2025-08-01@22:47:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7251

«Riek Machar»:

    Bugu da ƙari, Hukumar ta NPA ta bayyana cewa, tana kan ƙoƙarin inganta kayan aiki Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar, wanda ta zuba dala biliyan daya, domin fara gyaran Tashoshin Jiragen Ruwa ta Tin Can Island tare da yin ayyukan kwakwarima, a Tashoshin Jiragen Ruwa na, Apapa, Riɓers, Onne, Warri da kuma Kalaba. Ita kuwa a na ta ɓangaren, Kwalejin ta MAN ta bayyana cewa, nauyin da aka ɗora mata na gudanar da ayyukan ta, son yi daidai da ƙoƙarin ƙasar nan ke ci gaba da yi, na ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasar, mussaman wajen yaye haziƙai kuma ƙwararrun ɗirebobin Jiragen Ruwa da ƙasar nan ke buƙata. Shugaban Hukumar ta NPA darka Abubakar dantsho, a jawabinsa ewabinsa a taron shekara- shekara...
    Kasar Sin ta sake neman Amurka, da ta daina zarginta, da dora mata laifi, ya kamata kasar Amurka ta taka rawa wajen tsagaita bude wuta, da kara azama ga gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya. Jami’in ya ce, ana bukatar hadin kai wajen warware rikicin Ukraine, a maimakon rarrabuwar kawuna da yin fito-na-fito. (Tasallah Yuan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yanzu haka dai ratotannin sun tabbatar da cewa APC da ADC suna gogayya wajen neman samun goyon bayan mutanen arewa kafin babban zaɓen 2027 ya ƙariso. A ranar 1 ga Yuli, manyan ƴan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da dan takarar shugaban ƙasa a APC a 2023, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun gabatar da ADC a matsayin hadakar jam’iyyar adawa domin ƙalubalantar Tinubu a 2027. Shugabannin ADC sun ci gaba da yin ƙoƙari don samun goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya da sauran yankuna tun bayan buɗe jam’iyyar. A taron, Mark ya buƙaci shugabannin arewacin Nijeriya da...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Dangane da sanarwar da Amurka ta fitar ta kakaba takunkumi kan jami’an hukumar kare hakkin Falasdinawa da mambobin kungiyar ‘yantar da Falasdinu, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin ta kadu da hakan, kuma tana nuna takaici da rashin fahimta cewa, Amurka ta yi watsi da kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya ga Falasdinu. Kuma kasar Sin ta dage wajen goyon bayan tsari mai adalci ta al’ummar Falasdinu don maido da halastaccen hakkin al’ummar, kuma za ta ci gaba da yin namijin kokari a wannan fanni tare da sauran kasashen duniya. Dangane da umarnin da shugaban...
    Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce farin jinin jam’iyyar adawa ta PDP ya dusashe a jihar. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martanin da wasu jam’iyyun adawa suka yi, wajen zargin gwamnatin jihar da rashin bayyana yadda ta ke kashe kuɗaɗen da aka ware wa ilimi, lafiya, da gine-gine. Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya   Dungurawa, ya ce waɗannan zarge-zargen siyasa ce kawai, ba su da tushe ko makama. Ya ce waɗanda ke sukar gwamnati su ne suka gaza lokacin da suka yi mulki a Kano. “Da farko, muna gode musu da...
    Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou  ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama tamfar alaƙaƙai a Najeriya. Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya   “A cewarsa cutar Kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, inda ƙasar ke fama da ɓarkewar cutar a ‘yan shekarun nan.” “Ya zuwa ƙarshen watan Yuni, Najeriya ta samu adadin mutane 3,109 da ake zargin...
    An yi balaguro na cikin gida sama da biliyan 3.28 a kasar Sin a rabin farko na shekarar 2025, adadin da ya karu da kashi 20.6 cikin dari a mizanin duk shekara, bisa bayanan da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta fitar a yau Jumma’a. Masu yawon bude ido na cikin gida sun kashe jimillar yuan tiriliyan 3.15 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 441 a cikin wadannan watanni shida, inda adadin ya karu da kaso 15.2 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024. Bugu da kari, musamman an lura da yadda yawan tafiye-tafiyen cikin gida da mazauna yankunan karkara ke yi suka karu da kashi 30.6 cikin dari a mizanin duk shekara, inda aka samu karin kashi 30.1...
    A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari. Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa da kasuwar Ɗan Magaji saman gadar da ke kan hanyar  Zariya zuwa Kaduna. Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya   An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Awaki kusan sama da 100  suka mutu da kuma kaji kusan ɗari 500 ne aka ƙeyasta sun mutu. Sai dai ba a sami asarar rai ko ɗaya...
    Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta umarci Kwamishinan harkokin makamashi da albarkatun man Fetur, Hon. Sanusi Danfulani, da ya bayyana a gabanta ranar Talata, 5 ga watan Agusta, saboda gazawarsa wajen halartar ziyarar duba aiki da kwamitin majalisar mai kula da kimiyya da fasaha ya gudanar. Ziyarar da aka shirya a ranar Alhamis ta sami tsaiko sakamakon rashin halartar Danfulani da wasu manyan jami’an ma’aikatarsa, lamarin da shugaban kwamitin, Awaisu Aliyu, ya bayyana a matsayin “wulakanci da sakaci da aiki da ga rashin mutunta majalisar dokoki.” Ma’aikatar Cinikayya Ta Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Soke Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Sin Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar Aliyu ya ce, “An...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Matukar dai Trump ya bukaci dakatar da inganta sinadarin Uranium gaba daya a Iran, to ba za a cimma wata yarjejeniya ba Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada a wata hira da jaridar Financial Times cewa: Iran na neman a biya ta diyya kan irin hasarar da ta yi a harin wuce gona da irin kwanaki 12 na ta’addanci kan kasarta. Araqchi ya yi nuni da bukatar Amurka ta bayyana dalilin da ya sa ta kai farmaki kan Iran a tsakiyar shawarwari tare da bayar da tabbacin cewa ba za a sake daukar irin wannan mataki ba. Araqchi ya kara da cewa, warware rikicin makamashin nukiliya na bukatar nemo...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta mayar wa da gwamnati martanin cewa har yanzu tana ci gaba da gudanar da yajin aikin da take yi. Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ne dai ya bayyana cewa ƙungiyar ta janye yajin aikin gargaɗin. An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Da yake magana da manema labarai bayan wani taron sirri da aka yi a Abuja ranar Juma’a, Pate ya ce matakin ya biyo bayan yarjejeniyoyin da gwamnati da shugabannin Ƙungiyar NANNM suka cimma ne. Amma da aka tuntuɓi shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Morakinyo Rilwan ya ce ba gaskiya ba ne cewa an...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zarge-zargen da Amurka da kasashen yamma suka yi mata Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya musanta zarge-zargen da Amurka da Faransa da wasu kasashen yammacin Turai ke yi wa Iran a matsayin abin dariya da rashin tushe. Ya kuma jaddada cewa, suna daga cikin fito-na-fito na hasashe da kuma kokarin karkatar da ra’ayin jama’a daga muhimman batutuwan da ke faruwa a yanzu, wato kisan kiyashi da kashe-kashen jama’a da ake yi a kasar Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya jaddada a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Juma’a cewa: Amurka, Faransa da dukkan sauran kasashen da suka sanya hannu kan sanarwar baya-bayan nan kan Iran, a matsayin gwamnatin da...
    Limamin da ya jagoranci sallar Juma’ar birnin Tehran ya bayyana cewa: Iran za ta  mayar da birnin Tel Aviv kufai idan ta maimaita wautar ta Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, Ayatullah Ahmad Khatami, ya gargadi shugabannin yahudawan sahayoniyya kan illar duk wani keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, yana mai jaddada cewa: Idan aka sake yin wani wauta, to Iran za ta kaddamar da wani mummunan martani da zai mayar da Tel Aviv garin fatalwa.” A hudubar sallarsa ta Juma’a a a yau, Ayatullah Khatami ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce ta yi nasara a yakin wuce gona da iri da aka shafe kwanaki 12 ana yi,...
    Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan matakin. Fira Minista Robert Gollub ne ya kaddamar da wannan matakin domin nuna adawa da mummunan bala’in jin kai a Gaza. Wata sanarwa da ofishin fira ministan ya fitar ta tabbatar da hakan yayin wani taron majalisar ministocin da aka gudanar a farkon alhamis. A karkashin sabon kuduri, duk makamai da kayan aikin soja an hana aikewa da su daga Slovenia zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila,...
    Kasar Spain ta bayyana abin da ke faruwa a Gaza a matsayin abin kunya ga bil’adama Ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya yi kira ga mahukuntan Isra’ila a ranar Alhamis da su bude mashigar ruwa na dindindin domin ba da damar kai agajin jin kai zuwa zirin Gaza, yana mai gargadin cewa; Bala’in jin kai a yankin da aka killace zai iya ta’azzara. A nasa jawabin Albares ya jaddada cewa: Gaza na fuskantar yunwa sakamakon killacewar da haramtacciyar  kasar Isra’ila ta mata, kuma abin da ke faruwa a wurin abin kunya ne ga bil’adama. Ya kara da cewa yunwa na ci gaba da lakume rayukan fararen hula a yankin a kowace rana. Ministan na Spain ya jaddada...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, bayan sun yi artabu da wasu da ake zargin sun yi garkuwa da su a wani mummunan musayar wuta da aka yi a tsaunin Shanga. Waɗanda aka yi garkuwan da su sun haɗa da: Muhammad Nasamu Namata mai shekara 25, da Gide Namata mai shekara 20 da Hamidu Alhaji Namani mai shekara 35. INEC za ta fara rajistar ƙuri’a a ranar 18 ga Agusta Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi An  yin garkuwa da su ne a safiyar ranar 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da masu garkuwa da mutane ɗauke da makamai suka mamaye ƙauyen Sangara da ke...
    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta  Ya kuma ce sai a ranar 25 ga watan Agusta, 2025 za a fara rajistar ƙuri’a a zahiri. “Za a fara rajistar ƙuri’a ta Intanet a faɗin ƙasa daga ranar 18 ga watan Agusta,” in ji Farfesa Yakubu. “Rajistar ƙuri’ar a zahiri kuma za ta fara daga 25 ga watan Agusta, 2025,”...
    A kwanakin baya, an bude tashar jirgin ruwa ta fasinja ta kasa da kasa ta kasar Sin ta farko, wato tashar jirgin ruwa ta Shekou dake birnin Shenzhen. ’Yan kasuwa daga Argentina, da Chile, da Brazil sun shiga kasar Sin ta tashar bisa sabuwar manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, inda aka rage lokacin daidaita aikin canza jirgi daga awoyi biyu da rabi zuwa kasa da rabin awa. Wannan ya shaida cewa, an aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, ba ma kawai a filin jirgin sama ba, har ma a tashar jirgin ruwa. Hakan ya hanzarta raya cinikayyar Sin da kasashen waje. Wannan batu ya kasance wani misali, bayan da kasar Sin...
    Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Cututtuka ta Jihar Kano(KIRCT) a fannonin bincike, samar da rigakafi, habaka magunguna da kuma yaki da cututtuka masu nasaba da zafi (tropical diseases). Darakta Janar na Hukumar Binciken Harkokin Halittu ta Kasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar KIRCT  da ke Kano. Farfesa Mustapha ya ce ziyarar na da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin NBRDA da KIRCT domin magance kalubalen da kasa ke fuskanta ta hanyar binciken zamani. “A matsayina na shugaba a wata muhimmiyar hukuma da ke da alhakin bincike da ci gaban fasahar halittu a fannonin abinci da noma, lafiya, masana’antu da muhalli, muna da...
    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a Ƙaramar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi a wani mataki don bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa. Hakan na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Kebbi. Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta  ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa Sojojin sun kai ziayarar ne ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar. Rundunar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar. Patrick Nwatu ya yi tir da harin ta’addanci a kogin Neja, yana mai cewa yankin ya zama maɓoyar masu safarar makamai da sauran masu aikata...
    Jami’an tsaro sun tabbatar da kuɓutar wasu ɗalibai shida na Makarantar Horon Ilimin Shari’a ta Najeriya da aka sace. Rundunar ’yan sandan Jihar Binuwai ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a. ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Kakakin ’yan sandan, Udeme Edet, ya ce ɗaliban sun taso ne daga Jihar Anambra, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makarantar horon ilimin shari’a da ke Yola, a Jihar Adamawa. ’Yan bindiga ne suka tare su a iyakar Binuwai da Taraba. “An ceto ɗalibai shida da aka sace a ranar 26 ga watan Yuli, 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Anambra zuwa Adamawa. “An...
    “Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida.  A jawabinsa na fatan alkairi, mai riƙon muƙamin wakilin hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) a Nijeriya, dakta Aleɗ Gasasira, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen yin na mijin ƙoƙari kan cutar hanta, yana mai cewa cutar tana shafar miliyoyin jama’a a ƙasar nan.  Gasasira, wanda ya samu wakilcin dakta Mya Ngon, a faɗin ofishin WHO da ke Nahiyar...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da naɗin Sa’idu Yahya, mai shekaru 47, jami’i a fannin bincike kan cin hanci, inda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a Hukumar ICPC. Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya An bayyana cewa Yahya na da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano,...
    Karamar Hukumar Birnin Kudu ta shirya taron bita na kwanaki biyu ga kansiloli masu gafaka da masu bada shawara akan kara samun dabarun aiki.   Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba yace an shirya taron ne domin koyar da su dabarun sanin makamar aikin domin su fahimci tsarin mulkin tafiyar da kananan hukumomi.   Jami’in lura da kididdigar kashe kudade na shiyar Birnin Kudu Malam Usman Ya’u ya gabatar da makala kan alamuran gudanar da aiki ga kansiloli masu gafaka da masu bada shawara.   Shi ma Daraktan alamuran ma’aikata na yankin, Malam Tukur Ibrahim Doko yace taron bitar ga kansilolin masu gafaka zai kara zaburar da su akan ayyukan su.   A karshe, Malam Sani Makama da Malam...
    A cewar Adelabu, har yanzu dai wutar lantarki ne ƙashin bayan kamfanoni a Nijeriya da kuma tattalin arziki, ya nemi haɗin kan dukkanin wadanda lamarin ya shafa domin sake farfaɗo da sashin wutar lantarki yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta yi watsi da zarge-zargen marasa tushe balantana makama da kasashen yammacin duniya ke yi a kanta, kan cewa tana yunkurin kashe wasu mutane a cikin kasashensu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya yi Allah wadai da ikirarin da ya kira  na kin jinin Iran da Amurka da Canada da wasu kasashen Turai goma sha biyu suka yi a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a wannan Alhamis. Ya ce wannan  batu a fili  wani yunkuri ne na karkatar da hankulan jama’a daga batun da ya fi daukar hankali a wannan lokaci,  wato kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Palastinu da ta mamaye. Ya kara da cewa, “Amurka, Faransa, da sauran kasashen da suka...
    Wakilan kasashen Mali da Rasha sun gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin kasashen biyu, karkashin jagorancin ministan tattalin arziki da kudi na kasar Mali Husseini Sanou, da ministan makamashi na kasar Rasha Sergey Tsivlev, inda suka tattauna kan “hadin gwiwa a fannin makamashi, musamman wajen yin amfani da makamashin nukiliya domin ayyukn farar hula. Taron ya samu halartar wakilan “manyan kamfanonin makamashi na Rasha da ma’aikatun gwamnatin tarayya,” kamar yadda ya zo a cikin wata sanarwa da ma’aikatar makamashi ta Rasha ta fitar a shafinta na intanet, a cewar kafar yada labarai ta African Readings. Bangarorin biyu sun tattauna kan fagagen da suka yi alkawarin yin aikin hadin gwiwa a fannin hakar albarkatun kasa, binciken sararin...
    Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a baya dai sun yi hasashen ’yan Najeriya miliyan 33.1 za su iya fuskantar matsanancin karancin abinci daga tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025. Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul Hakan dai na nufin a yanzu yan kasar miliyan 34.7 ne ke nan suke...
    Ministan kasuwanci na Afirka ta Kudu Parks Tau ya fada jiya Alhamis cewa kasarsa na shirin yin shawarwarin kasuwanci da nufin kaucewa harajin kashi 30% na Amurka a kan kasarsa, wanda  zai fara aiki daga wannan Juma’a. A farkon watan Mayu ne Afirka ta Kudu ta gabatar da wani shirin  yarjejeniya ta kasuwanci ga gwamnatin Trump, amma kuma gwamnatin Amurka bat a bayar da amsa kan hakan ba. kuma ta sake duba ta a watan Yuni, ba tare da bayar da amsa ba. Ya kara da cewa, jami’an  Afirka ta Kudu sun yi magana da jami’an Amurka a yammacin Laraba a ofishin jakadancin Washington da ke Pretoria da kuma wakilin kasuwanci na Amurka, amma har yanzu akwai rashin tabbas game...
    Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya bayar da rahoto a wannan  Alhamis cewa, wani soja ya kashe kansa bayan ya kwashe fiye da kwanaki 300 a cikin sojojin wucin gadi. Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, adadin sojojin da suka kashe kansu a wannan watan kadai ya kai bakwai. A cikin wannan yanayi, wani bincike na Isra’ila ya nuni da karuwar masu kasha kansu a tsakanin sojojin Isra’ila tun daga lokacin fara yakin zirin Gaza. Bincike na hadin gwiwa da jami’ar Tel Aviv da sojoji suka gudanar ya nuna cewa kashi 12% na sojoji suna fama da matsalar damuwa da kunci. Adadin wadanda suka kashe kansu tun daga watan Oktoban 2023 ya haura sojoji 43, ya zuwa ranar...
    Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a yau Juma’a, inda ta kai munanan hare-hare kan yankunan fararen hula da sansanonin ‘yan gudun hijira. Wadannan hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu a fadin yankin, lamarin da ke kara zurfafa damuwar da ake da ita game da mawuyacin da al’ummar yankin suke ciki. Kamfanin Nasser Medical Complex ya bayar da rahoton a wannan  Juma’a cewa, wani harin da jiragen saman Isra’ila suka kai kan tantunan da mutane suke fakewa a yankin Al-Mawasi da ke yammacin Khan Younis, ya kashe mutane hudu tare da jikkata wasu da dama. A wani harin  na daban a kusa da Morag a kudancin birnin Gaza,...
    Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin tsaro ya zama babban abin damuwa, ƴan fashi, tada ƙayar baya, da kuma garkuwa da mutane na ci gaba da wanzuwa a sassan Arewa da dama, inda jihohi kaɗan ne kamar Kaduna da Bauchi suka samu kwanciyar hankali,” in ji shi. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito da manufofin siyasa don kawo ƙarshen rikicin. ɗalhatu ya kuma soki manufofin gwamnatin tarayya kan...
    Tauraron dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya kammala komawarsa ƙungiyar Galatasaray ta ƙasar Turkiyya daga Napoli, a wata yarjejeniya ta dindindin da ta kai Yuro miliyan 75. Ƙungiyar Galatasaray ta sanar da kammala ɗaukar Osimhen a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa yarjejeniyar ta fara aiki daga nan take. Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru huɗu tare da zakarun na ƙasar Turkiyya, kuma za a biya shi Yuro miliyan 15 a kowace kakar wasa. Hakazalika, zai karɓi ƙarin Yuro miliyan 5 a matsayin hakkinsa na mallakar hoto, yayin da Napoli za ta sami kashi 10 cikin 100 na duk wani kudi da za a sayar da shi...
    Sai dai girma, kima da ɗaukakar da matasa ke da ita ga al’umma ta ja baya ƙasa sosai a bisa ga yadda rayuwarsu ke iyo da ninƙaya a kogin  zubar da mutunci ta hanyar aiwatar da abubuwan da ke da alamar ayar tambaya. Matasa da dama a yau ba su ganin kowa da gashi, ba su girmama kowa, ba su ganin mutuncin kowa, ba su daraja kowa ballantana har a tsawata masu ko a ba su shawara da ɗora su kan hanyar yadda za su daidaita rayuwar su daga gurɓatacciyar hanya zuwa madaidaiciyar hanya. Abin takaici ne da matuƙar damuwa yadda matasa suka gurɓata rayuwarsu mamakon amfani da lokaci da damar da suke da ita amma sai suka zaɓi biyewa...
    Jim kadan bayan da kungiyar kai Dauki Gaggawa ta kasar Sudan ta sanar kafa gwamnatin mai mambobi 15, kungiyar tarayyar Afirka ta mayar da martanin kin amincewa da ita. Bugu da kari kingiyar ta tarayyar Afirka ta kira yi  kasashen  da suke mambobi a cikinta da kuma kungiyoyin  kasa da kasa da kar su amince da halarci wannan gwamnatin. Har ila yau kungiyar ta tarayyar Afirka ta kuma yi gargadin cewa matakin da kungiyar ta RSF ta dauka zai iya tarwatsa Sudan ya kuma rusa Shirin zaman lafiya wanda dama yana tangal-tangal. Kungiyar ta RSF ta bayyana Muhammad Hassan al-Ta’aysh a matsayin Fira ministan, sai kuma Janar Muhammad Dagalo a matsayin shugaban kasa. Kasar Sudan ta fada cikin yaki ne...
    Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” ya bayyana cewa; Ziyarar da shugaban kasar ta Iran zai kai zuwa Pakistan amsa karan Fira minister Shahbaz Sharif ne. Bugu da kari ziyarar za a yi ta ne a daidai lokacin da wannan yankin yake fama da sauye-sauye, haka nan kuma za ta mayar da hankali wajen bunkasa alakar kasashen biyu. Majiyar kasashen biyu, Iran da Pakistan sun ce shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan zai fara ziyarar tashi daga birnin Lahor ne, inda zai ziyarci hubbaren shahararren masanin kasar Allamha Muhammad Iqbal, sannan ya nufi binrin Islamaabab domin ganawa da jmai’an gwamnatin kasar.Daga cikin wadanda zai gana da su a can babban birnin kasar da akwai ‘yan siyasa da kuma jami’an soja da...
    A Alhamis din nan ne dai kasar ta Habasha ta fito da Shirin shuka bishiyoyi har miliyan 700 a rana daya, ta hanar shigar da miliyoyin mutanen kasar. Fira ministan kasar ta Habasha Abi Ahmad yana son a rika tunawa da shi anan gaba ta hanyar shuka bishiyoyin da za su kai biliyan 50, daga nan zuwa shekara ta 2026. Tun da safiyar jiya Alhamis ne dai miliyoyin mutanen kasar ta Habasha su ka fito zuwa wuraren yin shukar, inda su ka rika haka ramukan da za su yi dashen bishiyoyin. Kakakin gwamnatin kasar ta Habasha, Tesfahun Gobezay ya bayyana cewa, da jijjifin Safiya, gabanin cikar karfe; 6;a.m, mutane miliyan 14.9 sun dasa bishiyoyin da sun kai miliyan 355.  Shi...
    Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a jiya  Alhamis, ya bayyana abinda yake faruwa a Gaza da cewa, yana nuni da halayyar keta da mugunta ta ‘yan sahayoniya, don haka ya zama wajibi akan al’ummar musulmi da dukkanin jinsin bil’adama da su kalubalanci wannan irin zalunci da ba shi da tamka. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, wadanda aka fi cuta a Gaza su ne kananan yara, sannan kuma ya yi ishara da yadda kasashen larabawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa su ka kyale Gaza. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya ce; Da akwai kananan yara 100,000 da suke fuskantar hatsarin mutuwa saboda yunwa a Gaza, daga cikinsu da akwai jarirai 40,000 da suke fuskantar...
    Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun sojin. ɗuba da sashe na 217 na kudin tsarin mulikin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, wannan sashen, ayyukan soji tun daga na matakin rundunar sojin kasa da ta ruwa da kuma ta sama shi ne tabbatar da bai wa Nijeriya kariya, daga duk wani nau’in hare-haren, da ka iya zuwa,  daga ketare, musamman ta hanyar, bai wa iyakokin kasar kariya, musamman bayan shugban kasa,...
    Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cin ribar Naira biliyan 414 a watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya. Kamfanin ya bayyana hakan ne a rahotonsa na karshen wata shidan da ya gabatar a gaban Hukumar da ke Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya a ranar Alhamis. Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? A cewar rahoton, kamfanin ya kuma tafka asarar da ta kai ta Naira biliyan 90 saboda musayar kudaden kasashen waje. Rahoton ya kuma ce jimillar abin da kamfanin ya samu a tsawon lokacin kafin a cire riba ya kai Naira...
    Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya Aikin dai wani bangare ne na Naira biliyan 900 da aka ware domin inganta harkokin sufurin jiragen sama a fadin Najeriya. Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan jim kadan da kammala taron majalisar, inda ya ce tuni har an ba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban. Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na ganin hakan ya yi hannun riga ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa. Shin ko me dokar kasa ta ce game da wannan karin wa’adi da shugaban kasan ya yi? NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci...
    Mujallar Qiushi ta kasar Sin za ta wallafi jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping gobe Jumma’a 1 ga watan Agusta, wanda Xi ya taba gabatarwa a gun babban taron kiyaye muhallin halittu na kasar Sin a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2023. Jawabin ya bayyana cewa, bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin ta riga ta shiga sabon mataki na neman samun ci gaba mai inganci, wanda ke bukatar gaggauta kiyaye muhallin halittu da rage yawan iskar Carbon da ake fitarwa. Aikin kiyaye muhallin halittu na fuskantar matsin lamba. Ya kamata a yi kokarin zamanantar da kasar Sin bisa tushen samun daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. (Kande Gao) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
      Dandali na NINAuth, wanda NIMC ya tsara kuma ya aiwatar, yana bayar da damar tantance bayanan ‘yan kasa ta hanya mafi dacewa da aminci don tabbatar da asalinsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin. Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Hakan na zuwa ne bayan ganawar Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa a jiya Laraba. Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin. Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka Wata mata mai suna Misis Mary David, wacce ta yi rajista a asibitin duba lafiyar mata masu juna biyu, ta shaida wa wakilinmu cewa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis. Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya. Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Sakataren masarautar Gudi da ke Gadaka ne ya tabbatar da rasuwar Sarkin, ya kuma ce an shirya gudanar da Sallar Jana’izar marigayi Sarkin a ranar Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana a fadar Sarkin da ke Gadaka. Labarin rasuwar Sarkin dai ya tayar da hankalin a ɗaukacin al’ummar masarautar da ma Jihar Yobe...
    Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba.   Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke.   A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin Farfesa Yusuf Gana Balami a matsayin Shugaban Hukumar Ilimin Sakandare ta Jihar Borno.   Balami, Farfesa a fannin ilimi, ya fito ne daga Hawul da ke kudancin jihar.   Zulum ya taya Balami murna tare da bukatar sa da ya yi amfani da shekarunsa na gogewa a fannin ilimi, a matsayin shugaba a bangaren gudanarwa da karantarwa wajen sake fasalin ilimin sakandare a jihar. ...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta horas da Malaman makarantun sakandare kimanin dubu 20 ilimin fasahar sadarwar zamani (digital). Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Cibiyar Zaman Lafiya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Hauwa Ibrahim da take Amurka, a ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati da ke Dutse. Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah Ya ce: “Mun gabatar da cibiya ta dijital don malamai, don sadarwa da kuma kula da ilmantarwa a matakin farko, mun sanya hannu kan haɗin gwiwa na...
    A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai.   A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam Hafiz Khalid, ya gabatar da cikakken jadawalin ayyukan zaɓen. Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da gaskiya a kowane mataki, yana mai bayyana zaɓen a matsayin aikin gama gari da ke buƙatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki.   Mahalarta taron sun bayar da shawarwari masu amfani tare da gabatar da muhimman tambayoyi da suka shafi inganta sahihanci da nasarar zaɓen.   Wasu daga...
    A nasa tsokaci game da batun, wakilin musamman na kasar Sin a yankin kahon Afirka Xue Bing, ya ce Sin ta dade tana goyon bayan matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan kakabawa gwamnatin jeka na yi ka ta Falasdinawa takunkuman hadawa jami’anta visar shiga kasar a safiyar yau Alhamis. Shafin yanar gizo na labarai ‘abrabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa majiyar fadar white House ta bayyana cewa gwamnatin Palasdinawa musamman Mahmood Abbas suna zagon kasa ga kokarin da kasar Amurka ta ke yi don samar da zaman lafiya a Gaza. Labarin ya kara da cewa gwamnatin Falasdinawa tana mu’amala da wasu kasashen wai don amincewa da samuwar kasar Falasdinu a cikin watan satumba mai zuwa a MDD. A yau Alhamis ne wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya Steve Witkoff  Yake isa HKI don tattauna da gwamnatin saboda rage matsin lambar da wa HK...
    Ministan harkokin waje na kasar siriya ya isa birnin Mosco a yau Alhamis don bude sabon shafi da kasar Rasha bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-asad a shekarar da ta gabata. Shafin yanar gizo na larabai Arabnews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Asaad Hassan al-Shaibani tuna ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov sannan ya fada masa cewa, kasar Siriya tana son ta kara tabbatar da wasu yarjeniyoyi dake tsakanin Rasha da Siriya a can baya, sannan a samar da sabbin wuraren wadanda sabuwar gwamnatin rikon kasar Siriya take son ta kulla da Rasha, a cikin yanayin mutunta juna. A nashi bangaren Sergey Lavrov ya bayyana cewa kasar Rasha a shirye take ta taimakawa sabuwar gwamnatin...
    Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a birnin Athen na kasar Girka. Sun kuma kara da cewa tawagar yan wasan zun zama zakara a wannan gasar ne duk da cewa mutum guda daga cikinsu bai shaga wasan ba. Labarin ya kara da cewa matasan kasar Iran sun kware a wammam wasan gargajiya, wanda ake kiransa damben Roma. Tawagar ta sami, zinari 1, azurfa 1 da Tagulla 4 , ta kuma sami maki...
    Firay minisatan kasar Canada Mark Corney ya bada sanarwan cewa gwamnatin kasarsa zata amince da samuwar kasar Falasdinu a babban taron MDD a cikin watan satumba mai zuwa a birnin NewYork. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Carney yana fadar haka a yau Alhamis ya kuma kara da cewa gwamnatinsa ta dauki wannan matsayin ne, bayan abin bakin cikin da ke faruwa a Gaza, na amfani da yunwa a matsayin makami wanda HKI take yi. Sannan tare da matakan da gwamnatocin kasashen Faransa da Burtania suka dauki na yin haka a taron. Kasar Canada, a baya dai , tana daga cikin kasashen yamma wadanda suke goyon bayan HKI ido rufe. Bayan fara yakin Tufanaul Aska a ranar...
    Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu kasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban kasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alakar tarihi tsakanin kasar Laberiya da Amurka. Bugu da kari, Trump ya katse maganar shugaban kasar Mauritaniya Mohammed Ghazouani, inda ya nemi ya yi magana da sauri. A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar—ba domin neman karfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka din damar samun ma’adanan da take bukata,...
    Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya reshen Jihar Benuwe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa aƙalla shanu 340 na mambobinta ne aka sace a cikin watan Yuli na 2025. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jiha, Ibrahim Galma ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Makurdi. Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a garin Agatu da wasu sassan Ƙaramar hukumar Guma da ke Jihar Benuwe. Galma ya kuma yi zargin cewa, ɓarayin shanu da ke afkawa jama’a a Ƙaramar hukumar Agatu sun faɗaɗa hare-harensu zuwa sassan Jihar Kogi. “A ranar 19 ga Yuli, 2025...
    Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce wannan mataki na Tinubu zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyare da ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa a hukumar. Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje A cikin manyan ayyukan da ake son a kammala akwai shigar da...
    Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya ji ciwo mai tsanani a wajen. An garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Panorama inda aka ɗinke masa raunin da ƙwayoyin da suka kai guda shida. Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa Barcelona Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aris FC, wacce ta karɓi Perez aro daga Celta Vigo, ta tabbatar...
    Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani A cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025. Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026. Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu...
    Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani A cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025. Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026. Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu...
    Shugaban kasar Lebanon wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau ya ce; A cikin sakwannin da mu ka aike wa Amurka, mun bukaci ganin an kawo karshen hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kawo wa Lebanon, ta sama, kasa da ruwa, haka nan kuma kisan gillar da take yi wa mutane a cikin kasar.” Shugaba Aun ya kuma yi jinjina ga dukkanin shahidan kasar da su ka kwanta dama saboda kare Lebanon,kuma yana a matsayin wani abu ne mai kima da daraja a wurinmu.” Shugaba Aun na Lebanon ya kuma ce, Isra’ila abokiyar gaba ce wacce take hana mutanen da yaki ya tarwatsa komawa zuwa garuruwansu da kuma sake gina kudancin Lebanon da yaki ya rusa.” Haka nan...
    Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa. Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne. Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres Lamarin ya faru ne da ranar yammacin Lahadi, 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwalen ya taso daga ƙauyen Digawa a Ƙaramar Hukumar Jahun zuwa ƙauyen Zangon Maje da ke Ƙaramar Hukumar Taura. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis. Ofishin NEMA na Kano, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin. Wasu mazauna...
    Abdullahi ya ce tun kafin a kafa haɗakar, wasu sun riga sun fara yaɗa cewa an shirya ta ne domin Atiku. Ya ƙara da cewa: “Ni ina da shekara 56, wa ya ce ba zan iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba?” Da aka tambaye shi game da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Abdullahi ya ce Obi na cikin haɗakar har yanzu. Amma ya ce bai zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC ba har yanzu. Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta bai wa Obi da kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dama su fice daga jam’iyyunsu na yanzu wato LP da SDP. Ya kuma ce Obi ba zai koma jam’iyyar PDP ba, duk da cewa jam’iyyar...
    Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres,ya bayyana cewa, samar da makamashi mai tsabta da zai daidaita tsarin rayuwar dan Adam daga sarrafa wuta, ta hanyar yin amfani da tururi, zuwa rarrabuwar ma’adinan, shi ne ginshikin bunkasar al’umma. Mista Gutterres ya bayyana hakan ne a taron inganta samar da makamshi da aka gudanar a harabar ofishin Majalisar Dinkin Duniya. Ya ce “a yau, muna son tabbatar da yadda za a farka bisa tsarin sabon zamani. Rana tana fitowa don samar da makamashi mai tsabta ga al’umma. A bara, kusan dukkanin sabbin qarfin wutar lantarki sun fito ne daga abubuwan da ake sabuntawa. Zuba jari a harkar samar da makamashi mai tsafta darajarsa ta haura zuwa Dala tiriliyan 2...
    Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external) Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma Liverpool, Newcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta. (Mail – subscription required, external) Crystal Palace ta sanar da Arsenal cewa sai ta fara biya aƙalla fam miliyan 35 kafin ta ɗauko Eberechi Eze, daga baya ta cike sauran kuɗin. (Guardian, external) Palace a shirye take ta biya fam miliyan 27.6 domin ɗauko ɗanwasan baya na Jamus Yann Bisseck, mai shekara 24 daga Inter Milan domin maye gurbin Marc Guehi, da ake alaƙantawa da Liverpool. (Gazzetta dello Sport – in Italian, external) Chelsea na ci gaba da matsi kan Alejandro...
    Firaminista Mark Carney ya ce Canada ta shirya amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu a cikin watan Satumba, inda ta zamo ƙasa ta uku daga cikin ƙungiyar G7 da ta fitar da irin wannan sanarwa a cikin kwanakin nan. Carney ya ce za su ɗauki matakin ne ta la’akari da wasu sharuɗɗan gyara daga ɓangaren hukumomin Falasɗinu da suka haɗa da amincewa da tsarin dimokuraɗiyya da kuma gudanar da zaɓe ba tare da ƙungiyar Hamas ba a shekara mai zuwa. Sanarwar tasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan Birtaniya ta bayyana goyon bayan ta ga kafa ƙasar Falasɗinun a watan Satumba mai zuwa, kuma mako ɗaya bayan Faransa ta yi irin wannan sanarwa. Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta yi watsi da...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta saki tare da hada wadanda aka yi garkuwa da su talatin da biyar tare da iyalansu.   Sun kunshi mata goma sha shida da yara goma sha tara daga Kagara, Tegina da Agwara, bayan sun shafe makonni a hannun ‘yan sanda da ke tsare da kuma kawar da hankalinsu daga barayin da ke Minna.   Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman ya bayyana haka a lokacin wani takaitaccen bayani da ya mikawa shugaban karamar hukumar gidan rediyon Ayuba Usman Katako a Minna.   Kwamishinan ‘yan sandan wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Adamu ya wakilta, ya bayyana cewa za’a sake haduwa da wadanda abin ya shafa da iyalansu domin...
    Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai Ali Isah, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Majalisar bayan wata ganawa da mai kula da jihar Ribas Sole a Abuja.   Ali Isah, ya bayyana cewa mai kula da jihar ta Ribas ya kasance a gidan a wani bangare na ziyarar da ya saba yi domin yiwa kwamitin riko da ke sa ido kan al’amuran gwamnati.   Shugaban marasa rinjaye wanda ya jagoranci taron a madadin shugaban kwamitin wanda ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar Farfesa Julius Ihonvere, ya bayyana gamsuwa da kokarin da mai gudanarwa shi kadai yake yi na wanzar da zaman lafiya a jihar.   Ya ce mai kula da jihar ya tuntubi...
    Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta.   A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da ta zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Dauda Lawal da nuna halin ko in kula.   A cewar sanarwar, jam’iyyar ta damu matuka da wani faifan bidiyo na baya-bayan nan inda aka ga sama da mutane 200 mazauna Kaura Namoda suna rokon a taimaka musu biyo...
    Masu ruwa da tsakin Arewa sun yaba da kwazon Tinubu, inda suka bukaci a kara karfafa gwiwar ‘yan kasa a taron Kaduna.   Masu ruwa da tsaki a Arewacin Najeriya sun yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa irin ci gaban da ta samu wajen cika alkawuran zabe, musamman a muhimman batutuwan da suka shafi tsaron kasa, samar da ababen more rayuwa, da sake fasalin tattalin arziki.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban darakta na gidauniyar tunawa da Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello, Engr. Abubakar Gambo Umar, kuma ya rabawa manema labarai a karshen taron tattaunawa na kwanaki biyu da aka gudanar a Arewa House, Kaduna.   Ya yaba wa...
    Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya  bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.   Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.   Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.   “Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kori mabarata 94 daga titunan Ilorin, domin tantancewa, gurfanar da su da kuma mayar da su gida.   Da take magana da ‘yan jarida yayin aikin, kwamishiniyar jin dadin jama’a da ci gaban jihar Dr Mariam Nnafatima Imam ta ce wadanda aka kama domin dawo da su sun hada da mata 43 da maza 51.   Ta ce ma’aikatar ta yi aikin dawo da mabaratan domin an haramta barace-barace a jihar Kwara.   Imam ya godewa gwamnan jihar bisa kokarin da yake yi na ganin jihar ta kawar da barace-barace a kan tituna da sauran matsalolin zamantakewa .   Kwamishinan ta ce a ko da yaushe gwamnatin jihar tana tuntubar gwamnatocin jihohin masu bara a tituna...
    Ya ce har yanzu matsalar tsaro tana addabar sassan Nijeriya da dama, kuma ana yaudarar shugaban ƙasa game da hakan. Ya ce, “Idan Shugaba Tinubu yana sauraron labarai masu daɗi kawai daga waɗanda ke son faranta masa rai, to yana rayuwa ne a cikin duhu.” Abdullahi ya bayyana cewa al’umma da dama a Nijeriya har yanzu na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, kuma mutane na rayuwa cikin tsoro da fargaba. Ya ce ba daidai ba ne a riƙa nuna kamar abubuwa sun inganta, alhalin jama’a na cikin hali na ƙunci ba. Jam’iyyar ADC ta kuma soki gwamnatin Tinubu da cewa ba ta ɗauki matakan da suka dace ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Sun ce maimakon fadar shugaban ƙasa ta...
    Sama da mutum 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jihar Katsina, sakamakon sabbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Ƙananan Hukumomin Bakori da Faskari. Mutane daga ƙauyuka sama da 10 sun nemi mafaka a garin Bakori, inda da dama ke zaune wajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke kwana a waje ba tare da masauki ko abinci ba. Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kura Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa, maharan sukan shiga ƙauyuka da yawa, inda suka dinga harbi, ƙone gidaje, sannan suka sace mutane ciki har da mata da ƙananan yara....
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka ga sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa kasarta Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane, hukumomin shari’a da jiragen ruwa masu alaka da makamashi da man fetur na Iran sabbin takunkumi. Baqa’i ya gwada rashin amincewar Iran da bakar siyasar Amurka da na ‘yan sahayoniyya musamman farmakin da Amurka da gwamnatin sahayoniyya suka kaddamar na baya-bayan nan kan kasar Iran, yana mai bayyana kakaba takunkumin a matsayin baya da wani harumi na doka kawai matakin zalunci ne kan Iran lamarin da ke fayyace kiyayyar Amurka karara kan Iran. Baqa’i ya kara da cewa: Al’ummar Iran suna...
    Tawagar Iran ta fice daga taron majalisun dokokin kasashen duniya kafin fara jawabin jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a zaman taron A wata gagarumar nuna rashin amincewa da tushen zaluncin da ya addabi duniya, tawagogin kasashen Iran, Yemen, da Falasdinu sun fice daga zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, bayan da shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” zai fara gabatar da jawabinsa mai kunshe da bayanai neman tunzura jama’a, wanda kuma bayanai suka haifar da cece-kuce a tsakanin wadanda suka zauna suka saurara. A cikin jawabin shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” ya bayyana cewa; Akwai yiwuwar samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu a wajen yankunan Falasdinu, musamman a biranen London da Paris na kasashen Birtaniya da Faransa. Wannan matakin na nuna...
    Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran “IRGC” ya bayyana cewa: Hasashen Raunin Iran ya gushe, kuma ba zai sake dawowa ba Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Mohammad Na’eini ya jaddada cewa: Ra’ayin cewa Iran mai rauni ce ya raguje kwata-kwata, yana mai jaddada cewa; Yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan ya fallasa gazawar makiya wajen karya manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sannan kuma ya nuna cewa duk wani sabon harin wuce gona da iri zai fuskanci martani mai tsanani da gauni da zai wurga makiya cikin mummunar nadama. Hakan ya zo ne a jawabin da Birgediya Janar Na’eini ya gabatar a jiya Laraba a wajen bikin tunawa da shahidi Ramadan...
    Wani sojan Amurka ya ba da shaida game da kisan wani yaro da sojojin mamayar Isra’ila suka yi a cibiyar bada agaji ta Rafah Wani sojan Amurka da ke aiki a cibiyar rarraba kayan abinci a zirin Gaza ya yi furuci da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wani yaro Bafalasdine da ya yi tafiya mai nisan kilomita 12 a karkashin zafin rana, don neman kayan abincin agaji a yankin. A cikin wata sheda mai ratsa jiki da ya bayar a cikin wani dan gajeren faifan bidiyo a Amurka, Private Anthony Aguilar ya ba da labarin wani lokaci da ba za a manta da shi ba cewa: Wani yaro siriri mai suna Amir, babu takalmi a kafarsa, ya...
    Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu zafafan hare-hare guda 3 kan mayakan sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya Rundunar Sojin kasar Yemen ta sanar da cewa: Sojojinta sun kai wasu jerin zafafan hare-hare guda uku da jiragen saman yakin soji marasa matauka ciki, inda hare-haren suka janyo barna a muhimman wurare uku na makiya sojojin mamayar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta Yemen ta fitar ta bayyana cewa: Wadannan hare-hare wani bangare ne na matakin da ya dace na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kai wa kan zirin Gaza. Sannan sanarwar ta kara da cewa: Farmakin na farko an kai shi ne yankin Jaffa da aka mamaye...
    Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu ne kawai saboda ya fito daga Kudancin Najeriya. Yayin wata hira da Trust Radio, Onanuga ya ce maganar cewa ana yi wa Arewacin Najeriya wariya ba gaskiya ba ce, face tsantsar siyasa kawai. Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Ya ce ƙorafin da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi na cewa an yi watsi da Arewa wajen naɗe-naɗen muƙaman gwamnati da ayyukan ci gaba, wata dabara ce kawai don rage ƙimar shugabancin wanda ya fito daga Kudu. Ya shawarci ’yan siyasar Arewa...
    Da alama tallafin da matar Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta ba wadanda hare-haren jihar Binuwai ya raba da muhallansu na Naira biliyan daya ya bar baya da kura. Kwana daya da bayar da tallafin, ’yan gudun hijirar sun fito suna zanga-zangar yunwa, amma kakakin hukumar bayar da agaji ta jihar (SEMA), Terna Ager, ya ce musu kudin ba na sayen abinci ba ne. Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Aminiya ta rawaito yadda Sanata Remi a ranar Talata ta ziyarci jihar inda ta mika wa Gwamnan Jihar, Hyacinth Alia tallafin kudin, a madadin ’yan gudun hijirar....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan. Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar da martani ga kungiyar ta ACF. Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar? NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su.   Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan tsokaci ne a sakatariyar karamar hukumar Sule Tankarkar a ci gaba da rangadin kananan hukumomi da kwamatin yake yi.   A cewar sa, kwamatin zai tantance kasafin kudin karamar hukumar na shekarar 2024 da 2025 na ayyuka ta da jerin ayyukan raya kasa, da  takardun biyan kudaden ayyukan da littafin ta’ammalin kudaden na banki.   Yace kwamitin zai tantance takardun kudaden shiga tare da...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa. Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in  da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum. A wajen kaddamar da shirin a filin wasa na Dutse, Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin yana da manufa ta musamman domin tallafa wa jama’a kai tsaye. Ya ce ƙungiyoyin NURTW da mahauta suna da matuƙar tasiri, ba kawai ga membobinsu ba, har ma da al’umma gaba ɗaya, shi ya sa gwamnatinsa ta ga dacewar tallafa musu. Gwamnan ya kara da cewa taimakon...
    Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da aniyar ta ta bunƙasa harkar kiwon dabbobi a Nijeriya a matsayin wata muhimmiyar hanya ta magance rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, tare da amfani da damar tattalin arzikin da ke cikin ɓangaren. Ɗaya daga cikin Shugabannin Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Harkar Kiwo, Farfesa Attahiru Jega, shi ne ya bayyana hakan a wurin taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa, wanda Gidauniyar Sa Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna, a ranar Laraba. Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar Jega ya bayyana cewa sabuwar Ma’aikatar Bunƙasa...
      A shekara ta 2009, hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya ta dauki Yusuf aiki a matsayin mataimakin koci ga Samson Siasia  wanda ke rike da mukamin babban kocin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Yusuf har yanzu yana aiki da Siasia, ya taimakawa Pillars samun gurbin shiga gasar cin kofin CAF, a shekarar 2012 ya koma Enyimba inda ya maye gurbin Austin Eguavoen a matsayin koci kuma ya taimaka masu wajen lashe kofin gasar Federation Cup na shekarar 2013. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayanin da ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya yi a baya-bayan nan game da hasashe kan tattalin arzikin kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa ya jawo hankalin duniya sosai. Kuma sakamkon binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi a tsakanin masu bayyana ra’ayoyi 47,000 a kasashe 46 daga shekarar 2023 zuwa 2025, ya nuna jama’ar sun nuna yakini game da karfi da juriyar tattalin arzikin kasar Sin. Binciken ya nuna cewa, yawancin masu bayyana ra’ayoyin daga sassan duniya suna da kyakkyawan fata ga tattalin arzikin kasar Sin wajen samun bunkasa mai kyau a dogon lokaci, inda amincewarsu ta kai kashi 74.7 bisa dari, da 81.3 bisa...
    Wadannan ’yan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi sun sake nuna bajintar da kasar Sin ke nunawa a fagen kere-keren mutum-mutumi masu siffar dan’adam da kuma yadda masana’antar bangarensu ke samun ci gaba cikin hanzari a kasar. A watan Agusta mai kamawa ne kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na mutum-mutumi masu siffar dan’adam. Kuma wannan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi da aka gwabza fafatawar karshe a dandalin wasannin motsa jiki na fasahar zamani da ke birnin Beijing, wata kyakkyawar shaida ce a kan yadda kasar ta shirya wa karbar bakuncin wannan gasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba. Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali ya jaddada hakan ne a yayin jawabinsa a wajen wani taron tuntuɓa tsakanin ’yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a Jihar Kaduna. Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa A cewar ministan, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa kyale HKI wanda kasashen duniya suka yi ne, ya ke bawa HKI karfin giwan ci gaba da abinda take yi a gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokokin wanda ake gudanarwa a halin yanzu a birnin Geneva. Wannan dai shi ne taron shuwagabannin majalusun dokoki na duniya karo na 6 wanda MDD take daukar nauyinta. Dangane da hare-haren da HKI da Amurka suka kaiwa kasar Iran a cikin watan Yunin da ya gabata kuma ,Qalibof ya bayyana cewa manufarsu it ce lalata shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, kwata-kwata. Alhali hukumar...
    Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa falasdinawa 7 ne suka mutu a zirin gaza saboda yunwa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata  wanda ya sa adadin mutanen fa yunwa ta kashe a Gaza kai kai 154. Tashar talabijan ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto Asbitin Nasir na Gaza na cewa yawa wadanda yunwa ta kashe sanadiyyar kofar ragon da HKI ta yiwa Gaza ya kai  154 sannan 89 daga cikinsu jarirai ne suka fi yawa ya zuwa yau Laraba. A makon da ya gabata ne hukumar abinci ta duniya wato ‘, the United Nations World Food Program (WFP)” ta bada sanarwan cewa 1/3 na mutanen gaza suna kwana da yunwa saboda rashin abinci sanadayar hana...
    Firay ministan kasar Malta Robert Abela  ya bayyana cewa gwamnatinsa zata shelanta amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta a taron shuwagabannin kasashen duniya a cikin watan satumban mai zuwa. Robert Abela  ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Malta tana bukatar a samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Ya ce: kasar Malta tana bukatar samar da kasashen biyu\ masu zaman kansu a kasar Falasdinu da aka mamaye, sannan a halin yanzu hatta jam’iyyun adawa na kasar malta sun bayyana bukatar yin nhakan. Firay ministan ya bada wannan sanarwan ne bayan da tokwaransa na kasar Burtaniya Keir Starmer ya bada sanarwan mai kama da tashi, na cewa idan...
    Gwamnatin kasar Amurka ta umurci gwamnatin kasar Lebanon ta kwance damarar kungiyar Hizbullah a kudancin kasar ko kuma ba zata sake maganar tattaunawa da gwamnatin kasar kan samuwar sojojin HKI a wurare 5 a kudancin kasar ba, ko kuma maganar HKI ta dakatar da hare hare a kan kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayyana cewa dole gwamnatin kasar Lebanon ta kwamce damarar hizbullah . A kwanakin baya gwamnatin Amurka ta bawa gwamnatin kasar Lebanon zuwa karshen wannan shekarar ko ta kwance damarar kungiyar Hizbullah ko kuma HKI na da damar yin abinda taga dama da kasar Lebanon. A wani bangare kuma shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabi Beri ya tabbatar da cewa matukar...
    Ministocin harkokin wajen kasar Siriya da kuma na HKI zasu gudanar da taro a birnin Baku na kasar Azarbaijan a ranar Alhamis mai zuwa don tattauna maganar tsaro a kasar Siriya kamar yadda suka fada. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Asaad Al-Shaibani ministan harkokin wajen kasar Siriya da kuma ministan ayyuka na musamman na HKI Ron Dermer sun gudanar da taro a birnin Paris na kasar faransa a cikinn yan kwanakin da suka gabata, a halin yanzu kuma zasu gudanar da taron a birnin Baku na kasar Azrbaijan a ranar Alhamis mai zuwa. Labarin ya kara da cewa kafin haka dai Al-Shaibani ya ziyarci Moscow kamar yadda wata majiya wacce bata son a...
    Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa tun daga shekarar nan ta 2025 har zuwa 2026. IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya. Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa Asusun ya yi hasashen samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya da kashi 3.4 a 2025, ƙari a kan hasashen kashi 3.0 da ya yi a watan Afrilu. Haka kuma, IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai samun ƙarin bunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin...