Najeriya: An Bude Bincike Sojojin Da Suke Bayar Da Makamai Ga Kungiyoyi Masu Dauke Da Makamai
Published: 1st, June 2025 GMT
Mahukunta a tarayyar Najeriya sun sanar da kama wasu sojoji da ‘yan sanda 30 bisa tuhumarsu da sace makaman gwamnati da sayar da su ga kungiyoyi masu dauke da makamai, daga cikinsu har da kungiyoyin da suke ikirarin jihadi.
Sanarwar da rudnunar sojan kasar ta Najeriya ta fitar ta kunshi cewa; Farmakin da rundunar sojan kasar ta fara kai wa a cikin watan Ogusta na 2024 tana a matsayin mayar da martani ne akan satar makamai da alabarusai na gwamanti da ake yi, kuma ya zuwa yanzu bincike ya sa an kama sojoji 18 da kuma ‘yan sandan 15 sai kuma wasu fararen hula 8 da su ka hada da sarkin gargajiya daya.
Wannan sanarwar dai ta zo ne adaidai lokacin da kasar ta Najeriya take fuskantar kalubale mai girma ta fuskar tsaro, ta yadda a bayan nan kungiyoyin Bokoharam, da Iswap su ka dawo da hare-haren da suke kai wa musamman akan rundunar sojojin kasar.
Dama a baya wata cibiyar mai nazari da bincike akan yankunan da ake rikice-rikicen makamai a duniya mai matsuguni a Birtaniya, ta bayyana cewa; Kungiyoyin da suke ikirarin jihadi a yankin Sahel, suna samun kaso 20% na makamansu ne daga cikin kasashensu.
Baya ga matsalar masu ikirarin jihadi da ake fama da su da Najeriya, da akwai kuma ta barayin daji da suke sace mutane domin karbar kudin fansa, mafi yawancinsu a yankin Arewa maso yammacin kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.”
“Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!”
A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar Sin, tare da hada kai da kasar Sin da ma sauran baki ’yan kasuwa wajen kyautata tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp