A Shirye Nake Na Tattauna Da Shugaban Rasha – Zelensky
Published: 9th, February 2025 GMT
Shugaban Ukraine, Bolodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar kasarsa, wajibi ne a sanya kasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki.
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Bolodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Bladimir Putin, idan har hakan ne zai kawo karshen yakin da suka kwashe kusan shekara uku suna gwabzawa.
Sai dai shugaba Zelensky ya sake nanata bukatarsa ta karin makamai domin ci gaba da samun nasara kan Rashar.
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Afganistan Sun Tattauna Dangane Da Komawar Afganawa Gida
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Afganistan Amir Khan Muttaki a yau Lahadi inda bangarorin biyu suka tattauna dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al-amuran yankin wadanda suka hada da batun gaza da kuma halin da take ciki.
Kamfanin dillancin labaran Tasnima na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana cewa kasar Iran ta kira taron gaggabawa na kungiyar OIC ta kasashen musulmi don tattauna wannan batun.
A nashi bangaren muttaki ya bukaci gwamnatin kasar Iran ta maida yan kasar Afganistan wadanda suke zauna a kasar zuwa gida tare da mutuntasu. Kafin haka dai a lokacin yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da Iran jami’an tsaro a kasar Iran sun kama yan Afganistan da dama suna aikiwa HKI don dan kudade da suke samu