Aminiya:
2025-11-02@17:02:42 GMT

Matatar Dangote ta musanta dakatar da aiki

Published: 8th, September 2025 GMT

Matatar mai ta Dangote ta ƙaryata rahoton da ke cewa za ta iya dakatar da ayyukanta na sarrafa ɗanyen mai har nan da tsawon watanni biyu zuwa uku.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rukunin kamfanin na Dangote, Anthony Chiejina ya fitar, inda ya bayyana rahoton a matsayin “tsantsar ƙarya” wadda ba ta da tushe balle makama.

Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda da yaransa 5 a Kogi

An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan

A wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, ya bayyana cewa, ‘‘akwai yiwuwar rufe sashen matatar man kamfanin wadda ke samar da ganga 650,000 duk rana tsawon watanni biyu zuwa uku saboda aiwatar da wasu gyare-gyare, yana mai ambato shawarar da masana’antar IIR Energy da ke sa ido kan makamashi ta bayar.

A cewar rahoton, tun daga ranar 29 ga watan Agusta aka yi ikirarin rufe sashen matatar man bayan da aka samu matsala ta kwararar mai daga ɓangaren tace man masana’antar.

Kazalika rahoton ya ƙara da cewa, matatar za ta yi ƙoƙarin sake soma aikin tace mai na ganga 204,000 duk rana daga 20 ga watan Satumba, sai dai manyan gyare-gyare da kuma sauya wasu kayan aiki ka iya sanyawa a rufe ta tsawon wasu watanni.

Da yake mayar da martani kan rahoton, Anthony Chiejina, ya bayyana ikirarin a matsayin “labarin ƙarya” yana mai ɗiga ayar tambaya kan dalilin da Reuters zai yi amfani da kalmar ‘yiwuwa’ a rahoton idan har yana da tabbaci kan shirin rufewar matatar, kamar yadda ya shaida wa jaridar Punch a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters dai ya bayar da rahoton cewa ana sa ran rufe sashen kamfanin Dangote na RFCCU na aƙalla makonni biyu.

Matatar mai ta Dangote, wadda ta soma sarrafa ɗanyen mai a watan Janairun 2024, ta sauƙaƙa harkokin mai na cikin gida, lamarin da kuma ya kawo cikas ga harkar cinikayyar fitar da man fetur daga ƙasashen Turai zuwa Yamma.

Kazalika, kasuwancin fitar da man fetur daga ƙasashen Turai da Birtaniya zuwa Nijeriya ya ragu daga ganga kusan 200,000 a shekarar 2024 zuwa kusan 120,000 a watanni shidan farko na wannan shekara ta 2025, a cewar kafar tattara bayanai ta Kpler.

Haka kuma, matatar ta yi jigilar hanyoyin man fetur guda biyu zuwa gabar tekun Gabas ta Amurka, waɗanda ake sa ran isarsu yankin New York nan gaba a cikin wannan wata.

Wannan dai wani gagarumin ci gaba ne, inda masu sa ido kan masana’antu ke bibiyar lokacin da matatar za ta samar da mai da zai yi gogayya da na Amurka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Matatar Dangote

এছাড়াও পড়ুন:

An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda.

 

An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Kakakin rundunar a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, wanda ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, shi ne ya gabatar da takardun cakin kudin ga iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin.

“Harkokin da suka shafi jami’anmu da iyalansu ya kasance babban fifiko ga rundunar,” in ji CP Abdulmajid yayin taron.

Ya ce wannan shiri na nuna tausayi da rikon amana, da kuma jagoranci mai nagarta daga Sufeto Janar wajen girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyalan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace, musamman wajen tallafa wa ilimi, kiwon lafiya, da jin daɗin rayuwar iyalansu gaba ɗaya.

Ya yaba wa Sufeto Janar bisa ci gaba da tsare-tsaren jin daɗin jami’an rundunar, yana mai bayyana su a matsayin muhimman hanyoyin da ke samar da agaji da kwanciyar hankali ga iyalan waɗanda suka rasa masoyansu.

A nata jawabin a madadin iyalan da suka amfana, Misis Nana Goni ta nuna godiya ga Sufeto Janar bisa goyon bayan da ya bayar, tana mai tabbatar da cewa za su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata don inganta rayuwar iyalansu.

Rundunar ta bayyana cewa wannan rabon tallafi ya sake tabbatar da jajircewarta wajen kula da walwala da mutuncin jami’anta da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum