarin ke kunshe da ba, amma ya jaddada cewa za a duba su a kuma mayar da amsa wacce ta yi daidai da muradin...
Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah. Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa. Wani jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta CNN a ranar Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ba za ta hada kai da hukumar Falasdinu ta PA ba da ke neman karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya. Jami’in ya bayyana ziyarar a matsayin tsokana, yana mai...
Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayyana ambaliyar ruwa mai tsanani da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a matsayin babbar ibtila’i, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don tallafi da hana sake faruwar hakan. Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana haka a yayin mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ambaliyar da ta faru a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, sakamakon ruwan sama mai kamar da bakin ƙwarya da ya yi sanadin rasa rayuka, bacewar mutane, da lalacewar gidaje, gonaki, da kayan more rayuwa. Ya yaba da agajin gaggawa daga Gwamnatin Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago da kuma kokarin hukumomin agaji wajen aikin ceto da tallafa wa...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta bukaci masu shiga tsakanin Amurkawa su ngamtar da ita kan cewa HKI zata dakatar da yaki ta kuma fice daga zirin gaza. Amma shawarar da Steve Witkoff ya gabatar bata kunshi wani abu wanda zaia gamsar da kungiyar ta amince da wani sulhu ba. Jihad Taha kakakin kungiyar ya bayyana cewa Hamas tana nazarin shawarar da Witskoff ya gabatar da tsagaita wuta a gaza wanda ya amince da dakatar da wuta na wucin gadi sannan a sake komawa yaki da kuma shigo a kayakin agaji. Y ace shawarar bata ambaci ficewar sojojin HKI daga yankin ba. Taha ya bayyana cewa shawarar bata da wani abin dogaro wanda Hamas da kungiyoyin masu...
Aƙalla mutum 20 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da tawagar Jihar Kano da ke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa (NSF) da aka kammala a Jihar Ogun. Lamarin na ban tausayi ya faru ne a ranar Asabar a garin Dakatsalle, kimanin kilomita 50 daga Kano, yayin da tawagar ke gab da isa gida. Rahotannin farko daga masu bada agajin gaggawa da shaidun gani da ido sun nuna cewa waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun haɗa da ’yan wasa da ɗan jarida, ma’aikatan lafiya da jami’an gudanar da harkokin wasanni. Shugaban ƙungiyar marubutan wasanni ta Najeriya (SWAN) reshen Kano, Zahraddeen Saleh, ya tabbatar da wannan mummunan lamari. Ya kuma ƙara...
Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ahmed Musa, ya auri matarsa ta 4, Asmau Moriki, a wani biki na sirri da aka gudanar a jihar Kano, Musa da amaryarshi Asmau sun zama mata da miji watanni kadan bayan haduwarsu, Musa ya bar sansanin tawagar Super Eagles dake birnin Landan domin ya halarci bikin wanda aka gudanar a birnin Kano. Dan wasan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya shiga wasan da Nijeriya ta doke Ghana da ci 2-1 a minti 60 na wasan, Musa na daya daga cikin yan wasan da sukafi taka leda a tarihin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya inda kuma ya zamo wanda yafi jefawa Nijeriya kwallaye a gasar kofin Duniya a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen. Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa. Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga...

Cutar Kwalara Ta Yadu A Sudan Baya Ga Matsalar Tashe-Tashen Hankulan Da Suke Ci Gaba Da Yuduwa A Kasar
Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar Sudan na ci gaba da fama da tabarbarewar yanayin tsaro da lafiya bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan. A bangaren tsaro kuma, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces sun kai hare-haren bama-bamai a wasu asibitoci biyu da wasu unguwanni a birnin El Obeid da ke Arewacin Kordofan a tsakiyar kasar Sudan. Wata majiyar soji ta bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa sun afkawa Asibitin Al-Daman da kuma Jami’an lafiya da ke tsakiyar birnin da manyan bindigogi. Sojojin Sudan sun tabbatar da cewa: Sun yi luguden wuta kan sansanonin dakarun...
Da yake jawabi ga ɗimbin mutanen da suka halarci wannan tattaki, Gwamna Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kawar da duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar, tare da mai da hankali sosai kan ‘yan bindiga. Ya ce, “A yau mun fito dubunnan mu domin mu yi tattakin samun zaman lafiya, domin mu sanar da duniya cewa Zamfara ta samu ci gaba sosai ta fuskar tsaro. “Gwamnatina ta ba da himma da kayan aiki masu yawa don ƙarfafa sojoji, tattara bayanan sirri, da haɗa kai don dawo da zaman lafiya a jihar. “Mun sami gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga, yawancin wuraren da ake fama da rikici a baya, a halin yanzu sun kasance cikin kwanciyar...

Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Tattaunawa Ta Hudu Kan Musaya Da Koyi Da Juna A Tsakanin Al’ummomi Ta Fannin Wayewar Kansu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran Ali Shamkhani mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen siyasa ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta mai tsayayyen tsarin tsaro, al’umma masu tsayin daka, da jajayen layi. Ya jaddada cewa, “tattaunawa hanya ce ta ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba kayan aiki na tilastawa ko mika wuya ba.” Shamkhani ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa: “Burin isa ga cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma ‘tarwatsa su’ ba komai ba ne illa mafarki da shugabannin Amurka da suka gabata sun kasance sun yi has ashen hakan. Ya...
A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan ya biyo bayan sauya ra’ayi da Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bisa la’akari da goyon bayan siyasa da na soji da Amurka ke ba shi, a cikin shiru da kasashen duniya suka yi da kuma gazawar da ba a taba gani ba daga kungiyoyin kasa da kasa. Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa: Sojojin...
Sulhu da ‘Yan Bindiga Ya Fi Zubar Da Jinin Ɗan Adam A Kaduna – Uba Sani Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa Kazalika, wasu kwararrun, sun ayyna larurar, a matsayin cieon da ke yiawa mutane, kisan mummuke, musamman duba da cewa, bata nuna wasu alamu, idan an kamu da ita, sai dai kawai, ta ci gaba da zama barzana ga lafiyar ‘yan Adam, kamar kamuwa da masu larorin da suka hada da; mutuwar barin Jiki, lalata Koda da kuma rashin iya gani. An kiyasta cewa, a daukacin fadin duniya, sama da mutane, biliyan 1.3 ke fama da ciwon, wanda kuma rabin adadin wannan alkaluman ne kacal, aka yi masu gwaji aka...
A yau Alhamis ne aka gudanar da dandalin “Kasa da kasa na tattaunawa tsakanin magadan biranen duniya na Shanghai, da dandalin kawancen birane na kasa da kasa na Shanghai na shekarar 2025.” Magadan birane da wakilai daga birane 26 dake cikin kawancen, daga sassan kasashen duniya 22, sun hallara a bakin kogin Huangpu, domin tattaunawa, da musaya game da yanayin makomar birane a nan gaba, da hadin gwiwa, inda suka mayar da hankali kan “Bunkasa birane masu korayen itatuwa, da karancin fitar da iskar carbon, da ci gaba da kirkire-kirkire”. Kazalika a yau din, birnin Shanghai ya sanya hannu kan takardun bunkasa kawance da musaya tare da Tbilisi na Georgia, da Vientiane na Laos da sauransu. A shekarun baya bayan...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa: “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa: “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.
Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da yin kutse cikin Masallacin Al-Aqsa, yayin da kungiyar Hamas ta yi kira da a kalubalance su Daruruwan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a safiyar yau Alhamis suka kutsa cikin harabar Masallacin Al-Aqsa, karkashin kariyar da ‘yan sandan gwamnatin mamayar Isra’ila, yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen gudanar da taron gangami da kuma jaddada rashin amincewa da keta hurumin alkiblar musulmi na farko, kuma daya daga cikin Masallatai masu daraja na al’ummar musulmin duniya. Majiyoyin daga Qudus sun ba da rahoton cewa: Tsagerun yahudawan sahayoniyya mazauna matsugunai da dama sun gudanar da rangadi masu tayar da hankali a harabar Masallacin Al-Aqsa mai albarka, ciki har da gudanar da ibadar Talmud da raye-rayen neman tsokana.

Falasdinawa 23 Suka Yi Shahada A Farmakin Da Sojojin Mamayar Isra’ila Suka Kai Kan Sansanin Al-Bureij
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin Zirin Gaza Falasdinawa fararen hula 23 ne suka shahada tare da jikkata wani adadi masu yawa a wani sabon kisan kiyashi da sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila suka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin zirin Gaza. Rahotonni sun bayyana cewa: sojojin mamayar sun kai hare-hare ne ta hanyar jiragen saman kan gidajen jama’a, ciki har da gidan iyalan Al-Qarnawi da ke gabashin sansanin. Haka hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar wani Bafalasdine a yankin Qizan al-Najjar da ke kudancin Khan Yunus. Sannan jami’an ceto sun gano gawar wani Bafalasdine a wani gidan da aka...
Shugaban kwamitin kungiyar Tarayyar Afrika (AU) Mahmoud Ali Youssouf, ya nanata godiyar kungiyar bisa irin goyon bayan da kasar Sin ke ba ta da ma kasashen Afrika a muhimman bangarori kamar na cinikayya da raya ababen more rayuwa da aikin gona da kiwon lafiya da bunkasa kwarewar jami’ai. Wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba, ta ruwaito Mahmoud Ali Youssouf na bayyana haka ne yayin da yake bankwana da Hu Changchun, shugaban tawagar kasar Sin a AU. Shugaban na kwamitin AU ya kuma yaba wa jajircewar Hu tare da gode wa kasar Sin dangane da gudunmuwar da ta bayar na gina Cibiyar Kandagarki da Dakile Yaduwar Cututtuka ta Afrika, da taimakonta ga aikin wanzar da zaman lafiya da sauran taimakon...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
Daga baya, hukumar WAEC ta fitar da sanarwa tana mai bada hakuri, inda ta ce wasu ƙalubale ne suka hana isar da kayayyakin jarrabawa akan lokaci. Wannan lamari ba sabon abu ba ne, domin a watan Afrilu, LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu masu rubuta jarrabawar UTME sun bar gida da asuba domin isa cibiyoyin jarrabawa kafin ƙarfe 6:30 na safe, ba tare da wadataccen tsaro ko sufuri ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shima a nasa jawabin Janar Martin Luther Agwai cewa ya yi, “Aikin wanzar da zaman lafiya na daya daga cikin muhimman aikin Majalisar Dinkin Duniya da ake iya gani, inda sama da sojoji 87,000 ke sanye da rigar wanzar da zaman lafiya da farar hula suka taka rawa a cikin wasu ayyuka 12, daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa Lebanon, daga Sudan zuwa Mali. Nijeriya kuma na wakiltar ayyuka guda 8.” Wadannan jajirtattun maza da mata suna taimakawa wajen daidaita yankuna, ba wa fararen hula kariya, tallafawa tsagaita wuta, da sake gina da amana inda ta lalace. Mahimmanci lamari shi ne, tun lokacin da aka kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta farko a shekara ta 1948,...
A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba. A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata. Wani jirgin sama maras matuki ya kai wani harin a unguwar “Shuja’iyya” wnada ya yi sanadin shahadar mutum daya, sai kuma wasu shahidan 4 a unguwar “Shari’u 5”, da kuma wasu shahidan 4 a garin “Bani-Suhaila”. Wasu rahotannin sun ce, ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a garin ‘Abasan al-kabira’ da ya yi sanadin shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu masu yawa. A yankin Qizan kuwa, ‘yan sahayoniyar sun...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa; Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.” Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.” Haka...
Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin cika shekara 71 da aka gudanar a filin faretin RSM Zakari Kumasi dake harabar makarantar a zaria. Shugaban rundunar mayakan saman ya bayyana cewa makarantar ta NMS ta yi fice wajen baiwa yara horo a fannonin karatu da kuma ilimin aikin soja wanda hakan ya sa ta samar da manyan sojoji da dama har ma da shi a ciki. Air Marshal Abubakar ya ce bukin...
Kazalika, tashar teku ta Duisburg dake kasar Jamus ta kasance cibiyar sufurin layin dogo a tsakanin Sin da yammacin Turai, inda yawan kwantenonin da ake hada-hadarsu a tashar duk shekara suka kai miliyan hudu. Bugu da kari, sufurin layin dogo da ya sada Sin da Turai ya kara bude hanyoyin zuba jarin kamfanonin Sinawa a Duisburg. Sannan ana ci gaba da inganta sufurin dogo ta hanyar sabbin tsare-tsaren da ake kawowa kamar su na jirgin Tea Train da na dakon motocin sabbin makamashi da ake fitarwa zuwa waje, watau New Energy Vehicle Export Train, domin raya cinikayyar Sin da Turai. Har ila yau, layin dogo na Budapest zuwa Belgrade da ya sada kasashen Serbia da Hungary mai kusan tsawon kilomita...
A cikin wani mataki na ci gaba da sauya fasalin bangarorin noma da kiwo, Gwamnatin Jihar Jigawa na shirin kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da daya daga cikin manyan kamfanonin kiwon kaji na kasar Indiya, wato Srinivasa Farms. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar. Ya ce a wani bangare na ziyarar zuba jari a fannin noma da gwamnatin jihar ke gudanarwa zuwa kasar Indiya, tawagar jihar karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi ta kai ziyara ofishin babban kamfanin Srinivasa Farms dake birnin Hyderabad domin tattauna damar hadin gwiwa da nufin farfado da harkar kiwon kaji a Jigawa. Hamisu Mohammed Gumel ya kara da cewa...
Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba. Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba. Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani. Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka. Ministan ya...
A nasu jawabin, kwamishinonin kudi da kasafin kudi Misis Augustina Wandamiya da Mista Emanuel Pridimso sun bayyana cewa, an yi bitar kasafin ne da nufin gano wuraren da aka samu rarar kudi da kuma tabbatar da cewa, an kashe kudin kasafin shekarar 2024 a inda ya dace. Sun kara da cewa, jihar ta kula da tsari wajen aiwatar da kasafin kudi, tare da tabbatar da gaskiya, wanda hakan, ya taimaka wajen samar da kyakkyawan aiki a ayyukan raya jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump a tattaunawa ta wayar tarho da firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bukace shi ya daina shiha a cikin tattaunawar da Amurka take da JMI. Kafin haka dai firai ministan ya sha barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran a dai-dai lokacinda ake tattaunawar. Wanda kuma yake tasiri a cikin abubuwan da ake tattaunawa tsakanin kasashen biyu. Sishshigin da HKI suna zama manya-manyan labarai a kafafen yada labarai na duniya, wanda kuma yakan sa JMI ta maida martani. Don haka kutsawar da HKI take yi yana rikita tattaunawar, wasu suna fadar cewa HKI ce take fadar abinda wakilin Amurka zai fada a tattaunawar. Ya zuwa yanzu dai Washington da Tel Aviv suna da sabanin...
Falasdinawa da dama ne suka ji rauni a jiya Talata a lokacinda yahudawan Sahyoniyya suka bude rumbunajiyar kayakin abinda ga Falasdinawa a garin Rafah na kudancin gaza. Shafin yanar gizo na Afirka News ya bayyana cewa dubban Falasdinawa wadanda suka yi kwanaki 90 basu sami abinci ba saboda rufe kofar shiar da abinci zuwa gaza. Wannan dai yana daga cikin walakanci mafi girma wanda sojojin HKI suka yiwa Falasdinawa a Gaza, tun bayan fara yakin. An kiyasta cewa falasdinawa kimani dubu 180 ne suka fito don karban agajin HKI da Amurka. Sannan jiragen yakin HKI sun yi barin wuta a sama don tsorata falasdinawa masu neman agaji. A yayinda sojojin yahudawa suna harbi a sama don tsoratar da su. Duk...
Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na yankin zirin Gaza da su ka hada da sansanonin ‘yan hijira da kuma rusa gidajen da su ka saura a tsaye. Tashar talabijin din ‘almayadin” ta bayyana cewa; An sami shahidai 7 da safiyar yau Laraba, bayan harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai akan wani gida da yake a Deir-Balah,dake tsakiyar zirin Gaza. A can sansanin ‘yan hijira dake kusa da filin wasa na ‘al-Anan’ kuwa mutane 4 ne su ka jikkata. A yankin Safdawi dake cikin birnin Gaza, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan wani gida wanda ya haddasa gobara, da kuma shahadar mutane 8. A unguwar “Shuja’iyya” sojojin na mamaya sun rushe gidaje da...

Arakci: Idan Birtaniya Ta Ci Gaba Da Batun Dakatar Da Tace Uranium A Iran, Za A Dakatar Da Tattaunawa Da Ita
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Akaci ya bayyana cewa; Idan har kasar Birtaniya tana ci gaba a kiran Iran ta dakatar da tace sanadarin uranium a cikin kasarta, to kuwa Iran din za ta yanke tattaunawar da take yi da ita. Ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya rubuta a shaifnsa na hanyar sadarwa ta jama’a cewa: Iran ta tuntubi Birtaniya ne da kyakkyawar manufa,haka nan sauran kasashen turai da aka yi yarjejeniyar Nukiliya da su, duk da cewa, Amurka ba ta son su shiga cikin tattaunawar.” Arakci ya kuma ce; Idan har matsayar Birtaniya shi ne ta ga an daina tace sanadarin uranium baki daya a cikin Iran, wanda hakan keta yarjejeniyar da ita kanta tana...
Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakan ‘yan tawayen kasar na kungiyar Rapid Support Force daga sansanoninsu da ke kudancin Omdurman Hukumomin sojin Sudan a birnin Omdurman na jihar Khartoum, sun sanar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun tsare sun bar makamai da alburusai da dama da suka hada da haramtattun makamai da aka hana amfani da su a dokokin kasa da kasa, bayan da suka sha kashi a yankin Al-Saliha da ke kudancin birnin. Majiyoyin sun kuma tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawan suka kwace gidajen zaman jama’a da karfi da yaji domin amfani da su a matsayin ma’ajiyar makamai. Yakin baya- bayan nan da sojojin Sudan suka yi da dakarun kai daukin gaggawa...
Gwamnatin Jihar Kano ta cika alƙawarin da ta ɗauka ga al’ummar ƙauyen Gadan, ƙaramar hukumar Gezawa, inda aka kona masallata a lokacin Sallar Asuba. Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Litinin, yana mai cewa gwamnati ta amince da kashe Naira miliyan 151,863,895.97 domin gudanar da muhimman ayyukan ci gaba a garin. Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kona Masallata A Kano Yadda Rikici Ya Yi Sanadin Kashe DPO A Kano Ayyukan sun haɗa da gyara da faɗaɗan masallacin da aka ƙona masallatan a ciki, da ginin sabuwar makarantar Islamiyya da ofishin malamai, da gyaran banɗakuna guda shida, da kuma aikin famfon tuka-tuka mai amfani da...
Wani bafalasdine ya rasa ransa, bayan da harsasai da sojojin yahudawa suka cilla masa a garin Ariha na yankin yamma da kogin Jordan sun fada a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Falasdinawa WAFA ya na fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa Mohammed Yahya Asi Jalaytah ya yi shahada ne bayan da albarusan da sojojin suka cilla masa sun fada a kansa sun kuma ji masa munanan raunuka. Labarin ya kara da cewa bayan tsakiyar dare ne sojojin yahudawan suka soma barin wuta da bindigogi da kuma jefa hayaki mai sa hawaye a kan Falasdinawa a garin Ariha, Inda albarusai suka sami Asi Jalaita suka kuma kasashe shi. WAFA...
Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin. Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun falasdinawa a yakin shekara 1967 tsakanin yahudawan da kuma larabawa. Birnin Qudus ta gabas dai nan ne masallacin Al-aksa yake, kuma nan ne Falasdinawa suke da dama. Yahudawan dai su na ganin dukkan birnin Qudus wanda ya hada har da inda masallacin Al-aksa yake mallakinsu ne kuma su na da shirin rusa masallacin don gina wurin bautansu a inda masallacin yake.
Kasar Spain ta bukaci kasashen duniya dasu kakabawa Isra’ila taklunkumi saboda ci gaba da yin fatali da kiraye-kirayen da ake matana tadakatar da yakin da take a Gaza. Ministan harkokin wajen Spain José Manuel Albares ya ce kamata ya yi kasashen duniya su kakabawa Isra’ila takunkumi domin kawo karshen munanan hare-haren soji a zirin Gaza da aka yi wa kawanya. Shugaban diflomasiyyar Spain yana magana ne gabanin wani babban taron kasashen Turai da na Larabawa da za a yi ranar Lahadi a Madrid. “Dole ne mu komai, don kawo karshen wannan yakin,” in ji shi. M.Albares ya bukaci a shigar da agajin jin kai, ba tare da wani sharadi ba, ba tare da tsangwama ba, ta yadda Isra’ila ba ta...
Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai hari a makarantar Fahmi al-Jarjawi da ke yankin Daraj na zirin Gaza, inda daruruwan iyalai da suka rasa matsugunansu daga garin Beit Lahia da ke arewacin kasar da Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai suka samu mafaka. Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwakinmutum 20 daga makarantar, ciki har da yara da dama. A...
Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana. Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara suna gudu a cikin wuta suna kokaron kubutar da kansu. Labarin ya kara da cewa makarantar tana unguwar Daraj na birnin Gaza, mai suna Fahmi al-Jarjawi. Majiyar kungiyar kula da fararen hula a gazar ta bayyana cewa yahudawan kai hare haren a safiyar yau litinin a lokacinda suke barci. Labarin ya kara da cewa a cikin wadanda yahudawan suka kashe a Gaza, akwai Mohammad Al-kasih...
Shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar Burtaniya ya bayyana cewa HKI tana yakar Falasdinawa a Gaza ne a madadin gwamnatin kasar tunda har yanzun gwamnatin kasar Burtaniya tana ganin gwamnatin HKI tana kare kanta daga mayakan Hamas, kuma bata daukar abinda HKI take yi a Gaza, kissan kiyashi ne. Badenoch shugaban jam’iyyar ‘ Conservative’ ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Sky News dake birnin London a jiya Lahadi. A lokacinda aka tambaye shi idan ya yarda da maganar Banyamin natanyaho kan cewa hamas yan ta’adda ce, kuma yana kokarin kwace gaza da shafi yan ta’adda ne, sai shugaban Conservative ya ce banzo nan don binciken kalmomin Natanyahu ba. Abinda nake son bada sanarwansa shi...
Hare-haren sojojin HKI a yankin Gaza sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 57 Majiyar Asibiti a yankin na Gaza,ta sanar da cewa sojojin mamayar sun kai hari ne akan makarantar ” Fahmi al-jarjawi” wacce take a yankin al-Darj’ a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 25.” Harin ya yi sanadiyyar konewar gawawwakin shahidan da kuma tashin gagarumar gobara a makarantar da ‘yan hijira Falasdinawa suke ciki. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa ya haura dubu 53 da 939. Haka nan ma’aikatar ta ce; Wadanda su ka jikkata kuwa a wannan tsakanin sun kai dubu 122 da 797. Sojojin HKI sun shelanta yaki ne...
Daga Bello Wakili Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman, ya bayyana jerin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu daga cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin shaida mai karfi kan tsare-tsaren da gwamnati ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata. A yayin wata tattaunawa da ya yi da Radio Nigeria a Abuja, Mista Rahman ya ce goyon bayan da ke fitowa daga gwamnoni na APC, ‘yan majalisar dokoki da shugabannin jam’iyya, na nuna karuwar amincewa da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ya aiwatar. Ya ce wannan ya hada da cire tallafin fetur da daidaita farashin canjin kudade. “Wadannan goyon bayan suna da matukar...

‘Yar Majalisar Dokokin Ireland Ta Yi Suka Kan Shugabannin Turai Tare Da Neman Afuwa Daga Falasdinawa
‘Yar majalisar dokokin Ireland ta yi kakkausar suka kan shugabannin Turai tare da neman afuwa daga Falasdinawa Tana jaddada cewa: Muggan makaman gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da lakume rayukan fararen hula a zirin Gaza. Sannan a wani sabon kisan kiyashi, an kashe Falasdinawa 7 a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza. A wani kisan kiyashi kuma jami’an tsaron farar hula a Gaza sun sanar da mutuwar yara tara da suka kone kurmus a wani harin da sojoji mamayar Isra’ila suka kai kan Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza da aka killace. An kuma kashe wani Bafalasdine tare da raunata wasu a wani harin da...
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce goyon bayan da wasu gwamnonin APC suka nuna wa Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a 2027 bai dame su ba. Ya ce su a cikin ƙungiyarsu ta masu haɗaka sun fi mayar da hankali ne kan talakawa, ba shugabanni ba. Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai “Ko da dukkanin gwamnonin jihohi 36 da Abuja sun koma APC, babu abin da zai canja. “Su da danginsu ba su fi ƙuri’u 1000 ba. Abin da muke so shi ne jama’a,” in ji Lawal a hirarsa da jaridar Nigerian Tribune. Ƙungiyar masu...

Masu Zanga-Zanga A Mafi Yawan Kasashen Turai Sun Bukaci Kasashen A Kawo Karshen Kissan Kiyashi A Gaza
Dubban daruruwan masu zanga-zanga a biranen Barlin Paris da kuma Stockholm ne suka bukaci gwamnatocin kasashensu su kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a gaza, su kuma tabbatar da cewa abinci ya isa gaban Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zangar sun kira ga gwamnatocin kasashensu su dakatar da bawa HKI makaman da take kishe falasdinawa da su. A birnin Berlin da kasar Jamus dubban Jamusawa sun hadu a dandalin at Oranienplatz inda suke rera taken ‘a bawa Falasdinawa yenci, HKI yar ta’adda ce, kuma gwamnatin Jamas ta dakatar da tallafin da take bawa HKI. Labaran sun kara da cewa hatta mutanen kasar Jamus yan asalin yahudawa sun fito sun bayyana...
Jaridar ;The HIL’ ta kasar Amurka wacce take bada labaran majalisa da siyasar gwamnatin Amurka ta gargadi gwamnatin shugaba Donal Trump kada ta sake irin kuskuren da shugaban kasar Iran Sadam Hussain yaki na fadawa kasar Iran da yaki, tare da tsammanin cewa a cikin yan kwanaki zai ga faduwar jaririyar gwamnatin kasar Iran a lokacin. Amma sai wankin hula ya kai masa dare, inda ya share shekaru 8 yana fafatawa da mutanen kasar Iran ba kuma tare da samun nasarar ba. Jaridar ta kara da cewa Iran ba kasace wacce tana dab da faduwa ne sai aje a karasa faduwarta ba. Kasashen wacce kan mutanen kasar a hade yake a duk lokacinda na waje yayi kokarin mamayar kasar. Labarin...
Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki. Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da cewa; yadda al’ummar Iran su ka yi gwagwarmayar ‘yanto da garin Khurramshahr, bayan tsawon shekaru 8 na yaki, ya sa Amurka ta fahimci cewa yaki da Iran yana da tsada da kuma hatsari; kuma da ace sun san za su yi nasara ta hanyar karfin soja da ba su zauna akan teburin tattaunawa ba. Janar Sanaei ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su...

Afirka Ta Kudu Ta Zargi Shugaban Kasar Amurka Da Rashin Dalili Akan Zargin Yi Wa Fararen Fatar Kasar Kisan Kiyashi
Ministan ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi wa fararen fatar kasar kisan kiyashi a yayin ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai. A yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Amurka ya kunna wani faifen bidiyo da a ciki aka nuna gicciye a gefen hanya domin tunawa da fararen fata manoma da aka yi wa ksian gilla. Ministan ‘yan sandan kasar ta Afirka ta kuku Senzo Mchunu ta cewa; Wadannan gicciyen ba su nuni da cewa suna akan kabarurruka ne, ko wani wuri na tunawa da matatu, an Sanya su ne a 2020 domin tunawa da dukkanin...
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya. “Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara. “Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan...
Majiyoyin tsaro sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida kafin sanar da tsagaita bude wuta a ranar Larabar da ta gabata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ofishin yada labaran Gaza ya bayar da rahoton mutuwar Falastinawa 299 da suka fada cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, da karancin kayan masarufi da magunguna. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera na cewa, taimakon jin kai na cikin hadarin rubewa saboda haramcin da gwamnatin sahyoniyawan ta kakabawa na shiga Gaza a yayin da al’ummar zirin ke fama da yunwa. Ofishin yada labarai na Gaza ya kara da cewa: Gwamnatin Sahayoniya ta yi ikirarin cewa ta ba da izinin shigar da ayarin motocin agaji yayin da manyan motoci 300 ne kawai suka shiga zirin Gaza. Gwamnatin mamayar ta tilasta wa ayarin motocin agaji bin hanyoyin da ke da hatsarin gaske. Har ila...
Don haka, CHINADA tana nuna matukar adawarta ga duk wani yunkuri na bayyana shan kwayoyi masu kara kuzari a matsayin wai ci gaban kimiyya, tare da yin kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a harkar wasanni na duniya da su tashi tsaye, su hada kai wajen yin fatali da wasannin da aka amince a sha kwayoyin kara kuzari. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Idan ajiyewa za ki yi sai ki samu roba mai murfi, ki rufe sosai saboda kada ta yi kwari. Yadda za ki tuka: Sai ki dora ruwa a wuta, ya tafasa ki dauko garin doyar, ki rage wuta kina zubawa da kadan-kadan kina tukawa har ya tuku, ki tabbatar bai yi kulalai ba duk kin tuke shi, sai ki dan zuba ruwa kadan ki daddanna ki rufe ki barshi ya yi kamar minti 15, sai ki sauke ki sake tukawa, ki samu leda ki kwashe abinki, shi kenan kin kammala. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran bata amince da kafa kasashe biyu a matsayin hanyar warware rikicin Falasdinawa ba, saboda kafa kasashe biyu ba zai bawa Falasdinawa hakkinsu ba saboda matukar akwai ikon da HKI take da shi a yakin Falasdinawa ba zasu taba samun hakkinsu ba. Bil’hasali ma kasashe biyu a fahintar mu zai kara wahalar da Falasdinawa ne fiye da hadda suke sha a halin yanzu. Ministan ya bayyana haka ne a lokacinda ya kai ziyara birnin Vatikan na kasar Italiya inda ya gana da Cardinal Pietro Parolin a jiya Jumma’a. Aragchi ya kara da cewa an dade ana maganar raba gardamar ta hanyar kasashen biyu. Al-hali ba wanda ya amince da kafa kasashen biyu...
Jaridar “Maariv” ta buga labarin da yake cewa; Tattauanwa a tsakanin “Isra’ila” da kasashen Afirka akan yadda za su bayar da dama ga mutanen Gaza da su yi hijira zuwa can, ta yi isa sosai. Rahoton jaridar na jiya Juma’a ya ci gaba da cewa; Tattaunawar ana yinta akarkashin damar da za a bai wa Mutanen Gaza su yi hijira cikin zabin kansu, zuwa wasu kasashen na Afirka, kuma Amurka tana cikin wadanda ake tattaunawar da ita da wadannan kasashen na Afirka. Haka nan kuma jaridar ta ‘yan sahayoniya ta ce, kasashen da ake tattaunawa da su, sun nuna amincewarsu a matakin na farko ka karbar bakuncin mutanen Gaza. Tattaunawar dai ta kunshi yadda za a gina matsugunan Falasdinawan da...
A jiya Juma’a miliyoyin mutane Yemen sun cika dandalin ” Saba’in” dake birnin Sanaa, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu. An bai wa gangamin taken: ” Muna tare da Gaza” domin jaddada ci gaba da nuna goyon bayan al’ummar Falasdinu da suke fuskantan kisan kiyashi daga sojojin HKI, da kuma nuna kin amincewa da jefa mutanen yankin cikin yunwa. Masu gangamin sun yi tir da yadda kasashen larabawa da na musulmi su ka nuna gajiyawa da kuma yin abin kunya saboda yadda su ka yi shiru akan abinda yake faruwa da mutanen Gaza. Bugu da kari a yayin wannan gangamin an yi jinjina ga sojojin kasar da suke kai wa HKI hare-hare da kakaba takunkumi akan tasoshin jiragen...
Onyemekara ya sanar da cewa, rahoton na karya da kafar yada labaran ta wallafa kan zargin cin hancin na biliyoyin Naira, na kanzon Kurege ne, wanda kuma bai da wata tushe, ballantana wata makama. Kazalika, ya bayar da tabbacin cewa, NPA kamar yadda ta saba, za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa gaskiya da rikon amana, musamman kan abinda ya shafi, ayyukan kashe kudade. Onyemekara ya kuma yi watsi da batun zargin badakalar hada-hada a ofishin Hukumar NPA da ke a Birtaniya, inda ya sanar da cewa, babu wani batun wata hada-hadar ayyuka a ofishin makamancin haka, da aka gudanar a ofishin. Ya yi kira ga kafafen yada labarai na kasar nan, da su tabbatar da suna tuntubar...
Kasashen Sin da na ASEAN sun kammala tattaunawa game da kafa yankin ciniki cikin ‘yanci na Sin da ASEAN (CAFTA) karo na 3, wanda ke aikewa da sako mai karfi na goyon bayan gudanar ciniki cikin ‘yanci da hadin gwiwa mai bude kofa. A cewar Mao Ning, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, hakika wannan labari ne mai dadi, tana cewa, wani muhimmin mataki ne na rattaba hannu kan yarjejeniyar daukaka yankin a karo na 3. Ta kara da cewa, Sin da kasashen ASEAN, dukkansu masu goyon bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya ne da cudanyar bangarori da dama, haka kuma yankin na CAFTA na 3, zai taimakawa Sin da kasashen wajen kara zurfafa budewa juna kofa da samun ci gaba...
An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027. Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.” Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya. Kazalika, Ganduje...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Matsayin Amurka a cikin ɗakin tattaunawa da Iran ya bambanta da abin da suke shelantawa a waje Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Kalamai da matsayar da jami’an Amurka suka dauka a cikin dakin tattaunawa da Iran suna shan bamban a fili da abin da suke bayyanawa a bainar jama’a, yana mai cewa wannan sabani yana dakushe kwarin gwiwar bangaren Iran da kuma yin barazana ga makomar shawarwarin. A wata hira da ya yi da mujallar Der Spiegel ta Jamus, Takht-Ravanchi ya bayyana kin amincewar da Iran ta yi da bukatar “samar da sifili na Uranium da take sarrafawa”, yana...
An dai haifi Dakta Mubarak a Unguwar Hausawa Masallacin Murtala, da ke Karamar Jukumar Kumbotso ta Jihar Kano a Nijeriya. Ya yi karatun Firamare a Hausawa Model ta Jihar Kano; ya yi karatu a Kwalejin Kimiyya ta jeka ka dawo a Kano; daga nan ya tafi zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudi, inda a nan ne ya samu digiri na farko. Ya samu digiri na biyu a fannin noma da gandun daji; sannan ya samu digirin-digirgir kan Agro Paris Tech, Paris, a Kasar Faransa, ya sake yin karatun digiri na biyu a fannin sanin yanayi, Amfanin Kasa da Ayyuka na Muhalli; ya kuma samu digirin-digirgir a Jami’ar Paris a fannin Ecology. Ya yi aiki a...
A halin yanzu, jihohin da ke saman tebur wajen samun kyauttuka sun haɗa da Legas, Ogun da kuma Birnin Tarayya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
El-Rufai ya yi kira ga alkalai da lauyoyi da su ji tsoron Allah su koma kan asalin aikin da ke gabansu tare da himmatuwa wajen wanzar da adalci da gaskiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki? Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din. Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka? Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ganduje ya ce, baya ga samun nasara a jihohi 22 a cikin 36 da ke kasar nan, karin gwamna daya na kan hanyarsa ta komawa jam’iyyar nan ba da dadewa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp