Dokar Ta-ɓaci A Ribas: Gwamnonin PDP Sun Ƙalubalanci Hukuncin Tinubu A Kotun Ƙoli
Published: 24th, March 2025 GMT
A cewar takardun kotun, gwamnonin suna neman a bayyana cewa, hukuncin da shugaban kasa ya zartar ya saɓa wa sashe na 1 (2), 5 (2), da 305 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Sun kuma kara da cewa, shugaban kasa ba shi da wani iko ko kadan na dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da mataimakin gwamnan wata jiha a tarayyar Nijeriya bisa fakewa da dokar ta-ɓaci.
Gwamnonin kuma suna kalubalantar amincewa da dokar ta-ɓaci da majalisar dokokin kasar ta yi, suna masu cewa, yin amfani da kuri’a jin ra’ayi ta baki ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar, saboda dokar ta ce, dole sai an samu mafi rinjayen kuri’a biyu cikin uku na dukkan ‘yan majalisar.
A cikin jawabin da suka gabatar wa kotun, masu shigar da kara sun kara da cewa, dokar ta-ɓacin ba ta cika ka’idojin tsarin mulki da sashi na 305 ya gindaya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027
’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa.
Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa.
An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APCDuk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF).
Tsarin siyasar kasar nan ya sa dole ne kowane dan takara ya zaga kowane lungu da sako na kasar nan kafin ya iya samun kuri’un da yake bukata don ya samu nasara.
Masana harkokin siyasa na ganin kalaman na Hakeem da ire-irensa na kan hanya, amma idan aka cika sharadi daya kacal.
“Rawar da Arewa za ta taka a zaben 2027 ba ta da wani bambanci da wadda ta saba takawa, kuma hakan zai yiwu ne kawai idan ta ci gaba da zama dunkulalliya, mai alkibla daya,” in ji Malam Kabiru Sufi na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Jihar Kano.
Idan dai aka cika wannan sharaɗi, to duk wani ɗan takara ko datn Arewa ne sai ya nemi goyon bayan ‘yan Arewacin kafin ya yi nasara.
Ya bayar da misalin haɗakar da jam’iyyun siyasa suka yi kafin babban zaben 2015, inda jam’iyyun CPC da ACN da ANPP da wani ɓangare na APGA da wasu gwamnonin PDP suka kafa APC mai mulkin.
“Idan aka samu rarrabuwar kai kuma, to Arewa za ta zama kamar wani taron tsintsiya ne ba shara. Babu rawar da za ta taka”, in ji Sufi.
Malam Sufi ya ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ‘yan Arewa ke jin cewa sai da su za a ci zaɓe shi ne yawan al’umma.
A zaɓen 2023 da ya gabata, sahihan kuri’un da ‘yan takara huɗun farko suka samu a jihohin Arewa sun zarta na Kudu da kusan miliyan biyar.
Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC da Alhaji Atiku Abubakar na PDP da Mista Peter Obi na LP da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP, sun samu jimillar kuri’u miliyan 13,716,667 a jihohin Arewa. Sun samu jimillar 9,020,741 a jihohin Kudu.
Bola Tinubu da ya lashe zaɓen ya samu jimillar 5,346,404 a jihohin Arewa, yayin da ya samu 3,206,969 a jihohin Kudu.
“In dai Arewa ta sake yin abin da ta yi a 2015, tabbas dole ne sai an nemi goyon bayanta, amma idan aka samu rarrabuwar kai za ta zama mushen gizaka – ana yi mata kallon za ta iya, amma kuma ba za ta iya ba,” kamar yadda Sufi ya bayyana.
Shin ko Arewan za ta iya magana da murya ɗaya?
Farfesa Abubakar Ma’azu, masanin harkokin siyasa ne a Jami’ar Maiduguri yana ganin za ta iya yin hakan.
“Idan aka duba, wadanda suka kafa Jam’iyyar APC sun fara yunkurin ne tun a 2011.
“Abin bai yiwu ba, amma suka shiga zabe a haka kuma suka sha kaye. Sai daga baya suka gano kuskurensu kuma suka yi nasara a 2015 bayan cim ma hadakar,” in ji shi.
Ko zai yiwu a iya cin zabe da kuri’un Arewa kawai? Kamar yadda ’yan Arewa ke tutiya da cewa sai da goyon bayansu za a ci zaɓen Shugaban ƙasa, haka ma sai dan takara ya samu kuri’u a Kudanci kafin ya yi nasara.
Kafin hadakar APC ta kayar da PDP mai mulki, tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi takara har sau uku ba tare da nasara ba, har sai bayan da ya samu goyon bayan wasu jam’iyyu daga Kudu.
Buhari ya fara yin takara ce a Jam’iyyar APP a 2003, ya sake yi a 2007 a jam’iyyar bayan ta zama ANPP, sai a 2011 kuma ya yi a CPC.
Ana ganin shigar Jam’iyyar ACN ta Bola Tinubu cikin haɗakar APC ce ƙashin bayan nasarar Buhari, saboda yadda take da tasiri a jihohin Kudu maso Yamma da Yarabawa ke da rinjaye.
Kazalika, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya samu kuri’u mafiya yawa a Arewaci (4,834,767) sama da kudanci (1,751,047), amma duk da haka bai yi nasara ba.
“Dole ne sai ɗan takara ya karaɗe ƙasa baki ɗaya, ya samu kuri’u a Kudu da Arewa kafin ya samu kowace irin nasara,” in ji Farfesa Ma’azu.