Jami’in Siyasar Kungiyar Hamas Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Shugaban Amurka
Published: 4th, September 2025 GMT
Jami’in siyasar kungiyar Hamas ya mayar da martani ga shugaban kasar Amurka Trump cewa: Netanyahu yana son yaki mara iyaka ne
Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas Izzat al-Rishq ya fada a yammacin jiya Laraba, yayin da yake mayar da martani ga bukatar shugaban Amurka Donald Trump na sakin dukkan fursunonin Isra’ila, cewa “Hamas ta amince a ranar 18 ga watan Agusta kan shawarar masu shiga tsakani, wadda ta dogara ne kan shawarar Witkoff, kuma har yanzu Netanyahu bai bayyana matsayinsa ba.
A martanin da ya gabatar kan furucin Trump, al-Rishq ya tabbatar da cewa, kungiyar Hamas ta bayyana shirinta na cimma cikakkiyar yarjejeniya, inda za a saki dukkan fursunonin, a madadin adadin da aka amince na fursunonin Falasdinu da ke gidajen yarin Isra’ila, ta hanyar da za ta cimma tsagaita bude wuta da kuma janyewar sojojin mamayar Isra’ila daga Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa 79 A Yankin Zirin Gaza September 4, 2025 Araqchi: Iran ba ta fargabar tattaunawa kuma ba ta tsoron kare kanta idan aka kallafa mata yaki September 4, 2025 Najeriya ta ba da izinin binciken danyen mai a karkashin teku ga kamfanin TotalEnergies September 4, 2025 Yemen ta sanar da kai hare-hare biyu kan ‘Isra’ila’ September 4, 2025 Afirka ta Kudu ta aika da wakilai 30 zuwa IATF 2025 September 4, 2025 Ministan Najeriya ya bukaci Afirka da ta tsara makomar AI September 4, 2025 Bikin baje kolin Ciniki tsakanin kasashen Afirka (IATF) 2025 AFRICA24 September 4, 2025 Gharibabadi: Iran Ta Nuna Diflomasiyya A Taron Kungiyar Shanghai September 3, 2025 Baqaei: Babu Aminci Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA September 3, 2025 IRGC: Takunkumin Turai A Kan Iran Daukar Fansa Kan Juriyar Al’ummar Kasar September 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon.
A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.”
Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma.
Daga baya, karamar hukumar ta tabbatar da cewa Ibrahim Salameh, wanda ya kwana a cikin ginin, ya yi shahada bayan da sojojin mamaya suka harbe shi. Aoun ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa wani bangare ne na ayyukan “Isra’ila” kan fararen hula kuma ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan taron da kwamitin da ke sa ido kan yarjejeniyar dakatar da fadan ya gudanar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci