Firaministan Sin Ya Tattauna Da Baki Kwararru Dake Kasar
Published: 28th, January 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gudanar da taron tattaunawa da wakilan baki kwararru wadanda ke aiki a kasar da wadanda suka samu lambar yabo ta Abota ta Gwamnatin Sin.
Yayin taron wanda ya gudana jiya Lahadi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, Li Qiang ya kuma mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar Sinawa da fatan alheri ga bakin kwararru, ya kuma godewa goyon baya da kulawar da suka dade suna bayarwa ga kokarin Sin na zamanantar da kanta.
Kwararrun wadanda suka hada da ’yan kasashen Birtaniya da Poland da Mali da Romania da Jamus da Pakistan, sun gabatar da jawabai kan maudu’i daban daban, kamar na kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki da musayar al’adu da kuma musaya tsakanin jama’a da raya kwararru da ma cudanyar kasa da kasa.
Mataimakin firaminista Ding Xuexiang ma ya halarci taron. (Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA