Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Siyasantar Da Batun Asalin Cutar COVID-19
Published: 23rd, April 2025 GMT
Guo Jiakun ya kara da cewa, kasar Sin ta kiyaye amfani da tsarin kimiyya da babu rufa-rufa a ciki mai baje komai a faifai, tare da nuna goyon baya da kuma shiga cikin kokarin da kasashen duniya ke yi na gano ainihin inda cutar ta samo asali.
Ya bukaci Amurka da ta daina siyasantar da lamarin, da amfani da batun gano asalin cutar a matsayin makami, kana ya nemi Washington ta guji yin kafar ungulu ga wasu kasashe, da dora wa wasu laifi, da yin watsi da tababar da ake ta nunawa a game da ayyukanta masu nasaba da cutar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing
Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing.
Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800.
Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun ci gaba cikin sauye-sauye”, da “amfani da sarrafa sabbin fasahohi”, da kuma “kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha da sauye-sauyen yanayin yaki”. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp