Firaministan Kasar Pakistan: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Hangen Nesa
Published: 1st, September 2025 GMT
Yayin da yake zantawa da ’yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Pakistan Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa, Xi Jinping shugaban kasa ne mai matukar hangen nesa.
A cewar firaministan, Xi Jinping, shugaban kasa ne wanda ke mayar da hankali sosai kan kyautata rayuwar jama’a, kuma a karkashin jagorancinsa, kasar Sin ta samu nasarar yaki da matsanancin talauci, al’amarin da ke bukatar matukar hangen nesa da babbar hikima.
Firaminista Shehbaz ya kara da cewa, ba sauya yanayin tattalin arzikin kasar Sin kawai shugaba Xi ya yi ba, har ma ya mayar da kasar zuwa matsayi na biyu a karfin tattalin arziki a duniya, kuma babbar kasa mai karfin soja. Ya ce abu mafi muhimmanci a nan shi ne, shugaba Xi ya dade yana dukufa kan taimaka wa sauran kasashe ta yadda za su mori nasarorin da kasar Sin ta samu, tare da kokarin inganta hadin-gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe, ta yadda kasashe masu karamin karfi su ma za su iya cin gajiya, kuma jama’arsu za su iya ficewa daga kangin talauci, da jin dadin nasarorin da aka samu wajen raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma
A nata bangare, Amurka za ta dage aiwatar da matakai bisa bincikenta karkashin sashe na 301 na dokar cinikayya ta 1974, wanda zai shafi sashen jiragen ruwa na Sin, da hidimomin sufurinsu, da na kirar jiragen ruwan na Sin da karin shekara daya. Sakamakon hakan, ita kuma Sin za ta dage aiwatar da matakan martani ga sashen Amurka a wannan fanni da shekara daya, da zarar Amurkan ta aiwatar da na ta matakan.
Kakakin ya ce “An Kai Ruwa Rana” kafin cimma wannan sakamako, kuma Sin na fatan ganin ta ci gaba da aiki tare da tsagin Amurka, ta yadda za su hada karfi wajen tabbatar da an aiwatar da sakamakon, da ingiza karin tabbaci, da daidaito cikin dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, da kuma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA