Tsaro: ‘Yansanda Sun Kulle Tashar Dadin Kowa Da Sauransu A Gombe
Published: 2nd, June 2025 GMT
Rundunar ‘yansanda a jihar Gombe ta umurci rufe duk wata tashar sauka ko daukar fasinjoji a cikin garin Gombe ciki har da fitacciyar tashar Dadin Kowa, inda ta ce, tashar Ibrahim Hassan Dan-Kwambo ce kadai halastacciya.
Bugu da kari, motocin haya da ke dauke da amintaccen launin kala na gwamnati a cikin garin Gombe ne kadai suke da izinin zirga-zirgar daukar fasinjoji a birnin.
Wannan umarni na kunshe ne acikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, a ranar Litinin, 2 ga watan Yunin 2025.
“An dauki wannan matakin ne daidai da kudurin gwamnati na maido da bin doka, inganta tsaro, da kuma tabbatar da lafiyar fasinjoji. An umurci dukkan masu sana’ar tuki na kasuwanci da su gudanar da dukkan ayyukan lodi da sauke kaya a tashar motoci ta Ibrahim Hassan Dan-kwambo kadai da ke babban birnin jihar.
“Duk wani wanda aka samu ya taka doka zai fuskanci tsauraran sakamako na shari’a, gami da kamawa, gurfanar da shi, da yuwuwar kama motarsa.” In Ji DSP Abdullahi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyen Katsina, Sun Jikkata Mutane 2, Sun Sace Wasu
“Sun jikkata mutane biyu tare da sace maza, mata da yara da dama.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp