Gobara ta ƙone gidaje sama da 100 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno
Published: 21st, April 2025 GMT
Wata gobara ta ƙone gidajen wuccin gadi sama da 100 ma ’yan gudun hijira a sansanin ’yan gudun hijira na hukumar ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno.
Shaidu sun ce ba a samu asarar rai ba a gobarar da ta tashi da misalin karfe 10.40 na safe na ranar Alhamis da ta gabata, kuma cikin sauri ta bazu a unguwar, inda ta ƙona kayan abinci, da sauran kadarori masu ɗimbin yawa.
Majiyar da ke sansanin ta bayyana cewar an tura jami’an agaji zuwa wurin domin kula da jama’a da kuma hana sace-sacen kayayyakin jama’a da suka rage, yayin da jami’an kashe gobara tare da mazauna sansanin suka yi bakin ƙoƙarinsu wajen kashe wutar.
Tashin gobarar dai ba shi ne karo na farko ba a wannan sansanin, domin ko da a kwanakin baya ma an samu makamancin hakan, lamarin ya sa jama’a ke zargin akwai sakaci daga wasu mazauna wannan sansanin.
Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — HakeemDon haka suka jadadda buƙatar a riƙa yin hattara don kauce wa ci gaba da faruwar irin haka nan gaba, kasancewar yanayin bazara mai dauke da iska ne ke ƙara ƙaratowa a wannan yanki, wanda hakan kan haifar da barazanar yawaitar tashin gobara a lokacin bazara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
Harin Ta’addanci A Wani Coci Ya Lashe Rayukan Mutane Fiye Da 21 A Gabashin Kongo
Fiye da mutane 21 ne suka mutu a wani harin ta’addanci da aka kai kan wani coci a gabashin Kongo
Rahotonni sun tabbatar da cewa; Sama da mutane 21 ne aka kashe a wani hari da mayakan ‘yan tawayen kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) suka kai kan wani cocin Katolika da ke gabashin Kongo, wanda ya hada da kona gidaje da shaguna a yankin.
A ranar Lahadin da ta gabata ne mayakan da suke da alaka da kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) da ke samun goyon bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS suka kaddamar da harin ta’addanci kan wata majami’ar Katolika a gabashin Kongo.
“Sama da mutane 21 ne aka kashe a ciki da wajen cocin,” Dieudonné Duranthabo, wani jami’in kungiyoyin farar hula a Komanda, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa: “Sun gano akalla gawarwakin mutane uku da suka kone, sannan an kona gidaje da dama.”
Harin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na safiyar Lahadi a cikin wani cocin Katolika da ke yankin Komanda a gabashin Kongo. An kuma kona gidaje da shaguna da dama.