Sabon Fira Ministan Sudan Ya Bukaci Kasashen Dake Taimaka Wa “RSF” Da Su Daina
Published: 2nd, June 2025 GMT
Sabon fira ministan kasar Sudan Kamil Idris ya yi kira ga kasashen waje masu taimaka wa dakarun daukin gaggawa “RSF” da su kawo karshen taimakon da suke bawa masu aikata laifi.”
Idris wanda yake jawabin bayan kama aiki a jiya ya ce; Jami’an tsaro da kuma mahukuntan kasar ta Sudan suna da cikakken goyon baya a kasar don kawo karsehn ‘yan tawaye, masu dauke da makamai.
Idris ya kuma ce; A shirye yake ya yi wa kasa aiki a cikin kekyawar anniyya da kwazo.”
Gwamantin kasar Sudan dai tana zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da taimaka wa dakarun kai daukin gaggawa “RFS” wacce ta dauki shekaru biyu tana fafatawa da sojojin kasar.
Wasu daga cikin kasashen da Sudan take zargi da hannu a tawayen na “RSF” sun hada da Chadi, Libya da Sudan Ta Kudu.
Wasu rahotannin suna nuni da cewa, suna bawa wannan kungiyar makamai ne ta kan iyakokin da su ka hada wadannan kasashe da Sudan.
Tun barkewar yakin basasa a kasar Sudan a ranar 15 ga watan April 2023, zuwa yanzu adadin mutanen da su ka rasa rayukansu sun kai 24,000, yayin da wasu fiye da miliyan 14 su ka zama ‘yan gudun gijira, miliyan 4 daga cikinsu sun fice daga kasar, zuwa kasashen makwabta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco
Ministocin tsaro na kasar Rasha ta JMI sun hadu a birnin Mosco don tattauna batun karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yankin kudancin Asiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Iran a Mosco yana fadar haka.
Kazem Jalali, ya bayyana cewa kasashe biyu suna kara zurfin dangantakarsu da juna a dai-dai kasashen biyu suke kara fuskantar matsinn lamba daga kasashen yamma musamman Amurka, da kuma HKI.
Kasashen biyu sun ga yakamata su kara dankon zumunci a tsakaninsu a fagen tsaro, bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorowa kasar Iran.
A wannan zuwan dai ministan tsaron JMI ya raka Dr Ali Larijani babban mai bawa jagoran juyin njuya hali musulunci shawara a ganawarsa da shugaba Vladmir Putin a fadar Krimlin a ranar Lahadi.
Kazem Jalali, ya bayyana cewa a wannan karon ma bangarorin biyu sun tattauna baton karfafa dangantakar tsaron kasashen biyu.