Wata hajiyar Najeriya daga Filato ta rasu a Makkah
Published: 3rd, June 2025 GMT
Wata hajiyar Najeriya daga Jihar Filato ta rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Hajiya Jamila Muhammad ta rasu ne a yayin da alhazai ke shirin fara gudanar da aikin Hajji gadan-gadan.
Sakataren Hukumar Kin Dadin Alhazai ta Jirage Filato, Daiyabu Dauda, ya sanar a ranar Litinin cewa Hajiya Jamila ta rasu ne a asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah, sakamakon tashin cutar suga.
Ya ce Amirul Hajj na jihar da wasu manyan jami’ai sun halarci jana’izar marigayiyar, kamar yadda Musulunci ta tanada.
Yadda magidanci ya kuɓuta bayan wata 7 a hannun ’yan bindiga NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Hajji ta bayan fage: Saudiyya ta hana mahajjata 269,000 shiga MakkaDa rayuwarta, yawan alhazan Najeriya da suka rasu a aikin Hajjin bana ya ƙaru zuwa mutum uku.
Kafin ita, Najeriya ta rsa alhazai biyu da suka hada da Hajiya Adizatu Dazumi daga Jihar Edo da kuma Alhaji Saleh Saleh daga Jihar Abiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Saudiyya ta rasu
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.