2025-12-05@23:16:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12208
«a ƙasar Chana»:
Daga Usman Muhammad Zaria Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da gagarumin cigaba a harkar noma da Gwamna Umar Namadi ya samar cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa. Ya bayyana haka ne a masarautar Gumel cikin Jihar Jigawa, yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da Gidauniyar Kashim Shettima ta gina a matsayin wani ɓangare na bikin zagayowar cikar Sarkin Gumel shekaru 45 a kan karaga. A cewarsa, abin sha’awa ne yadda Gwamna Umar Namadi ya mayar da harkar noma a jihar Jigawa zuwa ta zamani cikin shekaru biyu kacal. Ya jinjina wa Gwamnan da al’ummar Jihar Jigawa bisa wannan ci gaba mai armashi. Kashim Shettima ya kara taya Sarkin Gumel, Alhaji Muhammadu Sani, murnar cika shekaru 45...
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026. Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026. Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara Rabon jadawalin ya gudana ne a birnin Washington na ƙasar Amurka a ranar Juma’a, inda Ingila ta samu kanta a rukuni ɗaya Croatia. Brazil za ta kara da Maroko, yayin da Amurka za ta kara da Australia. Faransa za ta ɓarje gumi da Senegal, sannan Argentina za ta fafata da Austria. Ga jerin yadda kowane...
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki. Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP. Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15 A ranar Juma’a, ‘yan majalisar Ribas guda 16, ciki har da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, da suka sauya sheƙa zuwa APC. Amaewhule, ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rarrabuwar kai da aka samu a PDP. Hakazalika, kakakin ya ce yana son ya yi aiki tare da...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama. Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15 Zulum ya yaba wa jami’an tsaro da al’umma kan ceto manoman mata 12 da aka yi garkuwa da su. Gwamnan, ya ce matsalar tsaro na hana samar da manyan ayyukan ci gaba a yankin. Ya kuma sake alƙawarin gina makarantu, asibiti, hanyoyi, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, tare da haɗin gwiwar maharba, sun samu nasarar tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane, tare da kama mutum bakwai da ake zargi da aikata laifuka a Jihohin Gombe, Bauchi, Yobe da Adamawa. Rundunar ta samu nasarar ne bayan kama Abdullahi Ibrahim, mai shekaru 40 daga ƙauyen Tilde a Funakaye, a ranar 23 ga watan Nuwamba 2025. An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara An kama shi ne bayan samun bayanan sirri kan hulɗa da masu satar shanu. Abdullahi, ya amsa cewa yana da hannu a garkuwa da mutane tare da bayyana sunayen waɗanda suke aikata laifin tare. A cewar kakakin...
It might be a daunting experience because making professional voiceovers may seem like a challenging process, particularly when you either do not want to use your own voice or you lack access to audio equipment with higher quality. Fortunately, CapCut PC makes this whole process easier with its strong text to speech AI services. YouTube recordings, educational tutorials, brand explanation, social media, don’t matter: CapCut provides the flexibility to cut a clean, professional, natural-sounding narration within a matter of minutes. You will also get to know in this article how to incorporate an AI avatar into your content to achieve even more compelling outcomes. Why Use CapCut PC for Voiceovers? Voiceovers have traditionally involved the use of microphones, silence, and...
Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo. A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take. Rundunar ’yan sandan...
Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa wasu masu safarar kaya suna kai magunguna daga Sakkwato domin kula da ’yan fashin daji da suka samu raunuka a dazukan jihar. Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi Majiyoyin tsaro sun ce da dama daga cikin waɗannan ƙungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga a fafatawar...
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara. Muna tafe da karin bayanai…
Kasashen Iran da Pakisatan sun amince sun dawo da zirga-zirgan jiragen kasa tsakanin birnin Istambul na kasar Turkiyya zuwa birnin Tehran na kasar Iran da kuma birnin Islamabda na kasar Pakistan a cikin wannan shekarar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran yanakalto jakadan kasar Iran a Islamabad Dr RezaAmiri Moghaddam yana fadar haka a lokacin ganawarsa da ministan zirga-zirgan jiragen kasa na kasar Pakisatan Mohammad Hanid Abbasi a birnin Isla,abad. Ya kuma kara da cewa zasu farfado da layin dogon a cikin wannan shekara ta 2025 sannan karkashin tsarin nan na ITI masu jigilar kaya da kuma na fasinja. Labarin ya kara da cewa idan hakan ya tabbata, wannan zai farfado da daya daga cikin layukan dogo masu muhimmanci...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare guda ta kasa da kasa wacce ba’a dade da samar da ita a farkon wannan shekarar. Isma’el Baghaei ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Alhamis, inda yayi tir da Amurka wace ta fara fara dorawa JMI takunkuman tattalin arziki tun fiye da shekaru fiye da 40 da suka gabata. Kuma hakan take hakkin bil’adama. Yace a farkon wannan shekarar ne dai...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya jagoranci taron rattaba hannu kan yarjeniyar sulhuntawa da kuma kawo karshen yakin gabacin Kongo tsakanin shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da tokwaransa na kasar Kongo Felix Tsetsekedi a birnin Washington a jiya Alhamis. Shafinyanar gizo na labarai ‘AfricaNews” ya bayyana cewa, shuwagabannin biyu sun rattaba hannun kan wannan yarjeniyar ne a gaban kafafen yada labarai da dama a duniya. Kuma a ganin masana shugaba Trump yana neman suna ne kawai da wannan yarjeniyar. Saboda babu tabbas kan cewa zaman lafiya zai dawo yankin Kivu na gabacin kasar Kongo. Banda haka, sun bayyana cewa hatta a dai dai lokacinda ake bikin rattaba hannu a kan yarjeniyar akwai labaran da suke tabbatar da cewa ana...
Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a gaban sanatoci a jiya Alhamis. Kafin haka shugaban ya gabatar da sunayen wasu yan siyasa 3 don nadasu jakadu. A cikin wasikar shugaban yace mutane 34 daga cikinsu kwararrun jakadune, sannan sauran 31 yan siyasa ne. Daga cikin wadanda shugaba yanada har da tsohon shugaban hukumar zabena kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu) sauran sun hada tsoffin gwamnonin jihohin. Enugu, Abia, tsohon mataimakin gwamnan...
Pars Today – Vladimir Putin ya yi tafiya zuwa Indiya don ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu. Vladimir Putin, shugaban Rasha, ya isa New Delhi a ranar Alhamis, 4 ga Disamba, a ziyararsa ta farko zuwa Indiya tun bayan fara yakin Ukraine a 2022. Ziyarar ta kwanaki biyu na da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin tsaro da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu. Putin yana tare da wata babbar tawaga wacce ta haɗa da ministan tsaron Rasha. Ana sa ran zai halarci wani cin abincin dare na sirri tare da Firayim Ministan Indiya Narendra Modi, sannan tattaunawa ta hukuma da zaman tattalin arziki, gami da taron kolin shekara-shekara na 23. A lokacin ziyarar, ana sa ran ɓangarorin biyu za su sanya hannu kan yarjejeniyoyi...
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa. Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa “Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2...
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghaei ya yi Allah wadai da kakkausar murya da sanarwar bayan taron shugabannin Kasashen Yankin Tekun Farisa (GCC) wanda suka fitar game da tsibiran Iran guda uku. Baghhaei ya nuna takaici kan dagewar da kungiyar GCC ta yi kan maimaita ikirari maras tushe na Hadaddiyar Daular Larabawa game da tsibiran Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb na Iran. Ya yi Allah wadai da ikirarin da ke cikin sanarwar karshe ta taron kolin GCC karo na 46 game da wadannan tsibirai na kasar Iran, yana mai jaddada cewa Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb muhimmin bangare ne na yankin Iran kuma duk wani ikirari sabanin hakan ba shi da inganci, kuma a bayyane...
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa. Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa “Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2...
A ranar Alhamis ne fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta sanar da cewa kasar za ta dauki hutu daga halartar tarukan G20 yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke jagorantar kungiyar a karkashin tsarin karba-karba, bayan da gwamnatinsa ta tabbatar da cewa ba za ta gayyaci Afirka ta Kudu a taro mai zuwa ba. Amurka ta karbi shugabancin G20 na karba-karba a makon da ya gabata, bayan kauracewa taron da Shugaba Cyril Ramaphosa ya shirya a Johannesburg. “A wannan lokacin a shekara mai zuwa, Birtaniya za ta karbi shugabancin G20. Za mu iya shiga cikin batutuwan da suka shafi duniya,” in ji mai magana da yawun Ramaphosa, Vincent Magwenya. “A yanzu haka, za mu dakatar da shirye-shiryen kasuwanci har...
Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa
Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan. A cikin wata budaddiyar wasika da aka aike wa kamfanin a ranar 2 ga wannan watan, wata kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa Microsoft da shugabanninta za su iya fuskantar hukunci na shari’a kan taimakawa da kuma tallafawa laifukan da aka aikata wa fararen hula Falasdinawa. Eric Saib, mai kula da harkokin ci gaban kafofin watsa labarun kasa da kasa na Cibiyar Larabawa don Ci gaban Kafafen Yada Labarai, ya jaddada cewa watannin baya-bayan nan sun nuna karara cewa ana amfani da ayyukan kamfanin wajen take hakkin...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da cewa tana sake duba dangantakarta da Tanzania a daidai lokacin da ake samun abin da Amurka ta kira damuwa game da ‘yancin addini, ‘yancin fadin albarkacin baki, cikas ga ayyukan zuba hannayen jarin Amurka, da kuma cin zarafin fararen hula. Amurka ta bayar da gargadin tsaro ga Amurkawa a kasar da ke Gabashin Afirka bayan babban zaben watan Oktoba, wanda zanga-zangar ta mamaye shi. Kungiyoyin kare hakkin dan adam, jam’iyyun adawa, da Majalisar Dinkin Duniya sun bayar da rahoton cewa an samu matsaloli bayan zaben, duk da cewa dai gwamnatin kasar ta musanta alkaluma na asarorin da aka samu, tana mai kiransu da alkalumman karin gishiri. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce kasar...
Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale
Hassan Fadlallah wanda dan majalisar kasar Lebanon ne daga kungiyar Hizbullahy a bayyana cewa; gwargwadon yadda ake ja da baya a gaban makiya, suke kara samun karfin gwiwa,don haka da akwai bukatar hadin kai a tsakanin kasashen larabawa da na musulmi domin fuskantar kalubalen dake gaba. Shi dai Hassan Fadlalalah yana halartar taron majalisun kasashe nahiyar Asiya da ake yi a birnin Mashhad na Iran, ya bayyana cewa: Laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi, yana nuni ne da yadda su ka kai koli wajen nuna keta a kan kasashen da suke da cin gashin kai da ‘yanci, da hakan yake a matsayin karya zaman lafiya da sulhu na duniya. Fadlallah ya kuma yi jinjina ga jamhuriyar musulunci ta Iran akan...
Rahotanni daga kasar Lebanon sun ambaci cewa da marecen yau jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garuruwan Mahruna,jibaa, Bar-ishit da Majadil dake kudancin Lebanon. Hare-haren sun rusa gidaje da dama na garuruwan da su ka kai wa harin. Wannan harin dai yana faruwa ne kwana daya bayan da Lebanon ta aike da wakili a cikin kwamitin ttataunawa da ‘yan sahayoniyar da tsohon jakadan kasar Simon Karam yake wakiltarta. Tashar talabijin din almanar ta ambato ofishin karamar hukumar garin Mahrunah tana yin tir da wannan harin wanda ya rusa wani gida na fararen hula a tsakiyar unguwa. Bayanin ya ci gaba da cewa; Kai hari a tsakiyar unguwar fararen hula keta dokokin ‘yan adamtaka na duniya. Kuma abinda...
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Canada sun shigar da kara ga jami’an ‘yan sandan kasar, da kuma ma’aikatar shari’a da su kama tsohon Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Olmert da kuma ministan harkokin waje Tzipi Livni bisa rawar da su ka taba a baya a laifukan yaki a Gaza a tsakanin 200-2009. Kungiyoyin sun bukacin ganin an fitar da sammacin kamo ‘yan sahayoniyar biyu a bisa dogaro da dokokin kare hakkin dan’adama da laifukan yaki na kasar Canada, saboda kasar tana karkashin yarjejeniyar Geneva ta 4 da ta bukaci kasashe su hukunta masu irin wadannan laifukan. Bugu da kari, kungiyoyin sun ce Olmert wanda ya yi fira minista daga 2006 zuwa 2009, shi ne mai rike da mukami...
Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ce an kashe shugaban kungiyar ‘yan daba na Gaza Yasi Abu Shaba,ba tare da an tantance wanda ya yi hakan ba. Kafafen watsa labarun “Isra’ilan”sun ce; Kashe Abu Shabab wani mummunan labari ne ga Isra’ila.” Tashar talabijin 12 ta ambato wani jami’in tsaro yana cewa; Abu Shabab ya cika ne a asibiti saboda raunin da ya samu daga harbin da aka yi masa a wani sabani na cikin gidan.” Sai dai wata majiyar ta ce, da akwai yiyuwar kungiyar Hamas ce ta kashe shi, bayan da ta tattara bayanai akansa daga makusantansa. An fara jin duriyar Abu Shabab ne a ranar 30 ga watan Mayu 2025 bayan da kungiyar Hamas ta watsa wani faifen bidiyo...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin bude tayin bada kwangilar samar da wutar lantarki a wasu garuruwa dake kananan hukumomin Jihar. A lokacin da yake jawabi a yayin gudanar da bikin daya gudana a sakatariyar Jihar dake Dutse, Shugaban hukumar, Injiniya Zubairu Musa ya bayyana cewar tayin bada kwangilar samar da wutar da gyara da fadadawa gami da kammala wasu ayyukan za a yi sune a garuruwa 17. Kazalika, Injiniya Zubairu Musa, yace wannan na daga cikin kudirori 12 na Gwamna Umar Namadi na hada wutar lantarki a kanana da matsakaitan garuruwan jihar da basu da wuta. A cewar sa, garuruwan da za’a samar da wutar lantarkin a Dutse sun hada da Sabuwar Takur...
Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa Ya ce ana zargin matashin ne mai shekaru 17 da aka fi sani da Amir, wanda makanike ne da kashe matar ta hanyar daba mata wuka. Wani makwabcin wajen ya shaida cewa ana zargin matashin ne...
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce Amurka na ɗaukar mataki mai ƙarfi kan munanan ayyuka da tashin hankali da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya. NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia “Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka (@StateDept) za ta takaita bizar Amurka ga waɗanda suka san da...
Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncina Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa Musulunci yana bai wa mata matsayi mai girma da daidaito tsakanin maza a rayuwar zamantakewa da siyasa, yayin da yake Allah wadai da “al’adun kasashen Yammacin duniya ” game da mata. “Maganar Alkur’ani game da asali da halayen mata ita ce mafi girma,” in ji Ayatollah Khamenei a ranar Laraba, a wata ganawa da dubban mata daga yankuna daban-daban na kasar. A cikin jawabinsa, Jagoran ya yi nuni da halayen Fatemeh Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta), ‘yar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da zuriyarsa), yana yabon matan Iran saboda “suna samun wahayi daga irin wannan haske mai...
Iran ta yi watsi da zarge-zargen da wakilan gwamnatin Isra’ila da gwamnatin Yemen mai murabus suka yi a zaman taron hukumar kula da harkokin teku ta duniya (IMO) karo na 34. A wata wasika da ta aike wa Sakatare Janar na IMO Arsenio Dominguez, Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kungiyar da ke Landan a ranar Laraba, ya bayyana damuwarsa game da yadd Isra’ila kesarrafa hukumar IMO don manufofinta. Wasikar ta jaddada cewa wannan dabi’a tana wargaza kwarewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a harkokin teku. Tawagar Iran ta kara da cewa wadannan zarge-zargen marasa tushe wani bangare ne na wani tsari da Isra’ila ke kokarin lalata dokokin kasa da kasa, raunana hanyoyin da suka shafi bangarori daban-daban, da...
MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu kudurori guda biyu da ke kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan na Siriya. Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Falasdinu ne suka gabatar da daftarin kuduri game da Falasdinu. Kasashe 151 ne suka kada kuri’a a kan hakan, yayin da kasashe 11, ciki har da Amurka, suka ki amincewa da hakan, sai kuma wasu 11 da suka ce ba ruwansu. Kudirin da aka amince da shi ya sake tabbatar da alhakin Majalisar Dinkin Duniya game da batun Falasdinu tare da yin kira da a kawo ƙarshen mamayar Isra’ila a yankunan da aka mamaye tun 1967, yayin da yake goyon bayan samar da kasashe guda...
Rundunar Sojan Ruwa ta IRGC ta fara wani atisayen soji a yankin kudancin Iran a Tekun Fasha, wanda ya kunshi rundunonin sojoji da dama. An yi wa atisayen lakabi da “Eightedar” (Ikon Kasa), domin girmama kwamandan da ya yi shahada Mohammad Nazeri, wani babban jami’in sojin ruwa na IRGC. Ana gudanar da atisayen a cikin ruwan Tekun Fasha, yankin tekun Nazeat (Abu Musa, Greater Tunb, Lesser Tunb, da Tsibiran Siri), Mashigar Hormuz. Abin lura ne cewa Mohammad Nazeri shi ne kwamandan rundunonin kwamando na rundunar sojin ruwa ta IRGC. An san shi sosai a Iran saboda rawar da ya taka wajen kama ma’aikatan jirgin ruwan Amurka goma—maza tara da mace daya—wadanda suka shiga ruwan Iran a ranar 12 ga Janairu,...
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene. Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja. Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa. Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a. Ya ce...
Dan wasan taekwando na kasar iran Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center dake kasar kenya kimanin yan wasa 452 da suka fito daga kasashen duniya 75 ne ke halartar gasar, kuma iran ta shiga gasar da yan wasa guda 16 da suka hada da mata 6 da kuma maza 8 da za su yi tasu karawar acikin kwanaki 4. Zandi da ya samu lambar yabo ta zinairiya a baya –bayan nan ya nuna gwaninta da ya cancanci...
Rahotanni sun bayyana cwa kungiyar Hamas tace za ta mikawa isra’ila sabon samfurin jikin dan Adama da ta samu a arewacin gaza, bayan da isra’ila ta yi ikirarin cewa gawarwakin da kungiyar gwagwarmaya ta basu ba su daga cikin gawarwaki guda biyu da su ke rike da su da har yanzu ba’a dawo da su ba, Kungiyar ta hamas ta bayyana cewa dakarunta da hadin guiwa dakarun kungiyar jihadil Islami suna aiki tare kuma sun gano wani burbushin jikin dan adam da suke ganin yana da alaka da bayahuden da suka kama ne beneath a karkashin burabutsai a yankin beit lahia, Kuma za ta mika samfurin zuwa isra’la ta hannun babban kwamitin kungiyar bada agaji ta red cross ta ksa...
Iran Ta ce Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya gargadi Amurka da kawayenta game da tsaron tekun fasha da mashigar Hurmuz, yace tsaron wadannan muhimman wurare jan layi ne ga kasar iran da zata mayar da martani mai tsanin ga duk wanda ya taba su Brigadier Janal Ali Fadavi da yake bayani game da muhimmancin mashigar Hurmuz ya fadi cewa babu wata yarjejeniya da za’a yi game da samun tabbaci ga makamashi na duniya, inda sama da ganga miliya 20 take wucewa ta wannan mashigar kullum , kuma duniya ta dogara ne da makamashin na tekun fasha Janar fadavi ya bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na kasar iran sun shirya tsaf wajen kare wannan yankin mai...
Gamayyar Kungiyoyin kare hakkin bil adama har da palastinian center for human right sun aike da takaradar korafi ga bangaren shari’a na kasar Kanada inda suka bukaci a kamam tsohon pira ministan Isara’ila Egud Olmaert da kuma tsohowar ministan harkokin wajen isra’ila tzipi Livnin idan suka kawo ziyara birnin Toranto. Zargin yayi dadai da dokar yaki da kare hakkin bil adama da kuma laifukan yaki mai lamba 146 na yarjejeniyar janeva da ta tilasta gwamnati ta kama wadanda ake zargi da keta dokokin , Olmert da Livnin suna da zarge-zarge akan su, da tafka laifukan yaki da kuma cin zarafin dan adama a shekara ta 2008 zuwa 2009 a yankin Gaza. Olmert da Livni suna fuskantar zargi iri daya ne...
Majalisar Dattawa a najeriya ta amince da tsohon hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin sabon Ministan Tsaro bayan tantance shi da aka dauki kusan awanni biyar. A lokacin tantancewar, Musa ya ce zai inganta tsaro ta hanyar hada kai tsakanin sojoji, ’yan sanda, sauran hukumomin tsaro da al’ummomi. Ya yi gargaɗin cewa ’yan ta’adda na kai hare-hare a Nijeriya ne saboda suna ganin kasar tana da arziki, Ya kuma yi alkawarin magance gibin tsaro da aka samu da kuma kara hadin gwiwa da kasashen makwabta. Ya yi nuni da cewa sojoji kadai ba za su iya magance matsalar tsaro ba, ya jaddada bukatar kyakkyawar gwamnati da goyon bayan al’umma. Sanatoci sun yaba da kwarewarsa kuma suka...
Jirgin Fadar Shugaban Kasa da Gwamnatin Najeriya ta saka a kasuwa da nufin sayarwa ya kasa samun mai saye kusan watanni biyar bayan ɗora shi a dandalin sayar da jiragen sama na duniya. A sakamakon haka, tuni ma kamfanin dillancin da ke kula da sayar da jirgin samfurin Boeing 737-700 Business Jet ya janye jerin sayar da shi daga shafinsa. ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe Jaridar Punch ta rawaito cewa jirgin da a baya aka saka a shafin kamfanin, yanzu an cire shi daga kai. A cikin wata amsa ga sakon imel, Laurie Barringer...
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Ya gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Najeriya saboda amincewa da suka yi da shi. Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan. Ya ce: “Da na ga irin martanin...
Gwamnonin Arewaci, na shirin dakatar da haƙar ma’adinai a wasu yankuna da ake fama da matsalar tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ta’addanci. Wannan batu ya fito ne daga taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna daga 1 zuwa 2 ga watan Disamba, 2025. ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce lamarin tsaro ya kai wani mataki da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa. Ya bayyana cewa wuraren haƙar ma’adinai sun zama mafakar ’yan bindiga, masu garkuwa da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta samu rahoton laifuka 25 na cin zarafin mata da ƙananan yara a Ƙananan Hukumomin Jakusko, Fika, Potiskum da Tarmuwa, inda aka kama mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan. Kakakin rundunar, SP Abdulkarim Dungus, ya ce an kama masu laifin ne cikin watanni uku da suka wuce, a wani yunƙuri na daƙile cin zarafin mata da yara a faɗin jihar. Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin ministan — Badaru Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani matashi mai shekara 23, Yusuf Garba, da ake zargi yi wa wata yarinya mai shekaru biyar...
Tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya san dalilin da ya sa ya yi murabus. Badaru, ya ajiye aiki ne a ranar Litinin, inda ya ce matsar rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus. Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Shugaban ƙasa ya amince da murabus ɗinsa kuma ya naɗa Janar Chris Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. Badaru, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi murabus ne saboda barazanar da Amurka ta yi na ɗaukar matakin soji kan Najeriya game da zargin kisan Kiristoci. “Ina so na bayyana a fili cewa wannan labari...
Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci. Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara ba. Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja Sanata Bamidele, ya ce ƙudirin ya yi daidai da yunƙurin gwamnati da majalisa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan. Yayin gabatar da ƙudirin, ya ce garkuwa da mutane na ƙara yawaita, kuma ƙungiyoyin miyagu na amfani da shi wajen tara k6udi, abin...
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa addinin musulunci ya daukaka matsayin macce ya kuma bada matsayin guda da maza a fagagen zamantakewa da siyasa, ya kuma yi watsi ya akidar kasashen yamma wadanda suka kaskasntata suka maida ita kayan aika don cimma bukatatun wasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a taron dubban mata daga yankunan daban daban na kasar a yau laraba a nan Tehran. Imam Khaminae ya ce, mata a Iran suna koikoyon Fatimah Azzahra (s) diyar manzon Allah (s) don haka suka kama hanyar daukaka wanda alah ya bawa mata. Fatima (s) makaranta ce ga mata kuma daukaka...
Babban zauren MDD ta amince da kudurori guda biyu wadanda suka yi tir da HKI a jiya talata dangane da mamayar da take yiwa kasar Falasdinu tun shekara 1967 da kuma tuddan golan na kasar Siriya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa HKI ta mamaye tuddan golan na kasar Siriya ne tun yakin kwanaki 6 a shekara 1967 sannan gwamnatin HKI ta tabbatar da kwace yankin a shekara ta 1981. Amma kwamatin tsaron MDD ta yi watsi da mamayar tun lokacin, ta bayyana hakan mamaya ne ba bisa ka’ida ba. Labarin ya kara da cewa, kasashen Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Palestinu ne suka gabatar da kudurin wanda ya sami amincewar kasashe 151, 11 na...
An ga jiragen ruwan yaki da kuma jiragen sana na yaki na Amurka Ponce, da kuma Puerto rico a jiya talata, wanda yake kara tabbatar da Shirin Amurka na mamayar tada rikici a yankin Caribian musamman kuma a kasar Venezuela. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar iran ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Trump tana kara yawan sojojinta a kudancin Amurka musamman kusa da kasar Venezuela da nufin kifar da gwamnatin Shugaba Nicolas Madoro. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu kasashen yankin kudancin Amurka da dama suna tunan makamarsu idan har shugaban Trump ya sami nasarar aiwatar da shirinsa na kwace iko da kasar Venezuela. Saboda ba’a san inda zai dosa bayan kasar Venezuela ba. Gwamnatin kasar Venezuela dai...
Kamfanonin jiragen sama kasashen yamma sun bukaci Amurka ta basu izinin ratsawa ko zuwa kasar Iran bayan dakatarwa saboda yakin kwanaki 12 a cikin watan yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wasu majiyoyin gwamnatin Amurka na fadar cewa a halin yanzu babu wata barazana ta sake komawa yaki da kasar Iran. Sannan jita-jitan da wasu kafafen yada labarai suke yadawa dange da sake komawa yaki da kasar Iran ba gaskiya bane. A cikin yan makonnin da suka gabata ne wasu kamfanonin jiragen saman fasinja na kasashen yamma suka farfado da zirga-zirga zuwa kasar Iran bayan bayan fara yakin watan yuni Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments...
Hukuma ko kungiyar ‘The Guinness World Records organization’ ta bada sanarwan cewa daga yanzu ta daina karban duk wata bajinta ko wani al-amiri da ya shafeta daga HKI saboda ta’asan da take aikatawa a Gaza, wanda kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama a duniya sun tabbatar da cewa, kissan kare dangine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar iran ya bayyana cewa kafin haka kungiyoyin kasa da kasa da dama da kuma fitattun mutanen sun tabbatar da cewa abinda HKI take aikatawa a Gaza laifukan yaki ne, don haka haramcin hukumar Guinness na karban duk wata bajinta daga HKI ya zo ne don ya tabbatar da abinda hukumomin da suka gabaceta suka yi. Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya. Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu, manyan sakatarorin biyar Abdulkarim Ibrahim, Dr John Ezeamama, Dr Abdul-Sule Garba, Dr Isiaku Mohammed da Dr Ukaire Chigbowu, sun dauki rantsuwar kama aiki, sannan suka sanya hannu a kundin rantsuwa. An kuma rantsar da Dr Aminu Yusuf, wanda shugaban kasa ya nada a matsayin Shugaban NPC a ranar 9 ga Oktoba, da kwamishinoni biyu ciki har da Dr Tonga Betara daga Jihar. NPC ita ce...
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gwamna Abba, ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF, domin ganin yadda suke shirin kare al’umma daga hare-haren ’yan bindiga a yankunan Tsanyawa da Shanono. Ya roƙi al’ummar yankunan da abin ya shafa da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani game da duk...
Wata gobara ta tashi a ranar Laraba ta ƙone kasuwar katako da ke kusa da Jabi Masallaci a Abuja. Gobarar ta lalata kaya da kayan gini na miliyoyin kuɗi, amma ba a yi asarar rai ba. CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina Kawo yanzu dak ba a san musababbin tashin gobarar ba. Sai dai wasu rahotanni na cewa gobarar na iya farawa ne sakamakon matsalar wutar lantarki, wanda wani lokacin wayoyin wuta na faɗowa kan rumfunan kasuwa. ’Yan kasuwa da mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kashe wutar, amma ta yaɗo cikin sauri saboda katako da sauran kayayyakin gini na da saurin...
Daga Ali Muhammad Rabi’u An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri. An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin. A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin. Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma...
Wata sabuwar badakala ta sake bata sunan kungiyar Tarayyar Turai, inda ‘yan sanda suka farmawa gidan toshuwar shugaban kula da manufofin harkokin wajen na kungiyar Federica Mogherini, tare da tsare ta a ranar Talata, a Belgium. Mogherini wacce ta yi aiki a mukamin tun daga 2014 zuwa 2019, Ita da wasu abokan aikinta biyu ana binciken su kan yadda aka yi amfani da kudaden Tarayyar Turai ba bisa ka’ida ba, cin hanci da rashawa. Federica Mogherini, jami’ar diflomasiyya ‘yar Italiya mai shekaru 52, ana tsare da ita tare da Stefano Sannino, babban jami’i a Hukumar da kuma mataimakin darakta na Kwalejin Turai. An kama su, su ukun a wani bangare na binciken da Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar...
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyar maka hamshakin kamfanin nan na hakar uranium na faransa (Orano) a gaban kotu bayan gano sinadarai masu guba a yankin Madaoulela, dake arewacin kasar. Dama dai Nijar da Orano sun sun shafe watanni suna takaddama kan sinadarin uranium da ake fitwarwa a kamfanin Somaïr, wanda aka mayar da shi mallakin kasar ta Nijar a watan Yuni. Ministan Shari’a na Nijar, Alio Daouda, ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata nan. Ministan ya ce an gano “ganguna 400 da ke dauke da samfuran sinadarai masu guba” a wani tsohon wurin hakar ma’adinan uranium a wani waje da Orano ya fice a yankin Arlit, wanda ke...
Gwamnatin Amurka ta sanar da soke bada mafaka ga wasu kasashen duniya 19 wadanda suka hada da na Afrika guda 10. Wannan matakin, ya zo ne bayan harin da aka kai a Washington kwanan nan, kuma ya shafi kasashe 19, da suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da kuma Togo, a cewar wata sanarwa da Hukumar Kula da ‘Yan Kasa da Shige da Fice ta Amurka (USCIS) ta fitar. Sauran kasashen su ne Afghanistan, Burma, Haiti, Iran, Yemen, Cuba, Laos, Turkmenistan, da Venezuela. Sanarwar ta umarci ma’aikatan hukumar da su “rike duk fom din bukatar Zaman Mafaka, ba tare da la’akari da kasar da bakon yake ba, har sai an sake duba shi.”...
Kasar Masar ta sanar da tattaunawa da Amurka kan batun shirya sake gina zirin Gaza bayan yakin kisan kare dangi na shekaru biyu da Isra’ila ta kaddamar kan yankin. “Yanayin da ke faruwa a Yammacin Kogin Jordan bai yi muni kamar na Gaza ba,” in ji Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Jamus. M. Abdelatty ya sanar da cewa Alkahira tana tattaunawa da Amurka game da wani taron kasa da kasa da nufin sake gina yankin Gaza, bayan yakin. A wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Berlin ranar Talata da takwaransa na Jamus, Johann Wadephul, Abdelatty ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa da Washington don...
Hukumar bada agaji da samar da ayyukan ga falasdinawa na majalisar dinkin duniya UNRWA ta fadi cewa isra’ila ta hana motoci makare da kayan agaji guda 6000 shiga yankin Gaza da suke dauke da abinci magunguna da za su iya wadatar da yankin na tsawon watanni 3. Kakakin kungiyar ta UNRWA Adnan Abu Hasna ya fadi cewa duk da yake cewa adadin kayan da ake shiga da shi yankin gaza ya karu tun bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta a watan oktoba, sai dai duk da haka isra’ila ta hana shigar da kayayyakin da ake bukata da zasu iya taimakwa wajen warware matsalar da yankin ke fuskata. A watan oktoba isra’ila ta shaidawa majalisar dinkin duniya cewa za ta...
Daga Aliyu Muraki Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Nasarawa (NSUBEB) ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da iyayen da ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a jihar. Shugaban Hukumar, Dr. Kasim Mohammed Kasim ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na ayyukan babban taron inganta ilimi da hukumar ta shirya. Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce, ilimin boko matakin farko haƙƙin kowanne yaro ne, ba gata ba, kuma ya sha alwashin tabbatar da cewa ba a bar wani yaro a baya ba. Shugaban Hukumar ya bayyana cewa hukumar ta yanke shawarar gudanar da gagarumin wayar da kan jama’a ta hanyar tarurrukan jin ra’ayoyin jama’a, da kafofin watsa labarai domin jaddada muhimmancin ilimin boko...
Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta Ana binciken wani tsohon ma’aikacin jinya a qasar Italiya bisa zargin ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu kuma ya je ma’aikatar fansho a matsayin mahaifiyarsa don neman fanshonta. Haka kuma an gano ya voye gawarta a cikin gidansa har tsawon shekaru uku bayan mutuwarta. Mutumin xan Italiya ya saka tufafin mahaifiyarsa da ta mutu sannan ya yi kwalliya da gazar da jan-baki kamar yada take yi, ya je bankin da take ajiya yana neman a biya shi kuxi fanshonta, bayan ya voye gawarta a gida. Mutumin mai shekaru 56, ma’aikacin jinya da ya rasa aikinsa a garin Mantua, ya sami damar karvar dubban kuxi na Yuro...
Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio Daga Musa Kutama, Kalaba Yusuf Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Yusuf Lazio, fitaccen jarumi ne a Masana’antar Finafinan Hausa, wato Kannywood. Jarumin ya yi shura a fim xin Na-Ladidi, inda ya ce, haxa waqa da fim a lokaci xaya, a wurinsa ba wani abu ba ne, hasali ma mawaqi ne shi kafin ya fara fitowa cikin fim. Ga yadda hirar ta kasance: Gabatar da kanka ? Sunana Yusuf Mohammad Abdullahi ana kira na da Yusuf Lazio. Dama can kana da alaqa da Lazio ne ko kuwa kulob xin ne ake kiran ka da shi? A’a sunan ya samo asali ne daga goya wa qungiyar wasan qwallon qafa ta Lazio baya da nake yi....
Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom ta ƙi amincewa da wani kudiri da ya nemi haramta ci da sayar da naman kare a jihar. Kudirin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Etinan, Uduak Ekpoufot ya gabatar ranar Talata, bai samu ko da dan majalisa daya da ya mara masa baya ba. Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi Jaridar nan ta gano cewa Uduak ya roki majalisar da ta yi la’akari da matsalolin kiwon lafiya da ke tattare da cin nama kare, yana gargadin cewa yadda ake yanka dabbobin ba tare da tsafta ba na iya jefa masu cin nama cikin haɗarin kamuwa da cututtuka irin su...
Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele. Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Sanarwar ta ce majalisar ta karɓi buƙatar Shugaban Ƙasa Tinubu na tabbatar da wanda aka naɗa Ministan Tsaro. Sanarwar ta ƙara da cewa za a karanta wasikar a gaban majalisar a ranar Laraba, sannan kuma za a ci gaba da tantance wanda aka naɗa nan take. Opeyemi ya bayyana cewa majalisar ba za...
Majalisar Wakilai za ta ƙada kuri’a a ranakun 10 da 11 ga watan Disamba kan muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ciki har da kirkirar sabbin jihohi da kafa ’yan sandan jihohi. Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya sanar da jadawalin a zaman majalisar, inda ya ce tattaunawa kan kudirin sauya kundin tsarin mulki za ta gudana yau da gobe kafin kada kuri’ar mako mai zuwa. An aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocin Majalisar Dattawa Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan nazarin kundin tsarin mulki, ya bukaci ’yan majalisa su halarci zaman. Ya shaida wa majalisar kwanan nan cewa kwamitin ya kammala aikin da ake...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar. Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci a yankuna daban-daban. Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban sabon ministan tsaron yayin da yake shirin kama aiki a ma’aikatar tsaro bayan majalisa ta tabbatar da shi? NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Sharhin bayan labarai, wand ani tahar amin zan karanta. A cikin shirimmu na yau zamu yi Magana dangane cewa, shin gaskiyar ne ‘HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin HKI a karon farko a hukumance, ta bada sanarwan cewa, tana fama da karancin sojoji a dukkan rassan sojojin kasar, kuma wannan Babbar barazana ce kuma hatsari ne ga samuwar kasar kai tsaye. Tambaya ta farko it ace, menene Alamar karancin sojoji a cikin rundunonin sojojin HKI? Sanarwan ma’aikatar yakin HKI dangane da wannan ta ce, tana fada da karancin sojoji...
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi. Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya. Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Litinin ce Janar Musa ya yi wata ganawar sirri da Shugaba...
Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya hana abokan gaba cimma mummunar manufarsu akan kasar. Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama ranar “Mutane Masu Bukata Ta Musamman” ta duniya ya bayyana cewa a yayin kallafaffen yaki na shekaru takwas tsakanin 1980-1988, dukkanin duniya ta kasance a bayan ‘yan Ba’asiyya da zummar kawo karshen jamhuriyar musulunci,amma goyon bayan da al’ummar Iran suke bai wa tsarin musulunci goyon baya, hakan ba ta faru ba. Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; “Yan Sahayoniya da Amurka sun kawo wa Iran hari da yakin kwanaki 12 a karkashin wannan irin tunanin...
A yau Talata ne mai bai wa shugaban kasar ta Nigeria, shawara akan watsa labaru Bayo Onanuaga ya sanar da Nadin na Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin wanda zai maye gurbin Alhaji Muhammad Badru Abubakar da ya yi murabus a jiya Litinin. Janar Musa ya rike mukamai masu yawa na soja gabanin Nadin nasa a yau. Daga cikin mukamin shugaban bangaren tsaro na soja a tsakanin 2023 zuwa oktoba 2025. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar...
Ma’aikatar harkokin wajen Njgeria ta sanar da bai wa dan takarar shugabanncin kasar Guinea Bissau, Fernando Dias da Costa, ya kuma tsaya takara ne a tare da shugaban kasar Umar Sisoko Embalo da sojoji su ka kifar da gwamnatinsa kwanaki kadan bayan zabe. A ranar 27 ga watan Nuwamba ne dai Dias Da Costa ya sanar da cewa,shi ne wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, tare da zargin Embalo da cewa shi ne ya shirya juyin mulkin da ya kawo karshen zaben kasar, tun kafin a sanar da sakamakon zaben. Haka nan kuma ya ce ya tsallake rijiya daga kokarin kama shi a ranar da aka yi jiyin Mulki, ya kuma boye, har sai da ya sami...
Rahotanni daga Ramallah sun ce a kalla sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila 3 ne su ka jikkata sanadiyyar taka su da mota da wani Bapalasdine ya yi , a yau Talata. Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ambaci cewa; Wani Bafalasdine ya soka wa dan shaayoniya wuka da aka dauke shi zuwa asibiti domin karbar magani.” Majiyar ta ce da akwai sojojin a wurin da aka kai hari, don haka su ka bude wuta akan maharin Bapalasdine.” Su kuwa jaridun Falasdinawa a Ramallah sun ce wanda ya kai harin na Yau Talata ya yi shahada bayan da sojojin mamaya su ka bude masa wuta. A gefe daya, kungiyoyin gwgawarmayar Falasdinawa sun yi maraba da harin akan ‘yan sahayoniya a kusa da Ramallah,...
Majalisar Dattawa ta sanar da aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta waɗanda suka haɗa har da na tsaro da na tattara bayanan sirri, sakamakon ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta. Shugaban Majalisar Dattawan, kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman na yau Talata. Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya A sabbin sauye-sauyen da majalisar ta aiwatar, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ya zama shugaban kwamitin tsaro da na tattara bayanan sirri bayan ya bar kujerar kwamitin tsare-tsare na ƙasa. An naɗa Sanata Shehu Buba daga Bauchi a matsayin shugaban kwamitin harkokin Kiwo, bayan cire shi...
Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin. Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025. An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da...
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi. Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya. Musa wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 har zuwa Oktoban 2025 lokacin da Shugaban Kasa ya sauke shi daga muƙamin a...
Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai. Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu. Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.4%, inda ya danganta hakan da dabarun yaƙi da cutar da ake aiwatarwa a jihar. “Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi. Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta...
Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu. Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba. Lamarin ya tayar da hankula a ƙauyukan da ke kewaye, inda iyalai da dama suka kwana cikin fargaba. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace matasa ne da suka tafi gona domin yin roron wake lokacin da aka...
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da matakin da isra’ila ke dauka na tsauraran mataken shigar da kayan agaji zuwa yankin gaza musamman bangaren sansanin yan gudunn hijira da kuma tanti-tanti da aka yi. Kakakin kungiyar hamas Hazem Qaseem ya jaddada cewa mafakar da suka rage a yankin tantuna ne da aka yi marasa karko, da ba za su iya jurewa iska ko yanayin sanyi ba. Yace har yanzu isra’ila tana bari a shiga da wani adadi kadan ne zuwa yankin gasa na kayayyakin agaji, wanda ba zai wadatar da abubuwan bukatatun yau da kullum na rayuwa ba ga yawan alummar dake bukatar agaji a daidai lokacin da ake fuskantar mawuyacin yanayi dake bukatar taimakon gaggawa,...
Rahotanni da suka fito daga Najeriya sun nuna cewa ministan tsaro Alh mohammadu Badaru Abubakar a ranar 1 ga watan Decemba ya mika takardar ajiye aiki a matsayinsa na ministan tsaron kasa, saboda wasu dalilai da suka shafi lafiyarsa, Kamar yadda kakakin shugaban kasa Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaba tinubu ya amince da takardar neman ajiye aikin, kuma ya gudemasa game da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasarsa, tuni kuma aka fara lalubo wanda zai maye gurbinsa domin mika sunansa ga majalisa don a tantance shi. Badaru Abubakar dan shekara 63 da haihuwa shi ne gwamnan jihar jigawa har na tsawon zango biyu wato daga shekara ta 2015 zuwa ta 2023 kuma shugaban kasa tunubu ya nada...
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadi cewa iran tana ci gaba da aiki da diplomasiya duk da cikas da Amurka take kawo wa a tattaunawar da ba ta kai tsaye ba, ganin cewa Amurka tana amfani da karfi wajen gudanar da harkokin duniya . Yace idan bangaren Amurka ta nuna shirinta na yin tattaunawa bisa mutunta jina da kare munufofin kowa, to iran za ta iya duba lamarin, saboda bamu taba barin teburin tattaunawa ba , saboda it ace ingantacciyar hanya ta fuskantar alumma. Dangane da Ziyarar da ya kai a bayan bayan nan a garin muscat da kuma tarurrukan da yayi, babban jami’in diplomasiyar iran yace babban abin takaici shi ne inda dokokin kasa da kasa...
Shugaban kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika kuma shugaban kasar saliyo Julius mada Bio yace ya tattauna da shugaban mulkin soji da ya yi juyin mulki a kasar Guinea Bissau , a kokarin da suke yi na ganin an yi aiki da kundin tsarin mulki a yankin na yammacin Afrika. A cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na X bio ya fadi cewa ganawar ta su ta zo ne bayan kudurin da kungiyar ta ECOWAS ta fitar a taron da ta gudanar kan irin mataken da zaa dauka game da batun juyin mulki da aka yi a kasar Guinea Bissau a makon jiya. Shiga tsakani a rikicin kasar Guinea Bissau ya zo ne sakamakon rashin zaman lafiya...
An gudanar da bikin cika shekaru 41 da kafa kungiyar hadin guiwa ta tatalin arziki ta ECO a nan birnin Tehran ne a jiya litinin inda sakatare janar din kungiyar Eco Majeed khan da ministan aladu reza salihi –amiri suka gabatar da jawabai a wajen, da ya shafi irin ci gaba da kungiyar ta samu a cikin wadannan shekaru da kuma bayyana muhimmancin yin aiki tare . Kungiyar Eco tana daga cikin mihimmiyar hanya ta duniya da ta fara daga yankin tekun fasha zuwa tsakiyar asiya , kuma kasashen dake mambobin kungiyar sun kai kusan rabin biliyan dake da arzikin makamashi da ma’adinai kasa, baya ga batun tattalin arziki , kungiyar tana matsayin jigo mai muhimmanci wajen huldodin diplomasiya a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi. NAJERIYA A YAU: Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? Wannan...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce: “Bayan zagaye biyar na tattaunawa, yayin da muke shirin zagaye na shida, ɓangaren Amurka ya karya hanyar diflomasiyya da kuma ƙoƙarin shiga tsakani da ake yi.” Seyyed Abbas Araghchi, Ministan Harkokin Wajen Iran, ya ce a wata hira da ya yi da shirin “Ma’a Musa al-Far’ei” a ranar Litinin: “Abin takaici dokokin ƙasa da ƙasa da tsarin duniya sun yi tasiri ga yanayin Amurka na amfani da ƙarfi a dangantakar ƙasa da ƙasa.” A cewar Pars Today, Araghchi ya ƙara da cewa: “Wannan ya bayyana a cikin tsoma bakin soja na ba bisa ƙa’ida ba da kuma aiwatar da ayyukan kisan kai duk inda suka ga dama.” Ya jaddada cewa: “Abin da muke gani...
Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana mulkin mallaka a matsayin laifi kan bil’adama, da kuma tabbatar da an biya diyya bisa ga barna da cin zarafi da aka yi wa al’ummomin Afirka. Taron, wanda aka gudanar a babban birnin Aljeriya, an gudanar da shi ne bisa wani kuduri na Tarayyar Afirka (AU) da aka amince da shi a farkon wannan shekarar wanda ke kira da a yi adalci wajen biyan diyya don magance illolin siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa da suka faru sakamakon mulkin mallaka. Ministan Harkokin Wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya ce tarihin Aljeriya a karkashin mamayar Faransa ya sanya...
Paparoma Leo XIV ya halarci taron Musulunci da Kiristanci da tattaunawa tsakanin addinai a dandalin Shahidai da ke Beirut. Bayan isowarsa, Paparoma ya samu tarba daga shugaban Mabiya addinin kirista na Lebanon Bechara Boutros al-Rahi, da shugaban Mabiya darikar Katolika na Syria Ignatius Joseph III Younan, da kuma Babban Mufti na Lebanon Sheikh Abdul Latif Derian, da Mataimakin Shugaban Majalisar koli ta Mabiya mazhabar Shi’a a Lebanon Sheikh Ali al-Khatib. A lokacin taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Shi’a a Lebanon ya yi maraba da Paparoma, yana mai cewa: “Muna farin ciki da zuwnku a Lebanon a madadin Majalisar da kuma daukacin mabiya mazhabar shi’a na Lebanon, Muna maraba da kuma godiya da ziyararku zuwa kasarmu a wannan mawuyacin lokaci da kasarmu...
Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai gabatar da kuduri don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela. Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai. A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri...
An kashe wani ɗan sanda a wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai gidan Babban Jami’in Ɗan Sanda (DPO) mai kula Babba Ofishin ’Yan Sanda da ke Aujara a Ƙaramar Hukumar Jahun ta a Jihar Jigawa. Da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, ranar 25 ga Nuwamba, 2025, ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan. Sanarwar rundunar ’yan sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa jami’an tsaro da ke gadin gidan sun yi ƙoƙarin dakile harin, inda aka samu musayar wuta. A yayin arangamar, biyu daga cikin jami’an sun samu munanan raunuka, aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa. Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus...
Matatar Man Fetur ta Dangote a Najeriya ta sanar a wannan Litinin cewa tana da ikon isar da lita biliyan 1.5 na man fetur a kowane wata, kuma ta yi kira ga hukumar kula da masana’antu da ta tabbatar da hakan a cikin alkalumanta na yau da kullun, bayan da hukumar ta fitar da bayanai da ke nuna cewa matatar tana samar da kusan kashi daya bisa uku ne kawai na wannan adadi. Ikirarin da ake yi cewa matatun man fetur na Najeriya ba su iya biyan bukatun kasa ba wani bangare ne na dalilin da ya sa gwamnati ta yi watsi da shirinta na hana shigo da kayayyakin man fetur da aka tace a watan da ya gabata ba....
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita. Trump ya sanar a ranar Laraba da ta gabata cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na 2026 a Florida ba, yana mai ambaton zargin da ake yi wa kasar na kin mika shugabancin G20 ga wakilin ofishin jakadancin Amurka a bikin rufe taron da aka yi a kasar a baya. Duk da haka, Pretoria ta dage cewa shugabancin da ake yi nak aba-karba an mika shi ga...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa da Janar CG Musa na da nasaba da shirin shugaban kasar na cike gurbin da Badaru ya bari da kuma garambawul a shugabancin tsaron Najeriya. Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanar cewa Badaru ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya. An kama ’yan bindiga 4 a Kano MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa da Janar CG Musa na da nasaba da shirin shugaban kasar na cike gurbin da Badaru ya bari da kuma garambawul a shugabancin tsaron Najeriya. Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanar cewa Badaru ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya. An kama ’yan bindiga 4 a Kano MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar...
Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon. Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har...
Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon. Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har...
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa. Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa. Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baqaei ya bayyana cewa Amurka ce Babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, saboda ganin abinda take yi a halin yanzu a kasar Venezuela da kuma wasu kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka a yau litinin a taro da ‘yan jirisa da ya saba a ko wace Litinin. Baqaei ya kara da cewa a ci gaba da goyon bayan da Washington take bawa HKI ta rufe sararin samaniyar kasar Venezuela, don goyon bayan Falasdinawa, mutanen Siriya da Lebanon da take yi. Wanda kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa. Dnagne da dangantakar Iran da Saudiya kuma Baqaei ya...
Paparoma Leo 14 wanda yake ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Lebanon ya gana da shugaban kasar Lebanon Josept Aun da kuma manya-manyan malamai da shuwagabannin kungiyoyin yan siyasa a kasar Lebanon. A jawabin da ya gabatar a gaban wadannan shuwagabannin kasar Lebanon Lio na 14 ya bukaci, su rungumi zaman tare da kuma hakuri wajen hada kai da kuma gina kasar Lebanon. Lio 14 ya ce mutanen kasar Lebanon sun sha wahala a tarihin kasar na zama, amma saboda gwazon da suke da shi wannan bai hana su zaman lafiya da juna ba. Wannan bai hanasu ci gaba da rayuwa ba. Duk da cewa akwai barazana mai yawa da ke fuskantar kasar. Yace, zama tare da wadanda kuke...
Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata. Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a cikin watan Octoban da ya gabata. Jami’an tsaro sun yi dirar mikiya kan masu goyon bayan Chiroma, kuma sun kashe mutane da dama sun kuma kama wasu Anicen Ekaney ana daga cikin wadan da aka kama a birnin Duala a ranar 24 ga watan Octoba. Kuma Ekane ya zargi jami’an tsaro da kwace maganin Oxigen dinsa, wanda ya jefa rayuwarsa cikin hatsari,...
Tawagar kungiyar raya tattalin arziki na kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bar bar birnin Bissau da sauri bayanda shugaban kasa Umaro Sissoco yayi barazanar zai fiddasu daga kasar ida sun kara jinkirin fita. A cikin watan da ya gabata ne kungiyar ta aiki tawagar zuwa kasar ta Gunea Bissai saboda gabatar da shawarorin kan yadda za’a gudanar da zabubbuka masu inganci a kasar. Tawagar ta kara da cewa tuni ta bawa manya manyan yan siyasa a kasar kofin shawarorin da suka gabatar, sun kuma fara nazarinsu. Sai dai tawagar ta gaggauta barin kasar a ranar Asabar bayan da ta sami sako daga fadar shugaban kasa mai cewa idan sun ki fita to zai sa a fiddasu da karfi. Tawagar ta...
Hukumar kididdiga ta HKI ta basa sanarwan cewa yawan yahudawa da suke ficewa daga haramtacciyar kasar . Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ta nakalto hukumar na bada labarin cewa a shekara ta 2010 yawan masana wadanda suke da shahadar Jami’a ya karu ha rya kai kashi 46% sannan wannan adadin ya cilla sama a shekara ta 2023 bayan fara yakin tufanul aksa zuwa kashi 60.4 %. Har’ila yau kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan shekarun da suka gabata, yahudawa masu ilmin Jami’a da dama sun bar kasar, saboda yana yaki wanda baya karewa a kasar. Hukumar kididdiga na HKI a cikin yan kwanakin da suka gabata ta yada rahoto dangane da...