2025-12-02@20:23:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12142

«Hukumar Shige da Ficen»:

    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Sharhin bayan labarai, wand ani tahar amin zan karanta. A cikin shirimmu na yau zamu yi Magana dangane cewa, shin gaskiyar ne ‘HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin HKI a karon farko a hukumance, ta bada sanarwan cewa, tana fama da karancin sojoji a dukkan rassan sojojin kasar, kuma wannan Babbar barazana ce kuma hatsari ne ga samuwar kasar kai tsaye. Tambaya ta farko it ace, menene Alamar karancin sojoji a cikin rundunonin sojojin HKI? Sanarwan ma’aikatar yakin HKI dangane da wannan ta ce, tana fada da karancin sojoji...
    Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya  Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe  Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi. Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya. Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Litinin ce Janar Musa ya yi wata ganawar sirri da Shugaba...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya          hana abokan gaba cimma mummunar manufarsu akan kasar. Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama ranar “Mutane Masu Bukata Ta Musamman” ta duniya ya bayyana cewa a yayin kallafaffen yaki na shekaru takwas tsakanin 1980-1988, dukkanin duniya ta kasance a bayan ‘yan Ba’asiyya da zummar kawo karshen jamhuriyar musulunci,amma goyon bayan da al’ummar Iran suke bai wa tsarin musulunci goyon baya, hakan ba ta faru ba. Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; “Yan Sahayoniya da Amurka sun kawo wa Iran hari da yakin kwanaki 12 a karkashin wannan irin tunanin...
    A yau Talata ne mai bai wa shugaban kasar ta Nigeria, shawara akan watsa labaru Bayo Onanuaga ya sanar da Nadin na Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin wanda zai maye gurbin Alhaji Muhammad Badru Abubakar da ya yi murabus a jiya Litinin. Janar Musa ya rike mukamai masu yawa na soja gabanin Nadin nasa a yau. Daga cikin mukamin shugaban bangaren tsaro na soja a tsakanin 2023 zuwa oktoba 2025.  Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar...
    Ma’aikatar harkokin wajen Njgeria ta sanar da bai wa dan takarar shugabanncin  kasar Guinea Bissau, Fernando Dias da Costa, ya kuma tsaya takara ne a tare da shugaban kasar  Umar Sisoko  Embalo da sojoji su ka kifar da gwamnatinsa kwanaki kadan bayan zabe. A ranar 27 ga watan Nuwamba ne dai Dias Da Costa ya sanar da cewa,shi ne wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, tare da zargin Embalo da cewa shi ne ya shirya juyin mulkin da ya kawo karshen zaben kasar, tun kafin a sanar da sakamakon zaben. Haka nan kuma ya ce ya tsallake rijiya daga kokarin kama shi a ranar da aka yi jiyin Mulki, ya kuma boye, har sai da ya sami...
    Rahotanni daga Ramallah sun ce a kalla sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila 3 ne su ka jikkata sanadiyyar  taka su da mota da wani Bapalasdine ya yi , a yau Talata. Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ambaci cewa; Wani Bafalasdine ya soka wa dan shaayoniya wuka da aka dauke shi zuwa asibiti domin karbar magani.” Majiyar ta ce da akwai sojojin a wurin da aka kai hari, don haka su ka bude wuta akan maharin Bapalasdine.” Su kuwa jaridun Falasdinawa a Ramallah sun ce wanda ya kai harin na Yau Talata ya yi shahada bayan da sojojin mamaya su ka bude masa wuta. A gefe daya, kungiyoyin gwgawarmayar Falasdinawa sun yi maraba da harin  akan ‘yan sahayoniya a kusa da Ramallah,...
    Majalisar Dattawa ta sanar da aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta waɗanda suka haɗa har da na tsaro da na tattara bayanan sirri, sakamakon ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta. Shugaban Majalisar Dattawan, kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman na yau Talata. Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe  Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya A sabbin sauye-sauyen da majalisar ta aiwatar, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ya zama shugaban kwamitin tsaro da na tattara bayanan sirri bayan ya bar kujerar kwamitin tsare-tsare na ƙasa. An naɗa Sanata Shehu Buba daga Bauchi a matsayin shugaban kwamitin harkokin Kiwo, bayan cire shi...
    Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin. Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025. An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da...
    Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya  Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi. Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya. Musa wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 har zuwa Oktoban 2025 lokacin da Shugaban Kasa ya sauke shi daga muƙamin a...
    Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai. Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu. Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.4%, inda ya danganta hakan da dabarun yaƙi da cutar da ake aiwatarwa a jihar. “Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi. Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta...
    Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu. Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba. Lamarin ya tayar da hankula a ƙauyukan da ke kewaye, inda iyalai da dama suka kwana cikin fargaba. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace matasa ne da suka tafi gona domin yin roron wake lokacin da aka...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da matakin da isra’ila ke dauka na tsauraran mataken shigar da kayan agaji zuwa yankin gaza musamman bangaren sansanin yan gudunn hijira da kuma tanti-tanti  da aka yi. Kakakin kungiyar hamas Hazem Qaseem ya jaddada cewa mafakar da suka rage a yankin tantuna ne da aka yi marasa karko, da ba za su iya jurewa iska ko yanayin sanyi ba. Yace har yanzu isra’ila tana bari a shiga da wani adadi kadan ne zuwa yankin gasa na kayayyakin agaji, wanda  ba zai wadatar da abubuwan bukatatun yau da kullum na rayuwa ba ga yawan alummar dake bukatar agaji a daidai lokacin da ake fuskantar mawuyacin yanayi dake bukatar taimakon gaggawa,...
    Rahotanni da suka fito daga Najeriya sun nuna cewa ministan tsaro Alh mohammadu Badaru Abubakar a ranar 1 ga watan Decemba ya mika takardar ajiye aiki a matsayinsa na ministan tsaron kasa, saboda wasu dalilai da suka shafi lafiyarsa, Kamar yadda kakakin shugaban kasa Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaba tinubu ya amince da takardar neman ajiye aikin,  kuma ya gudemasa game da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasarsa, tuni kuma aka fara lalubo wanda zai maye gurbinsa domin mika sunansa ga majalisa don a tantance shi. Badaru Abubakar dan shekara 63 da haihuwa shi ne gwamnan jihar jigawa har na tsawon zango biyu wato daga shekara ta 2015 zuwa ta 2023 kuma shugaban kasa tunubu ya  nada...
    Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi  ya fadi cewa iran tana ci gaba da aiki da diplomasiya duk da cikas da Amurka take kawo  wa a tattaunawar da ba ta kai tsaye ba, ganin cewa Amurka tana amfani da karfi wajen gudanar da harkokin duniya . Yace idan bangaren Amurka ta nuna shirinta na yin tattaunawa bisa mutunta jina da kare munufofin kowa, to iran za ta iya duba lamarin, saboda bamu taba barin teburin tattaunawa ba , saboda it ace ingantacciyar hanya ta fuskantar alumma. Dangane da Ziyarar da ya kai a bayan bayan nan a garin muscat da kuma tarurrukan da yayi, babban jami’in diplomasiyar iran yace babban abin takaici  shi ne inda dokokin kasa da kasa...
    Shugaban kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika kuma shugaban kasar saliyo Julius mada Bio yace ya tattauna da shugaban mulkin soji da ya yi juyin mulki a kasar Guinea Bissau , a kokarin da suke yi na ganin an yi aiki da kundin tsarin mulki a yankin na yammacin Afrika. A cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na X bio ya fadi cewa ganawar ta su ta zo ne bayan kudurin da kungiyar ta ECOWAS ta fitar a taron da ta gudanar kan irin mataken da zaa dauka game da batun juyin mulki da aka yi a kasar Guinea Bissau a makon jiya. Shiga tsakani a rikicin kasar Guinea Bissau ya zo ne sakamakon rashin zaman lafiya...
    An gudanar da bikin cika shekaru 41 da kafa kungiyar hadin guiwa ta tatalin arziki ta ECO a nan birnin Tehran ne a jiya litinin  inda sakatare janar din kungiyar Eco Majeed khan da ministan aladu reza salihi –amiri suka gabatar da jawabai a wajen, da ya shafi irin ci gaba da kungiyar ta samu a cikin wadannan shekaru da kuma bayyana muhimmancin yin aiki tare . Kungiyar Eco tana daga cikin mihimmiyar hanya ta duniya da ta fara daga yankin tekun fasha zuwa tsakiyar asiya , kuma kasashen dake mambobin kungiyar sun kai kusan rabin biliyan dake da arzikin makamashi da ma’adinai kasa, baya ga batun tattalin arziki , kungiyar tana matsayin jigo mai muhimmanci wajen huldodin diplomasiya a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.   An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi. NAJERIYA A YAU: Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? Wannan...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce: “Bayan zagaye biyar na tattaunawa, yayin da muke shirin zagaye na shida, ɓangaren Amurka ya karya hanyar diflomasiyya da kuma ƙoƙarin shiga tsakani da ake yi.” Seyyed Abbas Araghchi, Ministan Harkokin Wajen Iran, ya ce a wata hira da ya yi da shirin “Ma’a Musa al-Far’ei” a ranar Litinin: “Abin takaici dokokin ƙasa da ƙasa da tsarin duniya sun yi tasiri ga yanayin Amurka na amfani da ƙarfi a dangantakar ƙasa da ƙasa.” A cewar Pars Today, Araghchi ya ƙara da cewa: “Wannan ya bayyana a cikin tsoma bakin soja na ba bisa ƙa’ida ba da kuma aiwatar da ayyukan kisan kai duk inda suka ga dama.” Ya jaddada cewa: “Abin da muke gani...
    Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan  mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana mulkin mallaka a matsayin laifi kan bil’adama, da kuma tabbatar da an biya diyya bisa ga barna da cin zarafi da aka yi wa al’ummomin Afirka. Taron, wanda aka gudanar a babban birnin Aljeriya, an gudanar da shi  ne bisa wani kuduri na Tarayyar Afirka (AU) da aka amince da shi a farkon wannan shekarar wanda ke kira da a yi adalci wajen biyan diyya don magance illolin siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa da suka faru sakamakon mulkin mallaka. Ministan Harkokin Wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya ce tarihin Aljeriya a karkashin mamayar Faransa ya sanya...
    Paparoma Leo XIV ya halarci  taron Musulunci da Kiristanci da tattaunawa tsakanin addinai a dandalin Shahidai da ke Beirut. Bayan isowarsa, Paparoma ya samu tarba daga shugaban Mabiya addinin kirista na Lebanon Bechara Boutros al-Rahi, da shugaban Mabiya darikar Katolika na Syria Ignatius Joseph III Younan, da kuma Babban Mufti na Lebanon Sheikh Abdul Latif Derian, da Mataimakin Shugaban Majalisar koli ta Mabiya mazhabar Shi’a a Lebanon  Sheikh Ali al-Khatib. A lokacin taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Shi’a a Lebanon ya yi maraba da Paparoma, yana mai cewa: “Muna farin ciki da zuwnku a Lebanon a madadin Majalisar da kuma daukacin mabiya mazhabar shi’a na Lebanon, Muna maraba da kuma godiya da ziyararku zuwa kasarmu a wannan mawuyacin lokaci da kasarmu...
    Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya  yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai  gabatar da kuduri  don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela. Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana  cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai. A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri...
    An kashe wani ɗan sanda a wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai gidan Babban Jami’in Ɗan Sanda (DPO) mai kula Babba Ofishin ’Yan Sanda da ke Aujara a Ƙaramar Hukumar Jahun ta a Jihar Jigawa.   Da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, ranar 25 ga Nuwamba, 2025, ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan. Sanarwar rundunar ’yan sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa jami’an tsaro da ke gadin gidan sun yi ƙoƙarin dakile harin, inda aka samu musayar wuta. A yayin arangamar, biyu daga cikin jami’an sun samu munanan raunuka, aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa. Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus...
    Matatar Man Fetur ta Dangote a Najeriya ta sanar a wannan  Litinin cewa tana da ikon isar da lita biliyan 1.5 na man fetur a kowane wata, kuma ta yi kira ga hukumar kula da masana’antu da ta tabbatar da hakan a cikin alkalumanta na yau da kullun, bayan da hukumar ta fitar da bayanai da ke nuna cewa matatar tana samar da kusan kashi daya bisa uku ne kawai na wannan adadi. Ikirarin da ake yi cewa matatun man fetur na Najeriya ba su iya biyan bukatun kasa ba wani bangare ne na dalilin da ya sa gwamnati ta yi watsi da shirinta na hana shigo da kayayyakin man fetur da aka tace a watan da ya gabata ba....
    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa  ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita. Trump ya sanar a ranar Laraba da ta gabata cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na 2026 a Florida ba, yana mai ambaton zargin da ake yi wa kasar na kin mika shugabancin G20 ga wakilin ofishin jakadancin Amurka a bikin rufe taron da aka yi a kasar  a baya. Duk da haka, Pretoria ta dage cewa shugabancin da ake yi nak aba-karba  an mika shi ga...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa da Janar CG Musa na da nasaba da shirin shugaban kasar na cike gurbin da Badaru ya bari da kuma garambawul a shugabancin tsaron Najeriya. Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanar cewa Badaru ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya. An kama ’yan bindiga 4 a Kano MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa da Janar CG Musa na da nasaba da shirin shugaban kasar na cike gurbin da Badaru ya bari da kuma garambawul a shugabancin tsaron Najeriya. Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanar cewa Badaru ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya. An kama ’yan bindiga 4 a Kano MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar...
    Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon. Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har...
    Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon. Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har...
    Daga Shamsuddeen Mannir Atiku  Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a  zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa. Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa. Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baqaei ya bayyana cewa Amurka ce Babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, saboda ganin abinda take yi a halin yanzu a kasar Venezuela da kuma wasu kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka a yau litinin a taro da ‘yan jirisa da ya saba a ko wace Litinin. Baqaei ya kara da cewa a ci gaba da goyon bayan da Washington take bawa HKI ta rufe sararin samaniyar kasar Venezuela, don goyon bayan Falasdinawa, mutanen Siriya da Lebanon da take yi. Wanda kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa. Dnagne da dangantakar Iran da Saudiya kuma Baqaei ya...
    Paparoma Leo 14 wanda yake ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Lebanon ya gana da shugaban kasar Lebanon Josept Aun da kuma manya-manyan malamai da shuwagabannin kungiyoyin yan siyasa a kasar Lebanon. A jawabin da ya gabatar a gaban wadannan shuwagabannin kasar Lebanon Lio na 14 ya bukaci, su rungumi zaman tare da kuma hakuri wajen hada kai da kuma gina kasar Lebanon. Lio 14 ya ce mutanen kasar Lebanon sun sha wahala a tarihin kasar na zama, amma saboda gwazon da suke da shi wannan bai hana su zaman lafiya da juna ba. Wannan bai hanasu ci gaba da rayuwa ba. Duk da cewa akwai barazana mai yawa da ke fuskantar kasar. Yace, zama tare da wadanda kuke...
    Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan  siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata. Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a cikin watan Octoban da ya gabata. Jami’an tsaro sun yi dirar mikiya kan masu goyon bayan Chiroma, kuma sun kashe mutane da dama sun kuma kama wasu Anicen Ekaney ana daga cikin wadan da aka kama a birnin Duala a ranar 24 ga watan Octoba. Kuma Ekane ya zargi jami’an tsaro da kwace maganin Oxigen dinsa, wanda ya jefa rayuwarsa cikin hatsari,...
    Tawagar kungiyar raya tattalin arziki na kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bar bar birnin Bissau da sauri bayanda shugaban kasa Umaro Sissoco yayi barazanar zai fiddasu daga kasar ida sun kara jinkirin fita. A cikin watan da ya gabata ne kungiyar ta aiki tawagar zuwa kasar ta Gunea Bissai saboda gabatar da shawarorin kan yadda za’a gudanar da zabubbuka masu inganci a kasar. Tawagar ta kara da cewa tuni ta bawa manya manyan yan siyasa a kasar kofin shawarorin da suka gabatar, sun kuma fara nazarinsu. Sai dai tawagar ta gaggauta barin kasar a ranar Asabar bayan da ta sami sako daga fadar shugaban kasa mai cewa idan sun ki fita to zai sa a fiddasu da karfi. Tawagar ta...
    Hukumar kididdiga ta HKI ta basa sanarwan cewa yawan yahudawa da suke ficewa daga haramtacciyar kasar . Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ta nakalto hukumar na bada labarin cewa a shekara ta 2010 yawan masana wadanda suke da shahadar Jami’a ya karu ha rya kai kashi 46% sannan wannan adadin ya cilla sama a shekara ta 2023 bayan fara yakin tufanul aksa zuwa kashi 60.4 %. Har’ila yau kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan shekarun da suka gabata, yahudawa masu ilmin Jami’a da dama sun bar kasar, saboda yana yaki wanda baya karewa a kasar. Hukumar kididdiga na HKI a cikin yan kwanakin da suka gabata ta yada rahoto dangane da...
    Shugaban Ƙungiyar Iyaye na Jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa jami’ar ta yanke wasu kuɗi masu yawa domin yaye ɗalibai. A wata sanarwa da ya fitar tare da sakataren ƙungiyar, Hajiya Habiba Sarki, ya ce koken da aka kai wa PCACC da kuma rahotannin da aka wallafa ba su da tushe. Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno Ya bayyana zargin a matsayin yunƙurin ɓata wa jami’ar suna. Ya ce MAAUN na daga cikin jami’o’in masu zaman kansu mafi sauƙin farashi a Kano, kuma tana ba da ingantaccen ilimi. “MAAUN na ɗaya daga cikin jami’o’i masu zaman kansu masu...
    Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu. Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna. ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi  Sarkin Musulmi, ya ce bai kamata shugabanni su yi biris da ƙorafin jama’a ba, musamman a wannan lokaci da Arewa ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziƙi. A cewarsa, babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai nemi ƙuri’un jama’a sannan bayan ya...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace tuna shakarar 2012, waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu...
    Daga Bello Wakili  Najeriya ta ƙarfafa ƙoƙarinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya, shugabanni da jami’an lafiya su haɗa hannu wajen cimma wannan manufa. Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu ta jaddada cewa za a iya kawar da cutar HIV a Najeriya idan aka ci gaba da yin aiki cikin tsari, haɗin kai da kuma samun tallafi. Ta ce duk da cewa an samu cigaba a fannoni na rigakafi, magani da kulawa, ana buƙatar ci gaba da dagewa domin tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya na samun kariya....
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda, kuma ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta samu ’yantar da mambobin Cocin Christ Apostolic Church (CAC) 38 da aka yi garkuwa da su a yankin. Majiyar da ta yi magana da Rediyon Najeriya ta ce ’yan bindigar sun farmaki Aasaru ne a wani daji da ke kan hanyar Koro. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta...
    Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa. A cewar ofishin, sojojin Isra’ila na kuma tsare da mutane 38 ba bisa ka’ida ba.   ofishin ya ce ya lissafa laifukan tsagaita wuta guda 591, ciki har da harbi kai tsaye kan fararen hula, gidajensu, da tantuna, da kuma bama-bamai da rushe gidaje. Sanarwar ta ce, wadannan laifukan, suna “nufin mamayar na wargaza yarjejeniyar da kuma haifar da mummunan yanayi wanda ke barazana ga...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma. Mai magana da yawun Hamas, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta sosai, gwamnatin mamayar Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda ya tanadi dakatar da yaki da kuma cika alkawarinta. Hazem Qassem, ya fayyace cewa ci gaba da neman gawarwakin fursunoni, duk da wahalhalun da suke fuskanta, yana nuna cikakken jajircewar kungiyar ga yarjejeniyar. A wata hira da ya yi da Al Jazeera, ya kara da cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda ke kawo cikas ga aiwatar da ita. Kakakin...
    Daga Abdullahi Jalaluddeen  Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da  babura a fadin jihar. Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya da babura a cikin birnin Kano, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya a jihar. Danladi Karfi ya jaddada cewa dokar da ta haramta zirga-zirgar babura a matsayin sufuri na haya har yanzu tana nan daram, kuma za a aiwatar da ita sosai, inda ya gargadi masu karya doka da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani. Ya kara da cewa Kano...
    Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni. Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace mulki a shekarar 2023, da kuma kamfanin Orano, mallakin kasar Faransa wacce ke da kashi 90% a arzikin urinum da ake fitawar shekarun baya. A wani rahoto da gidan talabijin din kasar ta Nijar ya watsa da yammacin ranar Lahadi, an ambato shugaban kasar, Janar Abdourahamane Tiani, na tabbatar da “hakkin kasar na baje hajarta da albarkatunta da kuma sayar da su ga duk wanda...
    Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta aika da wata babbar tawaga zuwa Bissau a wannan Litinin. Tawagar, wacce shugaban ECOWAS na yanzu ke jagoranta, Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, ta hada da shugabannin kasashen Senegal, Cape Verde, da Togo, ko wakilansu don ganawa da sabbin hukumomi, da manyan ‘yan siyasa da na farar hula, don tattauna sharuddan komawa ga tsarin mulki.  “Sakon zai kasance mai karfi,” in ji wata majiya kusa da tawagar ta ECOWAS. Kafin nan sojojin da suka kwace  mulki a Giunea Bissau sun sanar da cewa zasuyi mulkin rikon kwarya na shekara daya. Tunda farko dama Kungiyar ta (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a  Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta. “Mutane sun qarshe ta ko’ina, har da faston, wanda aka fi sani da Baba Orlando da matarsa da wasu masu ibada duk an yi garkuwa da su. Gaskiya harin ya yi muni, dukkanmu tserewa muka yi daga cocin.” Sace masu ibadar a ranar Lahadi a Cocin Cherubim and Seraphim ya auku ne bayan a kwanan nan Gwamna Usman Ododo, ya koka da cewa wasu  manyan...
    Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai, kafin ta ba shi takardar shaidar kammala karatu da gabatar da bayanansa domin samun damar halartar aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC). Sai dai kuma, Hukumar Karɓar Ƙorafi ta Jihar Kano (PCACC) ta umarci iyayen ɗaliban cewa su dakata da biyan kuɗin har sai ta kammala bincike kan ƙorafin da suka gabatar mata a kan lamarin. Sanarwar...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma  ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi. Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki dama duniya baki daya. Bugu da kari bayan ganawarsa da Araqchi da musayar ra’ayoyi kan batutuwa daban daban, zai gana da sauran manyan jami’an gwammnatin kasar, da ake saran za su tattauna kan alakar dake tsakaninsu da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin da dai sauran batutuwa na kasa da kasa. Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan a lokacin ganawarsa...
    Pars Today – Shugaban Iran, a wata ganawa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, ya ce a lokacin da maƙiyan ƙasashen Musulmi ke neman ƙara matsin lamba, ana sa ran ƙasashen Musulunci za su sauƙaƙa wa junansu yanayi da kuma guje wa matsaloli masu sarkakiya. Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, a ranar Lahadi da yamma a ganawarsa da Hakan Fidan, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, ya yi magana game da tarihin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, al’adu, da kuma ‘yan’uwa. Ya bayyana waɗannan alaƙar a matsayin mai zurfi, na gaskiya, kuma cike da fa’idodi masu yawa na ci gaba. Ya ƙara da cewa idan ƙasashen Musulunci suka yi aiki da niyya ɗaya bisa haɗin kai, haɗin kai, da musayar gogewa, babu wani iko da...
    Nicolas Maduro shugaban kasar Venzuwela yayi tir da barazanar da Washington ke ta nanatawa na yin amfani da karfin soji kan karakas, kuma yayi gargadi game da shirin Amurka na kwace ikon kila da rijiyoyin mai na kasar a hanyar amfani da karfin soji. Maduro yayi wannan bayanin ne a cikin wata wasika da ya aikewa sakatare janar din hukumar kula da hakon manfetur ta duniya OPEC, Kasar venuzuwela a hukumance ta bayyanawa hukumar cewa gwamnatin Amurka tana so kwace kula da rijiyoyin manta, mafi girma a duniya, ta hanyar yin amfani da karfin soja akanta da mutane da sauran humumomin kasar, Haka zalika ya fadi a cikin wasikar cewa zai ci gaba da tsayawa kyam wajen kare arzikin makamashi...
    Fira ministan HKI Benjamin natanyaho ya bukaci yafiyar shugaban kasa game da shari’a da aka dade ana yi kan zargin da ake masa na cin hancin da rashawa da mutane da sauran yan siyasa ke Allah wadarai da shi. Mazu zanga zanga sun mamaye gidan shugaban gwamnatin isra’ila Isaac Herzog inda suka yi tir da wanna mataki kuma suka bayyana shi a matsayin keta doka , suna ta daga ganyen Ayaba da aciki aka rubuta afuwa, wanda ke kwatanta wani shiri ne na jamhuriyar ayaba. Natanyaho mai shekaru 76 da haihuwa ya nemi afuwar shugaba Herzog a hukumance yana kokarin tsrewa daga gidan kaso idan aka yanke masa hukumci, shekaru da yawa ke nan natanyaho yake neman afuwa kamar yadda...
    A wani bangare na huldar duplomasiya tsakanin iran da saudiya , mataimakin ministan harkokin wajen kasar saudiya Saud bin mohammad Al-sati ya gana da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a nan birnin tehran inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafin alakokin dake tsakani da kuma ci gaban yankin. Ganawar wani bangare ne na kokarin da kasashen biyu ke yi na kara karfafa dangantakar dake tsakaninsu da kuma ci gaba da tattaunawa kan batutuwa masu tsauri, saudiya da iran sun kara fifita huldar diplomasiya domin shawo kan rikicin da ake ciki a yankin da kuma samar da damarmakin yin aiki tare. Ganawar tasu ta zo ne adaidai lokacin da ake cikin mawuyacin halin a yankin  da suka hada...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa.   Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen jakadu da yake sa ran majalisar kasa ta tantance ne dai batun ke ta shan suka daga manazarta kan sunayen da ya fitar. Ko wadanne irin halaye ya kamata jakada ya mallaka a yayin da za a tura shi a matsayin wakili a wata kasa? NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini DAGA LARABA:...
    A daidai lokacin ziyarar Paparoma Leo na XIV  shugaban Katolika na duniya a kasar Lebanon, kungiyar Hezbollah ta fitar da wata sanarwa a hukumance da aka aike masa. Kungiyar ta yi maraba da ziyarar Paparoma, ta kuma jaddada muhimmancin Lebanon a matsayin kasa mai bambance-bambance na addini da kabilu da akidu, wadda al’ummominta suke bukatar rayuwa tare juna a cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna a zamantakewa da siyasa. A cikin wannan sakon, Hezbollah ta gabatar da Lebanon a matsayin gada wadda ta hada tsohon tarihi tsakanin Musulunci da Kiristanci da kuma tsakanin al’adu da akidu daban-daban. Wasikar ta ambaci kalaman Paparoma John Paul II, wanda ya dauki Lebanon ba wai kawai a matsayin gida ba, a’a a ya dauki...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ya zuwa yanzu ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga maniyyatan jihar na shekarar 2026, biyo bayan rage kudin kujerar aikin Hajji da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar. Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an mayar da kudaden ga maniyyatan da suka riga suka biya kudin kujerunsu ga hukumar kafin a rage farashin. Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta sake fasalin kudin Hajj na Yankin Arewa wanda yanzu ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600 yana mai jaddada cewa mayar da kudin umarni ne...
    Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasarar ceto ’yan mata 12 da ’yan ta’addan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno. An sace su ne ranar 23 ga watan Nuwamba 2025, yayin da suke girbe amfanin gonakin iyayensu. Yaran ’yan shekaru 15 zuwa 20 ne. Wannan ya haifar da firgici a yankin, lamarin da ya sa mazauna yankin da dama suka tsere zuwa wasu garuruwa. Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa an ceto su lafiya, duk da cewa ba a bayyana yadda aka ceto su ba. Har yanzu ba a san ko an biya kuɗin fansa. Waɗanda aka ceto sun haɗa da Fatima Shaibu (17), Fatima Umaru (15), Hauwa Abubakar (18),...
    A birnin Dublin na kasar Ireland an cire sunan tsohon sugaban “Isra’ila” Chaim Herzog,daga wata lambu na shakatawa a unguwar Ratgar, tare da maye gurbinsa da sunan Shahida Hind Rajab. Jaridar “Vadiot-Ahranot” ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa, hukumar birnin Dublin a Ireland ta amince da a sauya sunan shugaban “Isra’ila” ta shida Chaim Herzog daga Lambun shakatawa,saboda matsin lambar kungiyoyin da suke goyon bayan Falasdinawa. Jaridar ta ce sauya sunan wannan lambun yana da alaka ne da yakin Gaza, kuma an amince da shawarar da aka bijiro da ita a hukumar birnin ta hanyar kada kuri’u mafi rinjaye. Wasu kungiyoyin da suke nuna goyon bayansu ga “Isra’ila” sun nuna rashin jin dadinsu da wannan matakin na sauya sunan...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.  Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki. Ofishin gwamnatin a yankin Gaza ya yi tir da hare-haren na Haramtacciyar Kasar Isra’ila, tare da yin kira ga kasashen duniya da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya masu keta dokokin kasa da kasa. Kididdiga ta bayyana cewa daga tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba 2025, adadin Falasdinawa da su ka yi shahada sun kai 356,yayin da wadanda su ka jikkata sun...
    Jaridar Washington Post ta buga rahoto akan Shirin Donald Trump na aikewa da sojoji zuwa Gaza, tare da cewa tana fuskantar matsala, domin har yanzu ana Magana akan yadda za a raba ‘yan gwgawarmaya da makamansu. Jaridar ta ci gaba da cewa; Da akwai damuwa a cikin manyan biranen kasashen duniya danagne da yiyuwar a bukaci sojojin da za a aika su yi amfani da karfi akan Falasdinawa. A ranar 17 ga  watan Nuwamba ne dai kwamitin tsaro na MDD ya fitar da kuduri na amincewa da Shirin da Trump yake da shi akan abinda ya kira zaman lafiya a Gaza. Kasar Indonesia ta yi alkawalin aikewa da sojojin da za su kai 20,000 domin aikin tabbatar da zaman lafiya....
    Hukumar Agaji ta MDD ta sanar da cewa, kasar Somaliya ta shiga cikin wani mawuyacin yanaki saboda fari, da yanki mai yawa na kasar ya bushe bayan da aka dauki shekaru hudu a jere babu ruwan sama. Hukumar ta MDD ta kuma ce, da akwai miliyoyin mutanen kasar da suke fuskantar yunwa mai tsanani, yayin da wasu kuma suke ficewa daga garuruwan nasu. A can kasar ta Somalia, gwamnati ta shelanta shiga ” halin- ko- ta- kwana’ saboda farin, tare da yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kai dauki na gaggawa,musamman a yankunan Arewa da Kudancin kasa da kuma tsakiya.” Yankin Portland ne ya fi cutuwa daga fari, inda gwamantin Somaliya ta yi kiyasin cewa da akwai...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya gana da takwaransa na Turkiya Hakan Fidan da safiyar Lahadi a nan birnin Tehran. Ministan harkokin wajen na Turkiya ya kawo ziyarar Iran ne domin tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma tattauna halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta bayyana halin da Falasdinawa ke ciki da rauni mufi da aka wa dan adam a doron kasa November 30, 2025 An yi...
    ’Yan bindiga sun shiga garin Chaco da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sakkwato, inda suka sace amarya da ƙawayenta guda 14. Yayin da mutane ke tsaka shagalin bikin auren, sai ’yan bindigar suka afka musu tare da tarwatsa komai. Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano Sun shigo garin a ƙafa, inda suka wuce kai-tsaye zuwa gidansu amaryar ba tare da sun taɓa kowa ba. Wani daga cikin iyayen ƙawayen amaryar ya shaida wa Aminiya cewa ba a tantance adadin waɗanda aka sace ba, amma wasu na cewa 15 ne, wasu kuma na cewa 13, amma amaryar da ’yarsa na cikin waɗanda aka...
    Aƙalla mutum shida ne suka jikkata bayan da wani rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Kangire da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa. Ishak Ibrahim Fanini, mai taimaka wa shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Muhammad Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali A cewarsa, an zargi makiyaya da shigar da dabbobinsu cikin gonakinsu wasu manoma. Wannan ya haddasa faɗa tsakanin manoma da makiyayan. Ya ƙara da cewa shugaban Ƙaramar Hukumar ya gudanar da taron sulhu tsakanin ɓangarorin biyu, inda ya gargaɗi su kan...
    Dakarun Sojin Najeriya, sun ceto wasu mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace a Ƙaramar Hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano. Wannan zuwa ne bayan mazauna Yankamaye Cikin Gari suka sanar da jami’an tsaro cewa ’yan bindiga sun shiga ƙauyensu a daren ranar Juma’a. ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika Wannan na cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Lahadi. Ya ce sojin ƙasa tare da haɗin guiwar sojin sama da ’yan sanda sun garzaya wajen, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, sannan suka ceto mutanen da abin ya shafa. Sai dai...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana halin da Falasdinu ke ciki da rauni mafi muni da aka aikata kan bil adama a doron kasa. A yayin bikin Ranar Falasdinu ta Duniya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sake nanata goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bai wa Falasdinawa, tana mai bayyana halin da suke ciki a matsayin “mafi munin rauni ga lamirin dan adam, Kamar yadda mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya bayyana. Kisan kare dangi, wanda ya fara a watan Oktoba na 2023, ya kashe Falasdinawa sama da 70,000, galibi mata da yara, kuma ya mayar da yankin kufai. Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon watan Oktoba tare da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa...
    An yi gangami a fadin duniya domin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu a daidai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Falasdinu a ranar 29 ga watan Nuwamba da MDD ta kebe. A faransa a gudanar da irin wannan gangamin, inda suka yi Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza da Yammacin Kogin Jordan, tare da bayyana goyon bayansu ga adawar Falasdinu. Baya ga Faransa, Birtaniya, Jordan, Kuwait, Slovenia, Sweden, da Morocco an shirya zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da mamayar Isra’ila, ayyukan matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, korarsu, da kuma kisan kiyashin Falasdinawa a Gaza da kuma cin zarafin fararen hula. Daga cikin taken da aka yi da...
    Cinikin kasashen waje na kasar Iran a cikin watanni takwas na farko na bana ya kai tan 131,540, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 76.5. kwatankwacin tagomashi na kashi 1.53% idan aka kwatanta da bara warhaka. Bayanin da aka samu daga hukumar kwastam ta Iran ya ce: “A wannan lokacin, an fitar da tan 105,231,000 na kayayyaki daban-daban, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 37, zuwa kasashe daban-daban. Wannan adadi yana wakiltar karuwar kashi 1.17% idan aka kwatanta da wannan lokacin a shekarar da ta gabata. A daya bangaren kuma ” Iran ta kara fitar da kayayyaki zuwa ga Kungiyar Tattalin Arziki ta Eurasia (EAEU), kimanin shekaru biyu bayan yarjejeniyar cinikayyar ‘yanci da aka sanya wa hannu tsakanin Tehran da...
    Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kubutar da wasu yan mata 12 da mayakan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke yankin karamar hukumar Askira/Uba da ke jihar Borno. Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar da maraicen ranar Asabar, sun ce yanzu haka yan matan na wani sansanin soji mai tsaro domin kula da lafiyarsu, kafin sada su da iyalansu. Saidai sanarwar dai ba ta yi cikakken bayanin yadda aka ceto daliban ba. An dai sace yan matan ne ranar 23 ga watan Nuwamba, lokacin da suke tsaka da aiki a wata gona a jihar Borno, inda mayakan ISWAP ke gudanar da harkokinsu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
    A Jamhuriyar Kamaru, an sake zabar Samuel Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasar (Fecafoot) Duk da kin amincewa da Ma’aikatar Wasannin kasar ta yi. An sake zabar Eto’o ne wanda shi ne Tsohon kyaftin din kungiyar Indomitable Lions ne a wani wa’adi na tsawon shekaru hudu a kasa da shekaru hudu bayan ya hau kan karagar shugabancin Hukumar. Saidai ma’aikatar Wasanni ta kasar ta nuna matukar adawa da zaben wanda ta a matsayin wanda bai dace ba. A nata bangaren, hukumar ta Fecafoot, ta sake nanata cewa dokokin FIFA sun haramta duk wani tsoma baki na siyasa a cikin harkokin wassani. Zaben ya gudana ne a gaban wakilan FIFA da CAF, wadanda suka kasance a wurin don...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar. Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni huɗu, domin bai wa gwamnatin Tarayya damar aiwatar da muhimman buƙatun da suka gabatar. Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a Faransa Ya ce an cimma matsayar ne bayan saka hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ta ƙunshi ci gaban da aka samu kan manyan buƙatu 19 na ƙungiyar,...
    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ADC ne saboda ita kaɗai yake gani za ta iya ceto Najeriya daga matsalolin tsaro da na tattalin arziki da take fama da su. Yayin ƙaddamar da ofishin jam’iyyar a Jihar Taraba ranar Asabar, Atiku duk da a baya ya kasance a jam’iyyar APC da PDP, yanzu ya fahimci cewa ba za su kawo wa ƙasar nan mafita ta matsalolin da ake fuskanta. A makon da ya gabata ne Atiku ya karɓi katin zama mamba na ADC, abin da ya tabbatar da shigarsa jam’iyyar a hukumance. Ya yi kira ga jama’ar Taraba, musamman mata da matasa, su shiga ADC domin, a cewarsa, jam’iyyar za ta taimaka wajen inganta...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar najeriya Bola Ahmad tunubu ya mika sunayen mutane 32 ciki har da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mahamud yakubu da tsohon ministan sufurin jiragen sama femi kayode ga majalisar dokokin kasar domin a tantancesu kwanaki bayan tura sunayen mutane 3 a fara da su. Mai magana da yawun shugaban kasar bayo Onanuga shi ne ya fitar da sanarwa, a cikin wasu wasiku ma banbanta da shugaban kasar ya turawa shugaban majalisa Godswill Akpabiyo ya bukaci majalisar ta amince da sunaye 15 a matsayin jakadun aiki da kuma wasu 17 da bana aiki ba, Akwai mata guda 4 daga cikin sunayen a matsayin jakadu na aiki da kuma wasu guda 6 a matsayin jakadu...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar hizbullah ta kasar Labanon ta yi kira ga shugaban cocin katolika na duniya pope leo na 14 da zai kai ziyara kasar labanon da yayi tir da hare hare da rashin adalcin da isra’ila ke yi kan kasar labanon duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a shekarar bara. Wannan sanarwar ta zo ne adaidai lokacin da shugaban cocin katoli na duniaya Pope Leo na 14 zai kai ziyara kasar labanon a wannan makon inda ake sa ran zai gana da kungiyoyin farar hula da kungiyoyin addini, inda zai ziyarci masallatai da majami’u, da yin adduoi a gabar tekun Beirut domin tunawa ga wadanda hari 2020 ya shafa, kana kuma yayi ganawa...
    Rahotanni sun bayyana cewa iran ta yi tir da sanarwar da shugaban Amurka ta fitar na rufe sararin samaniyar kasar venuzuwela kuma ta bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da kasa, da kuma dokokin kula da zirga –zirgar jiragen sama. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’ila Baghae ne ya fitar da wannan sanarwa inda ya jaddada cewa abin da Washington ta kira a matsayin sanarwa wani bangare ne na adawa na dogon lokaci da kokarin karbe ikon kasar venuzuwela, kuma ya bayyana matakin a matsayin na son rai da ya sabama doka. Wannan sanarwar ta trump ta ja hankali sosai a bangaren diplomasiya da kuma masana harkokin zirga zirgar jiragen sama, inda wasu kwararru ke ganin babu wata...
    A ranar nuna goyon baya ga alummar falasdinu shugaban kasar Pakistan Asif Ali zardari ya jinjinawa Alummar falasdinu game da juriya da tsayin Dakar da suka nuna, yace jarumtar da suka nuna ta bude sabon shafin tarihi, don haka gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka yana da muhimmanci sosai. Kasar Pakistan tana da tarihin nuna goyon bayan alummar falasdinu , inda suka nuna goyon bayan alummar falasdinu na hakkin fayyacewa kansu makoma, a kudurin Lahore na shekara ta 1940,don haka wannan kiran na zardari ya kara jaddada tsohon matsayin Pakistan da ya doru kan nuna goyon baya, kwatar yanci da daidaito da kuma adalci. Kiran da zardari yayi na gudanar da bincike kan laifukan yakin Israila...
    Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita wajen kare hakkin falasdinawa da kuma matsa kaimi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa, adaidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da labanon da kuma kasar siriya, Wannan bayanin yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman dar-dar da cin zarafin dan adam ke kara Kamari a yankin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jodan, inda hankalin duniya ya tashi...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake aike wa Majalisar Dattawa ƙarin sunayen mutum 32 domin tantance su a matsayin jakadu. Sunayen sun haɗa da manyan mutane kamar tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Femi Fani-Kayode, da Reno Omokri. Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe An raba sunayen zuwa kashi biyu; na farko yana ɗauke da sunan mutum 15 waɗanda suke da gogewar aikin jakadanci da kuma waɗanda ba su gogewar aikin jakadanci mutim 17. Wasu daga cikin fitattu da suka shiga jerin sun haɗa da tsofaffin gwamnonin kamar Ifeanyi Ugwuanyi da Victor Okezie Ikpeazu, matan tsofaffin gwamnoni kamar Angela Adebayo da Florence Ajimobi, da...
    Babban kwamandan sojojin kasa na JMI Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su maida martani ko kuma kai hari kan makiya a duk lokacinda suka takali kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hatami  yana fadar haka a bikin kaddamar da jiragen ruwan yaki masu suna Shand da kuma Kurdestan a yau Asabar. Janar Hatami ya bayyana cewa tsarin tsaro a JMI shi ne kare kai da kuma hana kai hare-hare. Hatamiya ce ‘wannan yana nufin ba zamu jira sai an kawo mana hari ba, idan ya tabbata a garemu makiya suna kokarin kawo mana farmaki muna hana su hakan tun basu kawo na. Dangane da yakin shekaru 8 masu tsarki...
    Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kakkabo jiragen yakin HKI fiye da 196 a cikin yakin kwanaki 12 da aka dora mata a cikin watan Yunin da ya gabata. Daga ciki har da jiragen yaki samfurin Heron da Hermes -900 wadanda ke aiki da kayakin zamani. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wata tashar talabijin ta cikin gida tana fadar haka a yau Asabar ta kuma kara da cewa Sashen garkuwar sararin samaniya na sojojin sama sun nuna hutunan lokacin da suke kakkabo jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na HKI a lokacinda suka shigo sararin samaniyar kasar kafin su kai ga bararsu. Burgediya Janar Reza Khajeh mataimakin kwamandan garkuwar sararin samaniya na sojojin...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan rufe zirga zirgan jiragen sama kwata-kwata a kan sararin samaniyar kasar Venezuel daga yau, a cikin shirinsa na fara mamayar kasar. Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Trump yana fadar haka a shafinsa na sadarwa True Social. Ya kuma bayyana cewa wannan sako ne ga dukkan kamfanonin jiragen sama da matuka jiragen sama. Trump ya aika da wannan sakon ne bayanda kasashen Espaniya da Potigal suka bukaci dukkan kamfanonin jiragen sama na kasar da su daina wucewa ta sararin samaniyar kasar Venezuela. Shugaban ya kara da cewa, sojojinsa a shirye suke su shiga farautar masu safarar miyagun kwayoyi a kasar ta Venezuela, a aikin sojojin kasa a cikin yan...
    Kamfanin kera jiragen sama na ‘Airbus’ ya bukaci duk wadanda suka sayi jiragen sama samfurin A320 ya dawo da shi saboda aiwatar da wata gyra a tsarin tuka jiragen. Kamfanin dillancin Labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto kamfanin yana bada wannan sanarwan a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Wannan shine karon farko wanda kamfanin yake fuskantar matsala irin wannan, wanda ya sanya ta bukaci a dawo da jirage masu yawa don gyara. Kamfanin Aie Bus shi ne kamfanin jirage mafi girma a nahiyar Turai kuma a karon farko cikin shekara 55 da suka gabata da fara kera jiragen a wannan karo ne ta fara samun irin wannan matsalar. Gyaran inji sanarwan kamfanin ya shafi wata manhajan tuki...
    An kammala gasar gina manhajan komfuta ta kasa da kasa farko a jami’ar Amir Kabir take nan Tehran . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an gudanar da gasar ne  tsakanin kasashe 30 daga yankuna daban daban na duniya, kuma an kammala gasar a jiya Jumma’a 28 ga watan Nuwamban da muke ciki. Gasar Rayan dai ita ce gasa na manhajan AI ko kirkirarren fasaha mafi girma a duniya. Gasa wanda yake samar da mahaja ya kula da ita tare da amfani da fasahar AI. Gasar sharar fage ta Rayan wanda aka gudanar a dukkan jihohon Iran ya sami halattar mutane 30,000 daga kasashe 137 a duniya. Amma a gasa ta karshe da aka kammala mutane...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya na buƙatar taimakon ƙasashen waje don dakatar da kashe-kashe da rashin tsaro, domin gwamnati ta gaza kare al’umma. Ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana Jihar Filato, inda ya ce a ci gaba ya kawo fasahar da za a iya gano masu aikata laifi, amma ta gaza yin hakan. Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano Obasanjo, ya yi gargaɗin cewa ana kashe ’yan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko ƙabilanci ba, don haka gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki. Ya ce idan gwamnati ta kasa kare jama’a, ’yan ƙasa na da damar...
    Cibiyar HANs Centre for Social Justice and Development tare da Kanady Academy, sun kammala horon kwana uku domin koya wa yara marasa galihu da matasa mata sana’o’in dogaro da kai a Jihar Gombe. Shugabar HANs, Barista Hannatu Dauda Simon, ta ce an shirya horon ne domin ƙarfafa gwiwar mahalarta, tare da koya musu yadda za su iya rayuwa ba tare da dogaro da wasu ba. Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali Ta ce halin tattalin arziƙin ƙasar nan ya ƙara nuna muhimmancin sana’ar hannu ga matasa. Ta bayyana cewa matasa mata 100, ciki har da ɗaliban Kanady Academy ne, suka halarci horon. Masu horarwa daga...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya buƙaci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya daina siyasantar da harkar tsaro a jihar. Ya ce kamata ya yi gwamnan ya mayar da hankali kan matsalolin da ke damun jihar. Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali Barau, ya yi wannan bayani ne bayan gwamnatin Kano ta zarge shi da yin magana inda ya nemi gwamnatin ta mayar da hankali kan tsaro. Ya ce matsalolin tsaro a ƙasar nan, ciki har da hare-haren ’yan bindiga a wasu yankunan Kano, suna buƙatar haɗin kai daga kowa. A cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa, Ismail Mudashiru, ya...
    Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya jaddada ‘yancin da kasashen Yammacin Asiya ke da shi na kare ‘yancinsu da kuma ‘yancin yankinsu daga harin Isra’ila. Ya kuma soki rashin daukar matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan take ‘yancin kai na kasashen yankin, musamman Siriya da Lebanon. A nata bangaren, Qatar ta yi gargadin cewa wannan “yana kara ta’azzara tashin hankali kuma yana kawo cikas ga...
    Ofishin Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike bayan kisan gillar da sojojin Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a ranar Alhamis a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, bayan sun daga hannayensu suka mika wuya. “Mun firgita da kisan gillar da ‘yan sandan kan iyaka na Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a Jenin, a Yammacin Kogin Jordan ” in ji mai magana da yawun Babban Kwamishinan Jeremy Laurence ga manema labarai. “Babban Kwamishinan (Volker Türk) ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaggawa, kuma ya bukaci a hukunta wadanda suka aikata wadannan laifukan,” Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil). A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ne ta shigar da ƙarar gaban membobi 15 na kwamitiin Tsaron. Labanon ta yi kira ga kwamitin Tsaro da Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya da su ɗauki matakan gaggawa don hana Isra’ila keta hurumin Lebanon. A cewar ƙarar, keta hurumin ya kunshi gina katanga biyu da Isra’ila ta yi a kudu maso yamma da kudu...
    Kungiyar Tarayyar Afirka, AU ta sanar da dakatar da kasar Guinea-Bissau daga zama mamba a kungiyar bayan hambarar da shugaban kasar, Umaro Sissico-Embalo da sojoji suka yi. Shugaban Kungiyar Mahamoud Youssouf ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na AFP. Matakin na AU na zuwa ne sa’o’i bayan kungiyar ECOWAS, ta dakatar da kasar saboda juyin mulkin. Ecowas ta ɗauki matakin dakatar da ƙasar ne a wani taro da ta gudanar a ranar Alhamis. Sojoji sun yi juyin mulki a kasar ne yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasar. Tunda farko dama Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea...
    An yi jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi ranar Juma’a. Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne ya jagoranci yi waa malamin sallar jana’iza, kuma an binne shi ne kusa da wasu daga cikin iyalansa da suka rasu a baya. Sheikh Dahiru wanda jagora ne na darikar Tijjaniyya ya rasu yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya, a kalandar Musulunci kuma yana da shekara 100 da yan watanni. Shehin malamin ya rasu ne a asibitin sojojin sama da ke jihar Bauchi ranar Alhamis bayan gajeriyar jinya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ya jaddada cewa ayyukan Isra’ila, ciki har da kisan kai da ayyukan ta’addanci, ba komai ba ne illa wauta, domin “muna da dubban ƙwararrun nukiliya a Iran.” Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce a ranar Juma’a a wata hira da HUM News a Islamabad cewa ra’ayin da Amurka da gwamnatin Isra’ila ke da shi game da lalata ƙarfin nukiliyar Iran abin dariya ne kuma wauta ne, domin masana’antar nukiliya kimiyya ce ta asali da Tehran ke bi da gaske. A cewar Pars Today, yana ambaton Fars News, Larijani ya ƙara da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa an dakatar da ayyukan nukiliyar Iran kuma...
    Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon abokin takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaben 2023 tare da Peter Obi. DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed ne a daren Juma’a bisa zargin ci gaba da bayyana ra’ayoyi da take ganin na iya tayar da hankali a Najeriya. Wata majiyar tsaro ta ce DSS ta daɗe tana bibiyar kalaman Baba-Ahmed a kafafen yada labarai, musamman kan iƙirarin da ya yi na cewa akwai “rikicin kundin tsarin mulki” a Najeriya. A cewar majiyar, “Kwanan nan Datti Baba-Ahmed ya bayyana a talabijin inda ya zargi kotuna da rundunar sojoji da rashin hana rantsar da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima. Har ma ya yi nuni da cewa...
    Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sake bayar da wani dauki a Kasuwar hada-hadar musayar kudade, da nufin samar da sauki wajen samun kudade a cikin kasar. Hakan ya sanya Bankin, ya sayar da dala miliyan hamsin, ga dilolin da aka yarjewa yin hada-hadar musayar kudade a cikin kasar. Kazalika, Bankin ya yi hakan ne, domin samar da daidaito, wajen yin hada-hadar musayar kudaden Naira dai, ta fara fuskantar tarnaki ne, biyo bayan samun raguwarta a kasuwar hada-hadar musayar kudade, inda kuma bukatar dalar, ya kara karuwa. Tun bayan da Naira ta samu farfadowa, Bankin na CBN, ya samu sauki kan hada-hadar musayar kudaden da aka yi. Sai dai, Bankin na CBN ya tura dala miliyan hamsin musamman domin dillalen da...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana. A cikin bayani da ya fitar a jiya jumaa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghai ya jadda game da hakkin kasashe a yammacin asiya na kare martabar su da yankunansu game da wuce gona da irin Isra’ila. Har ila yau yayi suka game da kasa tabuka komai da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan hare haren da isra’ila ke kai wa kan wasu kasashe kamar labanon da siriya wanda...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayyana ziyara da babban sakatare tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya kai kasar a matsayin babban ginshiki a alakar dake tsakanin Tehran da kuma Islam Abad , domin ya kara karfafa danganatar dake tsakanin a bangarorin siyasa, tattalin arziki, da kuma tsaro dake tsakanin kasashen makwabtan juna. Kasashen iran da Pakistan masu makwabtaka da juna za su iya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da yankin gaba ta hanyar yin aiki tare da karfafa dangantaka, musamman a yanayin da ake ciki, domin kasashen biyu baya ga aladu da addini da suka yi tarayyar, a bangaren tarihi ma sun yi nisa. Babban sakataren tsaron kasar iran Dr Ali larijani ya kai ziyara ne kasar Pakistan...
    Shaikh Naim Qasim babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar labanon ya bayyana cewa kisan babban kwamanda Haitham Ali tabataba’I da isra’ila ta yi bai zai sa ta cimma manufofinta ba, don haka hizbulla za ta mayar da martani a lokacin da ya dace, Wadanan kalaman suna zuwa ne a lokacin da ake zaman dar-dar tun bayan kisan gillan da isra’ila ta yi wa babban kwamandan hizbulla , kuma wani mataki ne kamar yadda shaikh naim Qasem ya bayyana ta yi kisan ne don karya bangaren soji na kungiyar sai dai hakarta ba za ta cimma ruwa ba, Babban sakataren ya bayyana jin dadinsa game da sakonnin ta’azziya da aka aiko daga bangarorin shuwagabannin jam’iyun siyasa a ciki da...
    Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun sanarwa da hukumar kwallon kafa ta duniya fifa cewa wannan matakin ba shi da wata alaka da wasanni , kuma wakilan kasar iran din ba za su halarci gasar kofin duniya ba . Wannan yazo ne bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa Amurka ta hana wasu daga cikin jami’anta visa shiga Amurka ciki har da shugaban hukumar Mahdi Taj, Ana...
    Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar ƙwaƙwalwa a Arewacin Najeriya — Farfesa Aishatu Armiya’u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u, ta tabbatar da kudirin asibitin na ci gaba da jagorantar gyaran tsarin kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, inda ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen fafutukar manufofi, kara yawan ayyuka, da karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa daban-daban a cikin shekaru uku da suka gabata. Farfesa Armiya’u ta bayyana cewa horon da ta samu a shirye-shiryen shugabancin harkokin lafiya na Africa ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta salon...
    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan wasa ke samu a lokacin gasar, tare da bai wa masu horaswa damar samun zaɓin ’yan wasa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi Haka kuma, an amincewa kowace ƙasa za ta je gasar da mutum 17 daga cikin masu horaswa da likitoci. Hukumar ta bayyana cewa...
    Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe. An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti na 32 da fara buga wasan a filin wasa na Khalifa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi A hanyarta ta kaiwa  wasan ƙarshen, Portugal ta doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Austria ta fitar da Italiya bayan lallasa ta da ci 2-0....