Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Published: 23rd, April 2025 GMT
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula
Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”.
Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris.
Rahoton ya yi nuni da wani tsari na cin zarafi da ake yi wa fararen hula, da suka hada da kashe-kashen gilla, azabtarwa, tilasta yin gudun hijira, da wawure dukiyoyi. Har ila yau, rahoton ya yi nuni da yadda dakarun gwamnati da kungiyoyin masu dauke da makamai suka shiga cikin wadannan laifuka, da kuma dogaro da shaidar iyalan wadanda abin ya shafa na tattara bayanan da aka hana binne mutane da kuma wulakanta fararen hula.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: fararen hula
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.