Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand
Published: 28th, March 2025 GMT
Kimanin mutum 150 ne suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wata mummunar girgizar ƙasa daban-daban da suka auku a ƙasashen Myanmar da Thailand.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa girgizar ƙasar wadda ta auku a wannan Juma’ar ta jikkata ɗaruruwan mutane a yayin da baraguzai suka danne gommai.
Hukumar binciken yanayin ƙasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa an fuskanci wata mummunar girgizar kasa har kashi biyu masu ƙarfin awo 7.7 da 6.4 a Myanmar, tare kuma da wata girgizar ƙasar mai karfi da ta yi ɓarna a kasar Thailand wacce ta shafi wasu wurare a yankin.
Girgizar ƙasa ta farko ta afku ne a wani wuri mai nisan kilomita 16 a arewa maso yammacin birnin Sagaing wacce ta mamayi aƙalla kilomita 10 da misalin ƙarfe 12:50 na daren ƙasar ranar Juma’a, a cewar hukumar binciken yanayin ƙasar ta Amurka USGS.
Gwamnatin ƙasar da za ta gudanar da bincike kan lamarin cikin gaggawa tare da fara ayyukan ceto da kuma samar da kayayyakin agajin jin kai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Telegram.
A cewar wasu shaidu biyu daga garin Taungnoo da ke yankin Bago da suka zanta da kamfanin dillancin labaru na Reuters, aƙalla mutane uku ne suka mutu bayan wani ɓangare na wani masallaci ya rufta.
Girgizar ƙasar ta yi kaca kaca da cibiyar kasuwancin Bangkok haɗi da tituna da gadoji da kuma wani dogon gini mai hawa 30 da ko kammala shi ba a yi ba.
Tuni dai Firaministan Thailand, Paetongtarn Shinawatra ya ayyana dokar ta ɓaci a Bangkok.
Haka kuma, sojojin da ke mulki a Myanmar sun sanar da ayyana dokar ta ɓaci a babban birnin da kuma birni na biyu mafi girma a ƙasar da wasu jihohi shida.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Girgizar ƙasa Myanmar girgizar ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya
Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi.
Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a ChinaUwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu.
Ana iya tuna cewa, tun a daren ranar 13 ga watan Yuni zuwa wayewar gari 14 ga watan ne aka kashe fiye da mutum 100 a ƙauyen Yelwata, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar.
Jihar Benuwe dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, musamman rikicin manoma da makiyaya da kuma na ƙabilanci, wanda ke sanadiyyar salwantar rayuka da dama.