Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Darakta-Janar Na Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya
Published: 1st, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho.
A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan sabon ci gaban da aka samu a shawarwarin nukiliyar da kuma dage takunkumin. Sun kuma tattauna rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan Iran.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da yadda Iran ke ci gaba da ba da hadin kai ga hukumar ta IAEA, da aiwatar da dukkan ayyukan nukiliyar kasar Iran karkashin kulawar hukumar IAEA, da kuma cikin tsarin yarjejeniyar kariya, da rashin karkata ayyukan nukiliya da kayayyaki, ministan harkokin wajen na Iran ya yi kira ga babban darektan hukumar ta IAEA da ya fayyace gaskiyar lamarin ta hanyar da za ta hana wasu bangarori yin amfani da wannan cibiya ta kasa da kasa wajen cimma manufofinsu na siyasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya baki daya.
Guo Jiakun, ya jaddada muhimmancin taron, kasancewar ya zo a gabar da harkokin cudanyar kasa da kasa ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, da ma karuwar daukar matakan kashin kai daga bangare guda, da kariyar cinikayya.
Ya ce, hadin gwiwar sassan biyu, ya haifar da manyan nasarori a baya, wanda hakan ya bunkasa ci gaba da daukakarsu, tare da samar da tarin alfanu ga jama’arsu da yawanta ya kai biliyan biyu, kana ya samar da babbar gudummawa ga raya zaman lafiya, da ci gaban duniya baki daya. Kazalika, hadin gwiwar sassan biyu ya zamo misali na hadin gwiwar cimma moriyar juna, a sabon zamani na dunkulewar tattalin arzikin duniya.
Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar Sin ta yin aiki tare da EU, wajen cimma nasarar taron, matakin da zai aike da kyakkyawan sako ga duniya, game da aniyarsu ta hada karfi da karfe, wajen kafa hadin gwiwa mai karfin gaske, da daga martabar cudanyar mabambantan sassa, da bude kofa da aiwatar da hadin gwiwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp