Ranar Hausa: Masana Sun Bayyana Bunkasa Da Tasirin Harshen A Duniya
Published: 29th, August 2025 GMT
Harshen Hausa shine kan gaba a yawan masu magana a Afrika ta Yamma ta yadda yake da karbuwa a Nijeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Benin, Gabon, Togo, Afrika ta Tsakiya, Sudan da Saudiyya da sauran su. Hasalima kowace nahiya ta duniya akwai jami’ar da ake koyar da harshen Hausa da Hausanci.
Bunkasar Harshen Hausa ya sa harshen ke barazanar batar da kananam harsuna wadanda tuni wasu da dama a yau suka bace ba amo ba labarin su a bisa ga yadda yake mamaye harsuna a mabambantan kasashe.
Sai dai duk da kima da martabar da Harshen Hausa yake da shi da yadda daruruwan miliyoyin al’umma ke magana da Harshen har yau Jamhuriyar Nijar kadai ce kasar da ke amfani da Hausa a hukumance a matsayin harshen kasa.
Farfesan al’adun Hausawa na farko a duniya (2009) Aliyu Muhammad Bunza ya ce a na gudanar da taron ranar Hausa ta duniya domin jin amon Hausawa da al’adun su da gudunmuwar da suka bayar a duniyar zamanin su domin sun mamaye kasashe da yawa a Afrika sun kuma kafa sansani da yawa.
Shehin Malamin wanda ke koyarwa a jami’ar Usmanu Danfodoyo da ke Sakkwato ya kuma ce manufar taron shine domin Hausawa su san ina aka kwana ina aka tashi, samun hadin kan su a duk inda suke da wadanda ke a kasar Hausa da wajen kasar Hausa.
A bana a ranar 26 ga Agusta ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar Hausa ta duniya an gudanar da gagarumin bukin ne a Daura da ke jihar Katsina a hamshakiyar fitacciyar masarautar da ta kafa ingantaccen tarihin zama tushen Hausa da Hausawa, tarihin da babu wata kasa a kasar Hausa da ke da irin sa.
Basarake mai magana daya da murya daya, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, kasaitaccen Sarkin da ya yi fice wajen daga darajar Hausawa da al’adunsu tare da gudanar da mulkin gaskiya da adalci ne ya karbi bakuncin dubun- dubatar al’ummar ciki da wajen kasar Hausa da suka halarci taron
Taron ranar Hausa na bana a Daura wanda shine karo na 10 an yi masa taken “Amfani da Harshen Hausa wajen wanzar da zaman lafiyya” ya kayatar da da jama’a musamman yadda Hausa da Hausawa suka hadu, suka raya harshen, baje kolin al’adunsu su, tattauna matsaloli da kalubalen da harshen ke fuskanta da hanyoyin magance su.
A taron an gudanar da kayataccin wasannin Hausawa da suka yi fice da su, kama daga hawan daba tsakanin kasashen Hausa Bakwai da na Kanne Bakwai da kokawa da wasannin wuta na makere, haka ma mawaka sun baje fasahar hikimar su.
Abdulbaki Jari, matashin da ya jagoranci assasa ranar Hausa ta duniya ya bayyana cewar ba wai ana tunawa da ranar Hausa kadai a Afrika ta Yamma da Afrika ta Tsakiya ba, har ma a wurare da dama na duniya ciki har da Turai, Amurka da Asiya.
Dan jaridar ya bayyana cewar Harshen zai kai matakin da ya kamata a duniya idan har masu amfani da harshen suka hada kai domin magance kalubalen da ya dabaibaye harshen.
A kan gudanar da taron a Daura kuwa, Jari ya bayyana cewar Daura ita ce tushen Hausa kuma cibiyar dukkanin kasashen Hausa wadda ke martabawa, mutuntawa da daga dajar al’adun Hausawa don haka ta ke da kima a wajen Hausawa.
Jari ya ce ba wai sun assasa taron domin a rika gudanar da buki ba kawai, a’a, ya ce hanya ce da Hausa da Hausawa a fadin duniya za su hada kai su tattauna kalubalen da ke damun su da samar da zaman lafiya mai dorewa.
Matashin ya bayyana cewar harshen Hausa yana da girma da daukaka, don haka ya bambanta da sauran harsunan da ke bacewa, ya ce a na magana da harshen a nahiyar Afrika tsakanin mutane fiye da miliyan 170.
Jari wanda ma’aikaci ne a kafar yada labarai ta TRT Afrika ya bayyana cewar Harshen ya riga ya samu gurbi a kasashen Afurka musamman a Jamhuriyar Nijar a inda ya ce sama da kaso 80 cikin 100 na al’ummar kasar suna magana ne da Hausa. Haka ma a Ghana suna da amfani da Hausa sosai.
Ya ce girman harshen Hausa da karbuwar sa a duniya ne ya sa kafafen yada labarai da dama a fadin duniya ke yada shirye- shiryen su da Hausa domin isar da sako ga dinbin mabiyan su a fadin duniyar Hausawa.
Matashin ya bayyana cewar kamar wasa suka assasa ranar Hausa ta duniya a 2015, a kafafen sada zumunta amma ba zato ba tsammani saboda karbuwa da tasirin harshen, a yanzu duk duniya a na maganar tare da gudanar da taron a kasashe kusan 25.
Jari wanda ya kafa ingantaccen tarihi a kasar Hausa ya gabatar da bukatar da ke ci wa Hausawa tuwo a kwarya ta hanyar yin kira ga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma wato ECOWAS da ta duba yiyuwar sanya harshen Hausa a cikin harsunan da ake harkokin kasuwanci da shi da mu’amalar zamantakewa a hukumance a yankin wanda hakan zai kara taimakawa harshen da daga darajar harshen a idon duniya.
A tsokacinsa kan muhimmiyar ranar da tasirin ta, Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya bayyana cewar Hausawa na gudanar da bukin ranar Hausawa ta duniya ne domin bunkasa harshen tare da kokarin ganin ya zama daya daga cikin harsunan da ake koyar da ilimi da shi kamar yadda ake koyar da larabci, Turanci, Asiyanchi da Faransanchi da sauransu.
Farfesan ya bayyana cewar mashirya taron na son ganin Harshen Hausa ya kai matsayin da za a rika koyar da kowane irin limin duniya da shi.
A kan yadda za a inganta harshen kuwa, Bunza ya ce a yi kokarin samar mashi mazauna daga makarantun furamari, sakandire zuwa jami’o’i ya zama harshen hukuma a wajen da Hausawa suka rinjaye mutane.
Malamin ya bayyana cewar idan aka mayar da kowane ilimi a cikin harshen Uwa to ba yadda za a yi a rinjaye shi a harkokin ilimi da tsaro.
A cewar sa, Shehin Malamin Malamai, marigayi Farfesa Mahadi Adamu a 1975 ya yi rubutun musamman kan gudunmuwar Hausawa a tarihin Afrika ta Yamma kuma ba a samu wata al’umma da aka yi bayanin gudunmuwar ta ba kamar Hausawa da suka mamaye wuraren.
Ya ce taron ranar Hausa na da manufar hadin kan Bahaushe, sanin ina Bahaushe ya fito, yadda al’adunsa kyawawa suke, tabbatar da harshen Hausa da bunkasar sa da kokarin inganta Hausa da Hausawa da kara masu kwarin guiwa ga ci- gaban zamani.
Farfesa Bunza ya bayyana cewar ba a san adadin Hausawa da ake haihuwa da wadanda ke mutuwa ba don haka fadin adadin su abu ne mai wahala.
Ya ce a shekarar 2020 an bayyana cewar akwai Hausawa akalla miliyan 150 wanda ya ce adadin ba daidai ba ne domin adadin ya baiwa Hausa matsayin Harshe na 11 a duniya a cikin harsuna 7500.
Ya ce “idan aka bi adadin kwarai Hausa ta na da akalla adadin mutane miliyan 300 a duniya tare da zama harshe na hudu ko na biyar da ake jin sa a duniya saboda duk duniya a bakar fata da turai babu mai auren mace hudu in ba Bahaushe ba, ya fi su iyali da mata, haka ma a Afrika babu al’umma mafi harkokin kasuwanci irin Hausawa.”
A jawabinsa Firamin Ministan Jamhuriyar Nijar, Muhammad Lamine Zain ya bayyana cewar taron ya kara tabbatarwa duniya cewar Nijeriya da Nijar abu daya ne, ya ce suna fatar taron zai taimaka wajen warware matsalar diflomasiyya da ke akwai tsakanin kasashen biyu.
Gwamnan soji daga Jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, Kanal Muhammad Sani masallatchi wanda ya wakilci Firayim Ministan bayyana cewar yadda Hausa da Hausawa suka hadu domin bunkasa harshen su ya nuna tasirin da harshen yake da shi a duniya.
Firayim Ministan ya bayyana cewar taron zai kara hada kan Hausawa a ko’ina suke a duniya a matsayin ‘yan uwa daya al’umma daya. Haka ma Sarkin Musulmin Damagaram Aboubacar Oumarou Sanda ya albarkaci taron da kakkarfar tawaga.
Duk da kalubalen bacewar wasu kalmomi da harshen ke fuskanta, yadda dubun- dubatar al’umma a kasar Hausa suka rungumi ranar Hausa ta duniya tare da tunawa da ranar ya nuna kima da tasirin harshen da yadda yake kara bunkasa a idanun duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp ShareTweetSendShare Previous Post Me Ya Sa Wasu Kafofin Watsa Labarun Japan Suke Kokarin Musanta Kisan Kiyashin Nanjing? Relatedকীওয়ার্ড: ranar Hausa ta duniya Hausa da Hausawa da harshen Hausa Harshen Hausa ya da Harshen Hausa ya bayyana cewar Jamhuriyar Nijar Afrika ta Yamma Manyan Labarai a kasar Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu.
A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da Litinin (15-16 ga Satumba, 2025) za su kasance a Doha, babban birnin kasar Qatar, wanda zai karbi bakuncin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da na Islama, don ba da amsa ga baki daya kan harin da Isra’ila ta kai kan Qatar.
Ana gudanar da wannan taron gaggawa ne a cikin yanayi na musamman na yanki da na duniya kuma ya biyo bayan harin da Isra’ila ta kai kan Qatar. Ana dai kallonsa a matsayin wani gagarumin sauyi ba wai kawai dangane da batun Falasdinu ba, har ma da sauran ci gaban siyasa a yankin.
A cikin wannan mahallin, masana da kwararru kan harkokin yada labarai na Qatar sun jaddada cewa zaluncin da Isra’ila ke yi wa Qatar ya farfado da ra’ayin kishin kasa na Larabawa tare da sake fasalin wasu muhimman batutuwan yankin.
Hadin kan Matsayin Larabawa da Musulunci
Ahmed Al-Rumaihi, Darakta-Janar na Kamfanin Dillancin Labarai na Qatar, ya ce hanyar shari’a ta kasa da kasa ita ce mafi kyawu kuma zabin da ya dace don tunkarar ci gaba da keta haddin ‘yan mamaya na (Sionist) – na farko daga cikin laifuffukan da aka rubuta da Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Isra’ila ya yi. Kotunan duniya, musamman kotun shari’a ta duniya, sun kafa sharuɗɗa da yawa waɗanda ke tabbatar da girman waɗannan laifuka.
Al-Rumaihi ya kara da cewa, ana ci gaba da yin Allah-wadai da wannan mugunyar ta’addancin da Isra’ila ke yi wa kasar Qatar, a duniya, kuma wannan ba wani abu ba ne, illa dai sakamakon yadda duniya ke kara wayar da kan jama’a game da keta haddin majalisar ministocin Isra’ila.
Farfado da Ra’ayin kishin Kasa
Babban editan jaridar Al-Sharq na kasar Qatar Jaber Al-Harami ya bayyana cewa, ha’incin da Isra’ila ta yi wa Qatar ya farfado da ra’ayin kishin kasa na Larabawa zuwa wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ke karfafa imanin cewa ba kasa daya ba ce kawai, yankin gaba daya. Al-Harami ya jaddada cewa, Isra’ila ba ta amince da wani jan layi ba, ba ta bi yarjejeniyoyin da aka kulla ko yarjejeniya ba, a maimakon haka tana aiwatar da munanan manufofin ba tare da la’akari da ka’ida ba.
A cewar Al-Harami, ta hanyar wannan wuce gona da iri Isra’ila na neman kafa sabbin sharudda da bukatu a karkashin shirin da ake kira “Isra’ila Babba”, inda ta sanya kasashen Larabawa a gaban wani zabi na wanzuwa. Don haka wajibi ne taron na Doha ya tashi daga kace-nace zuwa aiki na hakika.
Hakazalika, Nasser Al-Azba, wani lauya na kasa da kasa, ya jaddada cewa, lokaci ya yi da ya wuce yin Allah wadai da take-take, maimakon daukar matakai masu amfani da kuma daukar matakai masu inganci a kasa.
Al-Azba ya bayyana cewa, harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, ya nuna karara karya ce ga yarjejeniyar Vienna ta 1968, wadda ta kafa tsarin doka na kare jami’an diflomasiyya da masu shiga tsakani na kasa da kasa. A tarihi, manzanni sun kasance suna samun cikakkiyar kariya, kuma wannan ka’ida tana cikin dokokin duniya a yau.
Lauyan dokar kasa da kasa ya kara da cewa mayar da martani bai kamata ya takaita ga matakan shari’a ba, amma kuma dole ne ya hada da kulla kawance da kasashe da ba na yammacin Turai ba kamar su China, Rasha, da kasashen BRICS, yayin da a lokaci guda za a tattara ra’ayoyin jama’a na duniya don fallasa irin ta’addancin Isra’ila.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025 Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci