Argentina: Lauyoyi sun yi kira da a cafke Netanyahu a kan laifukan yaki
Published: 31st, August 2025 GMT
Lauyoyin kare hakkin bil’adama a Argentina sun shigar da kara a gaban kotunan tarayya suna neman a kama firayim ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu idan ya saka kafarsa a kasar, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna yiwuwar cewa zai kai ziyara a kasar a wata mai zuwa.
Karar da lauyoyin kasar Argentina masu rajin kare hakkin bil adama suka shigar, na zargin Netanyahu da alhakin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama da ke da alaka da hare-haren sojin Isra’ila a Gaza.
Har ila yau, a cikin karar an bukaci a gudanar da bincike kan shugabannin siyasa da na soji na Isra’ila kan wani lamari da ya faru a ranar 23 ga Maris, inda aka kashe mutane 15, ciki har da wasu daga wadanda suke gudanar da ayyukan agaji da jin kai a Gaza.
Ya zoa cikin takadar shigar da karar cewa, “Netanyahu yana da alhakin aikata laifuka a matsayinsa na mai aikata laifukan yaki da haifar da kisa da gangan ta hanyar yunwa da laifukan cin zarafin bil’adama kamar kisan kai, zalunci, da sauran muggan laifukan cutar da bin adama.”
An yi ta yada bayanai a kafafen yada labaran Argentina cewa akwai yiwuwar Netanyahu ya kai Ziyara a kasar a watan Satumba, kodayake gwamnati ba ta tabbatar da wani shiri a hukumance kan hakan ba.
A watan Nuwamba 2024, Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta ba da sammacin kama Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin soji Yoav Gallant, bisa zargin laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Gaza.
Har ila yau Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan kiyashi a kotun kasa da kasa (ICJ) saboda yakin da ta yi a yankin zirin Gaza da ta yi kawanya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan: Hamedti ya yi rantsuwar shugabantar gwamnati mai kishiyantar gwamnatin kasar August 31, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Ba Za Su Kyale A Lalata Alakar Iran Da Armeniya Ba August 30, 2025 Larijani: Iran Tana Adawa Da Juya Akalar Siyasar Yankin Daga Wasu Masu Son Baba-Kere August 30, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Maraba Da Matakin Wasu Kasashen Turai Na Nuna Kyamarta Zaluncin Isra’ila August 30, 2025 Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila August 30, 2025 Moroko: Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da Kisan Kiyashi Da Kakaba Yunwa A Gaza August 30, 2025 Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki August 30, 2025 Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya August 30, 2025 Iran: IRGC Sun Kama Ma’aikatan Mosad A Arewa Maso Gabacin Kasar August 30, 2025 Iran Ta Yi Watsi Da Shirin ‘SnapBack’ Na Kasashen Turai August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: laifukan yaki
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza
Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa.
Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki daya.
Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta kasar Qatar ta ce,adadin wadanda su ka yi shahada har zuwa marecen yau sun kai 51,38 daga cikinsu a cikin birnin Gaza kadai.
A gefe daya rahoton tashar talbijin din ta ‘aljazira’ ya bayyana cewa; HKI ta yanke hanyoyin sadarrwa na “Internet’ a fadin Gaza, haka nan kuma ta hana hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) shigar da makamashi cikin asibitocin yankin.
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gazan ta kuma ce, matukar ba a bari aka shigar da makamashi cikin asibitocin yankin ba, to komai zai tsaya.
A can yankin yammacin kogin Jordan kuwa, sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 40 a garin ‘Assir” a yau Laraba kadai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci