Gobara Ta Ƙone Shaguna 3 Da Kayayyaki Masu Yawan Gaske A Ibadan
Published: 2nd, May 2025 GMT
Wuta ta tashi da safiyar yau Juma’a inda ta ƙone shaguna uku da wasu kayayyaki masu yawa a unguwar Sango da ke cikin babban birnin jihar Oyo, Ibadan. Manaja Janar na hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo, Akinyemi Akinyinka, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa wutar ta tashi a bayan wani gidan man da ke Sango.
Akinyinka ya ce an ba da rahoton faruwar gobarar da karfe 4:41 na safe ta wayar tarho, kuma ma’aikatan hukumar, ƙarƙashin jagorancin ACFS Adedeji (Mrs.), sun isa wurin nan da nan. “Lokacin da muka isa, mun gano cewa shaguna uku daga cikin goma na shagunan sun ƙone. Mun yi sauri mu kawar da wutar kuma mun hana ta yaɗuwa zuwa sauran shaguna,” in ji shi.
Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas Gobara Ta Tashi A Barikin Sojoji A Borno, Bama-bamai Sun FasheKo da yake ba a sami rahoton asarar rayuka ba, amma wutar ta lalata shaguna uku, da Firinji, da abubuwan sha. Akinyinka ya bayyana cewa wutar ta fara ne sakamakon wutar da ta fito daga firiji da aka sa a cikin shagon, wanda ya ƙona wasu abubuwa masu saurin kamawa kafin ya mamaye shagunan.
Ma’aikatan kashe gobara sun ceci wasu shaguna da kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gobara
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.
Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11.
Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu.
NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuA kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan