Aminiya:
2025-09-17@21:50:11 GMT

Gwamnati ta ba jami’an tsaro tallafin motoci 14 da babura 150

Published: 5th, September 2025 GMT

Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayar tallafin motoci 14 kirar Hilux da babura 150 ga dukkan jami’an tsaron jihar don karfafa aikin sintiri.

Tallafin kari ne a kan Hilux 170 da babura da gwamnatin ta bayar a baya.

Ba abin mamaki ba ne idan na fice daga NNPP – Abdulmumin Kofa ’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye

Sakataren Gwamnatin jihar, Muhammad Bello Sifawa ne ya miƙa kayan a madadin Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu a wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka yi a gidan gwamnatin jiha a ranar Alhamis.

Bello Sifawa ya ce hukumomin tsaro ne suka roki a ba su ababen hawan a lokacin zaman majalisar tsaro ta jihar, shi kuma Gwamnan ya amince

Ya nuna bukatar da ake da ita ga jami’an tsaron kan su yi amfani da motocin da baburan ga abin da ake son a yi domin kare dukiya da rayukan jama’a.

Hakan a cewar Sakataren na cikin babban kudurin gwamnatin.

Da yake jawabi a madadin dukkan jami’an tsaron, kwamishinan ’Yan Sanda na jiha Ahmad Musa ya gode wa gwamnatin jiha kan amincewa da rokon nasu cikin lokaci

Kwamishinan ya kuma gode wa gwamnatin kan hadin kai da take bai wa jami’an tsaro, tare da bayar da tabbacin yin amfani da ababen hawan domin karfafa tsaro a jihar.

Ahmad ya ba da tabbacin jami’an tsaro za su ci gaba da aiki ba dare ba rana don tabbatar da zaman lafiya da taron rayuwa da dukiyar al’umma, za su taimaki gwamnati don samun nasara.

Kwamishina ya yi kira ga mutane su rika ba da bayani duk wani bakon abu da suka gani a yankunan su da ba su amince da shi ba, domin inganta tsaro.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Sakkwato jami an tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta wuce yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6.

Darektan kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhang Yuzhuo ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 har zuwa yanzu, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnati ta karu daga kasa da yuan tiriliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka kimanin tiriliyan 10, zuwa sama da yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6, yayin da jimillar ribar da suka samu ta karu daga yuan tiriliyan 1.9, kwatankwacin sama da dalar Amurka biliyan 267, zuwa yuan tiriliyan 2.6, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 365. Matsakaicin karuwar jimlolin biyu a kowace shekara kuwa ya kai kashi 7.3 cikin dari da kashi 8.3 cikin dari bi da bi.

Bugu da kari, tun daga aka fara aiwatar da shirin, kamfanoni mallakar gwamnati sun biya kudin harajin da yawansu ya zarce yuan tiriliyan 10, kwatankwacin fiye da dalar Amurka triliyan 1.4, kuma darajar yawan hannun jarin da suka mikawa asusun inshorar zaman al’umma ta kai yuan tiriliyan 1.2, kwatankwacin fiye da dalar Amurka biliyan 168.(Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin