Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi
Published: 14th, March 2025 GMT
Jihohin Sakkwato da Kebbi na fuskantar ƙalubale sakamakon cutar sanƙarau da ta ɓulla a jihohin, inda rahotanni suka tabbatar da cewa cutar ta kashe aƙalla mutum 50, yayin da sama da mutum 200 suka kamu da cutar.
A Jihar Kebbi, ƙananan hukumomin Aliero, Jega, da Gwandu ne suka fi fuskantar matsalar, inda cutar ta fara yaɗuwa kafin a ɗauki matakan gaggawa.
A Jihar Sakkwato kuwa, ƙaramar hukumar Tambuwal ce ta fi fama da cutar, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka sanar da ɗaukar matakan daƙile cutar domin hana ta yaɗuwa zuwa sauran yankunan.
Dalilin Yawaitar CutarMasana kiwon lafiya sun danganta yawaitar cutar da tsananin zafi da ake fama da shi a yankin Arewa Maso Yamma, wanda ke haifar da bushewar iska da kuma saurin bazuwar ƙwayoyin cutar sanƙarau.
Rashin isassun matakan rigakafi da kuma ƙarancin kula da lafiyar jama’a a wasu yankuna na daga cikin dalilan da suka sa cutar ke bazuwa cikin sauri.
Matakan da Aka ƊaukaGwamnatocin jihohin Kebbi da Sakkwato sun ce sun fara ɗaukar matakan gaggawa, inda ake gudanar da allurar rigakafi domin daƙile cutar, musamman ga ƙananan yara da tsofaffi, waɗanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.
Hakazalika, an ƙara wayar da kan jama’a kan alamomin cutar da matakan kariya, domin daƙile yaɗuwarta a cikin al’umma.
Abubuwan da Jama’a Ke BuƙataDuk da matakan da hukumomi ke ɗauka, har yanzu jama’a na buƙatar ƙarin taimako, musamman wajen samun ingantattun cibiyoyin lafiya da isassun magunguna.
Akwai buƙatar gaggauta aika ƙarin kayayyakin kula da lafiya da ƙarfafa rigakafi domin hana aukuwar cutar a nan gaba.
A halin yanzu, hukumomin lafiya na ci gaba da sa ido kan lamarin, tare da jan hankalin jama’a da su guje wa cunkoso da kuma kai marasa lafiya asibiti da wuri idan suka fara ganin alamomin cutar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: lafiya Sakkwato Sanƙarau
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp