Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal
Published: 10th, September 2025 GMT
Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun banka wa gidansu wuta a unguwar Dallu da ke birnin Kathmandu a ranar Talata.
Bayanai sun ce masu zanga-zanga a ƙasar mai tsaunuka da ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama sun tarfa matar tsohon firaministan ne a cikin gida kafin su kunna wutar.
An garzaya da ita asibitin kula da waɗanda ibtila’in ƙuna ya afkawa da ke Kirtipur cikin mummunan yanayi, amma daga ƙarshe ta ce ga garinku nan sakamakon munanan raunuka da ta samu.
Rasuwarta ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar matasa a duk faɗin Nepal tsawon kwana biyu, duk da cewa gwamnati ta ɗage takunkumin da ta saka kan kafafen sada zumunta a farkon makon nan.
Masu zanga-zangar na neman jami’an gwamnati sauka daga kujeru saboda zargin cin hanci da rashawa, nuna son kai a siyasa da kuma taɓaɓarewar tattalin arziki.
Tun dai daga ranar Litinin aka fara tashin hankali, kuma rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 22 sun mutu yayin da sama da 300 suka ji rauni.
Kungiyar Amnesty International ta zargi ’yan sanda da amfani da harsasai wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Bidiyoyin da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ake jefa bama-bamai da aka haɗa da man fetur a gidajen fitattun ’yan siyasa, ciki har da na tsofaffin Firaministoci — K.P. Sharma Oli, Sher Bahadur Deuba, da kuma Pushpa Kamal Dahal.
Muhimman gine-ginen gwamnati, ciki har da Singha Durbar (hedikwatar gwamnati) da fadar shugaban ƙasa, Sheetal Niwas, su ma an kai musu hari.
A yayin da tashin hankali ke ƙara tsananta ne Firaminista K.P Sharma Oli mai shekaru 73, ya miƙa takardar murabus ga shugaban ƙasa a ranar Talata, yana mai cewa matakin “na da muhimmanci don ɗaukar matakan samun mafita a siyasar ƙasar.”
Haka kuma, wasu ministocin gwamnati da suka haɗa da na ruwa, noma da cikin gida, sun yi murabus, domin nuna adawa da yadda tarzomar ke ƙara tsananta.
Yanzu haka dai ƙasar ta faɗa cikin wani yanayi na fargaba a yayin da hukumomi ke ƙoƙarin dawo da doka da oda, inda ake ta kira da a koma kan teburin tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicin.
A yayin da sojoji suka ayyana dokar hana fita tare da gudanar da sintiri a birnin Kathmandu, matasan Nepal da suka gudanar da zanga-zangar da sunan adawa da cin hanci da rashawa sun yi iƙirarin cewa wasu masu neman dama ne suka ƙwace zanga-zangar wadda ta rikiɗe ta zuwa tashin hankali.
Ƙungiyoyin matasa sun nesanta kansu daga ɓarnar, suna masu cewa masu son yin amfani da dama ne suka shiga suka lalata zanga-zangar.
Sojojin da suka kafa dokar hana fita a faɗin ƙasa har zuwa safiyar Alhamis, sun yi gargaɗin hukunta duk wanda aka samu da hannu a tashin hankali ko ɓarna.
Rahotanni sun ce an kama mutum 27 da ake zargi da hannu a fashi da tarzoma, tare da ƙwato bindigogi 31.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rabi Laxmi Chitrakar zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a RibasMajiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.
“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.
Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).
Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.
Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.
Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.