2025-05-30@04:37:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5122

«Dakarun kai daukin»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    ’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina. Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance har ya kai ga kisa. Amaryar, mai shekara 23 a duniya, ta yi wa uwargida wannan aika-aika ne ranar Lahadi a unguwar Sabon Gari, daura da Makaranta Firamare ta Daɗi. DSP Abubakar Aliyu, ya ce a ranar ce bayan mijinsu ya dawo daga kasuwa ya kai ƙara Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Daura cewa ya iske uwar gidansa kwance a cikin jini. An yanke...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kotu ta yanke wa wani magidanci mai shekara 56 hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan laifin yin fyaɗe ga agolarsa ’yar shekara 14. Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa mutumin hukuncin ne byan an gurfanar da shi kan zargin aikata laifin a watan Oktoban shekarar 2024, watanni bakwai da suka gabata. A yayin zaman kotun da ke zamanta a garin Ado-Ekiti, mai gabatar da ƙara, Julius Ajibare ya gabatar da shaidu shida da ke tabbatar da laifin da ake tuhumar mijin mahaifiyar yarinyar da yi mata fyaɗe. Kazalika ya gabatar da wasu hujjoji da kuma sakamakon gwajin asibiti da suka tabbatar da laifin da ake zargin magidancin da aikatawa. Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano ...
    Mutanen garin Rano ake Jihar Kano sun kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta Fitattun jama’ar gari sun kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Rabin hari ne a sakamakon mutuwar matashin a hannun ’yan sandan. Wasu sanarwar da kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, S.P. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga mutuwar wani wanda ake zargi da aka tsare. Ya bayyana cewa an kama matashin ne bisa laifin tuka babur ba cikin danganci kuma zargin yana yin haka ne bayan shaye-shayen ƙwayoyi. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su Wani abu ya fashe...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su. Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun dade suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a kwarya. NAJERIYA A YAU: Tasirin Dangantakar Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan Talaka DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu” Yayin da ake bikin Ranar Yara, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan halin da ya...
    Sojojin kasar Yemen sun sake kai wani hari da makali mai linzami da safiyar yau Talata wanda ya sa jiniyar gargadi ta kada a cikin yankuna da dama na HKI. Wannan dai shi ne karo na 3 a cikin sa’o’i 24 da kungiyar Ansarullah ta Yemen ya harba wa HKI makamai masu linzami. Sojojin HKI sun bayyana cewa, makamin da aka harbo daga Yemen ya sa jiniyar gargadi ta kada a cikin yankuna masu yawa a Falasdinu dake karkashin mamaya. Yemen dai tana kai wa HKI hare-hare ne saboda taimaka Falasdinawa dake yi wa kisan kiyashi fiye da shekara daya da rabi,wanda kuma har yanzu bai tsaya ba. Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Husi ce; matukar ba a kawo karshen...
    Shugaban kasar Iran wanda ya karbi bakuncin Fira ministan Pakistan da marecen jiya Litinin, ya bayyana cewa; Kasar Pakistan, makwabciyar jamhuriyar musulunci da muhimmanci, ta dubban shekaru. Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake Magana a lokacin taron manena labaru na hadin gwiwa da Fira ministan na Pakistan, ya kuma ce; Da akwai haduwar mahanga a tsakanin kasashen biyu akan batutuwa masu yawa da su ka shafi wannan yankin da kuma duniyar musulunci da kuma a fagen siyasar kasa da kasa.” Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce: “A yayin ganawar da mu ka yi da dan’uwana Fira minisan Pakistan da tawagar da taek tre da shi, mun jaddada yadda za a bunkasa alaka ta siyasa, tattalin arziki da al’adu.”...
    Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wa gabashin zirin Gaza da kuma Khan-Yunus hare-hare, bayan sa’oi daga kisan kiyashin da su ka yi wanda ya ci rayukan mutane 80. Saandiyyar sabon harin na safiyar yau, wani karamin yaro ya yi shahada, a yankin al-karama dake Arewacin Gaza. A daren jiya ma dai sojojin na HKI sun kai wasu hare-haren a unguwar ” Zaytun” dake gabashin Gaza. Tashar talbijin din ‘al-Aqsa” ta bayar da labarin dake cewa; Unguwar Shuja’iyya’ da wasu unguwannin a gabashin birnin Gaza sun fsukanci hare-haren ‘yan sahayoniya daga manyan bindigogi. Wasu hare-haren na ‘yan sahayoniya sun shafi Arewacin zirin Gaza da su ka yi sanadin rushewar gidaje, haka nan kuma asibitocin da...
    Kasar Najeriya ta sanar da Shirin fara aiki a wasu sabbin masana’antu domin sarrafa sanadarin Lithium Ministan ma’adanai na kasar ta Najeriya Daili Alaki ne ya sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a wannan shekarar da ake ciki ta 2025, da hakan zai samar da gagarumin sauyi a fagen kayan da kasar za ta rika fitarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin “Reuters” ya ambato ministan ma’adanai na kasar yana ci gaba da cewa; ‘yan kasar China ne za su zuba hannun jari mafi grima a cikin wannan Shirin da hakan zai samar da ayyukan yi a cikin kasar da kuma bunkasar harkokin kere-kere. Haka nan kuma Alaki ya yi ishara da cewa; Msana’antar sarrafa Lithium din da za...
    Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, tun daga rubu’i na hudu na shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da matakai a jere na kula da harkokin tattalin arziki, da kyautata yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma hasashen kwarin gwiwa da ake yi kan kasuwanni cikin kwanciyar hankali. Matakin da kamfanin nazari na Moody’s ya dauka na tabbatar da daidaiton mizanin matsayin kasar Sin, wani lamari ne mai kyau, na kyakkyawan fatan bunkasar tattalin arzikin kasar.   Ma’aikatar kudin ta kasar Sin ta bayyana cewa, a mataki na gaba, wasu tsare-tsare za su gudana tare, kuma za su ci gaba da yin tasiri, da samar da cikakken goyon baya ga bunkasar tattalin arziki...
    Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, bayan ya ziyarci wurin da kuma kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Rano, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dr. Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19), ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya don gano musabbabin faruwar lamarin da gaggawa da kuma gurfanar da wadanda suka aikata duk wani laifi a gaban kotu.   Rundunar, ta jajantawa iyalan marigayin DPO da ya rasu yayin aiki, ta kuma yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa daukar doka a hannunsu. Sannan, su kuma bar binciken ya ci gaba da tafiya ba tare da katsewa ba.   Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa al’umma aniyarta na ci gaba da wanzar...
    Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta buƙaci al’ummar da ke kewayen hanyar Mararaba zuwa Nyanya su kwantar da hankalinsu bayan jin ƙarar wani abu da ya fashe a yammacin ranar Litinin. Lamarin ya faru ne a wata tashar bas da ke kusa da barikin sojoji na Mogadishu a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya. A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Josephine Adeh, ta ce tuni ta tura jami’anta wajen domin bincike da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin. Kwastam ta kama Tiramol ta N150m, ta miƙa wa NAFDAC a Kano FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji “A ranar 26 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 2:15 na rana aka yi...
    Rundunar ‘yansanda ta fara gudanar da bincike kan fashewar wani abu a mashigar babban birnin tarayya Abuja a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya a ranar Litinin. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu rahoton kiran gaggawa a ranar 26 ga watan Mayun 2025 da misalin karfe 2:50 na rana, dangane da fashewar wani abu a kan hanyar. Sin Za Ta Harba Na’urar Binciken Samaniya Ta Tianwen-2 FCTA Ta Rufe Hedikwatar PDP Ta Ƙasa Saboda Ƙin Biyan Harajin Ƙasa “Bayan samun rahoton, nan take aka tura jami’an sashin warware bama-bamai (EOD) inda lamarin ya afku, cikin gaggawa aka killace yankin da lamarin ya shafa domin tantancewa...
    Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da shirye-shirye, domin harba na’urar binciken samaniya ta kasar Sin mai lakabin Tianwen-2, a ranar Alhamis 29 ga watan nan, na’urar da ake fatan za ta samar da bayanai game da sirrin dake tattare da tauraron dake kusa da sararin samaniyar bil adama, da karamin tauraron dake kewaya da’irar dake shiyyar, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta sanar a Litinin din nan. Ana sa ran na’urar Tianwen-2, za ta tattaro samfura daga tauraro mai lamba 2016HO3, aikin da zai zamo irinsa na farko a fannin, kana zai kewaya karamin tauraron “comet 311P”. Yanzu haka dai ana ci gaba da shirye-shirye domin tabbatar da nasarar...
    Iran ta yi kira da a karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka bisa tsarin yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar A yayin bikin karo na 62 na kafuwar kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a birnin Tehran, ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar Iran na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka, musamman ta hanyar yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA). A cikin jawabin da ya yi ga jakadun kasashen Afirka a Iran, Araghchi ya yaba da dabi’u da tarihin gwagwarmayar al’ummar Afirka, yana mai cewa Afirka, mai al’umma biliyan 1.4, na zaman kawa a huldar tattalin arziki ga Iran. Ya kara da cewa: “Iran da kasashen Afirka za...
    Firaministan Pakistan Muhammad Shehbaz Sharif ya na ziyara a birnin Tehran domin inda yake ganawa da manyan jami’an kasar kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu, shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya. A yau litinin ne Sharif ya jagoranci tawaga a Tehran bisa gayyatar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi masa. Da yake magana a wata hira da IRNA gabanin ziyarar tasa, Sharif ya yaba da diflomasiyyar zaman lafiya ta Iran a matsayin abin a yaba, yana mai jaddada goyon bayan al’ummarsa ga Jamhuriyar Musulunci. Ya ce babban makasudin ziyarar tasa a Tehran ita ce nuna godiya ga Iran bisa goyon bayan da ta bayar, musamman yadda ta amince da diflomasiyyar Iran a yankin, a lokacin da...
    Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya a ƙarƙashin jam’iyyar Labour a Zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ba dole ba ne sai ya zama shugaban ƙasar nan ba. Sai dai Peter Obi ya ce yana so ya ga ƙasar tana aiki yadda ya kamata a ƙarƙashin jagoranci nagari. Rikici ya barke a taron Atiku da kungiyoyin Arewa Kwastam ta kama Tiramol ta N150m, ta miƙa wa NAFDAC a Kano Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Obi yana bayyana haka ne lokacin bikin murnar cika shekara biyu kan mulki na Gwamnan Abia, Alex Otti. Ya ce ya kamata a samu shugabanni waɗanda mutane za su yi alfahari da su. Ya ƙara da cewa haƙƙin shugaba ne ya kare muradun waɗanda yake mulka....
    Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai hari a makarantar Fahmi al-Jarjawi da ke yankin Daraj na zirin Gaza, inda daruruwan iyalai da suka rasa matsugunansu daga garin Beit Lahia da ke arewacin kasar da Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai suka samu mafaka.   Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwakinmutum 20 daga makarantar, ciki har da yara da dama. A...
    A cewar jami’ai, za’a tsara yadda tsarin fitar da barasar zai kasance ta hanyar tabbatar da cewar an ba da horo ga masu sayar da ita da kuma basu takardar lasisin sayar da barasar. Hakazalika, za a tsaurara ka’idoji akan sayar da barasa a kasar, gwamnati ta jaddada cewa ana gabatar da sauye-sauyen ne cikin taka-tsantsan tare da kula da al’adun al’ummar kasar.   “Manufar ita ce, maraba da duniya ba tare da rasa asalin al’adu ba, sanya Saudiyya a matsayin mai ci gaba, duk da haka mai mutunta taswirar yawon shakatawa na duniya,” in ji hukumomin Saudiyya a cikin wata sanarwa.   Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Saudiyya ke neman yin gogayya da kasashe makwabta kamar...
          Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An fi sanin tsarin kusurwa uku a matsayin tsari mafi ba da fa’idar halitta, kuma tsarin dunkulewar aikin ba da ilmi da kimiyya da kwararru na Sin ya yi kama da tsarin kusurwa uku, hakan ya sa yake da ingantaccen karfin zamanintar da al’ummar Sinawa a sabon zamani. Wannan mataki ne da gwamnatin Sin ke dauka dake hada tarihi da kirkire-kirkire tare don raya kasar. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Matakin na FCTA ya kara jaddada daukar tsauraran matakai kan wadanda suka saba ka’idojin amfani da filaye a babban birnin kasar.   Jami’an sun ce, rufewar za ta ci gaba da aiki har sai an warware basussukan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a sabon zamani. William Samoei Ruto ya shedawa manema labaran CMG cewa, dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka na FOCAC ba samar da wani dandalin mu’ammalar ra’ayoyi kadai ya yi ba, ya kuma shimfida sharadi mai kyau ga bangarorin biyu wajen fidda sabbin damammakin hadin gwiwa da samun moriya tare. Ruto ya ce, FOCAC ya samar da wani ingantaccen dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Kwastam reshen Kano da Jigawa, ta kama nau’in ƙwayar Tiramol katan 491,000, tare da miƙa su ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC). An ƙiyasta kuɗin magungunan da aka kama sama da Naira miliyan 150, kuma an gano su a cikin wata mota ƙirar Lexus SUV, a hanyar Gumel zuwa Maigatari da ke Jihar Jigawa. FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato Kwanturolan hukumar a yankin, Dalhatu Abubakar, ya ce an yi wannan nasara ne bisa sahihan bayanan sirri, kuma yana daga cikin ƙoƙarin da suke yi tun bayan shigarsa ofis a watan Fabrairun 2025. Abubakar, ya ce an shigo da ƙwayoyin ne...
    Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA), ta rufe hedikwatar jam’iyyar PDP da ke unguwar Wuse a Abuja. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:05 na ranar Litinin. Wike ya rufe ofishin FIRS da Bankin Access kan rashin biyan haraji Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato Jami’an FCTA sun isa ginin tare da jami’an tsaro, inda suka rufe ofishin. Wasu ma’aikata sun nuna rashin jin daɗinsu, bayan tafka sa-in-sa na tsawo mintuna 15, jami’an FCTA sun bar ma’aikata su fitar da motoci da kayayyakinsu kafin kulle ginin. A makon da ya gabata, FCTA ta sanar da cewa za ta ƙwace sama da kadarori 4,700 a Abuja saboda rashin biyan haraji na tsawon shekaru 10 zuwa 43....
    Wani haɗarin mota da ya faru a yau Lahadi a hanyar Lokoja-Obajana ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, yayin da wasu 8 suka jikkata. Sakataren FRSC na jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da cewa haɗarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce ƙima. Mota bas da wata babbar mota sun yi karo da juna a Gada biyu, inda yara 5 suka ƙone har lahira. Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC  Kashi 25 Kawai Na Motocin Da Ke Nijeriya Suke Da Inshora – FRSC “Mutane 27 ne haɗarin haɗarin ya rutsa da su, 8 kacal suka tsira,” in ji Tsukwam. An kai wadanda suka tsira asibitin Fisayo a Obajana don samun kulawa. FRSC ta yi...
    Hukumar Kula da Babban Birnin (FCTA) Tarayya ta rufe ofishin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kuma ginin Bankin Access kan rashin biyan haraji na sama da shekaru 25. Daraktan Kula da Filaye na Hukumar FCTA, Chijioke Nwankwoeze, ya bayyana cewa hukumar bin ginin da bankin Access yake bashin harajin shekara 35, ofishin FIRS da ke unguwar Wuse Zone 5 kuma bashin harajin shekara 25. Babban Ofishin na FIRS na daga cikin fitattun gine-gine da Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji na Babban Birnin ta rufe a safiyar Litinin, kan zargin rashin biyan haraji. Sauran sun  shafa da ginin Bankin Access da da ofishin kamfanin mai Total Energy da fitaccen otel din Ibro Hotel a unguwar Wuse, da sauran wurare 4,700...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana. Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara suna gudu a cikin wuta suna kokaron kubutar da kansu. Labarin ya kara da cewa makarantar tana unguwar Daraj na birnin Gaza, mai suna Fahmi al-Jarjawi. Majiyar kungiyar kula da fararen hula a gazar ta bayyana cewa yahudawan kai hare haren a safiyar yau litinin a lokacinda suke barci. Labarin ya kara da cewa a cikin wadanda yahudawan suka kashe a Gaza, akwai Mohammad Al-kasih...
    Shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar Burtaniya ya bayyana cewa HKI tana yakar Falasdinawa a Gaza ne a madadin gwamnatin kasar tunda har yanzun gwamnatin kasar Burtaniya tana ganin gwamnatin HKI tana kare kanta daga mayakan Hamas, kuma bata daukar abinda HKI take yi a Gaza, kissan kiyashi ne. Badenoch shugaban jam’iyyar ‘ Conservative’ ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Sky News dake birnin London a jiya Lahadi. A lokacinda aka tambaye shi idan ya yarda da maganar Banyamin natanyaho kan cewa hamas yan ta’adda ce, kuma yana kokarin kwace gaza da shafi yan ta’adda ne, sai shugaban Conservative ya ce banzo nan don binciken kalmomin Natanyahu ba. Abinda nake son bada sanarwansa shi...
    Kasar Uganda ta dakatar da aikin hadin giuwa na soje dake tsakanin kasashen biyu, saboda sukan da jakadan kasar Jamus yayiwa dan shugaban kasar yake kuma goyon bayan wata jam’iyyar adawar kasar. Shafin yanar gizo na labarai Afirka News ya nakalto jami’iyyar shugaban kasar Uganda People’s Defence Forces (UPDF) tana bada rahoton cewa Jakada Schauer na kasar Jamus a Kamfani ya halarci wata taro tare da wata jam’iyyar adawa inda yake sukar dan shugaba Uwere Musevene jan yadda jam’iyyarsu take gudanar da harkokin shugabancin kasar. Kasashen Uganda da Jamus sun dade basu sami irin wannan rashin jituwa ba. Kuma harkokon kasuwanci tsakanin kasashen biyu yakai dalar Amurka miliyon $335 a shekara 2023 kadai. Sai dai muna iya cewa wannan ba...
    Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Bayan matsayinta a kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan yana maida martani ne ga tokwaransa na kasar Faransa Jean-Noel Barrot ya fada bayan da wani ba’irane ya sami lambar yabo mafi girma a gasar fina-fina mafi girma a duniya da ake kira ‘ Cannes Film Festival’ . Jafar Panohi dan kasar Iran ya lashe kyauta mafi girma a gasar ne saboda wani film da ya yi, wanda ya bashi makin samun wannan kyautar. Aragchi ya bayyana cewa, Faransa...
    05-Majiyar Sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar a safiyar yau ma sun cilla makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) na HKI. Inda faduwar makaman ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama a tashar.  Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Yahyah Sari yana fadar haka a yau, ya kuma tabbatar da cewa, makamin samfurin Bilistic ya sami bararsa kamar yadda aka tsara. Ya ce faduwar makamin ya dakatar da dukkan ayyukan sauka da tashin jiragen sama a wannan tashar banda haka cilla makamai ya sa miliyoyin yahudawa rugawa zuwa wararen buya. Tun watan maris da ya gabata ne sojojin yahudawan sahyoniyya suka sake farfado da yaki...
    Daliget sun tayar da jijiyoyin a wurin taron haɗakar siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi domin fafatawa da shuagaban kasa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. Ana tsaka da taron Kungiyar Tuntubar Siyasa ta Kasa Reshen Arewa a Abuja ne hayaniya ta kaure bayan tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya sanar da wanda suna daliget da zai wakilci Jihar Jigawa. Rashin gamsuwar sauran daliget din jihar dadi ba suka tayar da jijiyoyin wuya, inda suka hau kan mumbari suka dauke wanada aka ayyanan suka hana shi magana da yawunsu. Daba bisani an yi nasarar shawo kan rikicin, inda aka zabi dan...
    Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da furucin ministan harkokin wajen kasarsa da ya shafi batunci ga Iran. Muhammad Tanhaye wanda shi ne mai kula da bangaren kasashen turai a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran,  ya bukaci Karin bayani a hukumance dangane da abinda ministan harkokin wajen Faransa Jean Nuel Barrot ya fada akan Iran a yayin bikin ” Cannes” na fina-finai a da wani daga cikin fina-finan Iran ya sami kyauta. Har ila yau, Tanhaye ya yi suka akan yadda gwamnatin ta Faransa ta yi amfani da bikin fina-finan domin yada manufofinta na siyasa. Haka nan kuma ya ce; Faransa wacce kasa ce...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya danage da zagayowar cikar shekaru 25 daga korar ‘yan sahayoniya daga kasar Lebanon da gwgawarmaya ta yi, ya jaddada cewa; “Gwagwarmaya ba za ta yi shiru ba, ba kuma za ta mika wuya ba, tana yin hakuri ne saboda ta bayar da Karin lokacin,don haka ya zama wajibi a yunkura.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Gwamnati ce mai hakkin ganin an...
    Hare-haren sojojin HKI a yankin Gaza sun yi sanadiyyar shahadar  Falasdinawa 57 Majiyar Asibiti a yankin na Gaza,ta sanar da cewa sojojin mamayar sun kai hari ne akan makarantar ” Fahmi al-jarjawi” wacce take a yankin al-Darj’ a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 25.”  Harin ya yi sanadiyyar konewar gawawwakin shahidan da kuma tashin gagarumar gobara a makarantar da  ‘yan hijira Falasdinawa suke ciki.  Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa  daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa ya haura dubu 53 da 939. Haka  nan ma’aikatar ta ce; Wadanda su ka jikkata kuwa a wannan tsakanin sun kai dubu 122 da 797. Sojojin HKI sun shelanta yaki ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma. A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci-gaban kasa. Sai dai a Najeriya, a wasu lokutan akan zargi ’yan majalisa da zama ’yan-amshin-Shata. Ko me ya sa haka? Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya? NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Baki a Nijeriya da abokansu Sinawa sun nishadantu yayin da suka halarci taron gabatar da fasahar hada shayi ta 2025 da al’adun Yaji, wanda aka yi jiya Asabar a Abuja babban birnin kasar. An gudanar da taron ne a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin da hadin gwiwar cibiyar raya al’adu ta lardin Zhejiang, wadda ta samu wakilcin masana hada shayi da ‘yan wasan kwaikwayo na Yue Opera da masu wasan kayan Pipa.   Taron ya samu halartar mutane daga dukkan bangarorin rayuwa da suka hada da jami’an diplomasiyya da na gwamnati da malamai da daliban sakandare da ‘yan wasa da manema labarai da masoya al’adun shayi ta kasar Sin. An kuma gabatar da fasahar rubutun gargajiya ta Sin da...
    Adadin “nau’i uku na manyan kamfanoni 500” da suka halarci bikin baje kolin a bana ya kai 114, wanda ya kai kashi 55.6 bisa dari. Daga cikin su, akwai kamfanoni 61 dake cikin manyan kamfanoni 500 na duniya, adadin da ya karu da kashi 74.3 bisa dari kan na baje kolin da ya gabata. (Bello Wang, Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An shiga ruɗani a unguwar CBN Quarters da ke cikin birnin Sakkwato, inda wani ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu mai suna Ayman Abubakar, ya ɓace, amma daga bisani aka gano gawarsa a cikin ramin sokawe. Ana zargin wani maƙwabcin iyayen yaron da wata mata da aikata wannan ɗanyen aiki. An kashe matashi yayin rikici a ƙauyukan Kano Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole Ƙngiyoyi da ke fafutukar kare haƙƙin yara da martabar bil adama sun bayyana wannan kisa a matsayin babban cin zarafi. A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, shugaban NACTAL na ƙasa Abdulganiyu Abubakar, Usman Ahmad daga ƙungiyar kare haƙƙin yara, da Rabi’u Bello Gandi shugaban hukumar kare...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya bayyana cewa: Suna yin aiki ne bisa maslahar kasa, kuma ba su yarda da karbar umarni daga waje ba Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, ya ce Iran tana dogara ne kan manufofinta na kasa da kuma manufofinta na koli, kuma ba zata yarda wasu kasashen waje su tsara mata ko bata umurnin abin da zata yi ba. Kalaman na Islami sun zo ne a lokacin da yake halartar wani taron juyayin tunawa da shahadar marigayi tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian a jiya Asabar, wanda ya samu halartar manyan jami’an siyasa da na diflomasiyya. A cikin jawabin nasa, Islami ya jaddada cewa asalin kasa da dabi’unta sune abubuwan...
    Mene ne dalilin da ya sa Amurka da Isra’ila suke barazanar jefa bama-baman nukiliya a Gaza? Masanin siyasa kuma mai sharhi Abdel Bari Atwan ya rubuta labarin game da barazanar da Amurka ta yi na kai wa Gaza hari da makamin nukiliya, yana mai cewa; “Domin dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican Randy Fein ya yi kira da a kai hari kan Zirin Gaza da bama-baman nukiliya, kwatankwacin abin da kasarsa ta yi a Hiroshima da Nagasaki na Japan, a karshen yakin duniya na biyu, da kuma samun wanda ya yaba masa a gwamnatin Shugaba Donald Trump, wannan shi ne kololuwar ta’addanci, rashin mutuntaka, da kishir ruwan zubar da jini a duniya daga jagororin da ke da’awar kare hakkin bil’adama...
    Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tulkaram da sansanoninsa da ke gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tulkaram da sansanoninsa a rana ta 119 a jere, da kuma sansanin Nour Shams a rana ta 106, a daidai lokacin da sojojin suke ci gaba da tsananta kai hare-hare kan yankuna Falasdinawa da kuma kma su tare da yinawungaba da su zuwa wuraren da baa san ko’ina ba ne. Da sanyin safiyar Lahadi ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki gidan Essam Odeh, sakataren kungiyar hadin kan iyalan shahidai da ke yankin kudancin Falasdinu, inda suka kama shi da diyarsa Sarah mai shekaru 20...
    ‘Yar majalisar dokokin Ireland ta yi kakkausar suka kan shugabannin Turai tare da neman afuwa daga Falasdinawa Tana jaddada cewa: Muggan makaman gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da lakume rayukan fararen hula a zirin Gaza. Sannan a wani sabon kisan kiyashi, an kashe Falasdinawa 7 a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza. A wani kisan kiyashi kuma jami’an tsaron farar hula a Gaza sun sanar da mutuwar yara tara da suka kone kurmus a wani harin da sojoji mamayar Isra’ila suka kai kan Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza da aka killace. An kuma kashe wani Bafalasdine tare da raunata wasu a wani harin da...
    Fastan nan mai suna Rev. Azzaman David, shugaban majami’ar The King Worship Chapel da ke Kaduna, ya rasu a wani hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawowarsa daga Makurdi, jihar Benue zuwa Kaduna. Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na Jihohin Arewa 19 da FCT, Rev. John Joseph Hayab, ya tabbatar da mutuwar fastan, inda ya bayyana cewa al’ummar Kirista ta yi hasarar babban jarumi. “Evangelist Azzaman ya kasance mai himmar wa’azi, mai kare addinin Kirista, kuma mai fafutukar kare hakkin masu ƙaramin ƙarfi. Rayuwarsa ta kasance cikin jarumtaka da ƙwarin gwuiwa ga gaskiya da adalci,” in ji Hayab. CAN ta yi wa iyalansa, da ‘yan cocinsa, da duk wanda rayuwarsa ta shafa ta’aziyya, tare da addu’ar Allah ya ba...
    A halin yanzu, a gonaki masu samar da shinkafar da aka tagwaita a Madagascar, ana farin cikin girbar shinkafa mai armashi. Masanan aikin gona na kasar Sin sun bi sahun Yuan Longping don tabbatar da burinsa na hadin gwiwa da manoman kasar wajen samar da isashen hatsi. (Mai zane da rubutu: MINA)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rikici ya ɓarke tsakanin wasu matasa a ƙauyukan Faruruwa da Tarandai da ke Ƙaramar Hukumar Takai a Jihar Kano, inda aka kashe wani matashin har lahira. Rikicin ya faru ne a ranar cin kasuwa kuma ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka ƙone rumfunan kasuwar. Ko gwamnoni duka za su koma APC ba zai hana mu kayar da Tinubu a 2027 ba — Babachir.Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole Wani masani kan harkar tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Lahadi. Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar 23 ga watan Mayu, 2025, a kasuwar Faruruwa. A cewarsa, rikicin ya...
    George Iniobong ɗan shekara ashirin da biyu daga tawagar Jihar Binuwai ya samu kyautar azurfa a gasar maza ta Judo mai nauyin kilo 60 a yau Lahadi, yayinda ake cigaba da gasar wasanni ta ƙasa karo na 22 (NSF) da ke gudana a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Nasarar da George ya samu ya sa tawagar ta Jihar Binuwai ta samu kyautukan tagulla da Azurfa 9 jimilla a gasar, wakilinmu ya ruwaito cewa, Iniobong, ya yi matuƙar taka rawar gani a wasan inda ya samu nasara a kan abokin karawarshi daga jihar Ogun cikin mintunan ƙarshe na karawar. An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An kaddamar da wani sabon babban filin wasa a birnin N’Djamena na kasar Chadi, wanda kasar Sin ta gina wa kasar kyauta. Yayin bikin kaddamarwar da ya gudana ranar Juma’a, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby, ya buga kwallon kafa da kansa, a matsayin alamar fara amfani da babban filin wasan. Cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Deby ya gode wa kasar Sin, gami da bayyana filin wasan a matsayin daya daga cikin sakamakon da aka cimma, bisa huldar hadin kai, da mutunta juna, da ta kasance tsakanin kasashen Chadi da Sin. Wani kamfanin kasar Sin ne ya gina babban filin wasan tare da mika shi ga kasar Chadi a ranar 12 ga wata. Girman filin wasan ya kai muraba’in...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Gombe, na shirin taimaka wa wata yarinya ’yar shekara 14 da aka tilasta yi mata auren dole a Jihar Taraba. Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwala, Asma’u Iganus, ta ce yarinyar ta nemi taimako bayan da kakanta ya ɗaura mata aure da wani mutum a matsayin mata ta huɗu. An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja Jami’an Sibil Difens sun bude wuta a garin Jos Ta ce hakan ya ci zarafin yarinyar kuma gwamnati ba za ta zuba ido ba. “Mun fara ɗaukar matakan kare ta. Mun tuntuɓi kotu kuma lauyoyin gwamnati za su shiga shari’ar don kare ta,” in ji Asma’u. Ta ce yarinyar ta ce tana son ci gaba da karatu, don haka...
    Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an yi garkuwa da Ilya ne daga kauyen Gatawa tare da mahaifinsa.   Iliya da mahaifinsa dukkansu daga karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a cikin watan Afrilu, yayin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyensu, suna ta harbe-harbe, inda daga nan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.     Ilya ya bayyanawa ‘yansanda cewa, ya tsere daga sansanin ‘yan bindigar ne bayan ya yi ta gudu a dajin har na tsawon kwanaki takwas sannan ya hadu da jami’an ‘yansanda a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Jami’an da aka kashen da suka hada da Kwamandan CWC Mallam Sanusi, rahotanni sun bayyana cewa, suna cikin wani aikin kai dauki ne yayin da wasu ‘yan bindiga kusan ashirin (20) dauke da makamai a babura suka yi musu kwanton bauna a madatsar wani rafi.   A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula ya fitar, maharan wadanda suka boye jikin bishiyar mangwaro, sun kona motar jami’an tsaro kirar Hilux a yayin harin.     Gwamna Radda ya samu rakiyar kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Dr. Nasiru Danmusa; Kwamishinan ’Yansandan Jihar, Daraktan Ma’aikata na Jihar, Shugaban Ma’aikata, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir; da sauran manyan jami’an tsaro.   Shugaban karamar hukumar, Alhaji...
    “Kuma taron zai baiwa jama’a damar yi wa gwamna tambayoyi kai tsaye, kuma su sami bayani kan ayyukan gwamnati.” “Wannan shi ne ci gaba a siyasance, kuma ba sabon abu bane a duniya, amma a jihar Yobe, wannan wani sabon salo ne. Mataki ne na sauke nauyi, gaskiyar da jama’a suka baiwa gwamnati, samun hadin kai, da sauran jama’a kai tsaye.” In ji shi. Dakta Yabani ya jaddada cewa, taron an shirya shi ne domin baiwa al’ummar jihar Yobe kwarin gwiwa, a tafarkin gudanar da ayyukan da gwamnati take aiwatarwa na ci gaba da kyauta jindadin su, tare da basu dama wajen tofa albarkacin su wajen tsara manufofi gwamnati. “Maigirma Gwamna Buni a shirye yake ya amsa duk wata tambayar...
    Jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama hakimin ƙauyen Guiwa da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja. Hakimin mai suna Garba Mohammed ana zarginsa da taimaka wa ’yan bindiga wajen aikata ta’addanci a yankin. Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a Ilori An kama shi tare da wasu mutum 13 a safiyar ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewar suna hannu wajen taikoman ’yan bindiga. Rahotanni sun bayyana cewa hakimin yana bai wa ’yan bindiga mafaka a gidansa, inda suke taruwa suna shirya kai hare-haren. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja,...
    Dubban daruruwan masu zanga-zanga a biranen Barlin Paris da kuma Stockholm ne suka bukaci gwamnatocin kasashensu su kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a gaza, su kuma tabbatar da cewa abinci ya isa gaban Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zangar sun kira ga gwamnatocin kasashensu su dakatar da bawa HKI makaman da take kishe falasdinawa da su. A birnin Berlin da kasar Jamus dubban Jamusawa sun hadu a dandalin at Oranienplatz inda suke rera taken ‘a bawa Falasdinawa yenci, HKI yar ta’adda ce, kuma gwamnatin Jamas ta dakatar da tallafin da take bawa HKI. Labaran sun kara da cewa hatta mutanen kasar Jamus yan asalin yahudawa sun fito sun bayyana...
    Ministan gina hanyoyi da ci gaban kasa na JMI Farzaneh Sadegh ta ziyarci kasar Iraki don bin duddugin aikin layin dogo da ake ginawa tsakanin kasashen biyu. Farzaneh Sadegh ta isa bienin Bagdaza a jiya Asabar inda mataimakin ministan sifiri na kasar Iraki da kuma jakadan kasar Iran a Bagdaza suka yi maraba da ita. Ministan ta ziyarci inda sojojin Amurka suka kashe kwamandojin yaki da yan  ta’adda Janar Kasim Sulaimani da kuma Mahdi Almuhandis a cikin watan Jenerun shekara ta 2020. Farzaneh Sadegh zata gana da firai ministan kasar Iraki Mohammad shiaa Assudani, da wasu jami’an gwamnatin kasar Iraki. Sannan zata ziyarci aikin shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 33 wadanda kasashen biyu suke yi don hada garin Chalamce...
    Mutanen kasar Lebanon sun gudanar da zabubbukan larduna a kudancin kasar a ranar Asabar da ta gabata duk tare da barazanar tsaron da kasar take fama da sun\ Jiragen yakin HKI sun ci gaba da yin luguden boma bomai a kudancin kasar Lebanon duk tare da yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta da suka cimma da kungiyar hizbulla a karshen shekarar da ta gabat. Kafafen yada labarai sun nakalto mutane suna zabe a garin Jwayya kilomiya 15 kacal kan iyaklar da kasar Falasdinu da aka mamayae. Sunce bas a jin tsoron HKI zata kawo hirik o ba zata kawo  ba saboda zabe wajibinsu ne .
    A jiya Asabar ce kasashen Rasha da Ukraine suka yi musayar Fursinoni a tsakanin, karon farko irinsa tun bayan fara yaki a tsakaninsu fiye da shekaru 3 da suka gabata. Shafin yanar gizo na Labarai Arabs News ya bayyana cewa an yi musayar furisnonin ne a jiya Asabar kuma ko wace kasa ta sake fursinonin yaki har 390. Labarin ya kara da cewa a dai dai lokacinda aka yi musayar fursinonin sojojin Rasha sun yi loguden wuta a kan birnin Kiyev babban birnin kasar ta Ukraine. Majiyar gwamnatin kasar Ukraine ta bada sanarwan cewa akalla mutane 10 sun ji rauni saboda luguden watan. A makon da ya gabata ne kasashen biyu suka tattauna a tsakaninsu a birnin Istambul na kasar...
    Jaridar ;The HIL’ ta kasar Amurka wacce take bada labaran majalisa da siyasar gwamnatin Amurka ta gargadi gwamnatin shugaba Donal Trump kada ta sake irin kuskuren da shugaban kasar Iran Sadam Hussain yaki na fadawa kasar Iran da yaki, tare da tsammanin cewa a cikin yan kwanaki zai ga faduwar jaririyar gwamnatin kasar Iran a lokacin. Amma sai wankin hula ya kai masa dare, inda ya share shekaru 8 yana fafatawa da mutanen kasar Iran ba kuma tare da samun nasarar ba. Jaridar ta kara da cewa Iran ba kasace wacce tana dab da faduwa ne sai aje a karasa faduwarta ba. Kasashen wacce kan mutanen kasar a hade yake a duk lokacinda na waje yayi kokarin mamayar kasar. Labarin...
    Shugaban Wanda Alhaji Ahmed Aliyu Zarma ya wakilta ya kara da cewa, wannan cibiya ba itace ta farko ba da shugaban ya fara ginawa ba, a cewarsa ya gina irinsu a sassa daban-daban a fadin kasar nan. Yana Mai Cewa, baya ga cibiyoyin koyar da addinin musulunci ya samar da makarantu a majami’un addnin kirista da gyaran makarantu da kuma tallafawa marayu da marasa galihu a cikin al’umma. Zarma ya ce, sama da shekaru goma shugaban yana gudanar da irin wadannan Ayyukan tallafawa Rayuwar al’umma musamman marayu da marasa galihu a fadin kasar nan Baki daya. Sarki Musulmi tare da Sarkin Zazzau a wurin taron A nasa jawabin, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubukar lll Ya jinjiwa shugaban na DSS na...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ce, Amurka ta bayyana cewa, MDD ta ki aiki tare da kamfanonin Amurka da na Isra’ila domin raba kayan agaji a Gaza. Majiyar ta HKI ta kuma kara da cewa; An jinkirta aiwatar da Shirin na raba kayan agajin saboda wasu dalilai na kayan aiki. Wuraren hudu ne dai aka ware domin raba kayan agajin a kudancin Gaza, an kuma kai shi zuwa mako na gaba. Wasu kafofin watsa labaru sun ambato babban magatakardar MDD yana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani shiri a Gaza wanda ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba.  A cikin wani bayani da wata kungiya mai kula da iyalai a yankin Gaza ta fitar, ta nuna...
     Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki. Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da cewa; yadda al’ummar Iran su ka yi gwagwarmayar ‘yanto da garin Khurramshahr, bayan tsawon shekaru 8 na yaki, ya sa Amurka ta fahimci cewa yaki da Iran yana da tsada da kuma hatsari; kuma da ace sun san za su yi nasara ta hanyar karfin soja da ba su zauna akan teburin tattaunawa ba. Janar Sanaei ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su...
    Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100 dake dauke da makamai a tashar jiragen ruwa ta Odessa. Sanarwar ta kuma kunshi cewa makaman da sojojin na Rasha su ka tarwatsa sun hada kananan jiragen ruwa na yaki na kai farmaki da ba su da matuki, jiragen sama marasa matuki, da kuma albarusai. Haka nan kuma harin ya shafi manyan dakunan ajiye makamai a cikin tashar jiragen ruwan na Odessa. Sanadiyyar wannan harin harshen wuta ya tashi wanda ya dauki lokaci yana ci.  A gefe daya an yi musayar fursunoni a tsakanin sojojin Rasha da kuma na Ukiraniya wanda shi ne mafi girma...
    Ministan ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi wa fararen fatar kasar kisan kiyashi a yayin ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai. A yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Amurka ya kunna wani faifen bidiyo da a ciki  aka  nuna  gicciye a gefen hanya domin tunawa da fararen fata manoma da aka yi wa ksian gilla. Ministan ‘yan sandan kasar ta Afirka ta kuku Senzo Mchunu ta cewa; Wadannan gicciyen ba su nuni da cewa suna akan kabarurruka ne, ko wani wuri na tunawa da matatu, an Sanya su ne a 2020 domin tunawa da dukkanin...
    City ta ba da sanarwa a gabanin fafatawar cewa ta shirya wani babban kyalle mai dauke da sunansa tare da sanya wa wata hanya sunan De Bruyne a makarantar horarwa ta kungiyar, Guardiola yana girmama De Bruyne sosai har ya bayyana dan kasar Belgium din a matsayin dan wasan da ya fi iya kwallo a cikin ‘yan wasan da ya taba horarwa bayan Lionel Messi. De Bruyne ya fara buga wa City wasa a watan Satumban shekarar 2015, De Bruyne ya buga wasanni 283 a matakin farko, ya ci kwallaye 72 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 119 wanda hakan ya sa ya zama na biyu a jerin wadanda suka fi kowa taimakawa wajen zura kwallo a gasar Firimiya bayan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Asabar ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sauka a birnin Jakarta domin ziyarar aiki a kasar Indonesia bisa gayyatar da shugaban kasar Indonesia Prabowo Subianto ya yi masa. Li ya bayyana cewa, kasashen Sin da Indonesia sun bayar da misali kan yadda manyan kasashe masu tasowa suke aiki tare don kara karfi da cin moriyar juna da kuma samun nasara ga kowane bangare. CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Indonesia don ci gaba da samar da wadata ga al’ummomin Sin da...
    Majiyoyin tsaro sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida kafin sanar da tsagaita bude wuta a ranar Larabar da ta gabata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan kasar Sin Li Qiang ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda ya amince da shirin aiwatar da ayyukan raya amfani da makamashi mai tsafta a bangaren masana’antu na shekarar 2025 zuwa ta 2027, tare da sake duba matakan da za a dauka na inganta tsarin biyan diyya domin kiyaye lafiyar muhalli. Taron ya jaddada bukatar hanzarta yin kirkire-kirkire na fasahohin makamashi mai tsafta da kuma fadada hanyoyin samar da mafita, yayin da ake kiran gudanar da gagarumin sauyi mai zurfi a bangaren tsoffin masana’antu. Har ila yau, ya bukaci sassa masu tasowa da su ci gaba da samar da ingantaccen ci gaba wajen amfani da makamashi mara gurbata muhalli tun daga tushe, tare da mai da hankali kan...
    Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami ya ce duk wanimataki da Tehran ta dauka ya dogara ne kan manufofi da muradun kasar. “Muna ci gaba bisa ga manufofinmu da bukatun kasa,” in ji Eslami Babban jami’in nukiliya na kasar Iran ya jaddada cewa daya daga cikin muhimman nasarorin juyin juya halin Musulunci shi ne yadda kasar ke tsara tafarkinta da kuma yanke hukunci bisa muradun kasa. Eslami ya bayyana cewa, a halin yanzu Iran tana matsayi mai kyau a fannin kimiyya da fasaha na masana’antu, daidai da kasashen da suka ci gaba da suka zuba jarin miliyoyin daloli. Kafin hakan dama Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a ranar Talata ya bayyana cewa “ba...
    Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu ta yi kakkausar suka kan kalaman baya-bayan nan da dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican Randy Fine ya yi, wanda ya yi kira da a kai wa zirin Gaza hari da makamin Nukiliya. Kungiyar Hamas, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana kalaman dan ‘majalisar a matsayin “laifuffuka” da kuma nuna wariyar launin fata na wasu sassan Amurka. Kungiyar ta bukaci hukumomin Amurka da na majalisar dokokin kasar da su fito fili su yi Allah-wadai da irin wadannan kalamai. Hamas ta jaddada cewa furucin dan majalisar Republican na nuni ne karara ta keta dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kuma yana nufin tunzura kai tsaye don amfani...
    A karon farko an fara tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da ta AES ta kawancen kasashen nan guda uku na Sahel da suka balle. Shugaban hukumar ECOWAS, dan kasar Gambia Omar Touray, ya tattauna a birnin Bamako da ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar AES wato Mali, Burkina da kuma Nijar. Wannan dai shi ne karon farko tun bayan ficewar kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar daga kungiyar ECOWAS a watan Janairun 2024. Bangarorin sun tattauna kan manyan batutuwan da suka hada da siyasa, diflomasiyya, shari’a, tsaro, da kuma ci gaban tattalin arziki da zamantakewa. An dai amince, bisa bukatar shugabannin yankin, na kiyaye nasarorin da aka cimma a hadin gwiwar yankin, da tabbatar da zirga-zirgar jama’a da kayayyaki...
    Don haka, CHINADA tana nuna matukar adawarta ga duk wani yunkuri na bayyana shan kwayoyi masu kara kuzari a matsayin wai ci gaban kimiyya, tare da yin kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a harkar wasanni na duniya da su tashi tsaye, su hada kai wajen yin fatali da wasannin da aka amince a sha kwayoyin kara kuzari. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB) ta sanar cewa mutanen da suka tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Kwara suna samun kulawa a asibiti Da yake tabbatar da cewe duka mutanen cikin jirgin horon sun tsira da ransu, Babban Daraktan NSIB, Kyaftin Alex Badeh Junior, ya ce hukumar ta gano katin nadar bayanai daga jirgin, bayan aukuwar hatsarin a filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilorin, Jirgin, nau’in Diamond, mai lamba BNI, mallakin Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama ta Ilorin (IAC) ne, kuma ya yi hatsarin ne a yayin atisayen sauka na gwaji, inda ya kauce daga titi, ya yi cikin daji ya lalace fiye da yadda za a iya...
    Jami’an gwamnati daga jihohin Gombe da Bauchi sun gudanar da wani taron kwana biyu tare da wakilan kamfanin NNPC da Kamfanin AOML, waɗanda ke gudanar da aikin hakar danyen mai a yankin Kolmani. An kira taron ne don neman ƙarin bayani kan matakan da AOML ta riga ta ɗauka da kuma gyara kura-kuran da aka gani daidai da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), da nufin kauce wasau matsalolin da suka addabi sauran yankuna masu arzikin mai. Wata sanarwa da Kwamishinan Ma’adinai da Makamashi na Jihar Gombe, Sanusi Ahmed Pindiga, ya fitar, ta ce Kwamitin Haɗin Gwiwa da ke wakiltar jihohin biyu ya gano muhimman fannoni huɗu da ke kawo damuwa, waɗanda suka haɗa da sayen filaye, rashin gudanar da ‘Yancin...
    An kaddamar da bikin baje koli na aikin noma da albarkatun dabbobi na kasa da kasa karo na 7 na kasar Cote d’Ivoire a cibiyar bukukuwan baje koli ta kasa da kasa dake birnin Abidjan, a jiya Jumma’a 23 ga wannan watan. A matsayin muhimmiyar bakuwar kasa a gun bikin baje kolin, kasar Sin ta kafa rumfarta a tsakiyar cibiyar, inda aka gwada fasahohin zamani na aikin noma da injuna na kasar Sin. Firaministan kasar Cote d’Ivoire Robert Beugre Manbe, ya bayyana a yayin bude bikin cewa, kasar Sin tana kan gaba a duniya a fannin fasahohin zamani na aikin noma. Kuma kasar Cote d’Ivoire za ta ci gaba da yin kirkire-kirkire kan fasahohin zamani don sa kaimi ga zamanantar...
    Mene ne burinki na gaba game da fim? Burina shi ne a ce yau ga ni ni ma na fito da kudina a ce yau ni ce furodusa ta kaina da kaina, ina rokon ubangiji Allah ya nuna mun ranar nan inada wannan burin sosai ace ni zan yi furodusin fim dina da kaina kuma in sha Allahu muna nan muna rokon Allah yayi mana zabin abin da ya fi zama alkhairi, in sha Allah. Wadanne jarumai ne suke burge ki tun kafin ki fara fim har ma da yanzu da ki ke cikin masana’antar su waye suka zama allon kwaikwayonki? Zan iya ce miki ‘acting’ din kowa yana burge ni kowa da yanayin aktin din da za ka ga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mazauna garin Jos sun shiga cikin zullumi bayan da jami’an Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) suka yi ta harbe-harbe a ranar Asabar. Jami’an na Sibil Difens da ke aiki karkashi Hukumar Kula da Ci-gaban Garin Jos (JMDB) sun bude wuta ne a yayin wani samame da suka kai katafare shagon sayar da kayayyaki na S.O Plaza, lamarin da ya haifar da rikici. Jami’an hukumar sun kuma lakada wa wani matashi mai aiki a plazar duka, lamarin da ya rincabe zuwa tayar da jijiyoyin wuya. A yayin samamen, jami’an tsaron sun ce sun je ne domin kama wata babbar mota da ta keta dokar  hana manyan motoci shiga garin. Za mu gina mayankar dabbobi ta Naira biliyan 3 a Gombe...
    Kafin wasan ƙarshe na bana da za su kara da Crystal Palace a ranar Lahadi, Salah ya riga ya ci ƙwallaye 28 a Firimiyar bana kuma ya taimaka a ci wasu 18. Kusan taimako biyu kawai suka rage masa ya kai tarihin taimako 20 da Thierry Henry da Kevin de Bruyne suka kafa. A wannan kakar, Salah ya zama ɗan wasan da ba na Ingila ba da ya fi zura ƙwallaye kwallaye a tarihin Firimiyar Ingila, inda ya zarce ƙwallaye 184 da Sergio Aguero ya ci. Haka kuma ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool har zuwa shekarar 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Abin da ma yake faruwa kenan yanzu wallahi matasan nan maza! namiji babu sana’a babu isasshen ilimin zamani ke wallahi na addini ma wani babu sai ya tattago aure ko da yake an ce adashi suke shiga da an dauka sai zancen kai kudi karshe dai abar iyaye da wahala shi ya sa auren ma baya cin Litinin da Laraba an watse. Abin cewa nan yaro dai ya nutsu ya nemi sana’a da zai dogara da kansa sannan ya iya daukar nauyin iyali kuma a nemi karatu bakin iyawa. Su iyaye suna gujewa yaro abin da zai je ya zo ne ka dauko ‘yar mutane babu sana’a za a ci soyayya ne ina kai ba karatu ba sai kame-kame wani...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe. Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar. An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025. An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar. Sojoji sun kashe mayaƙan...
    Idan ajiyewa za ki yi sai ki samu roba mai murfi, ki rufe sosai saboda kada ta yi kwari. Yadda za ki tuka: Sai ki dora ruwa a wuta, ya tafasa ki dauko garin doyar, ki rage wuta kina zubawa da kadan-kadan kina tukawa har ya tuku, ki tabbatar bai yi kulalai ba duk kin tuke shi, sai ki dan zuba ruwa kadan ki daddanna ki rufe ki barshi ya yi kamar minti 15, sai ki sauke ki sake tukawa, ki samu leda ki kwashe abinki, shi kenan kin kammala. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    ‘Yansanda sun ce ana ci gaba da bincike don gano cikakken bayani game da lamarin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL) ya sanar da rufe matatar mai ta Fatakwal (PHRC) don gudanar da gyare-gyare da kimanta ingancin aiki, wanda zai fara a ranar 24 ga Mayu, 2025. A wata sanarwa da babban Jami’in sadarwa na NNPCL, Femi Soneye, ya fitar a yau Asabar, ya bayyana cewa wannan shiri ne na yau da kullum don tabbatar da inganci aikin gidan matatar. Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Bayan Fara Aikin Matatar Mai Ta Fatakwal, Sai Kuma Me? NNPCL ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomi kamar hukumar kula da albarkatun Mai ta tsakiya da kuma kasa (NMDPRA) don tabbatar da ingancin aikin gyara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar ISWAP guda biyar sa’annan suka fatattaki ragowar da suka kawo hari a sansanin soji da ke kauyen Gajibo da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno. Wata majiyar daga Zagàzola makama na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari kauyen Gajibo ne da misalin karfe 10:20 na daren ranar alhamis, inda sojojin rundunar Operation Hadin Kai suka yi musayar wata da su suka fatattaki maharan da hadin gwiwar dakarun rundunar ta 134 da suka isa garin. A yayin arangamar ’yan ta’addan sun tsere sun bar nau’uka daban-daban na makamai da suka hada da kuma na’urar sadarwa. Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da ta’addanci, musamman bisa la’akari da...
    Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, James Lashen, ya tabbatar da cewa an kashe mutane huɗu a harin, yayin da babu wani ɗansanda da ya jikkata a faɗan da suka yi da maharan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Na yi imanin za mu iya hakan Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan? Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin yuwuwar bunkasa damar samar da MSG na cikin gida ta hanyar amfani da wadannan albarkatun kasa da ake samu. Muna da injiniyoyi da yawa wadanda za su iya gyara injinan. Muna da dukkan abubuwan da ake bukata a Nijeriya don samar da kayan dandano. Yawanci muna samun abubuwan da duk da muke bukata. Idan kana bukatar ruwa mai yawa, muna da madatsun ruwa a Shiroro,...
    Sojojin HKI sun sabonta hare-hare a ranar Jumma’a kan fararen hula a kan Falasdinawa a Gaza, inda suka kashe akalla mutane 76 ajiya jumma’a kadai sannan wasu dadama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa sojojin HKI sun kai hare-hare a kan wani gida a Khan Yunus inda suka kashe akalla mutane. A wani  harin da sojojin yahudawan suka kai khan yunus har’ila yau ya kashe falasdinawa akalla 8. Alaa Al-Najjar, likita a asbitin Nasir ya bayyana cewa ta rasa yayanta har 9 a cikin asbitin sanadiyyar hare-haren HKI a kan shi. Harin da yahudawan suka kai kan gidan Annajjar dai ya rusa gidan daga sama har kasa sannan...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sallami ma’aikata da dama a majalisar tsaron kasar Amuka saboda gazawarsu wajen magance wasu al-amuran tsaro da siyasa a kasar. Tashar talabijin Ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Rauters yana cewa ma’aikatan maimakon su magance al-amuran tsaro da suka shafi tsaron kasa, sai sun zauna suna jiran abinda shugaban zai fada don su yi aiki a kansa. Labarin ya kara da cewa shugaban ya dauki wannan matakin ne don ya mika wasu ayyukansu ga Pentagon da FBI da wasu ma’aikatun tsaro don magance wasu matsaloli masu muhimmanci a cikin sauri.
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran bata amince da kafa kasashe biyu a matsayin hanyar warware rikicin Falasdinawa ba, saboda kafa kasashe biyu ba zai bawa Falasdinawa hakkinsu ba saboda matukar akwai ikon da HKI take  da shi a yakin Falasdinawa ba zasu taba samun hakkinsu ba. Bil’hasali ma kasashe biyu a fahintar mu zai kara wahalar da Falasdinawa ne fiye da hadda suke sha a halin yanzu. Ministan ya bayyana haka ne a lokacinda ya kai ziyara birnin Vatikan na kasar Italiya inda ya gana da Cardinal Pietro Parolin a jiya Jumma’a. Aragchi ya kara da cewa an dade ana maganar raba gardamar ta hanyar kasashen biyu. Al-hali ba wanda ya amince da kafa kasashen biyu...
    Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so. Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta    Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu. Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan...
    Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dilancin labaran IP na klasar  Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran ita ce yakin da zai biyo bayan wannan kokarin, Kerry yana magana ne don maida martani ga maganar cewa HKI tana shirin kai hare-hare ko yiyuwan ta kai harehare kan cibiyoyin nukliya kasar Iran idan ta ki amincea ta dakatar da tashe makamashiun uranium a cikin gida a tattaunawan da take da Amurka kan shirin nata. Labarin ya kara da cewa wannan yana tabbatar da...
    Samun Gurbin Shiga Jami’a Da Sauran Manyan Makarantu Samun damar shiga jami’a a Nijeriya na da matukar wahala a koda-yaushe, sai ga shi wannan shekara ta 2025 ta bullo da wasu sabbin kalubale. Daga kura-kuren da aka samu yayin yin rajista da kuma gwajin kwamfuta, don rage yawan masu shiga jami’ar, tsarin ragewar na wannan shekarar ya fi na kowace shekara. Sama da dalibai miliyan 1.9 ne suka rubuta jarrabawar a wannan shekarar, wanda hakan yasa ta zama jarrabawa mafi girma a tarihin hukumar shirya jarrabawar. Wannan karuwar, ta nuna karuwar yawan al’umma da kuma karuwar bukatar neman ilimi a tsakanin matasan Nijeriya. Har ila yau, wannan na nuni da cewa; adadin guraben da ake da su a jami’o’in kasar...