2025-05-20@01:50:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4736
«kasar Sin a»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Kasar Faransa ta mika iko na sansanin soja na Contre-Amiral Protet ga kasar Senegel, wanda shi ne sansanin soja na 3 da aka mikawa kasar a bana. An mika sauran sansanoni biyu da suka hada da Marechal da Sanit-Exupery ne a watan Maris din da ya gabata, Kuma dukkan sansanonin na da mazauni ne a Dakar, babban birnin Senegal. Wata sanarwa da ofishin jakadancin Faransa ya fitar, ta ce an tsara mika dukkan wasu sansanonin dake karkarshin ikon Faransa a Senegal a bana, biyo bayan yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi. A ranar 31 ga watan Disamban 2024, shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar a jawabinsa na sabuwar shekara cewa, za a bukaci dakarun Faransa su fara janyewa daga...
Wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yeman ya fada a yankuna Falasdinawa da aka mamaye. Yemen ta jima da take kai hare-hare kan Isra’ila a matsayin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza dake fuskantar mamaya da ukuba da kisan kare dangi daga Isra’ila. A cikin bayanin da ya yi bayan harin, babban jami’in gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen Nasr al-Din Amer, ya yi ishara da yadda gwamnatin Isra’ila ta yi watsi da kiran da kasashen Larabawa suka yi na neman zaman lafiya, ya kuma jaddada cewa hare-haren da ke faruwa a yankunan da aka mamaye, shi ne yare daya tilo da gwamnatin Isra’ila ke fahimta. Hare-haren na Yemen sun yi matukar tasiri wajen durkusar da tattalin arzikin...
A farkon wannan sati ne wata takardar neman raba Masarautar Katsina ta bayyana, wadda take neman a ƙirƙiro ƙarin masarautu uku da suka haɗa da ƙarin sarki mai daraja ta ɗaya da mai daraja ta biyu da kuma mai daraja ta uku. Takardar wadda aka gani da tambarin da ke nuna alamar an miƙa ta ga Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tayar da ƙura, inda ake ta musayar yawu kan abin da ta ƙunsa da kuma abin da zai iya biyo baya. Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno Wakilinmu ya gano cewa takardar, wadda kafar yaɗa labarai ta Katsina Times ta fara wallafa wa a kafofin sada zumunta,...
Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya karɓi tawagar jami’an Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) tare da kamfanin Max Air domin duba kayayyakin aikin hukumar. A jawabinsa, mataimakin mai kula da ofishin hukumar da ke Kano, Mista Barnabas Anderson, ya ce manufar wannan ziyarar ita ce don yin binciken gaggawa da tabbatar da ingancin kayan aikin hukumar kula da alhazai ta jihar. Ya ƙara da cewa, tawagar ta tantance kayan aiki, shirin jigilar maniyyata na jihar, takardun tafiya, fasfo da kuma kayan aikin sansanin Alhazai. Ya bayyana cewa, za a yi jigilar rukuni na farko na maniyyata 550 daga jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan...
Aƙalla manoma 50 ne suka rasu, sakamakon wani mummunan hari da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai garin Malam Karanti da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa, a jihar Borno. Majiyoyi sun ce mayaƙan sun afka wa manoma yayin da suke noma da kamun kifi, duk da cewar suna biyan haraji kafin yin noma. Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani “Sun mallaki takardun izini daga kwamandan ISWAP da ke kula da yankin Malam Karanti har zuwa Dawashi. Sun jima suna samun kariya daga Amir Akilu, wanda shi ne kwamandan yankin,” in ji wani mazaunin yankin. Sai dai harin ya faru ne a lokacin da kwamandan bai kasance a...
Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ta ce masu bincike sun tabbatar da wata sabuwar halitta da aka samu a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, wanda aka yi wa lakabi da Niallia Tiangongensis A watan Mayun 2023 ne, tawagar ‘yan sama jannati ta kumbon Shenzhou-15 ta gano wani samfurin halitta a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin yayin da take cikin da’irarta. An kuma adana ta cikin yanayi mai sanyi, sannan daga bisani aka kawo ta duniyar dan Adam domin gudanar da nazari. Kuma bayan binciken kimiyya da ya shafi nazarin sauyawar yanayinta da tsarin kwayar halittarta da sauransu, masana sun tabbatar da cewa sabuwar halitta ce da ba a taba...
Yanzu haka, ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta za ta kammala kakar ba tare da lashe kofi ba. A wannan kakar kuwa, Liverpool ce ta lashe gasar Firimiya, yayin da Real Madrid ta fitar da Manchester City daga gasar Zakarun Turai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar. Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci kamar yadda doka ta tanada. Dukkan ‘yan takarar sun bayyana gamsuwarsu kan shigowar gwamnatin tarayya cikin lamarin, inda suke yi kira ga ministan ilimi ya sake duba dukkan matakan da da aka bi domin yin gaskiya kamar yadda dokar makarantar ta tanada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirarren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da Dala biliyan 1 a kudin tikitin shiga a kasuwar cikin gida kadai. Bugu da kari, wannan adadi, ya haura sama da Dala biliyan 2 a kudaden shiga...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Rome na Ƙasar Italiya domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo na XIV. Za a gudanar da bikin ne a wajen wani taron addu’a da ake kira “solemn mass” a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu. Crystal Palace ta lashe kofin FA na farko a tarihinta Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso An tarbi Shugaba Tinubu a filin jirgin sojin Mario De Bernardo, inda jakadiyar Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da jami’an diflomasiyya daga Vatican da ofishin jakadancin Najeriya suka tarbe shi. Tinubu ya samu gayyata ta musamman daga Sakatare Janar na Vatican, Cardinal Pietro Parolin. A cikin wasiƙar gayyatar, Fafaroma Leo XIV ya bayyana cewa ya...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Iraqi Abdul Latif Rashid, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na majalisar shugabannin kasashen kungiyar Larabawa, tare da taya murnar kaddamar da babban taron kungiyar na 34, a birnin Baghdad na Iraqi. Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da 80 da kafata, kungiyar kasashen Larabawa ta kasance mai mayar da hankali kan inganta hadin kai da karfafa yankin Larabawa da furta matsalolin kasashen da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Larabawa wajen zurfafa aminci da ingiza hadin gwiwar moriyar juna da kara musayar...
Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar. Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci kamar yadda doka ta tanada. Dukkan ‘yan takarar sun bayyana gamsuwarsu kan shigowar gwamnatin tarayya cikin lamarin, inda suke yi kira ga ministan ilimi ya sake duba dukkan matakan da da aka bi domin yin gaskiya kamar yadda dokar makarantar ta tanada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Crystal Palace ta doke Manchester City da ci ɗaya mai ban haushi a filin wasa na Wembley a ranar Asabar, inda ta lashe Kofin FA karo na farko a tarihinta. Eberechi Eze ne, ya zura ƙwallo ɗaya tilo tun da aka fara wasan, yayin da mai tsaron ragar Crystal Palace, Dean Henderson ya taka rawar gani a wasan wajen hana Man City zura ƙwallo. Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya Man City ta rasa damar yin kunnen doki a wasan bayan Omar Marmoush ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron raga. Henderson, ya tsallake rijiya da baya, bayan duba VAR kan...

Jagora: Jawaban Trump A Ziyar Da Ya Kai Wasu Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Abin Kunya Ne Gare Shi Ga Kuma Amurkawa
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa da dama daga cikin maganganunsa basu cancanci maida martani ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabar, a lokacinda yake ganawa da wasu malaman makaransu daga larduna daban daban na kasar, a Husainiyyar Imam Khonaini (q) a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa : Trump yace yana son amfani da karfin da Amurka...

Iran: Aiwatarda Yarjeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Armenia Da Arzerbaijan Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Kasashen Biyu
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan da gaggawa zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Armenia, Armen Grigoryan wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran a yau Asabar. Ministan ya kara da cewa JMI zata tabbatar da cewa an aiwatar da sulhu tsakanin kasashen biyu da gaggawa saboda tana dasawa da kasashen biyu makobta gareta. A cikin watan Maris da ya gabata ne kasashen Armenia da Arzerbaijan suka amince a rubuta yarjeniyar...
A taron kasashen larabawa karo na 34Th wanda ake gudanarwa a birnin Bagdaza na kasar Iraki, shuwagabannin kasashen larabawa sun bukaci tsagaita wuta a gaza sannan sun yi kira da aka kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, shuwagabannin sun bukaci a magance matsalolin da suke faruwa a Siriya Lebanon da kuma sudan. Ana taron shuwagabannin kasashen larabwa a Bagdaza ne a dai dai lokacinda gwamnatin HKI take kara fadada hare-hare a kan zirin Gaza da kuma kashe Falasdinawa maza da mata da yara mutkar abinda zata iya kashewa. Majiyar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu sojojin HKI sun kashe falasdinawa kimani 53,272 mafi yawansu mata da...

Gidan Adana Kayayyakin Tarihi Na Amurka Ya Mayarwa Kasar Sin Rubuce-rubucen Hannu Masu Daraja Na Lokacin Yake-yake A Kasar
Cikin jawabin da ya gabatar ta bidiyo, mataimakin ministan kula da al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Rao Quan, ya ce dawowar rubuce-rubucen na Wuxing Ling da Gongshou Zhan, na tabbatar da cewa za a iya nazarta da kare wadannan kayayyakin gargajiya masu daraja yadda ya kamata a mahaifarsu. (Fa’iza) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani babban jami’in kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza ya bada sanarwan cewa an fara tattaunawa da HKI ta kawo karshen wannan yakin a birnin doha ba tare da shimfida wasu sharudda ba. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto Taher Annunu daga daga cikin manya-manyan jami’an kungiyar ta Hamas yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa tattaunawar zata hada dukkan matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu. Annunu ya ce kungiyarsa zata gabatar da dukkan abubuwan da yakamata a tattaunawa a kansu kama daga tsagaita wuta, musayar fursinoni da kuma ficewar sojojin HKI daga Gaza. Majiyar HKI ta nakalto firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa ya aika tawagar tattaunawarsa zuwa birnin Doha na kasar Qatar.
Kwanan nan ne Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton dake sabunta hasashen yanayin tattalin arzikin duniya gami da makomarsa na shekara ta 2025 a tsakiyar shekarar da muke ciki, inda rahoton ke ganin kara harajin kwastam da rashin sanin tabbas game da manufofin cinikayya sun janyo tabarbarewar makomar tattalin arzikin duk duniya, tare da haifar da tarin kalubaloli ga kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin. Rahoton na hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya na bana, zai ragu zuwa kaso 2.4 bisa dari, yayin da saurin karuwar cinikayya zai ragu zuwa kaso 1.6 bisa dari. Kana, rahoton na ganin cewa, daidaita manufofi gami da hadin-gwiwar kasa da kasa, na da muhimmanci gaya ga...
A makon da ya gabata, wasu ma’aikatan hukumar ilimi ta ƙaramar hukumar Damboa guda biyu sun mutu a irin wannan hari a hanyar Damboa zuwa Maiduguri. ’Yan ta’addan Boko Haram sun dawo da amfani da bama-bamai da suke birnewa a hanya domin kai hari kan matafiya da motocin da ke amfani da manyan hanyoyin Jihar Borno, abin da ya janyo asarar rayuka da dama a baya-bayan nan. A halin yanzu kuma, dakarun sojin Nijeriya na ci gaba da kai farmaki a dazukan Sambisa da sauran maɓoyar ’yan ta’adda a faɗin jihar domin murƙushe su da kawar da su gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Tsaro da Gyaran Matasa, ya kama ’yan daba 31 a wani samame da ya gudana a unguwanni bakwai a jihar. An kai samamen ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Mayu, 2025 ƙarƙashin jagorancin Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata. Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno Unguwannin da aka kai samamen sun haɗa da Ɗorayi, Ja’in, Sharada, Unguwar Dabai, Dukawa, Kabuga, Kofar Mata da sauransu, wuraren da suka yi ƙaurin suna wajen aikata laifuka. Daga cikin waɗanda aka kama, mutum 25 ana zargin ’yan daba ne, yayin da shida ake zarginsu dallacin miyagun ƙwayoyi....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsafta tana kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwar mace. Duk da cewa galibi ana alaƙanta tsafta da kyawun gani ko ƙamshi, sai dai a zahirin gaskiya tsafta ta wuce gaban haka ce. Ita ce turbar zaman lafiya a gidan aure, makamin janyo soyayya, da ginshiƙin lafiyar jiki da tunani. Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya Gwamnatin Kano ta haramta ‘Ƙauyawa Day’ a lokacin bikin aure Wasu matan na iya cika ido da kwalliya a wajen biki ko taro, amma su kan bar gidansu cikin ƙazanta da rashin tsafta. A wasu lokuta kuma, akwai matan da rashin tsaftarsu ke janyo mutuwar aurensu, rashin kulawa da miji, ko kuma sa mijin ya ɗauki matakin ƙaro aure. Tsafta...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta sanar cewa, za a fara jigilar maniyyatan jihar a ranar Lahadi 18 ga wannan wata na Mayu, 2025, zuwa Ƙasa Mai Tsarki. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Badaru Bello Karofi, ya shaida wa wakilinmu, cewa maniyyatan da suka fito daga Malunfashi da Bakori, Ƙanƙara, Dandume, Ƙafur da Ɗanja sune rukunin farko da ake sa ran za su tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa da ke cikin babban birnin jihar. Tun farko sai da jagoran mahajjatan jahar, wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Joɓe ya bayyana cewar, gwamnatin jihar ta ɗauki duk wasu matakan da suka wajaba tun daga gida har zuwa Ƙasa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, ta dakatar da dukkanin cibiyoyin gudanar da taro da ke faɗin jihar, tare da haramta gudanar da bikin ‘Kauyawa Day’ gaba ɗaya. Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar, bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar. ISWAP ta yi wa manoma 15 yankan rago a Borno Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas Ya ce wannan mataki na cikin sabuwar doka da majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya wa hannu. “Daga yanzu, duk wanda ya shirya wani taro da sunan Kauyawa ko Villagers Day, ya karya doka,” in ji El-Mustapha. Sabuwar dokar ta bai wa hukumar...
A Premier League, kungiyoyi sun gama sanin Man United ciki da waje. “Dalili shi ne su kan hadu sau biyu duk shekara. Sun san abin da za su tarar game da ‘yanwasan United din da kuma filin wasanta, a gasar zakarun Turai kuma, akasari wannan ne karon farko da suke zuwa filin wasa na Old Trafford da kuma karawa da United. Ba su san yadda ya kamata su tunkare su ba” in ji shi. Sai dai ya ce Manchester United dole sai ta yi da gaske a kan kungiyarTottenham saboda duka daga Ingila suka fito kuma sun hadu da su sau uku a wannan kakar duka Tottenham tana samun nasara kuma Tottenham din ta san lagon Manchester United sosai saboda...
Sojoji da mafarauta don halaka mayaƙan Boko Haram biyar tare da daƙile wani hari da ’yan ta’addan suka kai a ƙauyen Warambe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa. Shugaban mafarautan wanda ɗan asalin garin ne ya ce a safiyar Juma’a ne maharan suka nemi shiga ƙauyen, “amma muka gana su, muka kashe mutum biyar daga cikinsu. An miƙa makaman da muka ƙwato daga hannunsu ga sojoji.” Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno, ya jinjina wa ƙoƙarin jami’an tsaron, musamman wajen ɗaukar mataki cikin gaggawa yana mai ba su ƙwarin gwiwar su ƙara...
Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna, wani lokaci yana magana kan zaman lafiya sannan a wasu lokutan yana barazana da yaki. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru biyu da samun nasarar tawagar “Rukunin Jirgin Ruwa na 86” na sojojin ruwan Iran, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yaba da sadaukarwar da jaruman da suka yi wannan hidimar, yana mai cewa: “Suna alfahari da kasancewar dakarunsu, yana mai...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Kiyaye ci gaba da sarrafa sinadarin yuraniyon da tushen kayan aikin makamashin nukiliya ba abubuwa ba ne da za a tattauna a kansu Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta samar da kwarin gwiwa dangane da ci gaba da zaman lafiya a shirinta na makamashin nukiliya, amma ba za ta iya tauye hakkin jama’ar Iran na halal da kuma hakkinsu na samar da makamashin nukiliya cikin lumana ba, ciki har da inganta sinadarin yuraniyom domin zaman lafiya ba. A wata ganawa ta hadin gwiwa da tare da tawagar babban taron kasa da kasa na Pugwash da hukumar makamashin nukiliya ta Iran ta shirya a yammacin...
Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana ‘yan jarida shiga taron gwamnonin Arewa. Duk jaridun kasar nan sun je a wurin. Duk gidajen rediyo da talbijin na Kaduna suna wurin. Duk wakilan manyan gidajen Talabijin da Rediyo da ke wajen Kaduna su ma suna nan. Kada ka dauki maganata a wani bangare daban, je ka bincika. Duk wadannan labarai ne irin na teburin mai shayi. Ni kuma ban sani ba. Abin da...
“Dangote ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba wanda ya cancanci yabo. Muna kan tattauna yadda za a kawo karshen rigimar. Nan gaba, za mu yi aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da wadataccen mai ga al’ummar Nijeriya,” in ji shi. Ya nuna cewa ta hanyar zaman sulhu za su kawo karshen matsalar, “Nan gaba kadan ba za ku ji wata rigima tsakanin NNPCL da matatar mai ta Dangote ba. Za mu yi aikin hadin guiwa domin amfanuwar ‘yan kasa.” Ojulari ya kuma yi tsokaci kan faduwar farashin danyen mai a duniya a baya-bayan nan, wanda ya rage kudaden shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu. “Wannan raguwar ta shafi kasafin kudin Nijeriya tun da babban...
An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar wasu da dama sakamakon turmutsutsu a yayin wani taron rabon kuɗaɗen tallafi a garin Bama da ke jihar Borno. Wasu bayanai sun bayyana cewa ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya da UNICEF suka shirya rabon tallafin. Shaidun gani da ido sun ce, turmutsitsin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 8:00 na safe a makarantar firamare ta Kasugula, daya daga cikin cibiyoyin bayar da tallafi da aka kebe a garin Bama. Rahoton na nuni da cewar waɗanda suka ci gajiyar shirin sun taru ne domin karɓar tallafin kuɗi na naira 28,500 kowannensu. Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo...
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.8 a shekarar 2023 (7.2 na kudaden shiga) zuwa kimanin naira tiriliyan 31.200. Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki. Ko...
Sai dai dan majalisar wakilai Ali Isah na (PDP, Gombe), bai amince da matsayin Madaki ba. Ya ce sanya shugaban kasa na a tsarin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai samar da adalci da sanin ya kamata ga dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan. Dan majalisa Sada Soli na (APC, Katsina), yayin da yake adawa da kudurin, ya ce dokar da aka gabatar “Na da illa sosai ga hadin kan kasa.” Ya ce sanya ka’idar shugabancin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai kai ga samar da abubuwa bisa cancanta. “Hakan zai iya sanya muradun yanki da na kabilanci a gaba su zamo mafi cancanta. Zai karfafin zabin mutanen da za su iya tsayawa takara kuma zai kara...
Wata mata da age zargin ta cije mazakutar saurayinta ta shiga hannun ’yan sanda. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta kama matar mai shekara 43 ne bayan ta yi wa masoyin nata wannan aika-aika ne a lokacin da suke rikici a cikin gida a unguwar Mile 3 da ke yankin Diobu a garin Fatakwal babban birnin jihar. Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, ya girgiza mazauna titin Bishop Okoye mai yawan jama’a lokacin da aka samu labarin lamarin. A cewar majiyoyi, rikicin ya fara ne lokacin da masoyin matar ya nemi kwanciya da ita. An bayar da rahoton cewa matar ta ƙi amincewa da buƙatar saurayin nata, inda ta zarge shi da yin amfani da ƙwayoyin masu ƙara kuzarin...
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza ya kai 53,119 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023. Adadin ya karu ne sakamakon wasu hare-haren Isra’ila na baya baya nan wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 93 wayewar safiyar Juma’a. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, ma’aikatar ta ce an kuma mika wasu mutane fiye da 200 da suka jikkata zuwa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri da sojojin Isra’ila suka kai a yankuna da dama. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an sami rahoton mutuwar mutane 109 da...
“Amma sai ku ga cewa daya bayan daya, mun magance yawancin wadannan matsalolin. Har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu, amma muna kan samun nasarori.” Da yake jawabi a wajen taron, wakilin AON, Obiora Okonkwo ya yi maraba da wannan sabon ci gaban, inda ya bayyana cewa zai inganta ayyukansu. A cewarsa, “Abin da muke gani a nan a yau wani babban ci gaba ne daga jerin abubuwa da dama.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iran da kasashen turan nan guda uku sun da ake wa lakabi da E3 sun kudiri anniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar kasar ta Iran. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran da kasashen Turan uku Birtaniya da Faransa da Jamus (EU-3) sun kuduri aniyar yin amfani da diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Gharibabadi ya bayyana hakan ne a shafinsa na X bayan ganawarsa da wakilan kasashen Turan uku na yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi shi ma ya halarci taron. Ya ce, wakilan...
Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan Isra’ilar don goyon bayan Falasdinu. Ministan harkokin soji na gwamnatin, Isra’ila Katz ya ce idan har Yemen ta ci gaba da ayyukanta “za su sha azaba mai radadi.” Katz ya ce kisan da gwamnatin za ta wa al-Houthi zai yi kama da kisan gilla kan “Deif da Sinwars a Gaza.” Ministan na Isra’ila yana magana ne a kan tsohon kwamandan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da ke Zirin Gaza, Mohammed Deif, wanda gwamnatin kasar ta sanar da kashe shi a watan Janairu. Katz ya kuma ce yuwuwar nasarar kisan gillar da gwamnati...
Adadin kudaden harkar soji a nahiyar Afirka a bara, musamman a Aljeriya da kasashen kawancen Sahel, ya karu. A cewar wani bincike da Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Duniya ta Stockholm (SIPRI) ta gudanar, kashe kudaden soji a Afirka ya karu zuwa dala biliyan 52.1 a shekarar 2024 a fadin Nahiyar, wanda ya karu da kashi 3 bisa 100 a shekarar 2023 da kuma karuwar kashi 22 cikin 100 a shekarar 2015. A cewar rahoton na SIPRI, kudaden da ake kashe wa sojojin na Arewacin Afirka ya kai dala biliyan 30.2 a shekarar 2024, ya kuma karu da kashi 4 cikin 100 a shekarar 2024. Kudaden da Aljeriya da Maroko kadai suka kashe ya kai kashi 90% na adadin kudaden...
A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki. “Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum biyar ne sun jikkata bayan da gobara ta tashi a gidan man Nobpet da ke kusa da mahaɗar Sojojin Sama a garin Fatakwal, Jihar Ribas. Gobarar ta kuma ƙone sama da motoci takwas da aka ajiye kusa da ofishin Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi. Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Ma’aikatan kashe gobara na Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar na Sojojin Sama ne suka yi aiki tare har suka iya kashe gobarar. Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Emmanuel Ninyaegwu, wanda direba motar haya ne, ya ce motarsa mai ɗaukar fasinja 18 ta ƙone gaba ɗaya. Ya...
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu. Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar hukumar Jin dadin alhazan jihar Jigawa dake Dutse babban birnin jihar. A cewarsa, ana sa fara jigilar maniyatan jihar zuwa kasar Saudi Arabia a ranar 20 da kuma 21 ga watan Mayun 2025. Ya ce jirgin Max air zai yi sawun farko da maniyata su 550 zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan Mayu. Mr Anderson yace a ranar 21...
A cewarsa, ba ga wannan akwai shirin kawo sauyi kan manyan kalubale da suka hada da lalata na’urorin wutar lantarki, gudanarwa, matsalolin yankuna da suke janyo cikas ga gudanar da ayyuka. Ya umarci hukumar kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) da ta tabbatar kamfanonin rabar da wutar lantarki sun bayar da hadin kan da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban hukumar Spain Pedro Sanchez ya bayyana ” Isra’ila” da cewa; “Mai Kisan Kiyashi Ce,” wacce kasarsa ba za yi mu’amala da ita ba. Fira ministan na kasar Spain ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martnni ga wani dan majalisar kasar daga yankin Catalonia, Gabrel Rovian yana wanda ya tuhume shi da cewa, yana huldar kasuwanci da Isra’ila,alhali tana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi. Kafafen watsa labarun Spain sun ce wannan shi ne karon farko da firma ministan kasar ya bayyana abinda Isra’ila take yi da cewa kisan kiyasn kare dangi ne. HKI ta fusata akan furucin da Fira ministan Spain tare da kiran jakadan kasar domin nuna masa rashin amincewa.
Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce; Jragen HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan tasoshin jiragen ruwa na Hudaidah, da Salif a gudunar Hudaidah dake yammacin kasar. Majiyar tsaron ta Yemen ta ci gaba da cewa; An yi amfani da bama-bamai masu yawa da aka jefa akan wadannan tasoshin jiragen ruwan,kuma fiye da jiragen sama na yaki 10 ne su ka kai harin. Wata majiyar HKI ta fada wa tashar talabijin din “Kan” cewa; manufar kai wadannan hare-haren su ne kakaba wa Yemen takunkumi ta ruwa.” A ranar 6 ga watan nan na Mayu da ake ciki, ma HKI ta kai wani harin akan filin saukar jiragen saman a Sana’a tare da kona jirgen saman kasar da dama. Ita dai...
Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Succès Masra. Jam’iyyar hamayya da Masra yake jagoranta, ta bayyana abinda jami’an tsaron su ka yi wa jagoran nata da cewa, garkuwa ce. Ita kuwa hukumar kasar ba ta fitar da wani bayani akan kamun Masra ba,wanda shi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata. A yayin wancan zaben dai shugaban ‘yan hamayyar siyasar ya riya cewa shi ne wanda ya lashe zaben,amma kuma daga baya ya amince da sakamakon da hukumar zabe ta sanar duk da cewa yana cike da kura-kurai kamar yadda...
A yau Jumma’a, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya yi hadin gwiwa da kawancen gidajen rediyon Turai na EBU wajen gabatar da rahoton Report ITU-R BT.2550, wato fasahar tsara shirye-shiryen bidiyo da rediyo ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta 5G, a shafin intanet na kwancen harkokin sadarwa na duniya wato ITU. Lamarin da ya nuna cewa, CMG ya taka muhimmiyar rawa a fannin tsara shirye-shirye masu inganci, ya kuma kai matsayi na gaba a fannin fitar da fasahohin tsara shirye-shiryen zamani masu inganci. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Sojojin da suke aiki a ƙarƙashin rundunar birget ta 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun kashe ’yan bindiga biyu tare da ƙwato shanu guda dubu ɗaya daga hannun ɓarayin shanu. Muƙaddashin Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojoji ta birget ta 6 da ke garin Jalingo, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Jalingo a ranar Juma’a. Tinubu zai halarci rantsar da sabon Fafaroma Leo An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Ya ce, nasarar ƙwato shanu tare da kashe ’yan bindigar ya kasance ne biyo bayan wani bayanan sirri da rundunar ta samu dangane da shuguban wasu guggun ’yan bindigar akan bubura talatin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kididdigar da ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun bana, adadin yarjejeniyoyin da suka shafi fasaha da aka kulla ya kai dubu 228 a kasar Sin, wadanda suka shafi Yuan triliyan 1 da biliyan 600, adadin da ya karu da kaso 13.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Lamarin da ya nuna cewa, kasuwar fasaha ta kasar Sin tana bunkasuwa yadda ya kamata. A matsayin daya daga cikin muhimman kasuwanni 5 na kasar Sin, bunkasuwar kasuwar fasaha tana da muhimmanci ga aikin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sana’o’i. Kididdigar ta nuna cewa, a shekarar 2024, jimillar kudaden da aka samu daga...
Firaminista Li ya nanata cewa, ya kamata dukkan sassan gwamnati da larduna su karfafa tsara manufofi da aiwatar da su, da inganta hadin gwiwa, domin kyautata kuzarin kasuwa da warware matsalolin al’umma yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Asabar ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Rome na ƙasar Italiya bisa gayyatar da sabon Fafaroma Leo XIV ya aike masa. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya sanar da cewa, shugaba Tinubu zai yi bulaguron ne tare da manyan jagororin ɗariƙar Katolika na Najeriya domin halartar bikin rantsar da sabon fafaroman wanda shi ne na 267. Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno A cewar Onanuga, Cardinal Pietro Parolin ya aike da goron gayyata daga Fafaroma Leo XIV, wanda...
Dangane da sake fasalin dokar zabe, shugaban hukumar INEC, ya ce hukumar na yin cudanya da majalisar dokokin kasar, inda ya ce makwanni biyu da suka gabata, ta yi wani taro a Legas tare da kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan sake fasalin zabe. “Majalisar dokoki ta kasa za ta shirya taron jin bahasin jama’a, bayan nan za a samar da kudirin doka, a karshen zancen za a mika wa shugaban kasa domin sanya hannu,” ya shaida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan. Ya ce zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da ci gaban tattalin arziƙi duk suna dogara ne da tsaron ƙasa. An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a Yobe Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu ƙirar Agusta 109 Trekker a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Bikin ya kasance wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne, ya wakilci Tinubu a wajen bikin. Ya ce Najeriya na...
“Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne. “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.” Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi. Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane uku da ake zargi ɗauke da buhuna 20 na haramtattun takin zamani samfurin “Urea”. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno DSP, Nahum Kenneth Daso ya fitar a ranar 15 ga Mayu, 2025. Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe Boko Haram — Atiku Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka Rundunar kai ɗaukin gaggawar (RRS), ƙarƙashin jagorancin Kwamishin ‘Yan sandan jihar CP Yusufu Mohammed Lawal ne ta kama waɗanda ake zargin a ranar 13 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe a unguwar Tashan Journey, Maiduguri. Waɗanda ake zargin sun haɗa da, Shamsuddeen Rabiu mai kimanin shekara 35,...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya murƙushe ƙungiyar Boko Haram lokacin da ta fara bayyana a shekarar 2002. Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Jihar Kogi a birnin Abuja. Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka Ƙungiya mai alaƙa da Alƙa’ida ta yi iƙirarin kashe sojoji 200 a Buarkina Faso Ya bayyana cewa lokacin da Boko Haram ta fara tayar da hankali a Jihar Yobe, Obasanjo ya kira shi domin neman shawararsa. Atiku, ya bayar da shawarar a kira shugabannin tsaro a ba su wa’adin daƙile lamarin, ko su...
Gwamnatin Jihar Katsina ta samu sahalewar Hukumar Wasanni ta Kasa domin gina Birnin Dawakai na farko a nahiyar Afirka. Wannan amincewa ta biyo bayan wata ganawa ta musammam tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda — wanda Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina Dokta Kabir Ali Masanawa ya wakilta — da Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Malam Shehu Dikko da Ministar Al’adu, Yawon Bude da kuma Tattalin Arziqin Kirkire-kirkire Barista Hannatu Musa Musawa. Gwamna Radda wanda ya bayyana cewa, gagarumin aikin Birnin Dawakan zai lakume biliyoyin Naira kuma zai kara inganta qokarin gwamnatin jihar na raya al’adun jihar tare da samar da hanyoyin tattalin arziki mai dorewa ga al’ummar jihar da arewacin Najeriya gaba daya. Sabon birnin Dawakan na...

Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista
“Wannan ya ba wasu jihohi fiye da goma sha daya ‘yancin kai, tare da karin wadanda ake sa ran za su biyo baya. Wadannan jihohin yanzu suna iya shiga cikin masana’antar wutar lantarki, daga samarwa har zuwa isarwa, rarraba, har ma da samar da mitoci.” “Na biyu, dole ne mu magance rashin ingancin ababen more rayuwa, wanda ya taru a cikin shekaru 60 da suka wuce saboda rashin kula da rashin isasshen zuba jari don farfado da tsarin zamanantar da wutar lantarki.” Ministan ya kuma jaddada bukatar cike gibin mita na sama da kashi 50 bisa dari, yana mai cewa shirin shugaban kasa yana nufin cimma wannan ta hanyar girka mita miliyan 18 a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ya...
Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta shiga rudani a ranar Alhamis bayan da aka samu rahotanni masu karo da juna game da matsayin yajin aikin da reshenta na Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke yi. Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya gudanar da taron manema labarai inda ya sanar da cewa ASUU-KASU ta dakatar da yajin aikin nata, kuma za a ci gaba da karatun nan take. Ya danganta matakin janye yajin aikin da shiga tsakani da Gwamna Uba Sani ya yi, wanda ya amince da biyan Naira miliyan 50 miliyan don walwalar ma’aikata, tare da fitar da N146 miliyan don biyan wasu albashin da aka rike da kuma alawus-alawus na shirin koyon makamar aiki na dalibai (SIWES). Farfesa Musa ya...
Adepoyigi an sace shi ne da ƙarfe 10:00 na dare yayin da yake ƙoƙarin ajiye motarsa a gidansa da ke Ifon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yayin da Babbar Sallah ke ƙara ƙaratowa, ’yan kasuwar dabbobi sun bayyana fargaba game da yiwuwar farashin raguna da sauran dabbobin lauya zai yi tashi gwauro a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar ta sanya takunkumin wucin gadi kan fitar da dabbobi zuwa ƙetare, gami da yawaitar sace-sacen dabbobi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. A farkon watan nan na Mayu ne Gwamnatin Nijar ta sanar cewa matakin na da nufin daidaita farashi dabbobin layya a cikin gida da kuma tabbatar da wadatarsu ga al’ummarta —waɗanda mafi rinjaye Musulmi ne — kafin zuwan Babbar Sallah a farkon watan Yuni. Haramcin ya shafi fitar da shanu da tumaki da awaki da raƙuma, tare da...
Harajin ya kuma kai kasa da kimanin kaso 11 a cikin dari, wanda ya kai kasa da wanda ake karba, idan aka kwatanta da duniya. “Abinda muka yi shi ne, mun cire daukacin ma’aikatan da karbar kasa kaso uku a cikin darei a cikin tsarin na karabar harajin,” Inji tsohon Shugaban LLP. Ya shedawa manyan Malaman Makaranta da Jami’an da ke katbar haraji hakan ne, a wani taro da aka gudanar a jihar Legas Nijeriya dai, ta kasance kasar da sama da alumominta miliyan 8o, ke fama da kangin talauci. Hakan ya kuma kara haifar da hauhawan farashin kayan masarufi, musamman yadda kayan suka tashi a 2024, kafin su sauka zuwa kaso 24.2 a cikin dari. Kazalika, hauhauwan farashi da...
Dubban falasdinawa ma zauna Amurka ne suka fito gagarumar zanga-zanga don tunawa da zagayowar Ranar musiba a jiya Al-Hamis a birnin NewYork. Inda suka bukaci a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne musiba na shekaru 77 da suka gabata. Wato ranar da HKI to kore falasdinawa daga kasarsu bayan sun shelanta kafiwar HKI a kan kasarsu. Falasdinawa da kawayensu daga kasashen duniya da dama su kan fito zanga-zangar tunawa da wannan ranar shekaru 77 da suka gabata a ranar 15 ga watan Mayun shekara 1948., sannan ranar Nakba ta bana tazo a dai-dai lokacinda HKI take kara kissan Falasdinawa a Gaza. Yansanda a birnin NewYork...
Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun kashe wasu karin mutane 21 wato a safiyar yau Jumma’a, a sansanin yan gudun hijira na Jabaliya. wato sa’o’ii 5 bayan tsakiyar dare a kuma lokacin bada wannan labarin. Labarin ya kara da cewa a wasu hare haren guda biyu a Khan Yunus sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa 5 wasu daga cikinsu yara. Gwamnatin Hamas a Gaza, ta bayyana cewa, tun lokacinda sojojin yahudawan suka...
Ma’aikatar kiwon lafiya a kasar Saudia ta kaddamarda wata manhaja don kula da lafiyan mahajjata a hajjin bana, wanda aka tarjamata zuwa harsuna 8 a duniya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto kamfanin dillancin labaran Saudi Press Agency (SPA) na fadar haka a yau Jumma’a. Ya kuma kara da cewa harsunan da ake samun manhajar a ciki suna hada da Arabiyya, Inglishi, Faransaci, Urdu, Farisanci, Indonesia, Malay da kuma Turkanci. Manufar wannan manhajar ita ce bada shawara ga mahajjata kan yadda zasu kula da lafiyarsu a cikin wannan lokacinda Hajji na bana, wanda yake zuwa tare da zafi sosai. Da farko manhajan ya bukaci mahajjata su yi amfani da laima don rage zafin da ke fadawa a kansu....
Jakadan JMI a MDD ya bayyana cewa ranar Nakba ko musiba ga Falasdinawa, abin bakinciki ba karshen musubar ba ce sai faraway ne, don a yau shekaru 77 da suka gabata kenen da musibar da ta faru da Falasdinawa tana ci gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Amir Sa’id Iravani yaana fadar haka a jiya Alhamis a MDD inda ake taron tunawa da ranar musiba ta falasdina. Iravani ya kara da cewa taron tunawa da Nakba ta bana ta zo a dai-dai lokacinda Falasdinawa a Gaza suke cikin musiba wacce ba zata yi kasa da ranar Nakba ta shekara ta 1948 ba, ranar da aka kori Falasdinawa daga kasarsu, kuma ranar yahudawan suke bukukuwan kafa HKI shekaru...
Wata ƙungiyar ’yan ta’adda mai alaƙa da ƙungiyar Alƙa’ida ta ɗauki alhakin kashe sojoji 200 a ƙasar Burkina Faso. Ƙungiyar mai suna Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), ta ɗauki alhakin kai hari a Djibo, arewacin Burkina Faso, tana mai cewa ta kashe sojoji 200. Wannan ikirarin, wanda cibiyar SITE Intelligence Group mai hedkwata a Amurka ta ruwaito a ranar Alhamis, ya biyo bayan iƙirarin JNIM na baya da ta yi na kashe sojoji 60 a harin. SITE Intelligence Group, wacce ke sanya idanu kan ayyukan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ta intanet, ta nuna cewa harin wani bangare ne na ƙaruwar ayyukan JNIM a Burkina Faso a cikin watan da ya gabata, wanda ya haifar da asarar rayuka da dama. Ɗaukar...
Wakilan kafafen yada labaran, sun tattauna kan kalubalen da fannin aikin noman kasar ke fuskanta da suka hada da rashin samar ainahin bayanai kan abin da ya shafi aikin noma. Rashin bayar da ingantaccen dauki ga fannin daga bangaren gwamnati, kalubalen rashin tsaro da zabar wasu ‘yan lelen kafafen yada labarai, musaman da gwamnatin kasar ke yi, wajen bayar da tallace-tallacen da suka shafi bangaren aikin noma, inda suka yi nuni da cewa, kafafen yada labarai; sun dogara ne kacokan a kan samun tallace-tallace, wanda akasari shi ne ke rike da su. Sun kuma bukaci a samar wa da kafafen yada labaran kasar, wata hanyar sadarwa ta bai daya, musamman domin su kara wallafa rahotannin da suka shafi ayyukan gwamnatin...
Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun. Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon. Kai tsaye sojojin suka kai hari kan sansanonin ’yan ta’addar da ke Garin Malam Ali da Garin Glucose da kuma da Ukuba, waɗanda ke cikin Dajin Sambisa. Wannan matakin da aka ɗauka ya biyo bayan jerin hare-hare da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Talata kan sansanonin sojoji guda uku a Rann da Gajiram da kuma da Dikwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu....
Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu. Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya. Shigowarsa ta farfaɗo da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa. Sai dai rikicin cikin gida da na shugabanci sun dabaibaye jam’iyyar, wanda hakan ya haddasa ficewar wasu manyan ’ya’yanta zuwa APC, lamarin da ke haifar da tambaya kan makomar NNPP a Kano. Shin NNPP za ta kai labari a Kano, musamman bayan ficewar wasu jiga-jiganta? NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai...

Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Imanin Iran Da Tattaunawan Zaman Lafiya Amma Ba Za Ta Amince Da Barazana Ba
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan shirin makamashin nukiliyar Iran cikin karfin gwiwa da mutunta juna, yana mai jaddada wajabcin rashin mika wuya ko mika kai ga duk wata barazana. Shugaba Pezeshkiyon ya jaddada cewa yin shawarwari ɗaya ne daga cikin ka’idodin hankali da zurfin tunani, amma ba a kan kowane farashi ba. Dole ne a gudanar da shawarwari cikin aminci da mutuntawa tare da bin ka’idojin kasa da kare kima....

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Karfin Tsaro Da Makamansu Masu Linzami Ne Suka Hana Makiya Kai Musu Hari
Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, da a ce Amurka za ta iya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba za ta shiga zaman tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ta dogara da karfin sojanta, kuma shi ne ya tilasta wa makiya zaman tattaunawa da ita. A ziyarar da ya kai wajen baje kolin littafai na birnin Tehran, Araqchi ya ce dangane da tattaunawa wand aba na kai tsaye ba da Amurka: Idan da a ce Amurka na da karfin lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba ta shiga tattaunawa ita ba. Araqcgi ya kara da cewa:...
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu dumu-dumu a muggan ayyukan da gwamnatin ‘yan shayoniyya suka aikata nakisan kare dangi a Gaza Jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya yi nuni da ire-iren laifuffukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke ci gaba da aikatawa kan al’ummar Falastinu, yana mai bayyana wadannan laifuka a matsayin wani misali karara na kisan kiyashi yana kuma daukar Amurka a matsayin babbar kawa a aikata wadannan muggan laifuka. A yayin zama na musamman a Majalisar Dinkin Duniya a yammacin jiya Alhamis kan batun boren Falasdinawa “Ankaba” na musamman ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya tana so da cikakken goyon baya...

Sojojin Yemen Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Babban Filin Jirgin Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Rundunar sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami Rundunar sojin Yemen ta sanar da kaddamar da farmakin soji kan babban filin tashin jiragen saman Ben Gurion da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma yin nuna kiyayya ga kisan kiyashin da makiya ‘yan sahayoniyya suke yi wa ‘yan uwansu a Zirin Gaza. Kakakin rundunar sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya bayyana cewa: Don goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmaya da kuma nuna rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya ‘yan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a yankin Zirin Gaza, sojojin Yemen suna ci gaba da...

Kungiyar Hamas Ta Shirya Zanga-Zangar Goyon Bayan Halaccin Yunkurin ‘Yantar Da Kasarsu Daga Mamayar Yahudawa
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta shirya wata zanga-zanga da Falasdinawa ke jaddada cewa: babu halacci ga ‘yan mamaya kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da gwagwarmaya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da halacci ko kuma wani ikon mallakar wani yanki na Falasdinu da ta mamaye, kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da kare kansu ta hanyar gudanar da gwagwarmaya har sai sun kwato dukkanin Falastinu tare da kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci kai wacce Qudus zata kasance a matsayin babban birninta. A yayin bikin cika shekaru 77 da kafuwar Nakba, -boren Falasdinawa na farko- kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: “Ba za a yi wani sabon...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, He Yongqian, ta bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka ta dakatar da matakan kakaba harajin da ta dauka bisa binciken sashe na 232 ba tare da wani bata lokaci ba. A yayin taron manema labaru na yau da kullum, jami’ar ta ce, harajin kwastam na sashe na 232 da aka kakaba wa motocin da ake shigar da su daga waje, da karafa, da holoko, da kuma binciken sashe na 232 kan magunguna, “zallar aiki ne na mamayar bangare daya da kuma kariyar cinikayya.” Jami’ar ta kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta gaggauta kawo karshen matakan harajin na sashe na 232, tare...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa. Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’ Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom....
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa. Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’ Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom....
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta ce ta dauki mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar kafa Kwamitin Ladabtarwa da kuma Kwamitin Ilimi da Horaswa. A cikin wata sanarwa da Sakatariyar kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed ta fitar, ta bayyana cewa Kwamared Sabo Abdullahi Guri ne zai jagoranci Kwamitin Ladabtarwar tare da Kwamared Mati Ali, da Dr. Musa Idris Barnawa da Yusuf Sulaiman a matsayin mambobi, yayin da Muhammad Askira Musa zai kasance Sakataren kwamitin. Sanarwar ta bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da bin ka’idojin aikin jarida, warware matsalolin rashin ladabi ko sabawa doka cikin aikin, da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikin jarida a...
Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya koka da cewa, da yawa daga cikin daliban, sun yi tafiya mai nisa domin zana jarabawar UTME a cibiyoyin jarabawar. Amma abin takaici, sai ga sakamakon ya fito da koma baya da yawa. Duk da cewa, hukumar JAMB ta amince cewa, tangardar na’ura ce ta janyo faduwar amma akwai bukatar a binciki hukumar. Idan za a iya tunawa, sakamakon jarabawar UTME na 2025 da JAMB...
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya mayar da martani ga shugaba Donald Trump na Amurka, yana mai cewa Iran kasa ce son zaman lafiya ba yaki ba. Zaman lafiya muke nema, ba yaki ba; Su ne ke haifar da rikici. Muna fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar nan da ma makwabtanmu, inji shugaba Pezeshkian. Muna neman ‘yan uwantaka da daidaito tsakanin kasashen Azarbaijan, Rasha, Afghanistan, Pakistan, Iraki da Saudiyya, in ji shugaban na Iran a, yayin da yake ishara da kalaman Trump. Trump yana ganin zai iya yi mana barazana, ya sanya mana takunkumi, da kuma yin magana game da hakkin dan Adam, amma a lokaci guda suna da hannu a tashe-tashen hankula da laifuffuka a...
Iran ta bayyana cewa za ta yi zama gobe Juma’a da kasashen nan na turai guda uku da ake kira E3, wato Biritaniya, Jamus da kuma Faransa kan shirinta na nukiliya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa, a ranar Juma’a 16 ga watan Mayu ne za a yi shawarwari karo na hudu da Teheran da kasashen Turan da suka kulla yarjejeniyar nukiliyar 2015. Ya ce za a gudanar da taron ne a birnin Istanbul na kasar Turkiyya. Babban ajandar taron dai shi ne ci gaba da tuntubar juna da kasashen uku, musamman kan shawarwarin dake tsakanin Tehran da Washington. Ya zuwa yanzu dai Iran da kasashen turai sun gudanar da shawarwari guda uku kan batun nukiliyar...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da amfani da katangewar da ta yi wa Gaza a matsayin makamin kawar da wata al’umma. A wani rahoto data fitar yau Alhamis, kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da yin amfani da shingen da aka yi wa Zirin Gaza a matsayin “wani makami na share al’umma,” yayin da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da duk wani agajin jin kai cikin yankin Falasdinu tun ranar 2 ga Maris. Katange zirin da Isra’ila ta yi ya fi karfin dabarun soji, ya kai wani yunkuri na share al’umma inji Federico Borello, darakan zatarwa mai riko na kungiyar a cikin wata sanarwa da ya caccaki shirin Isra’ila na zaunar da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rasha da Ukraine sun tabbatar da aikewa da tawaga dukkansu domin gudanar da tattaunawa ta kai tsaye tsakanin kasashen dake rikici da juna. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya aike da tawagar Ukraine zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya domin ganawa da wakilan Rasha domin tattaunawa kan zaman lafiya, amma shi da kansa ba zai je can ba, kamar yadda wani babban jami’in Ukraine ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP. Jami’in ya ce “Shugaban ya yanke shawarar cewa Ukraine za ta shiga tattaunawa da Rasha a Istanbul amma Volodymyr Zelensky ba zai je Istanbul ba saboda taron “ba a matakin shugabanni ba. Ita ma fadar Kremlin ta sanar da jerin sunayen wakilan kasar don tattaunawa da Ukraine a Istanbul....
Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Aljeriya su hada kai wajen kai kayan agaji a zirin Gaza da yaki ya daidaita. Qalibaf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar al’ummar kasar Aljeriya Ibrahim Boughali a ranar Laraba a birnin Jakarta na kasar Indonesiya, a gefen taron ‘yan majalisar dokokin na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta PUIC karo na 19. Ya jaddada muhimmancin samar da hadin kai wajen tunkarar hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke yi a Falasdinu da kuma maido da hakkokin al’ummar Falastinu da ake zalunta a zirin Gaza. Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su hada kai su nemo...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Alhamis din nan, wasu hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai sun kai ziyara hedikwatar hukumar ta NOA inda suka yi amfani da damar wajen lekawa daya daga cikin kayayyakin tarihin Nijeriya a baya – ofishin marigayi shugaba Shagari. Bayan kammala ziyarar, daya daga cikin hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook domin bayyana abin da suka gani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A makon nan ne aka ga hotunan Sheikh Alƙali Zariya ya halarci zauren tattaunawa na fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, wanda ake kira ‘Gabon Talkshow’, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Gabon Talkshow dandali ne da jaruma Hadiza ke gayyatar mashahuran jarumai da mawaƙa domin tattauna game da rayuwarsu da ayyukansu a masana’antar nishaɗi. Tsaro: Tinubu ya ƙaddamar da rundunar tsaron daji a faɗin Najeriya Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS Bayyanar Sheikh Alƙali a wannan dandali ya jawo suka mai tarin yawa daga al’umma. Wasu na ganin bai dace da matsayin malami irinsa ya halarci irin wannan dandali ba, domin ba wajen ilmantarwa ba ne ko karantarwa. A cewar wasu, hakan zai...
An karrama Injiniya Dr. Mohammed Uba da lambar yabo ta kasa ta Rootswatch ta shekarar 2025, a matsayin girmamawa bisa gagarumin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma, aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa, da kuma kyakkyawan jagoranci. An mika wannan lambar yabo ne a yau a Cibiyar Karramawa ta Kasa da Kasa da ke Abuja. An karrama Dr. Uba tare da wasu shugabannin kananan hukumomi guda uku daga Jihar Jigawa da suka hada da Abdullahi Na Layi, Jarma na Garki, da Malam Madori, saboda hadin gwiwarsu wajen bunkasa ci gaban al’umma tun daga yankunan karkara. Taron ya jawo hankalin manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar, kuma ya kasance wata hanya ta ƙarfafa gwiwar shugabannin kananan hukumomi...
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri. Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis. Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Kakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da Doma a cikin Jihar Nasarawa don taimakon masu aikata laifuka a Katsina, inda take zaune. “Cikin gaggawa kan bayanan sirri da aka samu, Kwamishinan ’yan sanda CP Shetima J. Mohammed, ya ba da umarnin tura sashin yaƙi da masu garkuwa da...