Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha
Published: 1st, April 2025 GMT
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar, ta ce taron barka da sallah da ta yi a mazaɓarta a yammacin Talata duk da haramta taruka da gwamnatin jihar ta yi ba karya doka ba ne.
Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kogin dai ta hana duk wani nau’in taro ko gangami a jihar, saboda dalilin da ta ce na tsaro ne.
Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Miller Ɗantawaye, ya ce hana taron ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu cewa za a samu barzanar tsaro, wanda ya tilasta gwamnatin jihar ɗaukar matakin.
Sai dai Natasha wadda ta isa jihar a wani jirgi mai saukar ungulu, ta bayyana wa magoya bayanta cewa tana da ’yancin kasancewa da mutanenta ta kuma yi shagalin farin ciki tare da su.
“A duk abin da za mu yi, mu sanya Allah a farko kuma mu shigar masa da buƙatunmu ta hanyar addu’a.
“Mijina ya kasance ɗaya daga cikin addu’o’ina da Allah Ya amsa. In banda haka ta yaya ni da ba kowa ba ce fa ce talaka daga ƙabilar Ebira na samu ƙarfin samun jirgin da zai kawo ni gida?
“Goyon bayan mijina ne ya kawo haka, kuma shi ke ciyar da ni gaba a koda yaushe.
“Tun jiya da na samu labarin za a rufe hanyoyi, aka kuma haramta taruka da jerin gwanon motoci a cikin gari na san cewa mu ne ake so a muzgunawa.
“Amma sai na faɗa wa kaina ai ba kakar siyasa ko yaƙin neman zaɓe ba ne yanzu.
“Don haka ni ba yaƙin neman zaɓe zan yi ba. Ni kaɗai ce zan shigo gari cikin mutane na, na yi shagalin bikin Sallah tare da su.
“Don haka babu wani laifi a ciki, babu dokar da na karya. A Najeriya muke. Ina da ’yancin shiga taruka da bukukuwa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa October 31, 2025
Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025