2025-11-03@21:09:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 211

«a gidajen Yarin»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Bangarori mabanbanta na kasar Lebanon suna mayarwa da ‘yar sakon Amurka martani saboda tsoma baki da ta yi a kan yadda za a kafa gwamnati a kasar. Morgan Ortagus wacce ta gana da jami’an kasar Lebanon ta bayyana cewa, bai kamata a kafa gwamnati a kasar ta wakilan kungiyar Hizbullah a ciki ba. Kungiyar malaman addinin musulunci ta fitar da bayani da a ciki ta ce; “Furucin mataimakin manzon Amurka a gabas ta tsakiya, Morgan Ortagus wacce ‘yar sahayoniya ce,tsoma baki ne a harkokin cikin gidan Lebanon wanda ya tsallake ka’idojin aikin diplomasiyya.” Ita ma gwamnatin kasar ta Lebanon ta fitar da bayani tana mai cewa abinda Ortugas din ta furta, ra’ayinta ne, bai shafi gwamnatin Lebanon ba. Shi kuwa...
    Kotu ta ba da umarnin tsare tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje. Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu ta Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ne bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf kan zargin almundahana. A safiyar Litinin ne EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf, inda bayan an karanta masa tuhumar da ake masa ya musanta aikata laifin. Daga nan ne lauyansa O.I Habeeb, ya buƙaci umarnin kotu na tsare shi a ofisoshin EFCC zuwa lokacin zai shigar da buƙatar beli. Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe...
    Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon. “Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa ido da masu shiga tsakani don dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” in ji shi a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin dazu. Sheik Qasem ya ce kungiyar Hizbullah na taka-tsan-tsan don bai wa gwamnatin Lebanon damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Faransa da Amurka suka shiga tsakani...
    A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...
    Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio. Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin. Wani Ɗan Pakistan Ya Kashe ‘Yarsa Kan Ɗora Bidiyon Kanta A TikTok Hisbah Ta Kama Matashi Da Matashiya Kan Yin Aure Saɓanin Dokokin Musulunci A Kano Yarjejeniyar tsagaita wutar an ƙulla ta ne don bayar da damar musayar fursunonin da Hamas ke riƙe da su da kuma waɗanda ke tsare a Isra’ila. Sai dai wannan matakin ba zato ba tsammani ya haifar da rashin tabbas kan ci...
    Baloch ya ce “Na amince da laifin kashe ‘yata, saboda abinda take yi, zubar da mutuncin dangina ne.”   ‘Yansandan dai tuni suka sanya shari’ar cikin wani lamari na ‘kisan mutuntaka’, wacce al’ada ce ga ‘yan uwa, musamman maza, ke kashe mata, wanda suke imanin cewa, sun kawo “abin kunya” ga danginsu.
    Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
    An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan. Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon. “Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,”...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare kasar Lebanon daga ha’incin makiya ba wai kawai tawada ne a takarda ba, don haka sun daurawa kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen da suke daukar nauyin yarjejeniyar da aka cimma alhakin take hakki da laifuffukan makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta mata ficewa gaba daya daga yankin Lebanon. ‎Tun daga shekara ta 2000 har zuwa yau, lamarin ya ci gaba da maimaita kansa, domin al’ummar...
    Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas. A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza. Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke...
    Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...