Leadership News Hausa:
2025-09-17@21:52:07 GMT

Shawara Ga Matashin Da Matarsa Ta Samu Juna Biyu (1)

Published: 7th, September 2025 GMT

Shawara Ga Matashin Da Matarsa Ta Samu Juna Biyu (1)

Domin kuwa wasu matan kwanciya kan iya zama sanadi na lalacewar cikin. So, akan ce ma a rage ko a bari a watanni uku na farkon ciki. Don haka idan ka ga wadannan matsalolin kar ka ce wai kirkira take, ko da gangan take. Ba gaskiya bane. Lalura ce babba, kuma da take bukatar kallo na musamman.

Idan kaga wannan lokacin yazo, anan ne ake so ka nuna soyayyarka, da kulawarka, da taimakonka.

Wajibi ka bata hadin-kai don ta wuce wannan watanni uku na farko din. Domin cikin jikinta a wannan lokacin kamar akan siratsi yake, duk abinda aka ce ana halittarta ’yan Adam a cikinsa ai yaga taka kansa. Komai zai iya faruwa. Namiji dan kirki shine sai kaga ya shiga kokarin yin hidimar gida da kansa. Shine wanke wanke, shara, girki, kaye kaye da sauransu. Sannan duk abinda tace tana sha’awa indai da hali a saya mata. Wallahi ba daga ita bane, daga yanayin cikin ne. Za Mu Ci Gaba Mako Mai Idan Allah Ya Kai Mu

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Rayuwa

এছাড়াও পড়ুন:

Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona.

Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar.

Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro

An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka gyara, amma sai mahukuntan Ƙungiyar suka yanke shawarar yin wasan a filin Johan Cruyff mai ƙarfin ɗaukar ‘yan kallo 6,000 kacal, wanda mafi yawan lokuta Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta mata Barcelona ke amfani da shi.

A gaba kuma, Barcelona za ta bakunci Newcastle United a filin wasa na St James’ Park a zagayen farko na gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) a ranar 18 ga Satumba. A gefe guda, Valencia za ta karɓi baƙuncin Atletico Bilbao a wasan mako na biyar na La Liga a ranar 20 ga Satumba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff