2027: ’Yan Najeriya suna fama da yunwa, sun san abin da za su yi — Kwankwaso
Published: 30th, August 2025 GMT
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci.
“Mutanen wannan kasa sun yanke shawara kan abin da za su yi a 2027. Shi ya sa muke farin ciki da kanmu—saboda muna tare da jama’a. Kuma jama’a sun san muna tare da su. Ba mu gamsu da abubuwa da dama ba da suke faruwa a faɗin kasar nan, musamman batun talauci.
“Talauci ya mamaye ƙasar nan, musamman a wannan yanki (arewa). Talauci ne mai tsanani. Al’ummomi da dama ba za su iya zuwa gona ba. Wasu ba za su iya zuwa kasuwa ba. Wasu ma ba za su iya komawa gidajensu ba.”
Kwankwaso ya gargaɗi mambobin NNPP da kada su bari sauya sheƙa da tattaunawar kawance tsakanin ’yan siyasa su ɗauke hankalinsu.
“Bari in tunatar da mu: kada mu bari sauya sheƙa da jita-jita su ɗauke mana hankali.
Wasu mutane na sauya jam’iyya cikin sauki, suna tunanin sun san komai—alhali ba su fahimta sosai ba. Idan suna son sanin gaskiya, sai su zo su tambaye mu,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya Kwankwaso Zaɓe ba za su iya
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya.
Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDPA lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu.
Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama sun ƙaryata jita-jitar.
A ranar Juma’a, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewar masu tsattsauran ra’ayi suna yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya .
Ya umarci ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar, Tom Cole, su binciki lamarin, sannan su gabatar masa da rahoto.
Shugaban ya ƙara da cewa ƙasarsa ba za ta zuba ido yayin da irin wannan “ta’addanci” ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe ba.
Ya lashi takobin cewar Amurka za ta ci gaba da kare Kiristoci a duniya baki ɗaya.
Bayan wannan furuci, wasu sun zargi Trump da amfani da matsalar tsaron Najeriya don samun goyon bayan siyasa.
Har yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta yi martani a kan lamarin ba, amma jami’an gwamnati a baya sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar suna da nasaba da ayyukan ta’addanci, fashi, da rikicin ƙabilanci, ba addini ba.
Kalmar “Ƙasa Mai Matsala Ta Musamman” na nufin ƙasashen da Amurka ke ganin suna take haƙƙin ’yancin addini, kuma hakan na iya sa wa ta ƙaƙaba wa Najeriya takunkumai.
Idan ba a manta Najeriya ta fara shiga jerin irin waɗanda ƙasashe tun a shekarar 2020.