Editan BBC Hausa ya magantu kan zargin musguna wa ma’aikciya
Published: 30th, August 2025 GMT
Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ce zargin cin zarafi a wurin aiki da ake yi masa ba su da tushe.
Lamarin ya samo asali ne bayan wata tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa, Halima Umar Saleh, a yayin wata tattaunawa da tashar Arewa24 ta bayyana cewa ta fuskanci musgunawa a lokacin aikin ta, kodayake ba ta ambaci sunan editan da ya yi mata hakan ba.
A cikin bidiyon, Halima ta ce ta sha wahala a lokacin da take aiki a sashen, tana mai cewa wani babban jami’i ya nuna mata ƙiyayya ba tare da wani dalili ba, abin da ya sa ta shiga damuwa ta kan yi kuka akai-akai.
Ta bayyana cewa ta sha barazanar korar aiki duk da cewa ba ta aikata wani laifi ba, har ma ya yaba mata cewa tana yin aikinta yadda ya kamata.
2027: ’Yan Najeriya suna fama da yunwa, sun san abin da za su yi — Kwankwaso Yadda jami’an tsaro suka kashe ’yan ta’adda a musayar wuta 50 a NejaBidiyon ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka buƙaci a gudanar da bincike kai tsaye.
Amma Aliyu Tanko, wanda mutane da dama suka nuna a matsayin wanda ake zargi, ya ce lamarin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa siyasar ofis ce kawai ta haddasa haka.
A lokacin da wakilinmu ya tuntuɓe shi, ya ƙi yin ƙarin bayani kan rahotannin da ke cewa an dakatar da shi daga aiki. Amma dai ya kuma tabbatar da cewa ya miƙa takardar murabus, sai dai har yanzu bai samu amsa daga mahukunta ba.
BBC ta bayyana cewa ba ta yin tsokaci kan lamurran ma’aikata kai tsaye, amma tana daukar duk wani ƙorafi kan halayya a wurin aiki da muhimmanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: musgunawa
এছাড়াও পড়ুন:
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.
Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp