2025-07-23@16:30:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6822
«Hadarin mota»:
Datti Baba-Ahmed, wanda ya yi wa Peter Obi, takarar mataimaki a zaɓen 2023, ya ce yana goyon bayan Obi idan yana so ya sake yin takara a 2027, ko da ba tare da shi ba. Peter Obi da Datti sun tsaya takara tare a 2023 sai dai sun ƙare a na uku. NEDC ta raba...
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ta kasar Sin ta fidda bayani a jiya Talata cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, yawan zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ya kai ton-kilomita biliyan 78.35, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Kana, yawan zirga-zirgar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe, sun fara rabon kayayyakin gini ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙananan hukumomi 13 na jihar. Wannan taimako na da nufin tallafa wa mutanen da ambaliya ta rushe musu gidaje. Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin kuɗi da ya danganci makomar yara. Shugaban ofishin UNICEF na Kano,...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce...
Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin kuncin rayuwa. Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu. An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa An ga gawarwakin yara biyu a gidan...
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci. Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa; Ba zai yiwu Iran ta iya yin watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Har yanzu ba a daina sarrafa sinadarin Uranium ba a Iran, duk da irin barnar da hare-haren Amurka ya yi wa cibiyoyin makamashin nukiliyar...
Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Iran ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskure, za su fuskanci mayar da martani da karfi Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin wani kuskure, to za su fuskanci mayar da martani mai karfi da zai wurga su...
Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taɓa, a kowace hanya ko salo, tauye ko hana ci gaban aikace-aikacen kafafen yaɗa labarai a wannan ƙasa ba. Amma dole ne mu duka ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai mu haɗa kai, mu bi wannan hanya mai sarƙaƙiya, mu tabbatar da cewa...
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Lod da makami mai linzami nau’in ‘Palestine 2’ Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani harin soji na musamman da aka kai kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami kirar “Palestine...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Barack Obama da cin amanar kasa tare da yin kira da a yi masa shari’a Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi magabacinsa, Barack Obama da cin amanar kasa, inda ya bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya kan wani rahoton sirri da ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da...
“Farfaɗowa na samuwa, kuma a bayyane yake cewa sabon yanayi na sauyi yana faruwa a Kaduna,” in ji shi. Ya jaddada cewa kyakkyawar gwamnati na nufin kula da buƙatun al’umma, musamman waɗanda rikici ya shafa. “Muna share hawayen waɗanda rikice-rikice suka shafa. Muna haɗa kan al’umma. Muna tabbatar da cewa kowa yana da wajen zama...
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin masani a harkar hulɗa da jama’a kuma ma’aikacin gwamnati na gari da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga jihar. Ya ce aikin wayar da kai da ya yi ba za a manta da shi ba. Gwamna...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran. Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta...
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka...
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata. Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa. Kamfanin dillancin...
Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba. Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata....
“Sun jikkata mutane biyu tare da sace maza, mata da yara da dama.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata sabuwar tashin-tashina ta sake kunno kai a yankin kahon Afirka a daidai lokacin da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi gargadi kai tsaye ga firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda ya yi kashedin sake kaddamar da wani yaki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin shiga bangaren ruwa...
An miƙa batun zuwa Rundunar ‘yansandan Jihar don ci gaba da bincike kafin gurfanar da wanda ake zargin a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta lashi takobin sake maka shugabancin Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a gaban kotun daukaka kara bayan an hana ta shiga harabar majalisar a ranar Talata. Cikin bacin rai, Natasha ta shaida wa ’yan jarida cewa za ta tattauna da lauyoyinta cikin gaggawa domin fara shigar da karar, tana...
A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa. Sanarwar ta bayyana cewa bikin...
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, da shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Huning, sun gana da shugaban majalisar dattijan kasar Madagascar Richard Ravalomanana. Yayin ganawar, Zhao Leji ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin kokari tare da Madagascar, don sa kaimi ga raya hadin...
Kwamatin kananan hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Kirikasamma ta samu nasarar gudanarwa daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya kafa kananan kwamitoci guda biyu domin samun nasarar tantance ayyukan a cikin garin Kirikasamma da kauyuka. Karamin Kwamati na daya bisa jagorancin...
Gwamna Bala Muhammad ya ƙaddamar da aikin gyare-gyare da sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi kan kuɗin da ya haura Naira biliyan bakwai, wanda ya haɗa da inganta kayan aiki, ofisoshi, da kuma gina sabon ofishin hukumar kula da harkokin majalisa. A yayin ƙaddamarwar da aka gudanar ranar Talata, Gwamna Bala ya bayyana cewa wannan gyara...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya...
Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi ta yanke hukunci a kan gwamnatin jihar Bauchi da ta biya tsohon Akanta-Janar na jihar, Dakta Sa’idu Abubakar, Naira miliyan 100 a matsayin diyyar take masa haƙƙi da kuma tsare shi ba bisa ƙa’ida ba. Kotun ta kuma umarci gwamnati ta wallafa ban haƙuri a manyan jaridu guda biyu...
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026. Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau Talata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai na jerin taruka masu jigon “Kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”. Yayin taron, jami’in kungiyar nakasassu ta Sin ya bayyana cewa, yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, an kiyaye...
Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna. Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Batun kare hakkin bil’adama da ake yi a duniya ba komai ba ne sai karya. Shugaba Fizishkiyan ya yi ishara da yadda masu ikirarin kare hakkin bil’adama suke sa kafafunsu suna take hakkin mutanen Gaza da cikin kasashen yammacin Asiya da kuma tafka manyan laifuka. A yau...
Na san zuwa yanzu kowa zai amince cewa, kasar Sin ta bullo da sabuwar dabara ta abota da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da ya bambanta da ta masu son cin zali da neman iko. Koyar da fasahohin da za su taimakawa kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika, zai kai su ga habaka ayyukansu...
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai...
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani...
Su kuwa mahalarta taron, sun yaba da kyautatuwar dangantakar kasashen biyu da rawar da SCO ke takawa. Sun kuma bayyana fatan Masar da Sin za su yi amfani da damarmakin ci gaba da SCO ta samar domin su hada hannu tare, su inganta tsarin jagorantar harkokin duniya da farfadowar kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Fa’iza...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga...
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100...
Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ’yan rakiyarta shiga haramar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ta je da niyyar halartar zaman Majlasiar Dattawa a ranar Talata. Jami’an tsaro a daukacin kofofin shiga harabar majalisar sun hana ta shiga harabar majalisar ne a lokacin da ta yi yunkurin shiga domin halartar zaman ranar Talata,...
Lauyanta, SAN West Idahosa, ya ce kotu ta tabbatar da cewa Natasha na da damar komawa majalisa ba tare da wata matsala ba. Amma majalisar dattawa ta dage cewa har yanzu tana nan kan matsayinta na dakatar da Natasha har sai wa’adin dakatarwar ya cika. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan...
Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati. Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan...
Gwamnatin ƙasar Guinea ta rufe wasu sassan kamfanoni guda 1,724 sakamakon kama su da laifin ƙin bin dokokin hukuma, yayin da aka janye kayayyakin da suke sarrafawa daga kasuwa. Sanarwar na zuwa ne ƙarƙashin ma’aikatar kasuwanci a ƙasar, tana mai cewa an ɗauki matakin ne don kare lafiyar masu sayen kayayyakin da kuma tabbatar da...
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin...