NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin Sambisa
Published: 4th, September 2025 GMT
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kashe ’yan ta’adda sama da 15 a wani harin jiragen yaƙi da aka kai dajin Sambisa, da ke Jihar Borno.
Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya ce an ƙaddamar da harin ne a ranar Laraba karkashin Operation Haɗin Kai.
Umar FK ya fice daga PDP zuwa APC da magoya bayansa a Gombe Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin KofaYa ce sun samu bayanan sirri da suka nuna cewa mayaƙan da ke da hannu a hare-haren a yankin Bitta sun ɓuya a wajen.
Ya ce hare-haren sun lalata maɓoyar ’yan ta’addan tare da raunata da dama da cikinsu.
Ejodame ya ƙara da cewa wannan ya nuna ƙwarewar NAF da kuma jajircewarta wajen tallafa wa sojojin ƙasa da kare rayukan ’yan Najeriya.
“Duk nasarar da ake samu tana ƙara kusantar da Najeriya wajen samun zaman lafiya ta hanyar rushe hanyar sadarwar ’yan ta’adda,” in ji shi.
Hakazalika, a farkon makon nan dakarun Operation Haɗin Kai tare da tallafin sojin sama sun kashe ’yan ta’adda 20 a Jihar Borno da Yobe.
Har ila yau, sun kama wasu da ke taimaka musu da kuma lalata wasu bama-bamai da suka samu a wajensu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Hallakawa Operation Haɗin Kai yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.