Iran Ta Sanar Da Kasar Oman A Matsayin Wajen Tattaunawa Na Gaba Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Published: 15th, April 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukuliyar Iran zagaye na biyu ne a birnin Muscat na kasar Oman
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Zaman tattaunawa zageye na biyu wanda ba na kai tsaye ba, tsakanin Iran da Amurka zai kasance ne a birnin Muscat fadar mulkin kasar Oman.
Baghaei ya yi watsi da rade-radin da ake yi kan inda za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar kai tsaye tsakanin Iran da Amurka, Baghaei ya ce, “Bayan tuntubar juna, an yanke shawarar cewa birnin Muscat ne zai karbi bakwancin zagaye na biyu na shawarwarin, wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa.”
Wani abin lura a nan shi ne, an gudanar da shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da manzon Amurka na musamman kan yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff dangane da batun Shirin makamashin nukiliyar Iran da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata na rashin adalci da baya kan tubalin ka’ida. Tattaunawar ta samu halartar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i da mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi, da mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da na kasa da kasa Kazem Gharibabadi, da manyan masu shiga tsakani kan batun dage takunkumi da batun Shirin makamashin nukiliya, da kuma kwararrun da suka dace.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Abdullahi Ojlan Ya Sanar Da Kawo Karshen Fada Da Makami
Shugaban kungiyar Kurdawa ta kasar Turkiya ( PKK) Abdullah Ojlan ya sanar da kawo karshen amfani da makamai a fafutukar da kungiyarsu take yi na kare hakkokinsu a kasar Turkiya.
Shugaban kungiyar Kurdawan na Turkiya wanda yake tsare a kurkuku na shekaru masu tsawo, ya aiko da sako na bidiyo da a cikin ya ce; Har yanzu ina kan kiran da na yi a ranar 27 ga watan Febrairu na ajiye makamai”.
Ojlan ya kara da cewa; Muna sanar da kawo karshen amfani da makamai ne bisa radin kanmu, haka na kuma ya ce; Mun shiga Zangon aiki da doka da kuma siyasa da tsarin demokradiyya, wanda shi kanshi nasara ce mai dimbin tarihi ba asara ba.”
Kuniyar PKK ta kurdawan Turkiya dai ta yi fiye da shekaru 40 tana dauke da makamai a fadan da take yi da gwamnatin Turkiya. A watan Mayu da ya shude ne dai kungiyar ta sanar rusa kanta, sannan kuma ta sanar da Shirin ajiye makamanta na yaki.
Tun a 1999 ne gwamnatin kasar Turkiya take tsare da Abdullahi Ojlan.
An kafa kungiyar PKK ne a shekarar 1978, ya kuma fara kai hare-hare a cikin kasar Turkiya a 1984, da ya zuwa ajiye makaman kungiyar an kashe mutane fiye da 40,000.
A cikin shekarun bayan nan ne da aka bude tattaunawa a tsakanin kungiyar da kuma gwamnatin Turkiya akan batun kawo karshen tawaye, da samar da hanyoyin sulhi da zaman lafiya domin warware korafin Kurdawan.