Axios: Makomar Tsarin Jarin Hujja A Duniya Tana Girgiza
Published: 12th, April 2025 GMT
Kafar watsa labaru ta ” Axio ta Amurka ta watsa wani rahoto da yake nuni da cewa, an sami rashin yarda da juna a tsakanin masu zuba hannun jari na kasa da kasa da kuma Amurka.
Kafar watsa labaran ta buga a shafinta na “Internet” cewa; Rashin tabbaci da yake faruwa a halin yanzu a cikin kasuwanni yana tsoratar da masu zuba hannun jari a duniya.
Rahoton ya kuma ambaci girgizar da Dalar Amurka take yi, da kuma muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka.
Kafar watsa labarun ta ce, a baya muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka, wadanda kuma su ne ke bai wa Dalar Amurka kariya, sun kasance masu karfafa gwiwar masu zuba hannun jari, amma daga makon da ya shude an sami rashin aminci.
Abinda ya faru a makon da ya shude kamar yadda kafar watsa labarun ta ambata yana a matsayin karaurawar hatsari da aka kada, a tsakanin wadanda su ka yi Imani da tsarin kudade da Amurka take jagoranta, tun bayan kawo karshen yakin duniya da biyu.
Haka nan kuma ta yi ishara da cewa a lokacin da aka sami matsalar tattalin arziki a duniya a 2008, da kuma bullar cutar corona a 2020, Dalar Amurka ta rika habaka da tashi sama,amma yanzu akasin haka ne yake faruwa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Za Ta Yi Nazarin Sabuwar Gayyatar Da Amurka Ta Yi Mata Na Sabuwar Tattaunawa
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa, tana nazarin sabuwar gayyatar da Amurka ta yi mana na komawa teburin tattaunawa.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto wata majiya mai karfi tana cewa, bayan da Amurka ta kasa dakatar da Shirin kasar na makamashin Nukiliya, ta aiko ma ta da takardar gayyata domin yin zama da ita akan teburin tattaunawa.
Majiyar ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fada wa kamfanin dillancin labrun “Mehr” cewa, Amurka ta aiko da sakwanni ta hanyar ‘yan aike na kasashe masu yawa.”
Ma’aikatar harkokin wajen ta Jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin nazari akan hakikanin abinda Amurkan take so, da kuma yadda tattaunawar za ta kasance wacce za ta zama ta dage takunkumai, da kuma darajar uranium din da Iran za ta tace, sannan kuma da biyanta… na barnar da aka yi mata sanadiyyar kallafaffen yaki.
Tun da dari, Amurka ta yi kokarin nuna cewa Iran ce ta bukaci ayi tatttaunawar, lamarin da Jamhuriyar musulunci ta Iran ta kore.
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Akarci, ya sha bayyana cewa, duk wata tattaunawa idan har za a yi ta, to za ya kasance ne akan manufar kare maslahar jamhuriyar musulunci ta Iran. Batun ci gaba da tace nadarin uranium kuwa, wani abu wanda Iran ba za ta taba ja da baya a kansa ba.