Gwamnan Zamfara Ya Mika Sansanin Karbar Tubabbun ‘Yan Bindiga Ga Sojan Nijeriya
Published: 15th, February 2025 GMT
Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma.
Gwamnan a wajen bikin mika ragamar sansanin da aka samar, ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da bin sawun ‘yan bindiga har sai an fatattake su da ruguza su da murkushe su.
Dokta Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimakawa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ta’addanci da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma.
A cewarsa, shirin ya yi koyi ne da shirin ‘Operation Safe Corridor’ a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar kawar da tsaffin mayakan na Boko Haram tare da dawo da su cikin al’umma.
“Amma ga wadanda suka yi niyyar mika makamansu ba tare da wani sharadi ba suna da ‘yancin yin hakan.
Da yake jaddada cewa, kafa hedkwatar tsaro ta Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma zai bada damar kwance damara, da wargazawa, da kuma cudanya da tubabbun ‘yan fashi a cikin al’umma.
Ya kuma mika godiyarsa ga babban hafsan hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa bisa ganin jihar Zamfara ta cancanci karbar bakuncin rundunar Operation Safe Corridor na 3 a kasar nan.
“Ina kuma so in gode wa shugaban kwamitin aiwatar da ayyukan Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma, Manjo Janar EV Onumajoro, wanda kuma shi ne babban hafsan tsaro na hedikwatar tsaron Najeriya, da tawagarsa saboda ganin Zamfara ta dace da kafa hedkwatar wannan muhimmin sashi.
Tun da farko, Manjo Janar Onumajuru, wanda ya wakilci babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, ya yabawa Gwamna Lawal bisa goyon bayan da yake baiwa sojoji a yakin da ake da ‘yan bindiga a Zamfara.
Bayan karbar ragamar wannan sansanin, za mu ci gaba da hada kai da mai girma Gwamna da al’ummar Zamfara, wadanda su ne masu ruwa da tsaki a wannan aiki, domin tabbatar da hadin kai don kwalliya ta biyan kudin sabulu.
AMINU DALHATU.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Tsaro Zamfara Arewa maso Yamma
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin tsaro: Gwamnan AbdulRahman Ya Gana Da Sarakuna Masu Daraja Ta Daya A Jihar Kwara
“Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro.
“Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.”
Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.
Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp