‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido
Published: 5th, September 2025 GMT
“Tun lokacin Buhari har zuwa yanzu lokacin Tinubu, ‘yan Nijeriya na cikin wahala. Talauci tana nan a ko’ina, matasa ba su da aikin yi, kuma tattalin arziki yana lalacewa. Su na cewa suna yaki don Nijeriya, amma a zahirin gaskiya, suna yaki ne kawai don kansu da aljihunsu.
“Na kasance cikin gwagwarmaya tun daga shekarun 1970.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da fitina a Najeriya.
Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’uA ranar Juma’a ne, Trump ya wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta cewar Kiristanci yana cikin hatasri a Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewa ’yan ta’adda sun kashe dubban Kiristoci, amma ya ce Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen “ceto Kiristoci” a Najeriya da wasu ƙasashe.
Shehu Sani, ya mayar da martani da cewa wannan magana ba gaskiya ba ce, domin matsalar tsaro a Najeriya ba ta da nasaba da addini.
Ya ce Musulmai da Kiristoci dukkaninsu suna fuskantar hare-haren’yan ta’adda da garkuwa da su.
“Wannan zargi ƙarya ne. ’Yan ta’adda da ’yan bindiga a Najeriya suna kashe mutane ba tare da la’akari da addininsu ba. Wannan abin na faruwa tun kusan shekaru 15 da suka wuce,” in ji shi.
Sani, ya ƙara da cewa, saboda yawan Musulmai da Kiristoci a Najeriya, ba zai yiwu addini ɗaya ya zalunci ɗaya ba.
“Idan aka duba yadda Musulmai da Kiristoci suke kusan daidai a Najeriya, ba zai yiwu ɗaya ya zalunci ɗaya ba. Najeriya kamar zaki da damisa ce, dukkanin ɓangarorin suna da ƙarfi,” in ji shi.
Ya zargi waɗanda suka zuga Trump da amfani da rikice-rikicen cikin gida na Najeriya.
“Trump ya samu bayanan ƙarya daga mutanen da ke son raba Najeriya domin su ci moriya daga wannan,” in ji shi.
“Wannan makirci da aka yi wa ƙasar nan ba zai yi nasara ba.”
Sani, ya roƙi ƙasashen duniya su taimaka wa Najeriya wajen yaƙar ta’addanci, maimakon yaɗa labaran ƙarya.
“Najeriya na buƙatar taimako da haɗin kai wajen shawo kan matsalar tsaro, kamar sauran ƙasashen da ke fama da ta’addanci,” a cewarsa.