Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu a Sakkwato
Published: 4th, September 2025 GMT
Matasan Ƙaramar hukumar Shagari sun kashe wasu ’yan bindiga shidda da ake zargin suna cikin waɗanda suka addabi yankin Ƙaramar hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.
Wani matashi ya yi wa wakilinmu bayanin yadda lamarin ya faru ya ce, ’yan bindigar sun zo kan Jakuna a cikin dajin da ba kowa, a safiyar Alhamis inda mutane da ke tsare gari ba su watse ba suka gansu a nan ne suka yi masu ƙofar raggo, suna tare da shanun da suka sata da wasu baƙin shanu.
“An gansu su bakwai an kashe shidda daga cikinsu an bar guda raye aka ɗaure shi, su shiddan ga su a kwance ba rai, mutane sun yanke hukuncin kare kansu don sun ga gwamnatin Sakkwato ba da gaske take kan lamarin tsaro ba.” A cewarsu
Shugaban Ƙaramar hukumar Shagari, Alhaji Muhammad Maidawa ya ce da safiyar Alhamis labari ya zo masa akwai wasu baƙin Fulani jajaye da aka afkawa a garin Shagari, amma komai ya lafa sojoji sun kwantar da tarzomar.
Kan maganar adadin waɗanda aka kashe ya ce har yanzu jami’an tsaro ba su gama tantancewa ba, in sun ƙare za su sanar da shi ya ba da bayani.
Matasa a ƙarƙashin Ƙungiyar Shagari Youths a Ƙaramar hukumar Shagari ta jihar sun yi barazanar ɗaukar matakin kare kansu sakamakon taɓarɓarewar tsaro a yankin.
Matasan sun kuma zargi gwamnati da sakaci duk da hare-haren ’yan bindiga da ake ta fama da su tare da ƙorafe-ƙorafen jama’a.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Ƙungiyar ta hannun Bello Bala Shagari, ya bayyana cewa matasan sun yanke wannan shawara ne a wani taro na intanet da suka gudanar ranar Laraba.
Ya ce: “Da dama sun bayyana cewa, gwamnati ta gaza wajen cika alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Saboda haka, kare kai yanzu shi ne kaɗai zaɓin da ya rage.”
Ya ƙara da cewa, matasan sun yanke shawarar ɗaukar duk wani mataki da ya dace domin kare kansu daga cin zarafi da hare-haren ’yan bindiga.
Sai dai Shagari ya bayyana cewa, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Yabo/Shagari, Umar Yusuf-Yabo, ya yi kira da a yi haƙuri, a bi doka tare da samun ƙarin shawarwari.
Duk da ya nuna fahimtar takaicin da matasan ke ciki, ya roƙi gwamnati da ta hanzarta ɗaukar mataki domin daƙile abin da ya ce na iya “rikiɗewa zuwa barazana mai girma.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakkwato Shagari Ƙaramar hukumar Shagari yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria