Aminiya:
2025-11-02@16:59:22 GMT

N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi

Published: 12th, February 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja.

Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja.

Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum

“Ni mazaunin Abuja ne.

Makonni biyu da suka wuce, wani mutum ya aike ni domin karɓo masa harsasai a Jos zuwa Abuja.

“Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda ake zargi, ya ce an kama su ne bayan samun rahoton sirri kan ayyukansu.

“Mun kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanan sirri.

“Rundunar na ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za a miƙa su zuwa kotu domin fuskantar hukunci.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Harsasai Masu Safarar Makamai matsalar matsalar tsaro Safara

এছাড়াও পড়ুন:

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma  October 30, 2025 Daga Birnin Sin Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC October 30, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara