2025-09-17@21:49:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 63
«tsadar rayuwa»:
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa...
Rashin kishin wani mutum ya zama abin mamaki bayan ya bayyana cewa, yana zaune lafiya tare da matarsa da suka yi shekara uku da wani saurayinta har ma sun shigo da shi cikin gidansu. Prince Soy, matashi mai dafa abinci a kasar Japan kuma mai amfani da intanet, wanda ke tallatawa da siyar da abincin...

NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum,...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana...
Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin...
Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano...
Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce...
Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu dari da sittin da hudu wajen tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya da aka gudanar a...