Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi
Published: 29th, August 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike mai ƙarfi na ƙwararrun jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar rundunar ‘sojan Najeriya, domin gano abin da ya jawo aka kashe wani jami’in soja da wani sifeton ’yan sanda ya yi a jihar kwanan nan.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), CSP Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin Kwamishinan ’yan sandan, Sani-Omolori Aliyu a hedikwatar rundunar da ke Bauchi a ranar Juma’a.
Wakil ya ce, an ɗora wa kwamitin alhakin tattarawa da tantance duk bayanan da suka dace da suka shafi wannan lamari da kuma abubuwan da suka faru nan take”,
A cewarsa, masu binciken za su bi dukkan ƙa’idojin ƙwarewa na aikin bincike su ɗauki matakai da suka dace don samar da sahihin sakamakon bincike mai tushe da za a dogara da shi, Kuma ya zamo bincke ne da zai kawar da rashin tabbas da kuma tabbatar da cewa, an samu adalci ta hanyar yin nazari sosai.
Dangane da batun zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da kuma rakiyar jami’in tsaro ba bisa ƙa’ida ba.
Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa, “Bincike na farko, ya nuna cewa motar tana da alaƙa da kamfanin Guruje Mining Company Limited da ZURFI Company Limited, waɗanda ke da ingantaccen lasisin haƙar ma’adinai bisa doka a Gwana, ƙaramar hukumar Alƙaleri. Wannan izini ya shafi haƙar ma’adinan Zinc, wanda aka samu daga ofishin Kula da ma’adinan na Tarayyar Najeriya, daga ranar 12 ga Mayu 2023.
Waɗannan kamfanonin sun yi aiki tare da kamfanin Minco. Ƙarƙashin Dokar 2007 kuma sun mallaki takardar shaidar ƙa’idojin Kamfanoni na 2020.
“Kuma sun buƙaci jami’an ‘yan sandan da za su kare su waɗannan kamfanoni a hukumance kuma an amince da su an kuma basu ’yan sanda don samar da tsaro don kare lafiyar ma’aikatan da suka fito daga ƙasashen ƙetare da kuma sauran ayyukan tsaro da ke da alaƙa da kamfanin.
Sufeto Yusuf Ibrahim na daga cikin wadanda aka bai wa wannan aiki, ya ce “Kamfanin ya yi nasarar fitar da wani adadi mai yawa na ma’adanai na zinc, waɗanda aka gabatar da su don fitar da su, kuma sun biya dukkan kuɗaɗen da suka dace a matsayin kuɗaɗen shiga da aka biya ga Ma’aikatar Ma’adinai da ta Tarayya da lambar rasiti mai lamba 3212-7561-4841 Kamar yadda yake a doka”.
Ya kuma shawarci ’yan jarida da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen yin ayyuka na aikin jarida na binciken gaskiya da nufin tabbatar da haɗin kan ƙasa da nuna kishin ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.
A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.
Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp