HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
Published: 21st, April 2025 GMT
Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Filato ta gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna adawa da matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Zanga-zangar ta gudana ne makonni kaɗan bayan munanan hare-haren da aka kai a wasu ƙauyukan Bokkos da Mangu, waɗanda suka yi sanadiyyar aƙalla rayuka 100.
Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma FrancisWaɗanda suka yi zanga-zangar sun haɗa da maza da mata da matasa har da tsofaffi ɗauke da alluna waɗanda aka rubuta wa saƙonni daban-daban.
Bayanai sun ce maƙasudin zanga-zangar ita ce kiran gwamnati kan ta ɗauki mataki kan kashe-kashen da ake yi a yankin.
Jihar Filato da wasu jihohin Arewa maso tsakiyar Nijeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro duk da matakan da hukumomi ke cewa suna ɗauka domin kawar da matsalar.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma rikice-rikice masu alaƙa da bambancin addini da na ƙabila sun haifar da rasa rayukan ɗaruruwan mutane da tarwatsa wasu daga matsugunansu.
A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Filaton, Caleb Manasseh Mutfwang ya sanar da ɗaukan wasu sabbin matakai na daƙile matsalar, ciki har da hana kiwon dare da kuma farfaɗo da ƙungiyoyin ’yan sintiri na sa-kai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Filato matsalar tsaro zanga zangar da matsalar
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
“Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.
“Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.
“Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da wani asusu, a Zamfara a shirye muke mu ba da tallafin, idan kun shirya gobe, mu ma mun shirya.
“Mun shirya, kuma ƙofar mu a buɗe take, duk wani abu da zai kawo sauyi mai kyau a Zamfara muna maraba da shi, muna buƙatar tsari na abin da ku ke yi domin mu ci gaba da bin diddigin lamarin, zan samu wata tawaga da za ta riƙa hulɗa da cibiyar yaƙi da ta’addanci.
Tun da farko, Shugabar Rigakafi da Yaƙi da Ta’addanci (PCVE), Ambasada Mairo Musa Abbas ta ce, tawagar ta zo jihar Zamfara ne a madadin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da kuma kodinetan yaƙi da ta’addanci na ƙasa, Manjo Janar Adamu Garba Laka. “Muna nan a matsayin wani bangare na dabarun bayar da shawarwari na ƙasa baki ɗaya.”
“Muna son sake gode muku bisa irin karramawar da ka yi mana a Jihar Zamfara da kuma irin shugabancin da ka yi wa al’umma, muna sa ran haɗin kai don ganin cewa Zamfara ta zama kan gaba wajen yaƙi da ‘yan bindiga.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp