Dalilin da Najeriya ba ta jin tsoron matakan Trump — Tinubu
Published: 3rd, September 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu, ya ce kuɗaɗen da Najeriya ke samu daga hanyoyin da ba na man fetur ba sun isa wajen daƙile tasirin manufofin tattalin arziƙin shugaban Amurka, Donald Trump.
Trump, ya sanya sabbin dokoki, ciki har da haraji masu tsauri, wanda suka jawo suka daga sassa daban-daban na duniya.
Boko Haram ba kiristoci kaɗai suke kashewa a Arewa Maso Gabas — Ndume Kotu ta ɗaure wani mutum kan kashe saurayin ’yarsa a EkitiYayin da yake karɓar tawagar ‘The Buhari Organisation’ ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Almakura, a fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya ce Najeriya ta riga ta cimma burin samun kuɗaɗenta na shekarar 2024 tun daga watan Agusta.
“Mun riga mun cimma burin samun kuɗin shiga na wannan shekara tun a watan Agusta.
“Kuɗaɗen da ba na man fetur ba ne, ba ma jin tsoron abin da Trump yake yi a can,” in ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta daidaita tattalin arzikin ƙasa tare da rage dogaro da man fetur, don haka matsin lamba daga waje ba zai hana ci gaba da samum kuɗaɗen ƙasar ba.
Trump ya sha kiran ƙungiyar OPEC da ta ƙara fitar da adadin mai domin rage farashinsa a duniya.
A watan Yuli, OPEC da abokan haɗin gwiwarta sun amince da ƙara samar da ganga dubu 548 a kowace rana daga watan Agusta.
A watan Afrilu kuma, Trump ya sanya wa ƙasadhe haraji, ciki har da kaso 14 cikin 100 a kan kayayyakin da ake shigo da su daga Najeriya.
Bayan haka ya sanya hannu kan dokar dakatar da rangwamen haraji ga ƙasashe a ƙarƙashin dokar gaggawa ta tattalin arziƙin Amurka.
A shekarar 2023, Najeriya ta fitar da kaya zuwa Amurka da suka kai dala biliyan 6.29.
Daga Cikinsu akwai man fetur mai na dala biliyan 4.73, gas dala miliyan 920, da takin zamani dala miliyan 167.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tattalin Arziƙi
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.