Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan yakin sa Israel Kantz zuwa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram a yankin yamma da kogin Jordan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin HKI sun kutsa cikin sansanonin yan gudun hijira na Palasdinawa a Tulkaram da kuma Jenin tana rusa gidajen falasdinawa tana kuma kora da kuma kashe wadanda suka samu a cikin gidajen nasu.

A wani labarin kuma kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta yi allawadai da rushe-rushen gidajen da gwamnatin HKI take yi a yankin yamma da kogin Jordan.  Kungiyar ta yi kira da kasashen duniya su sa baki don dakatar da kashe Falasdinawa da kuma korarsu daga gidjensu da kuma rusa wasu gidajen.

Kungiyar ta kara da cewa kutsawa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram ci gaba da zaluncin da takewa Falasdinawa a tsawon shekaru 76  da suka gabata. Har’ila yau ministan harkokin wajen Falasdinawa ya yi tir da Natanyahu da kuma Kanzt kan abinda suke aikatawa a garin Tulkaram. Inda suke son korar faladinawa kimani 40000 da suke rayuwa a sansanin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.

Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.

Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Ya ce an tsara wannan asusu  ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.

Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.

Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin  ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.

Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a  wuraren.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa