Aminiya:
2025-09-17@21:49:33 GMT

Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 60 a Neja

Published: 4th, September 2025 GMT

Adadin mutanen da suka rasu a hatsarin jirgin ruwa da ya auku a yankin Malale, da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, ya kai 60.

Jirgin ruwan, wanda ya ɗauko kusan mutum 90, ya tashi daga Tugan Sule a gundumar Shagunu, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Dugga.

‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’ Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda

Mutanen da ke cikin sun tafi yin gaisuwar ta’aziyya ne, lokacin da hatsarin ya auku a ranar Talata, 2 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 11:30 na safe.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), ta ce hatsarin ya faru ne akamakon dukan wani itace da ke cikin ruwa.

Da farko, an gano gawarwakin mutum 29, sannan aka ceto mutum 50, yayin da mutum biyu suka ɓace.

Sai dai daga baya, shugaban Ƙaramar Hukumar Borgu, Abdullahi Baba Ara, ya tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasu ya ƙaru zuwa 60,

Hakazalika, ya ce ƙarin wasu mutum 10 na cikin mawuyacin hali, yayin da har yanzu ake neman wasu.

Dagacin yankin Shagunu, Sa’adu Inuwa Muhammad, ya ce ya je wajen bayan aukuwar hatsarin, inda ya tabbatar da cewa jirgin ya ɗauki mutane sama da 100, waɗanda mafi yawansu mata da yara ne.

Ya ce an gano gawarwakin mutum 31, kuma an binne huɗu daga cikinsu a ranar Talata.

A halin yanzu dai, ana ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda suka ɓace.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gawarwaki Hatsarin Jirgin Ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi

An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.

Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.

Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara