Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi
Published: 23rd, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huɗu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a ƙauyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo.
Aminiya ta ruwaito cewar mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi ne, ya sanar da Sarkin garinsu, Musa Isah, cewa a ranar 20 ga watan Maris, 2025, ɗansa ya ɓace.
Washegari, wani ya kira shi a waya yana neman kuɗin fansa.
Da farko, ya nemi miliyan uku (₦3,000,000), amma daga baya suka rage zuwa Naira dubu ɗari biyu (₦200,000).
A ranar 21 ga watan Maris, aka gano gawar yaron a cikin daji, an ɗaure masa wuya da igiya.
Nan take aka kai shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Daga nan aka bai wa iyalansa gawarsa domin yi masa jana’iza.
Kakakin ’yan sandan Jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce bayan samun rahoton lamarin, jami’an su suka fara bincike.
Sun fara binciken ne daga wajen POS da ke kusa da inda aka buƙaci a biya kuɗin fansar.
A yayin binciken, sun kama wani matashi mai shekara 23, Rabi’u Muhammadu daga ƙauyen Leka.
An gano cewa lambar wayarsa ce aka yi amfani da ita wajen kiran mahaifin yaron.
Sannan ’yan sanda sun gano asusun bankin da aka bayar don biyan kuɗin fansar: Lambar asusu: 0145285130 Sunan mai asusu: Ozochikelu Samson Banki: Union Bank PLC
Bayan kama Rabi’u, ya bayyana cewa Samson Ozochikel, mai shekara 35 daga ƙauyen Sade, shi ne ya shirya yadda za a sace yaron.
Ya kuma ambaci wasu matasa biyu, Muhammad Sani (Jingi), mai shekara 25, da Musa Usman (Kala), mai shekara 30, dukkaninsu daga ƙauyen Leka.
A halin yanzu, ’yan sanda suna tsare da su, kuma ana ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuka (SCID).
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, ya tabbatar da cewa za su tabbatar da an yi adalci.
Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai, tare da sanar da su duk wani abun zargi ta layin kiran wayar gaggawa 112 ko Police Control Room a lamba 08156814656.
Rundunar ta jaddada ƙudirinta na kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Garkuwa yaro mai shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Kira Jakadan Burtaniya A Tehran Saboda Tuhumar Da Akewa Iran Da Leken Asiri A London
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kira mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehran zuwa ma’aikatar don gabatar mata da korafi kan yadda jami’an tsaron kasar Burtaniya suke kama yan kasar Iran ma zauna birnin London tare da tuhumarsu da ayyukan Leken asiri wa JMI.
Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a cikin wannan watan Mayu da muke ciki Jami’an yansanda a kasar Burtaniya sun kama Iraniyawa mazauna birnin London har guda 7 a sumamen guda biyu da suka kaimasu a gidajensu.
Labarin ya kara da cewa an gabatar da mutane uku a gaban kotu a birnin London tare da tuhumar su da aikin leken asiri ga JMI.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa, kame kamen da gwamnatin kasar Burtaniya takewa Iraniyawa a London na siyasa ne.
Labarin ya kara da cewa saboda yawan kame-kamen ne ya sa ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kira mataimakon jakadan kasar Burtaniya a nan Birnin Tehran zuwa ma’aikatar don gabatar mata da wannan korafin.
Masana suna ganin gwamnatin Burtaniya tana yin haka ne don takurawa JMI inji ma’aikatar.
Labarin ya kara da cewa sakataren harkokin wajen kasar Burtaniya ya kira jakadan Iran a Lodon Sayyed Ali Musawi inda suka fada masa cewa gwamnatin Iran ce da alhakin wasu matsalolin tsaro a kasar Burtaniya.
Ya zuwa yanzu da an gurfanar da Iraniyawa uku a gaban kutu a binin Landa, kuma sun hada da Mostafa Sepahvand, dan shekara 39 a duniya, sai Farhad Javadi Manesh, dan shekara 44 a duniya da kuma Shapoor Qalehali Khani Noori dan shekara 55 a duniya dukkaninsu mazauna birnin Landon.